Showing 138001 words to 141000 words out of 196754 words
Chapter 47 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
sai ya shiga
hankalinsa tukunna.”
Basu dade da issa wajen makokin ba Baba karami ya duba agogo yaga sha daya saura don haka yayi
sallama da kowa a kan zai koma Abuja, yana fita ya kama hanyar Jigawa. Yana so yaje yaga Mommy a
nutse duk da yanzun ma ya ji dadin ganinta kwarai, ya fuskanci tana cikin walwala. Sai wajen sha biyu da
rabi sannan ya isa gidan. Da yake masu aikin Baraka sun san shi nan da nan aka hau hidima da shi. Bai
dade da zama ba Mommy ta sauko daga dakin Baraka ta same shi a falon kasa, bayan ya gaisheta tace
“Kai da za ka tafi Abuja shine ka tsaya a nan so kake dare yayi maka a hanya.”
“A’a Mommy ai yanzu zan tafi dama tsayawa nayi mu gaisa.”
Nan ya zauna suka yi ta hira, ta yi zaton ma zai yi mata maganar komawa gidan Abbanshi amma sai ta ji
bai ce komai ba. Suna nan zaune Baraka ma ta sauko suka gaisa da Baban. Ya tashi ya fita kofar gida
Sallah, kafin ya dawo an ajiye abincin rana a table. Gaba daya da shi da Rabin da Baraka suka zauna a
table din cin abincin suna yi suna hira. Baraka ta dubi Baban bayan ta ajiye cokalin da ke hannunta tace
“Baba mu na so a budewa Mommy bank account, amma bana son a bude mata a Jigawa ka ga zai fi sauki
a bude a branch din da yake Kano tunda nan za ta koma.”
“Hakane, to ai Anti Ahmad za a gayawa ya bude mata a bank dinsu kawai. Watakil ba ma sai ta je ba zai
iya bude mata sai dai ko ace signature wannan kuma za ta iya yi a paper a dauki hoton a tura masa yayi
scanning kawai, na san in 24 hours zai bude mata account.”
“Hmn, ka san na manta Ahmadu a banki yake, ai kuwa ina gamawa zan kirashi.”
Suka dan cigaba da cin abincinsu, jimawa kadan ta sake duban Baba tace
“Akwai kaya da nake so za a saro, mun gama magana da Mommy za ta fara business ne, kai ka san yanzu
an daina zama haka.”
“Gaskiya ne Anti, shawara ta yi. Ko nima sai na bada jarin, zai kai nawa?”
“Kada ka damu ma mun gama da wannan bangaren sai dai da yake kogi bai ‘ki dadi ba.”
Mommy ta ajiye cokalinta tace
“Hmn, ai Baraka ita kadai ta gama komai fa kudi sama da dubu dari biyu. Mubarak ma kuma bayan mun
rabu a Kano jiya ya turo min da dubu arba’in ta account din Baraka wai ko zan bukaci wani abu.”
Da murnarshi ya amsa
“Kai Allah ya bar zumunci.”
Baraka tayi gyaran murya tace
“Yauwa ka san gidan Umma yana hannun Baba Munzali ko?”
Ya jijjiga kai alamar eh.
“Toh mun yi magana da Yaya Shafa da Mubarak za a sayar da gidan a raba a bawa Mommy kasonta don
itama ta sayi gida, Mubarak da Yaya Shafa sun ce suma duk a hada da kasonsu a saya mata gida a
Kanon.”
“Hakan yayi Anti, ai ko nima sai na cika a sayi gidan in sha Allah.”
Sosai ya ji dadin wannan labarin ba don yana son mommy ta kashe aurenta ba yana dai so yaga ta samu
kudin kanta. Ya san tambayar kudi yana yi mata wahala, tun yana yaro ya kula tana hakura da abun
bukata indai bukatar kanta ce saboda bata son tambaya, ko da ta san in ta tambaya za a bata amma sai
ta kasa tambaya. Don haka ya ji dadi ya san ko ‘yan haya aka saka za ta dinga samun isassun kudi tunda
ko shi duk yanda yake nuna mata in tana son wani abu ta gaya masa amma bata fada. Abu daya ne ya
bashi tsoro kada a sayi gidan tazo ta ki komawa gidan Abba, yana so ta koma sai dai kawai ya yiwa kansa
alkawarin ba zai taba ce mata ta koma ba kuma suma kannen nashi tun dare suna shirin bacci ya ja musu
kunne a kan kada wanda ya dameta ta dawo. Shi Abban in ya matsu ya san yanda zai yi ya lallabata ta
dawo tunda shi ya koreta.
