Showing 135001 words to 138000 words out of 196754 words
Chapter 46 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
amsa da mamaki a fuskarta
“Don Allah idan ma fushi tayi ki taya ni bata hakuri kafin naje, kuma ku ma ina baku hakuri matsala irin
wannan ba za a sake samu ba in sha Allahu.”
“Mu ai dama bamu yi fushi ba Abban Khalifa, duk lokacin da kuka daidaita mu bamu da wata damuwa.
Allah dai ya kiyaye gaba.”
“Amin, in Sha Allahu za mu daidaita har Jigawan ma zan je.”
Suka yi sallama Salim ya tuko suka koma gidan makoki. Haka ya daure cikin yanayi na damuwa sai bayan
isha’I sannan shi da yaran suka dauki Saudah da Zulaiha suka koma gida. Sai da ya huta ya gama abinda
yake yi sannan ya fito ya shiga falon Mommy. Baba karami ne da Ahmad a falo sai Auta da yake zaune a
dining table yana homework. Bayan sun yi masa sannu da zuwa suka zauna jimawa kadan ya dubi Baba
yace
“Baba kun gano Mommyn lafiya take ko?”
“Lafiya kalau take Abba, yanzu muka gama waya da ita ashe sun koma Jigawan ita da Anti Baraka.”
“Haka Antinku tace min da naje.”
“Eh ai yanzu muka gama waya da ita ma.”
Ya zaro wayarsa daga aljihun ya mikawa Baban yace
“Yauwa saka min lambar a nan nima na kirawo ta.”
Sai da aka saka masa lambar sannan yayi musu sallama ya fice don yaje ya kwanta.
Da yake Saudah sun gaji ita da yaran tun da suka ci abinci ta sa sukayi bacci sannan itama ta kwanta. Don
haka shi kadai ne a dakinsa, har sha biyun dare yana nan ya kasa bacci yana ta tunani. Ya kirawo ta ne ko
ya bari sai da safe, yana so yaje Jigawan gobe yana jin kunyar ya tafi ya bar su Aliko a wajen makokin
Baffa. Ko daya ma bai taba zaton Rabin za ta iya sake tafiya ba tare da ta tsaya sun hadu ba, Allah ya sa
dai ba Baraka ce take zuge masa Rabin ba. Zai ga yanda za ayi don kuwa babu wanda ya isa ya raba shi
da Rabi. Da yake bacci barawo ne haka ya kwashe shi ba tare da ya shirya ba.
EPISODE 30
Yanda suka kwana da walwala haka suka tashi da walwala saboda sun ga Mommy. Suna dawowa daga
masallaci sallar asuba suka fara gyare gyare, don tunda aka ce ba a ga Mommy ba sai suyi sati ko shara
ba suyi ba don haka wajen duk yayi kura ga yana. Tsaf suka gyara kicin suka wanke komai sannan Salim
ya dora musu ruwan shayi ya soya musu kwai. Suna gama cin abinci suka rabu, wasu dakin Abban wanda
shima yayi datti sosai wasu dakin Mommy da kuma dakinsu, kafin karfe takwas an share an goge
dakunan saura falo. Ahmad ya zauna a kan kujerar dining table ya dubesu duk suna zaune kowa da
kayan aiki a hannu suna dan hutawa ya nuna dakin baki inda da Zulaiha take yace
“Saura dakin na, ku gyara shi sai na canza mana katifa in ya so ni da kai Ya Baba sai mu koma tunda mun
cika wannan kuma wadda aka bawa dakin ta canza uwa.”
Suka tuntsire da dariya, Madu yace
“Ah to ai tuntuni nace wasu su koma dakin kuka ce a’a.”
“Toh yanzu an ce.”
Khalifa da Auta ne suka fara mikewa suka shiga dakin, Baba karami ya dubi Madu yace
“Ka cire labulayen falon ka hada da na dakunan ka bawa Bala kafin mu dawo a wanke, in ya so gobe sai
ku gyara dakin don ni nan karfe sha daya zan kama hanya sai na je wajen Mommy na wuce Abuja.”
Nan ya mike ya fara aikin cire labulayen su kuma Ahmad da Baba suka koma dakinsu don su fara
shiryawa. Zuwa karfe tara sun gama duk sun shirya domin zuwa gidan makoki, sai da suka kirawo
Mommy suka gaisheta sannan suka zauna jiran Abban.
