Showing 27001 words to 30000 words out of 196754 words

Chapter 10 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15414

ci abinci.”

Ta karaso ta zauna, Rabi ta tashi ta dauki mata kofin shan shayi daga kichin ta hada da flask da kayan
shayin da ke kana tebur sin ta tura mata.

Tace

“Bsmillah.”

Ta karba ta hada shayin tana fadin

“Shayin ma kawai zan sha don na riga na ci abinci.”

Suka danyi jim. Rabi ta karya shirun tace

“Ina Mahmud din kika taho ke kadai.”

“Yana gida, da yake ita Zulaiha basu fara karatun ba tana gidan sai na bar mata shi.”

“Allah Sarki.”

Zulaiha yarinyarta ce ta biyu, Fatima ta fara haifa wadda suke kira Inna karama, sai Zulaiha, ragowar kanne
Zulaiha su uku duka maza ne. Ita Inna karama tana gama secondary aka yi mata aure, ita kuma Zulaiha
bana ta gama secondary. Sai da ta kula ya kusan gama cin abincin sanna ta dube shi ta ce

“Yaya dama wata alfarma na zo nema wajenka, da ke ma.”

Ta karasa tana kallon Rabin.

“To Allah ya bamu iko.”

Ya bata amsa yana yi yana kallon idon Rabin. Dukansu suka mayar da hankali kanta.

“Yaya dama Zulaiha ce ta sami gurbin karatu a nan Jami’ar Bayero, toh na samu mahaifinsu ya yarda harma
ya biya kudin registration. Amma da yake mu na da nisa sosai zuwan zai yi mata wahala ga shi da na
tamabaya sai aka ce min lalacewar da ake yi a hostels ta yi yawa. Shine nace don Allah kuyi min alfarma
ta zauna nan wajenku in ya so duk lokacin da aka yi hutu sai ta dawo gida.”

Cikin fara’arsa ya amsa
“Eh to ai wannan ba zai zama matsala ba, dama Saudah bata son zama ita kadai kinga shikenan sai ta
zauna wajenta.”

Rabi tace

“Eh, ai babu komai, Allah ya bada sa’a.”

Sa’a tace

“Amin.”

Ta mayar da hankalinta wajen Abban tace

“Amma Yaya sai na ga kamar gara ta zauna nan wajen Mommy, duka duka da nawa Saudan ta girmeta.
Yaro da Yaro sai a je a sami matsala kasan ‘dan yau. Gara nan ko ba komai Mommy za ta tsawatar mata
tunda ita mace sai da kula.”

Tana yi tana kallon Rabin. Ya dubi Rabin yace

“Wannan ai ba zai zama matsala ba ko? Ai yiwa kai ne, Kuma ma balle ita da take ‘ya ta ce.”

Rabi tace

“Haka ne Allah ya bada sa’a.”

Ta kalli Sa’an tace

“Ai duk gida ne babu wata damuwa.”

Ya mike zai tashi itama ta mike tana fadin

“Bari nayi sauri na gaida Umman Nawwara sai ka rage min hanya don sauri zanyi na koma.”

Yace

“Toh ba laifi.”

Ya shige dakinshi ita kuma Sa’an ta tsaya ta kara yiwa Mommy godiya sannan ta fice.

Ta dan tsaya a nan tana mamaki. Toh me hakan yake nufi, Sa’a zata kawo rikon ‘yarta, harda ma wani zaba
a nan take son ta zauna. Lallai akwai matsala Babba, don ta hango ‘kura. Ta daga hannu tace

“Allah kaine Allah, ka shiga tsakanina da fitnar matarnan. Ba zan iya ba Allah ka iya min, ka kare ni ka kare
yarana.”

Ta kwashe kayan abincin sanna ta bishi dakin. Ta so ta yi masa maganar kawo Zulaiha amma sai ta ga
kamar shi a wajensa an gama magana, ta san lallai idan ta yi magana toh ko gaba idan aka sami matsala
zai ce daga wajenta ne don haka ta bar zancen.

Ita kanta Saudah da ta ji labarin dawowar Zulaiha gidan ta so a ce wajenta zata zauna ko babu komai ta
sami mai mata aiki da rainon Nawwara da Ummi, amma Kuma sai aka ce ba nan zata zauna ba.