Mommy ta ajiye kofin ruwan da ta sha tace
“Baba ina Khairiyya kuwa, ban ji ana maganar ba.
Nan da nan fuskarshi ta canza, ya basu labarin abinda ya faru. Baraka tace
“Allah sarki kada ka damu, Allah ya sa haka ne yafi alkhairi a gareku da kai da ita.”
Mommy tace
“Amin. Wani baya auren matar wani, Allah ya nufa ita din ba matarka bace.”
Baraka tace
“Kace na rufe mana akwatunanmu tukuna ko kuma akwai wata na cigaba da tari.”
Kayan lefenshi take magana wanda yake turo mata kudi tana saya tana tara masa. Yayi dariya yace
“Toh, ana dai addua.”
Suka cigaba da cin abincinsu, mommy ta mike ta dauki kwanonta da yake ita ta cinye nata abincin ta
shige kicin don ta kai. Sai da Mommy ta shige ya dubi Baraka yace
“Da dai za a bani auren Fathiyyan Anti Shafa da sai na ce ki cigaba da tari kawai.”
Fara’arta ta karu, ta ajiye cokalin bayan ta cinye lomar karshe tace
“Me zai hana a baka auren Fathiyya kuwa, ai tari kawai zan cigaba.”
Yayi murmushi
“Kin san ‘yan gidansu sai sun gama degree ake musu aure, kuma ita kinga yanzu ma ta gama secondary
school ko admission din ma bata samu ba. Tun kafin ma mu hadu da Khairiyya na so nayi magana toh
amma na san za a ce tayi yarinta ba za ayi mata aure ba. Shi yasa na bari, yanzu kam da aka yi haka ina
ga zan jira ta gama jami’a kawai.”
Mommy ta karaso yayinda Baraka take cewa
“ Sarkin kauron baki. Ai ba ma sai ka jira ba, ba dai karatu bane kuma tunda za ka barta ai na san Daddy
ba zai hanamu ba. In aka fara magana yanzu nan da shekara daya sai a yi komai kafin nan ma yanzu haka
miskilin kaninka ya shirya. Wannan fa ma ina jin sai dai ka dinga zuwar masa zance in ba haka ba yayi
kwantai.”
Suka sa dariya gaba daya. Baraka ta mayarwa da Mommy abinda Baban ya fada. Mommy tace
“Eh, da wannan kam ana so sai sunyi karatu amma bana jin za a hanaka ita. Kai dai ka tabbatar kana
sonta kuma za ka rike min ita amana don in ka tozarta ta to ni ka tozarta.”
Baraka ta kalleshi tace
“Ka je ka tsarota kawai, shikenan an gama magana tunda kana da ni uwar amarya uwar ango.”
Suka karasa hirarrakinsu, yana mikewa daga table din yayi musu sallama ya kama hanya.
Tunda suka dawo daga Kano Baraka take ta fama da Rabi a kan ta shirya su tafi Abuja ranar litinin amma
ta ki. Baban Ummi ne zai dawo daga UK ranar Talata shine za taje tarenshi sai su dawo tare ranar
Juma’ah. Duk yanda taso su tafi da Rabi taki yarda ita gani take za ta dame su, ita kuma Baraka tace
“Ba fa zaman gidan yake ba, sai dare yake dawowa. In ba kya so ma ko haduwa ba za kuyi ba, in muka zo
nan ne ma yake zaman gida tunda a nan bashi da office.”
Ita dai Rabi taki yarda yayinda ita kuma Baraka take jin ya kamata su je tare don Mommy ta dan kara
zagawa tunda in ta koma gidanta ta san babu inda za ta dinga zuwa. Sai bayan isha’I sun kwanta za suyi
bacci Rabin ta taba Baraka tace
“Goben za ki tafi Abuja.”
“Eh, za kije ne.”
“Zan je.”
Tayi zumbura ta tashi zaune don bata zata haka za tace ba, tace
“Allah Bibi za kije.”