……..
Shi kuwa Abban haka ya kwana yana juyi yana tunaninta, har akayi assalatu bashi da tabbacin yayi bacci
ko kuma ido biyu ya kwana. Ko da gari ya waye ma haka ya cigaba da wasi wasi; ya kirawo ta a waya ko
kuma ya bari sai ya je Jigawan. Yau din kwana biyu kenan da rasuwar, da wani ya mutu ba Baffa ba
tabbas da yau din zai tafi Jigawan toh amma Baffa ne fa. Zaman makokin na kwana uku Baba Yalwa tace
a yi kuma gobe litinin shine kwana ukun don haka yana ganin gara ya bari in aka tashi daga makoki
goben jibi Talata sai ya je, yana jin ma Aliko zai ja su je don yasan tana matukar ganin girman Alikon.
Allah sarki Baffa, ya san da yana raye da yasa baki indai Rabi ce ba za ta iya yi masa musu ba. Sai da ya
share kwalla saboda tun yanzu ya fara kewar Baffan. Abokanan huldarsu ne suke ta zuwa gaisuwa daga
ko ina musamman shi da Aliko, domin shi Abba ma wasansu daga cikin masu zuwar masa sun zata Baffan
ne ya haifeshi da yake lokacin da nashi mahaifin ya rasu bai riga ya tara dukiya da suna haka ba.
Kwamishinoni da manyan ‘yan siyasa wadanda suka sani sai zuwa sukeyi harda ma ministoci a masu
zuwar wa Aliko musulmai da wadanda ba musulmai ba. Haka dai ya daure zuciyarshi ya yanke shawarar
sai Talata din zai je Jigawan, watakila ma kafin nan ta dawo Kanon.
Ya mika hannunshi kan durowar gafen gadon da yake kwance ya dauko wayarsa, ya latsa ya duba lokaci
karfe bakwai da minti goma. Sai a lokacin ya tuna ashe yau Lahadi babu kai yara makaranta yake kwance
yana jiran Saudah ta tashe shi. Ya shiga cikin lambobin wayar da ya adana wato contact, har ya zo kan
lambar Rabin da Ahmad ya saka masa jiya. Yana shirin ya danna mata kira sai kuma wata zuciyar tace
masa yanzu haka fa bacci take yi, don haka sai ya fasa ya ajiye wayar da niyyar idan ya gama cin abincin
safe zai kirawo ta kafin nan ta tashi. Nan ya cigaba da juyinsa a kan gado sai wajen karfe takwas da rabi
da ya fara jin motsin su Nawwara a falo sannan ya taso ya fito.
Saudah tana kichin tana ta shirya abincin safe su kuma su Nawwara suna nan a falon suna wasansu
yayinda Ummi da yake itace gwanar kallo tana zaune a gaban TV tana kallon cartoon. Nan ya zauna a
wajensu yana musu hira. Bai dade da zama ba ta fito daga kicin din da kayan abinci a hannunta ta jera a
kan dining table ta dawo inda yake ta gaisheshi, bayan ya amsa ta koma kichin din. Tun ranar alhamis da
suka yi fadansu da Zulaiha take ta cika tana batsewa amma yau fuskar tata da dan walwala. Ya so suyi
magana ranar alhamis din da daddare amma sai shi kuma bai zauna ba, Juma’ah kuma aka tashi da
rasuwar Baffa.
Ta dawo ta sake ajiye wasu kwanukan a kan table din sannan ta ajiye wasu a kasa kan tile inda yara suke
cin abinci. Tace
“Ga abincin Abban Nawwara.”
Ya taso ya dawo kan table din ita kuma ta zauna ta fara bawa yara nasu abincin itama tana cin nata.
Jimawa kadan ta dubi Abban tace
“Ya karin hakuri kuma.”
“Alhamdulillah.”
“Toh Allah ya sa ya huta.”
“Amin.”
Suka cigaba da cin abincinsu. Kafin ta gama da yaran shi har ya gama ya mike daga kan tebur din ya
dubeta yace
“Bari naje na shirya.”
“Toh sai ka fito.”