………
Ko sati ba’ayi ba da maganar sai ga Zulaiha da kayanta a akwati uwar ta rakota. Bayan sun gaisa a tsattsaye
ta juya ta koma gida. Dakin baki ta sauketa inda da aka ce za a saka amarya. Bata so zamanta a wanna
dakin ba saboda yana kusa da dakin yaranta, amma shi kadai ne dakin baki. Ita kuwa a kan ta hada daki
da ita ta gwammace ta zauna a nan kafin a je a gumbuda mata wani abun tana bacci. Dai dai ta bisu kowa
ta ja masa kunne a kan Zulaiha. Kowa tayi masa nasiha daidai da tunaninsa, kuma kowa ya fahimceta. Har
Auta ma sai da ta ja masa kunne a kan kar ya sake ta ji wata hayaniya tsakaninshu da Zulaiha, domin shi
ko lokacin da ta dawo ma cewa yayi BBC kawai Anti Sa’a ta turo.

Ba su fuskanci wata matsala da ita ba sai rawar kai kadan. Duk yanda ta so ta shigewa Rabi bata sami kofa
ba, aiyukan gidan da take tunanin za ta taimaka da su kullum yan gidan su yi; musamman Salim, Khalifa
da Auta da yake sune kanana. Duk yanda ta so suyi shiri da Salim ba ta samu ba, shine take gani sa’anta
gashi kuma makaranta daya suke duk da department din su da ban ne. Wajen Saudah nan take samu ta
dan sarara don ko ba komai za ta kulata, ta sata raino ko girki sune aiyukan da bata fiya bari mai aiki tana
yi mata ba. Idan kuma tana son ta bugi cikin ta ma har hira take zama suyi, ga kuma TV duk channels din
akwai su sai inda taga dama take kallo. Da yake can a wajen Rabi tunda ta fara zama tana kallon tashoshin
da Rabin bata so sai ta sa Ahmad duk ya goge channels din ta daina ganinsu kwata kwata, don haka yanzu
ma ta daina kunna TV din.

Rabi da yaranta suna yawan zama hira a falo musamman bayan sallar isha’I; don lokacin duk sun dawo
banda Baba karami da yake Abuja; sai su zauna suyi ta hirarsu wani lokacin harda ciye-ciye. Zulaiha ta so
shiga cikin wannan zaman a dinga yi da ita amma abun bai yiwu ba. Idan ta fito sai ta ga duk sun cike wajen
sun yi mata wani kwarjini, sai dai kawai ta ‘bige da shiga kichin ko ta huce su ta tafi wajen Saudah. Tun
tana gwadawa ma har ta gaji ta daina. Wani lokacin idan Abban ya shigo ya tarar da su suna wannan hirar
ya kan ce

“Ina ‘yar taki.”

Sai tace

“Tana daki tana karatu.”

Wani lokacin kuma yana ganinta a wajen Saudah don haka wataran ko bai ganta ba sai ya dauka tana can.
Don haka duk a ‘dari ‘dari take da su. Babu wanda yayi mata wani abu da za ta nuna tace an yi mata, amma
kuma duk wani abu da zai sa ka ji ka zama ‘dan gida ma bata same shi ba a wajensu.

……..

Karatu tuni ya kankama, kuma da yake Zulaiha tana da kokarinta bata sami wata matsala ba. Ta so dai su
dinga tafiya makarantar tare da Salim, amma sam ya ki yarda don haka kowa da kanshi yake tafiya.

Tana son ta dinga kai wa Saudah rahoton Rabi amma bata samu dama ba, kwata-kwata bata ga abin rahoto
ba. Haka ta hakura, duk abinda Saudah ta tambayeta sai dai tace bata sani ba. A haka har semester ta kare
suka gama jarrabawa. Ranar da Zulaiha ta ce za ta tafi gida ya kama ranar alhamis, su auta za su je
makaranta don haka Abba yace ta bari sai ranar Asabar babu makaranta sai Madu ya kaisu ita da Salim,
Khalifa da Auta don su je su yi zumunci. Haka kuwa aka yi, duk yanda suka so kada su je ba yanda suka iya,
itama Mommy bata basu hadin kai ba ce. Ta ce

“Ni ba gidan Sa’a nace ku je ba, Bichi ai ko ina danginku ne. Idan kuka kai ta gidansu toh ku shiga gida gida
ku gaisa in ya so sai ku huce gidan Inna Hajara ku huta a can ku ci abinci sai ku taho.”
Haka suka hakura suka tafi. Naira dubu uku ta kawo ta bawa Madu tace

“Ku sayi kanin gidan gona a yanka ku kaiwa Inna Hajara. Ni bani da kudi amma in da kudi a wajenka ko
biskit ne ku siya ku kaiwa yaran su Baffa don Allah.”