Dariya kawai tayi mata tace
“Bari na kirawo Baba Habu yayiwa driver magana in ya so wajen tara na safe sai mu tafi a mota, ticket
din sai na siyarwa Abban Ummi ya hada ya siya mana na dawowa sai mu dawo a jirgi.”
Sai da suka tashi suka hada kayan da suke bukata sannan suka koma suka kwanta. Gari yana wayewa
suka kama hanyar Abuja gaba dayansu har Zahra tunda itama ta gama SSCE dinta sai jiran admission.
Litinin ya kama kwana uku da rasuwar Baffa Kuma ranar za a share makoki. Duk yanda Aliko ya so ya tafi
da Baba Yalwa Lagos ta ki amincewa don haka dole ya hakura, Abba ya tabbatar masa babu komai ya
barta sannan ya sanar da shi yau dinnan Zulaiha za ta kwaso kayanta ta dawo gidan duk da akwai
yaruwar Baban wadda ta dawo gidan, sai dai itama tsohuwa ce kusan kamar Baba Yalwa. Ana idar da
sallar la’asar suka sallami kowa aka kwashe shimfidu aka tashi. Nan da nan Abba yace Zulaiha ta fito ta je
Salim ya kaita gida ta kwaso kaya ta dawo. Bata son zaman gidan Baffa amma a yanzu ta dan sami
natsuwa don itama ta tsani wannan zaman da suke da Saudah, fatanta kawai Mommy ta dawo don ta
samu ta koma can. Sai da suka iso gidan Zulaiha ta shige daki sannan Abba yakewa Saudah bayani, ai
kuwa tun daga fuskarta ya gane ta yi farinciki. Ta ciko akwati da kaya ta janyo ta fito, ta zo fita ta daure
ta dubi Saudan tace
“Ni na tafi sai an jima.”
Ta gatsine baki tana gintse dariya tace
“A sauka lafiya.”
Ta fice ta barta tana jaddadawa kanta lallai sai ta koyawa Saudah hankali.
Da yake yamma ta riga tayi dole haka Abba ya hakura da zuwa Jigawa, amma gobe Talata da sassafe zai
tafi. Nan take ya bugawa Lalo waya ya sanar da shi karfe tara za su je unguwa don ba zai je da Madu ba.
Da daddare ma ya son kiranta a waya amma sai ya kasa saboda baya son suyi magana ta waya, gani yake
idan suka hadu ga ta ga gashi sai ta fi sauraronshi. Gaba daya tunaninta da maganganunta na jiya sun
hanashi sukuni, don haka bayan ya gama cin abinci ya shiga daki wajen goman dare ya zauna a gefen
gado ya dauki waya zai kirawo ta kenan Saudah ta shigo dakin. Don haka sai ya mayar da wayar ya ajiye,
ya san in ba wani daga cikin yaran ta jiyo kukansu ba toh babu abinda zai fitar da ita daga dakin nan sai
wajen dayan dare. Ba wai tsoron kiranta yake a gaban Saudah ba amma lissafin da yake kansa yanzu duk
ya cike masa kwakwalwa baya son a kara masa da korafi komai kankantarsa don haka kawai sai ya
kwanta ya hakura da wayar; tunda gobe in sha Allah I yanzu Rabi tana cikin gidan nan. Da kyar da yake
bacci barawo ne ya dauke shi, amma ita kanta Saudan sai da ta gane gangar jikinsa ce kawai a nan
ruhinsa yana wani wajen.
Ko da gari ya waye sai da ya ci abinci gama shirinsa tsaf sannan ya fito ya sami Saudah a falo ita da su
Hanan, bayan ya amsa a dawo lafiya ta yace
“Jigawa zan tafi.”
“Jigawa Kuma”
“Eh kin san Rabi tana can wajen kanwarta, zan je in sha Allahu tare za mu dawo.”
Ta kawar da kai tace
“Uhm, Allah ya kiyaye hanya.”