Jimawa kadan ta gama basu abincin ta tashi ta kwashe kwanukan. Kafin ta dawo ta zauna mai yi mata
wanke wanke ta zo, ta kwashi kayan wanke wanken ta fitar da su fanfon da yake bayan kichin din
Saudan. Nan da nan yaran suka bita suna murna, sun riga sun saba haka za tayi ta wanken wanken suna
mata surutu don haka Saudah din ta kyalesu ta nufi dakin Abba. Kafin ta gama shiga dakin taji Zulaiha ta
bude kofar daki ta fito, ta san kichin zata je neman abinci. Haka suka koma tunda suka dambace to basa
haduwa, ita Zulaiha kullum tana daki sai ta tabbatar Saudah bata kichin sannan take zuwa diban abinci
sannan kuma ta daina tayata kowanne aiki sai dai kawai idan ta ci abinci za ta wanke iya kwanukan da
tayi amfani da su ta gyara abinda ta bata, da yake ma Juma’ah da Asabar ba a gidan suka wuni ba. Itama
bata son shiga shirginta yanzu da haka ta shige dakin ta turo kofa. A zaune ta same shi a gefen gadon
yana waya da manager, bayan ya ajiye wayar ya dubeta yace
“Ba za kuje gidan makokin bane yau.”
Ta karkata kai sannan ta bashi amsa
“I, gobe dai ma je in sha Allah. Yaran duk a takure suke wuni jiya haka Baffa Karami yayi ta faman koke
koke wallahi.”
“Hakane, Allah ya kaimu goben.”
Suka yi shiru na dan lokaci ya mike ya nufi wardrobe don zaro kayan da zai sa tace
“Na ji an ce an ga Mommyn su Halifa ko?”
Da fara’arshi ya juyo yana ‘yar dariya yace
“Eh wallahi an ganta, ko ta zo zance ne. Jigawa ta tafi gidan kanwarta tayi zamanta ta barmu muna ta
nemanta.”
Ya ajiye kayan da ya zaro ya juya wardrobe di don ya dauko wani abu. Ta tabe baki tace
“Allah sarki, ai kuwa dai an wahalarda da mutane.”
Bai bata amsa ba don haka itama sai ta yi shiru. Ya gama saka kayan ya dauki agogo a kan mudubin ya
fara kokawar daurawa, ta tashi daga inda take ta matsa ta karbi agogon ta karasa daura masa. Bayan ta
gama saka masa ya zauna a kan stool din mudubi ya bude durowa, ta koma ta zauna a gefen gadon tace
“Abban Nawwara.”
Ya bar abinda yake yi a cikin durowar ya juyo ya kalleta yace
“Na’am.”
“Ni dai don Allah ka rabani da Zulaiha, gaskiya zamanta ba zai yiwu a nan ba. Ka nema mata hostel ko
kuma ta koma gidan wani, kai ko wajen Mommyn nema ta koma amma ni dai ta bar min nan.”
Ya bata rai ya dubeta yace
“Au fadan bai kare ba kenan.”
Itama ta sake bata rai
“Ba haka bane amma raini ya riga ya shiga tsakaninmu, ba zai yiwu ba a gaban yarana ta dinga yi min
gani gani.”
“Ah zai yiwu mana, naga a gaban yaran kika zage kuka dambace to sai me kuma don tana miki gani gani
a gabansu? Ai haka kike so ko?”
“Ni dai ba haka nace ba don Allah ka raba ni da ita kawai.”
“Kin yi wauta Saudah, ban san lokacin da za ki girma ba wallahi. Yarinyar nan fa ke ce ma kike morarta da
kin bari kun zauna lafiya; girki, share share da hidimar yara duk ita ke tayaki ina jinku ma har aikenta kike
yi gashi ta tayaki dauko yara daga makaranta amma saboda abu daya kika kasa hakuri. Ai shi mutum ko
waye shi indai kana zaune da shi sai ka yi hakuri in ba haka ba ba za ka ci ribar zaman ba.”
Suka yi shiru na dan lokaci, ya juya ya cigaba da duba abinda yake nema a cikin durowar. Tace
“Ni dai don Allah nace maka ta bar min gida sai dai kuma idan ni ake yiwa kora da hali toh wannan kuma
sai na san abin yi.”
