Showing 30001 words to 33000 words out of 196754 words
Chapter 11 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
kunya. Sai a lokacin Ahmad ya sauke wayar daga fuskarsu
shi da auta ya kalleta sau daya ya cigaba da kallon wayar. Kafin kowa yayi magana Auta yace
“Eh wallahi Mommy ki sata a islamiyyarmu hadda malamai mata za suyi mata bayani dalla-dalla.”
Ya fada yana yarfa hannuwa sannan ya faki Ido yayi mata gwalo. Da kyar ta iya hadiye malolon da ya tokare
mata makogoro ta ce
“Au.”
Ta juya ta koma dakin da ta fito ta fada kan gado ta sa kukan bakin ciki.
Mommy ta dubi Auta tace
“Ba na hanaka sa baki idan ina yiwa wani fada ba?.”
Ya sunkuyar da kai shima yayi tsamo tsamo. Ta taso daga inda take ta nufo su tana fadin
“Wai ma me kukewa dariya ne kai da Ahmad din?”
Suka kara kyalkyalcewa da dariya. Ahmad ya daga wayar ya budo ya nuna mata: status din Saudah ne ta
dora hotonsu ita da Abban ga birthday cake a gabansu, shi Abban ya turbine fuska ita koma tana masa
wanni kallon soyayya ta ‘dan kwanta a jikinshi, kasan hoton kuma an rubuta ‘Birthday with Habibi’ yace
“Kinga fa abinda ya gani Mommy shine ya ce wai Laila da Majnun”
Itama saida tayi dariyar sannan ta rankwashi kan auta tace
“Kun kyauta! Uban naku ne Majanuni.”
Ta huce ta barsu a nan.
Tun daga wannan lokacin suka sami lafiyar Zulaiha, kusan ma ta daina shiga harkar kowa kuma suma sai
hakan ya fi musu dadi.
_____
Tun da yaga kwana biyu tana yawan kwanciya ranshi ya fara baci. Ya tamabayeta ko bata da lafiya ta ce
lafiyarta kalau sannan kuma ya tambayeta ko ciki ne da ita ta ce ba shi bane. Yau din ma haka ta tashi sai
wani bin bango takeyi tana gatsine fuska. Yana kallonta ya dauke kai saboda ta fara bashi haushi. Da kanshi
ya kaita asibiti ya sa aka bata maganin fimily planning (pills), kuma ta nuna masa tana sha toh yanzun
tangadin me takeyi. Abinda yake zargi ko bata sha ba domin dama ta gaya masa bata so don ita tana son
yara da yawa, shi kuma ya gaya mata ‘yayan da yake dasu yanzu sun isheshi.
Farfesun kaza ta dafa masa da burodi ta hada shayi ta ajiye masa a kan dining table. Ya kusan gama cin
abincin ta fito ta zauna a kujerar gefenshi ta dora Ummi a kan cinyarta tace
“Ina son zuwa asibiti, zazzabi nake yi kwana biyu don yau ko makaranta bazan iya zuwa ba.”
Ya kara hade fuska sannan yace
“Kin tabbata zazzabin ne kawai ko?”
Ta fahimci me yake nufi don haka tace
“Gaskiya shine, inaga malaria ne tu da dai ina shan pills dina.”
“Toh Allah ya sauwake, idan na dawo da daddare sai mu je asibin zan kira Doctor kafin na dawo.”
Tace
“Toh.”
Bai tambayi abincin ranarshi don ya san ita ko ciwon kai taji bata yin wannan girkin sai dai kawai ta daure
tayi na safe shima shayi da burodi, haka ya huce ya tafi kasuwa. A kwance ta wuni yaran ma mai aikinta ta
barwa su ta kulle dakinta sai daga baya Zulaiha ta dawo ta karbesu kuma tayi musu abinci.
Bayan ya dawo ya ci abincin dare ta shirya suka fice suka barwa Zulaiha Nawwara da Ummi. Da yake
asibitin kudi ne kuma ya yi waya da likitan suna zuwa suka shige. Tambayoyi likitan yayi mata ta bashi
amsa. Bayan ya gama rubutunshi ya dauko takardu guda biyu na gwaji ya cike mata, ya yi waya aka turo
masa mai daukan jini. Nan ofishin ta zo ta dauki jinin ta karbi takardun ta fice. Likita ya dube su yace
“Alhaji ku dan jira a waje naga next patient kafin a kawo sakamakon na rubuta mata magani.”