Ya fice ta bi bayansa da harara. Bata damu da ita ba amma gaskiya bata so ta dawo yanzu ba, gashi duk
wani tsari da ta tanada ya rushe. Ragowar maganin ma da Kaka ta bata na sakawa nemanshi tayi ta rasa
duk da tana tunanin faduwa yayi da yake a leda yake Zulaiha ta share shi da tana share mata daki. Ga shi
Ummanta ta fara yi mata waya tana tuna mata sai fa ta fito da kudin nan dubu dari an bawa malam don
itace bata yi amfani da abubuwan da ya bayarba saboda idan ba a bashi kudinshi ba komai zai iya
faruwa. Don haka wannan dawowar da Mommy zata yi kawai damuwa ta kara mata don ta san haka zai
yi ta rawar kai ba zai saurare ta ba balle ta samu ta yago wani abu. Da yake ta fara project to ta gaya
masa akwai kayan da zata saya na yin project din ta samu ya bata dubu goma kafin mutuwar Baffa. Gaba
daya yanzu tana cikin damuwa matuka wadda labarin dawowar Mommy ya kara mata.
Yana fita ya shiga wajen Mommy, Madu bai gama shiryawa ba don haka ya yi musu sallama shi da Salim
ya sanar da su zai je unguwa shi da Lalo in ya dawo za su hadu a kasuwa. Bai gaya musu Jigawa zai je
wajen Mommy ba da sun gaya masa bata nan domin su ma tun dare suka yi waya da ita ta sanar da su ai
gata nan a Abuja. Yayi musu sallama shi da Lalo suka dauki hanyar Jigawa. Ya san a kayan marmari Rabi
tana son apple da ayaba, don haka sai da ya samu apple da yaba masu kyau ya cika leda dasu sannan ya
sayi yoghurt roba hudu ya hada sannan suka kama hanya. Kafin sha daya sun isa gidan da yake ya je
daurin auren su Ummi ya riga ya san gidan. Tun daga bakin gate mai gadi ya sanar da shi ba sa nan suna
Abuja, ya dube shi da mamaki yace
“Akwai ‘yar uwarta Rabi da ta zo daga Kano, tare suka tafi Abujan ko ita tana ciki.”
“Ai wallahi Alhaji gaba dayansu suka tafi babu kowa a gidan sai ranar Juma’ah za su dawo.”
“Ikon Allah.”
Ya koma mota ya zauna, ya zaro waya ya kirawo Rabin bata dauka ba don haka ya kirawo Baraka. Bayan
ta amsa sallamarsa suka gaisa yace
“Baraka ina kuka tafi ne ke da Rabi, na zo megadi ya ce min ba kwa nan.”
“Lah, wai kana Dutse. Wallahi muna Abuja gaba daya ai ban san za ka zo ba da na gaya mata.”
“Kin dauke min Rabi.”
Tayi dariya tace
“A’ah, ni ban dauketa ba.”
“Bani ita muyi magana ina ta kiran wayarta bata dauka ba.”
“Eh, hakane saloon suka je ita da Zahra kuma sun bar wayar a gida, amma bari na yiwa maigadi waya sai
ya bude muku falo ku huta.”
“A’ah yanzu ma za mu juya in sha Allahu, na kirawo Rabin in an jima in ya so wajen ranar Asabar sai na
dawo.”
Har zata ajiye wayar yace
“Ki tayani bata hakuri kafin mu hadu, na san fushi tayi dani take boye min.”
“Ai bata san za ka zo yau din ba da na san za ta gaya maka bama nan, amma in sha Allahu zan gaya
mata.”
Suka yi sallama suka ajiye waya, ya kirawo Lalo wanda ya fita ya barshi a motar tun da ya fara waya, yace
“Mu tafi Lalo basa nan.”
Suka kama hanya suka dawo. Da yake Madu bai san inda suka je ba ya dauka Abban baya jin dadi ne da
yaga yanayinsa, ya zata sugansa ne yake neman tashi da yake kwana biyu ya ci abinci a gidan makoki.
Don haka tun kafin su koma gida yace Salim yayi wa Abban abinci. Sosai ya shiga damuwa saboda ya
gama sakankancewa yau zasu dawo da Rabi ga shi ko ganinta bai yiba, wayar ma da aka ce ta bari a gida
shi bai yarda ba gani yake kin dauka kawai tayi. Amma dole ya hakura tunda yanzu shi yake nema,
abinda ma yake kara bashi haushi yanda take ta faman yawo kamar wadda bata da aure ko tambayar shi
ma bata yi. Haka ya hakura ya bari sai da daddare ya kirawota.