Ya juyo ya fuskanceta, sai da ya kare wa fuskarta kallo kamar mai nazartar wani abu sannan yace
“Hmm, toh yanzu ina kike so ta koma? Kin san dai ba zai yiwu ta dinga zuwa BUK daga Bichi ba ko? Kuma
ba zan koreta ba don nima da dadi babu dadi haka kanin mahaifina ya rike ni saboda zumunci don haka
babu yanda za a yi na tozarta zumunci. Abu daya zan iya yi miki alkawari idan aka gama zaman makoki
idan Aliko bai tafi da Baba Yalwa Lagos ba zan ce ta koma can sai ki huta idan kuma ya tafi da ita Lagos
toh haka za kuyi ta hakuri tunda saura kadan ta karasa karatun sai ta koma gida.”
Ta kalleshi suka hada ido, ta dauke nata idon tace
“Toh ta koma inda take da mana, tunda dai dakin yana nan.”
“Cikin samarin za ta koma saboda a garin arna muke? Toh ai ko Rabin ce ta haifeta ba zan barta a cikin
wadannan samarinba ba tare da idon Mommyn ba.”
Ya juya ya cigaba da duba durowar ya dauko wallet dinshi da kuma mukullai, ya juyo yace
“Toh idan dai Mommyn ta dawo sai ta koma can din wajenta.”
Ta dago ta kalleshi tace
“Au yaushe za ta dawo Mommyn?”
Ya washe baki da fara’a kamar ba shine yanzu ya sha kunu yana mata fada ba sannan ya bata amsa
“Ko da wane lokaci ma za ki iya ganin ta dawo, ina fatan kin san ba sakinta nayi ba ko?”
“Um.”
“Yauwa, ni na fita gidan makoki.”
“A dawo lafiya.”
Ya amsa ya fice ya barta a dakin. Yana fitowa falon ya kwalawa Zulaihan kira ta fito a shirye bayan ta
gaishe shi yace
“Za mu wuce gidan makoki in kin shirya dauko mayafinki mu tafi.”
Nan da nan ta koma dakin ta dauko mayafi ta fito ta samesu a tsakar gida da su Baba. Bayan sun gaishe
shi Baba yayi masa bayanin karfe sha daya daga gidan makoki zai wuce Abuja amma bai gaya masa zai je
Jigawan ba. Har sun fara shiga mota yace
“Ina zuwa.”
Ya karbi mukulli a hannun Kahlifa ya bude falon Mommy ya wuce dakinshi, sai da yayi murmushi da yaga
yanda suka gyara dakin tabbas ya fara jiyo kamshin Rabi. Sai da ya turo kofar sannan ya zauna a gefen
gadon ya zaro wayarshi, nan da ya nemo lambar tata ya danna kira.
A zaune suke a kan dining table sun gama cin abincin safe har Zahra ta kwashe kwanukan su kuma basu
tashi ba suna ‘yan hirarrakinsu. Wayarta da take ajiye a kan fridge din da yake kusa da dining table din
tayi waka, ta mike ta dauko wayar ta dawo ta zauna. Bata saka lamabarshi a kan wayar ba amma da yake
ta riga ta haddace tana kalla ta san waye, murmushin da tayi ya sa Baraka ta gane wanda yake kiran.
Suka yi dariya gaba daya, kafin ta amsa wayar ta tsinke. Da yake Yaya Shafa ta basu labarin zuwan da
yayi ya sameta Barakan tace
“Abun ya zo kenan in ji mai fadar aurensa.”
Kafin ta bata amsa kiran ya sake shigowa, ta danna amsawa ta kara a kunnenta
“Salam alaikum.”
Dadin da yaji ba zai misaltu ba saboda yanda ya dade bai ji wannan muryar ba, shi bai ma taba sanin
akwai abinda zai sa shi yaji kewarta haka ba.
“Wa alaikum salam wa rahmatullah, Rabi.”
“Na’am. Ya hakurinmu.”
“Alhamdulillah.”
“Allah ya ji kan Baffa.”
Baraka ta mike ta barta ita kadai a wajen.
“Haba Rabi, mun gama shan wahalar nemanki ashe kina gefe kina kallonmu.”
Dariya tayi sannan tace
“Toh ai gani ko.”
Yayi murmushin jin dadi, ya gyara zama ya jingina da kan gadon yace
“Hakane. Yanzu yaushe za ki dawo Kanon?”
“Toh, sai kuma idan wani abun ya taso dama wannan din ma Baraka na rako ta yiwa Baba Yalwa gaisuwa
a madadina.”