Yace

“In Sha Allah za a siya Mommy.”

Haka suka fito suka kama hanya. Zulaiha ce a gaban mota yayin da su Salim suke baya, Madu yana tuki.
Duk rawar kanta saida ta nutsu domin shi Madu tsoro ma yake bata, tana ganin kamar in ta fiya kula shi
zai iya maketa kamar yanda yake make auta idan ya bashi haushi. Don haka ta tattaro duk wata
nutsuwarta, har suka isa Bichi bata ce komai ba, su Salim ne suke ta hirar su a bayan mota. Saida suka
tsaya a hanya suka sayi kajin, harda lemo da ayaba da burodi. Ledodi sun kai guda hudu taga Madu ya
rarraba kayan nan sannan ya zuba a but din motar. Gidan su Zulaiha suka fara zuwa, nan da nan ta dauki
akwatinta ta shige gida. Su Salim suka fito yayinda Madu yace

“Kuyi saura ku gaisa ku fito mu huce.”

Nan ya zauna yana jiransu a mota. A gurguje suka gaishe ta suka taso.

“Shi Madun ba zai shigo bane.”

Ta tamabaya

“Eh muna sauri ne.”

Inji Khalifa. Kafin ta kawo musu ruwan sha sun tashi, suka yi mata sallama suka huce. Suna fita ta hau zuba,
tace

“Harda su kaji naga an siya fa da kaya leda leda na ma zata nan Abbansu yace a kawo amma kinga za su
koma dashi.”

Sa’a tace

“Ai baza su bani ba, ‘yayan Rabi ai baza su so ni da arziki ba amma zan yi maganinsu daya bayan daya.”

Ta dauki waya ta kirawo Abban, bayan sun gama gaisawa tace

“Yara sun zo ai an gode Allah ya bar zumunci.”

Yace

“Amin Amin.”

Har zai ajiye waya tace

“Kai ka basu sako su kawo mana ko?”

Yace

“Ni ban basu komai ba, sai dai ko idan Mommy ce ta basu wani abu su kawo muku, ni babu abinda na
bawa kowa.”
Tace

“Au! Toh an gode, Allah ya saka da alkhairi.

Suka yi sallama suka ajiye wayar. Mamaki ya cika ta don Zulaiha tace mata an yi sayayya leda-leda. Ta sake
Kiran Zulaiha ta tambayeta inda ta tabbatar mata an yi sayayya harda su kaji, burodi, lemo da ayaba harda
ma biskit. Basu gama maida zancen ba yaran wajen Baffa Audu; wanda ‘dan wa da dan kani suke da su
Sa’an; suka shigo gidan da murnarsu kowa da biskit a hannunshi suna fadin su Yaya Madun Kano ne suka
kawo musu biskit harda lemo da burodi. Takaici ya cikata, wato ko biskit din baza’a bawa yaranta ba
saboda su ba ‘yaya bane. Ta San wannan aikin Madu ne don shi baya boye kiyayyarsa a gareta. Nan da
nan ta tura yaranta don su je su gano mata me da me aka kawo. Ai kuwa sun zo mata da labari kala-kala,
yanda suka ga an kaiwa Inna kaji da lemo harda kwai da Kuma yanda suka zauna a gidan Inna aka dafa
danwake suka ci suka huta kafin su tafi.

Sai da suka dawo Madu ya same shi a kasuwa yake tambayarsa me ya kaiwa Antin shi ne take godiya, nan
ya gaya masa bai kai mata komai ba, kaji ne da lemo Kuma Mommy ce ta bada kudi tace a saya a kaiwa
Inna Hajara kuma ita ya kaiwa da Baffa Audu.Take ya gane dalilin da ya sa Sa’an take tambaya don ya san
hali. Duk da haka ya ji dadin yanda Rabi tayiwa Inna Hajara, yana mamakin yanda bata kyashin yiwa
yanuwansa hidima ko da kuwa bata da hali.