Tunda suka fito yi masa sannu da zuwa bayan ya dawo daga kasuwa Salim yace masa
“Abba na dafa maka dashishi.”
Yace
“Toh sannu Salim, ka ajiye min a nan falon zan zo na ci.”
Don haka yana shiga ya sanar da ita a wajen Salim zai ci abinci. Tun abun yana bata haushi yanzu har ya
daina damunta don haka ta juye taliyarta ta saka a fridge gobe ta huta da abincin ‘yan makaranta. Bayan
yayi isha’I ya wuce falom Mommyn, a can ya zauna yaci abinci bayan ya gama kuma ya shige dakinsa.
Yana zama a gefen gadon ya zaro waya ya danna mata kira. Da sallama ta dauka bayan ya amsa
sallamarta suka gaisa yace
“Na je Jigawan ai bakwa nan.”
“Eh, haka Baraka ta gayan min.”
Suka yi shiru na dan lokaci, yace
“Yanzu ya za ayi, ina son ganinki yaushe za ku dawo.”
“Ranar Asabar.”
“Toh Allah ya kaimu.”
Suka sake yin shirun da ya tabbatar idan ba shi ya fara magana ba baza tace komai ba.
“Rabi.”
“Na’am.”
“Ki yi hakuri ki dawo dakinki mana.”
“Hmn! Shi nake kokarin yi dakin ne har yanzu ban sami wanda yayi min ba na siya.”
“Ban gane ba, wane daki kuma za ki siya.”
“Gida zan saya a nan Kano din.”
Sai da gabanshi ya fadi da yaji wannan maganar, zancen Baffa ya fado masa da yake cewa Madu su
sayawa mahaifiyarsu gida. Kaddai yaran ne za su saya mata gidan; ai kuwa zai yi fada da duk wanda yake
shirin raba shi da Rabi.
“Wane gida kuma za ki saya ga gidanki a nan, ni da yara duk sai shirin dawowarki muke yi. Don Allah kiyi
hakuri ki dawo, ni zan zo ma har Jigawan mu taho.”
“Wanna ai gidan kane kai da ‘yayanka, nima zan koma na sayar da gidan da nawa mahaifin ya barmin
gado na sayi wanda zan iya zama a ciki.”
Ya dafe kai ya fara hada gumi
“Don Allah ki daina wannan zancen Rabi, ai nace kiyi hakuri. Don Allah ki bari komai ya wuce. Ni fa bama
sakinki nayi ba kinga dai har yanzu ke matatace ko? Don Allah ki dawo muyi zaman mu.”
Cikin yanayi na kosawa tace
“Zan yi tunani.”
Gaba daya kanshi ya kulle ya rasa kalmomin da zai yi amfani da su wajen gamsar da ita ta dawo.
“Yanzu ranar Asabar din za ku dawo daga Abujan?”
“Eh.”
“Idan kun dawo zan zo amma don Allah kiyi hakuri ki hada kayanki idan na zo mu taho, kin ji Rabi.”
“Zan duba na gani.”
Ya fuskanci kosawa a maganganunta don haka ya hakura sukayi sallama ya ajiye wayar. Ya jefa wayarshi
kan gadon ya kwanta; toh me Rabi take nufi dashi? Gaba daya ma ji yake kamar bata son magana da shi.
Gabanshi ya Fadi da yayi wannan tunanin, ya za ayi ace wai Rabi ta daina son shi. Bai taba zaton wai Rabi
za ta iya rayuwa cikin walwala a wani waje da ba gidansa ba amma ga shi nema take ta yi haka. Ranar
Lahadi in sha Allahu zai je Jigawan kuma tare za su dawo don sai ya biya ya ga Yaya Munzali sannan ma
zai je, watakila idan Munzalin ya saka baki ta biyo shi su dawo gida kowa ya huta. Haka ya gama juya
zancen ya tashi ya koma wancan dakin nashi don kwanciya bacci.
Gaba daya kwanakin nan haka yayi su a cikin matsananciyar damuwa don duk wanda yake tare da shi ya
gane hakan. Su su Ahmad sun zata sugar din shi ne ita kuwa Saudah bata ma fahimci me yake faruwa
don bata san Rabin ta ki dawowa ba, ta dai yi zaton ana kan shirin dawowar. Don haka binshi kawai take
yi
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good