Ya tashi daga kashingide da yayi ya cire hularsa ya ajiye a kan gwiwarsa yace
“Ah, haba Rabi! Ya kike wannan zancen, ga gidanki da yaranki kuma kice sai wani abun ya taso?”
Murmushi tayi har sai da ya jiyo sautin murmushin ta wayar, tace
“A’ah, ni ai bani da gida a Kano sai dai sa rai ina nan wajen Baraka da yake ita tana da gida.”
Nan da nan murmushin da yake kan fuskarshi ya gushe
“Ya za kice haka? Ga gidanki da yaranki. Don Allah kar muyi haka dake Rabi, ke kin san abinda ya faru
tsautsayi ne in banda haka ya za ayi nace ki barmin gida.”
“Um, hakane kam.”
Suka yi shiru shi yana sauraronta ita kuma gaba daya ma maganar ta gundireta, sai da ya tabbatar ba za
ta bashi amsaba yace
“Zan zo dai har Jigawan na baki hakuri sai mu taho ko?”
“Hakurin me kuma? Ni baka yi min komai ba fa.”
Suka sake yin shiru, yaga dai in bai yi magana ba baza tace komai ba don haka yace
“Rabi.”
“Na’am”
“Ki san dai ba sakin ki nayi ba ko?”
“Eh, Amma in ta kama za sake nin ai.”
“Subhanallahi, Rabi wai kinsan me kike fada kuwa?”
Dariya ta dan yi kafin tace wani abu yace
“Rabi zan zo dai ina jin in na tsuguna na baki hakuri kya biyo ni mu dawo gidan.”
“Uhm, bari naje naci abinci.”
“Toh sai an jima in sha Allahu da daddare zan kiraki, ana gama zaman makokin nan kuma zan zo.”
Kafin ya ajiye wayar ta ajiye, don haka sai kawai ya jefe tashi wayar kan gadon. Ya saka tafukan
hannayenshi guda biyu ya dafe kansa da su, baya son irin wannan fushin na Rabi. Duk lokacin da suka
samu sabani in ta fito gaba daya ta nuna fushinta to ta fi saurin hakura, amma irin wannan da za ta dinga
magana kamar komai bai faru ba sai ta dade bata hakura ba. Kafin ma ta tsaya a tattauna maganar sai
yayi da gaske da ita don da yayi magana za tace babu abinda yayi mata. Yanda yake jinta yanzu tana
magana kamar babu abinda ya faru ya san sai yayi da gaske za ta saurareshi ma ayi maganar, amma
watakila saboda bayan ganinta ne in sha Allahu in yaje Jigawa ba zai dawo ba sai da ita.
Kwankwasa kofar da aka yi shi ya dawo dashi daga tunanin da yake ya cire kanshi daga tafukan
hannunsa ya ce
“Shigo.”
Khalifa ne ya turo kofar ya shigo yace
“Abba muna ta jira shine Ya Baba yace na duba ko lafiya.”
Ya sa hannu ya dauki wayarshi tare da mikewa tsaye yana fadin
“Mhm, muje babu komai.”
Ya taso Khalifa a gaba suka fito suka kama hanya suka tafi. Tun daga wannan lokacin yake cikin damuwa,
haka dai ya zauna a gidan makokin nan zuciyarshi tana Jigawa. Fata yake Allah dai ya sa kada Rabi ta ki
dawowa.
Tana ajiye wayar ta tashi ta hau sama ta tarar da Baraka a daki, tun kafin ta zauna Barakan ta kalleta
tana dariya tace
“Abun ya zo kenan, an tada tsohuwar soyayya.”
Sukayi dariya gaba daya, ta karasa ta zauna a kusa da ita a gefen gado sannan ta dubeta tace
“Hmn, ya dai gama kame kamensa. Wallahi auren duk ya fice daga raina, kayi ta zama kana amfanawa
kowa amma kai ba za a bari ka amfanawa kanka ba kuna ba za a amfana maka ba. Shifa magana ma yake
kawai wai na koma gidana wajen yarana, da ya so wulakantani ai cewa yayi gidansa yara kuma gidan
ubansu ni da bani da gidan uba.”
Ta share kwalla, Baraka ta dafa ta tace
“Ki daina damuwa komai ya wuce in sha Allah, ko za ki koma ai sai mun shirya kuma
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good