……….

Kwanci tashi har yan Jami’a sun gama level 1. Duk wata fitna da Rabi take sa ran gani daga wajen Zulaiha
bata ganta ba don haka har ta dan fara sakewa da ita. Su kuma yaran ganin uwarsu ta sake suma suka dan
fara raga mata. Hutun session sati hudu aka basu don haka suka rankaya tare da su Khalifa Madu ya kaisu
kamar yanda Abbansu ya mayar musu da shi wajibi, indai tace za ta je hutu toh suma dole sai sunje, yakan
ce su je suyi zumunci. Bayan hutu ya kare ta tattaro kayanta ta dawo.

Nan da nan aka fara registration, kuma tun daga wannan zango biyan kudin registration dinta ya dawo
wuyan Abba. Tana karbo takardun registration ta gayawa uwarta tace mata ta nunawa Abban, don haka
da yaga an bashi ba tare da wani musu ba kawai ya fitar da kudi ya bata. Sai daga baya suka fahimci ashe
sai an nunawa mahaifinta in ya bada kudin sai Sa’an ta rike ta ce mata ta nunawa Abba ya bata ita za ta yi
amfani da wancan. Tunda ta dawo wannan hutun kuma sai Rabi ta fuskanci wasu sauye -sauye daga
wajenta. Sun kara kullewa da Saudah sosai don yanzu tare suke tafiya makaranta ko kuma idan ita Zulaiha
bata da lecture sai ta zauna ta rike mata yara a gida. Wannan bai dami Rabi ba don ko babu komai kusan
sa’anni ne, sannan kuma ta san cewa duk mace da take da yara kanana kamar na Saudan toh lallai tana
bukatar duk wani taimako da zata samu.

Bayan kwana biyu kuma da taga an dan sake da ita sai ta fito da wata sabuwar sara; sai ta ji miryoyin su a
falon musamman idan harda Ahmad a wajen sai ta sako kananan kaya ta fito, wani lokacin ta huce su ta
je kichin kamar me shan ruwa wani lokacin kuma ta zauna a dining table ta sa litattafai a gaba kamar me
karatu. Su dai ba suyi magana ba kuma in tana yi basa kulata. Riga take sakawa body hug ta roba wadda
ta dame mata jiki da kuma pencil skirt shima na roba sannan ta yi parking gashin ta a tsakiyar kai babu
dankwali; dama gata da gashi baki kirin har bayanta yana sheki. Sai da abun ya ishi Rabi sannan ta taka
mata birki.

Ranar Asabar ce don haka bata da lecture. Wajen azuhar ta fito diban abincin rana; wanda tun safe
mommy take dafawa in ta zubawa Abba na zuwa kasuwa sai ta zuba sauran a flask da rana kowa sai ya
diba; ko ba itace da girki ba ma ya zamar mata jiki haka take yi. Mommy tana zaune a falon ita kadai don
haka ta ce

“Mommy sannu da hutawa.”

Tace

“Yauwa Zulaiha.”

Har zata huce Mommy tace

“Zo nan.”

Ta juyo ta dawo wajen Mommy ta zauna a kan kujera me me mazaunin mutum daya. Mommy tace

“Kin san cewa yaran gidan nan su Khalifa ba muharramanki bane ko? Ko da yeke ma tambayar ki zan fara
yo kin san menene muharrami?”

Ta Bude bakinta cike da mamaki tace

“Mommy duka na sani.”

Tace

“Yauwa, toh irin shigar da kikayi jiya da daddare kika fito nan kika zauna a cikin su KaDa ki sake yin irin
haka. Ko ba kya jin kunyarsu ai ya kamata ki kare mutuncinki. Ki saka hijabi ko Kuma ki saka riga ta mutunci
in za ki fito cikinsu. Kin ji ko?”

Da kyar ta dago ido ta kalli Mommyn tace

“Eh.”

“Yauwa toh je ki ki ci abincin ki.’

Ta tashi jikinta ba kwari ta huce kichin din. Tun daga wannan ranar bata sake irin wannan fitowar ba, ko
ta fito ma da hijabinta kuma hucewa take yi ta tafi wajen Saudah.

………….

A kwance take a dakin baki wanda shine dakinta tunda tazo gidan. Chatting take yi a waya ta jiyo dariyarshi
dago falo. Nan da nan ta jefar da wayar ta taso ta leko ta bular mukulli dake jikin kofar dakin. Ta hangoshi
kuwa shi da auta ne a falo, kamar kullum waya ce a hannunshi yayinda auta ke kwance a kafadarshi da
alama wani abu yake nunawa auta a wayar suke ta kyalkyala dariya har ta jiyo muryarshi da tunda ta zo
gidan baifi sau a kirga ta taba jin ta ba. Kafin ta taho gidan zuwan farko sai da mahaifiyarta ta ce mata

“Duk yanda za ayi kiyi kokari ki hilato Baba karami, idan kika aureshi kin huta tunda shine babba duk
dukiyar yayan hannunshi zata dawo ya hada da wadda zai tara a Abujan. Idan abun ya yiwu ma yanzu haka
Abujan za a kaiki kin ga ba ke ba ko nima dole na kece raini.”

Tsaf ta haddace wannan karatun kuma ta zo da niyyar ta ja hankalin Baba, amma tunda ta zo gidan ma bai
fi sau a kirga ba yazo hutu. Ta so shi saboda yana burgeta yanda in ya zo yake kashe kudi kullum yana
siyowa mommy da kannenshi kayan dadi; ta tabbatar in ta aureshi kanta wannan hidimar zata dawo. Duk
yanda za ta yi don Baba ya kulata tayi amma sam baya kulata, sai dai kawai in ta gaishe shi yana amsawa.
Tayi kokari in ya zo ta ce za ta debo masa ruwa da kansa yace mata baya so, ya fi so ya je kichin da kanshi
ya diba ya sha don haka ta sha jinin jikinta. A hankali ma sai ya fice mata daga rai. Dama tunda ta zo in ta
kalleshi tare da Ahmad sai ta ce ina ma Ahmad Ummanta tace za a aura mata, saboda Ahmad din ya fi
haduwa sosai, ya fi Baba tsaho kuma ya fi shi haske, ga shi da saje irin wanda take so. Shi matsalarshi daya
baya magana, miskili ne sosai, ko ita ta shaida don tunda take gaishe shi bata taba jin amsarshi ba, za dai
taga bakinshi yayi motsi ba tare da ya kalleta ba ya cigaba da abunda yake yi. Ga shi ba shi da fara’a ko
daya don ko murmushi ba za tace ta taba ganin yana yi ba, shi indai kaji dariyarsa toh shi da mommy ne
ko auta, ko Abban ma ba sosai yake hira dashi ba. Kullum kawai yan cikin kallon waya ko laptop.

Tun da taje hutun first semester ta gayawa Ummanta ita fi son Ahmad, ta ce mata

“In ma fa kudi ne Umma duk kudin gidan suna hannun wannan Madun, don har ATM card din Abban ma
a hannun Madun suke, sai dai kawai kiji Abban yana: Madu tura dubu kaza wannan account din, Madu
turo min katin 5k, Madu ka sa nana unit din wuta, Madu kayi mana subscription na tv. Haka dai ke hatta
Antin ma fa duk abinda ta nema shi ake cewa ya bata.”

Sa’a tace

“Toh ko Madun za ki aura tunda bakya son Baban?”

“Allah ya kiyaye in auri wannan mugun, kin san halinshi kuwa? Wallahi duk cikin gidan nan babu dan rainin
hankali kamarshi ga wulakanci. Ahmad din kawai nake so kuma in Sha Allah shi zan aura.”

Kawo yanzu ta gama kamuwa da son Ahmad don haka ta yi shirin janyo hankalinshi ko ta wane hali.

Yanda ta hangoshi yana dariya ya matukar burgeta don haka take ganin za ta yi amfanin da wannan damar,
ta ma manta da kayan dake jikinta ta bude kofa ta fito tana yauki ta nufi wajen da suke tana ta faman
yauki da murmushi. Kafin ta kai wajensu taji muryar Mommy wadda take zaune a dining table tana
chatting tace

“Ke Zulai me ye haka? Inaga dai islamiyya ya kamata na mayar dake sannan ki gane da Auta da Ahmadu
ba muharramanki bane bai kamata kina fitowa wajensu a haka ba.”

Ta fada tana nuna mata jikinta.

A nan tsakiyar falon Zulaiha ta daskare saboda

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login