Suka tashi suka fito. Jimawa kadan mai daukar jinin ta dawo da takardun a hannunta ta shige ofis din likita,
suka taso suka bi bayanta. Tana shiga ta ajiyewa likita takardun a kan tebur ta juya ta fice. Saudah da Abba
suka zauna a kujerun gaban tebur din.
Ya dauki takardun ya dan yi nazarinsu sannan ya dubi Abba yace
“Alhaji zazzabin malaria ne yake damunta sai kuma karamin ciki, inaga ba zai huce sati biyu ko uku ba.”
Abba yace
“Ciki kuma Doctor.”
“Eh Alhaji, ai babu matsala yanzu zan bata magungunan da suka dace in sha Allah za ta ji sauki.”
“Toh, toh shikenan likita.”
Suka dan yi shiru yayinda likita ya mayar da hankalinshi kan takardar da yake rubuta mata magani.
Abban ne ya karya shirun yace
“Likita tana shayarwa fa babu matsala?”
“Babu wata matsala Alhaji indai za ta daure ta dinga cin abinci mai kyau da kayan marmari. Yaron da take
shayarwa shekararsa nawa?”
Abba ya amsa
“Mace ce shekararta daya da rabi, saura kadan ma dai ta cika biyun.”
Likita ya ce
“Ah, ai ta girma ma. Hajiya za ki iya yayeta idan dai lafiyayyiya ce kuma tana cin abinci.”
Tace
“Lafiyarta kalau kuma tana cin abincinta sosai.”
Likita ya fadada murmushinsa yana kallon Abba wanda zuwa yanzu ya gama turbine fuska saboda takaici
yace
“Ai babu wata damuwa Alhaji, indai ta sha magungunan nan da na rubuta kuma ta sami abinci mai kyau
babu abinda zai samesu ita da yaran.”
Suka karbi takardar suka yi sallama da likita, sai da ya sayi magungunan a asibitin sannan suka tafi gida.
Tunda suka shiga mota babu wanda yayi magana har suka zo gida, yana tsayawa ta yi maza ta bude kofar
motar ta fice ta barshi. Ummi da Nawwara sun yi bacci har Zulaiha ta kwantar dasu a dakin baki itama ta
kwanta a tsakiyarsu tana bacci, a haka ta shiga ta samesu. Ta danna wayarta ta duba lokaci karfe 10:25pm
a hankali da sanda ta ja musu kofa ta huce dakinta. Tana shiga dakin ta kwabe kayan jikinta ta fito ta dauki
rigar bacci zata saka sai kuma zauna a gefen gadon tana rike da rigar. A haka ya turo kofar ya shigo ya
sameta, ya rufe kofar ya tsaya a bayan kofar ya dubeta ranshi a bace yace
“Kinga abinda kika janyo ko? Na gaya miki bana son haihuwar nan haka, ko zaki kara ma ki bari a kwana
biyu amma sai da kika yi fashin shan maganin nan ko?”
Da yake ranta a bace yake itama cikin fushi ta tare shi
“Na fa gaya maka bana fashi. Shikenan Allah ba zai yi yanda yaso ba sai ace nayi fashi? Maganin da ko jiya
ma kafin na kwanta sai da na sha.”
“Amman dai kina ji likita yace in dai ba kiyi fashi ba baza ki sami ciki ba ko?”
“Toh ni dai banyi wani fashi ba sai dai kuma idan zubar da cikin za a yi, wannan kuma kowa ma yasan
kafirci ne tunda dai yara ko nawa na haifa Allah ya bada abinda za’a basu.”
Ta bashi amsa a fusace. Tsaki kawai ya ja ya fice daga dakin ya rufe mata kofar da karfi. Itama ta ja tsaki ta
murgude baki tace
“Aikin banza saboda zalunci matarka ta haifi yara har shida maza ka auro ni da kiruciyata daga haihuwar
yara biyu mata duk wannan uban kudin daka tara kace wai bazan kuma ba, toh wallahi yanzu ma na fara
haihuwa don yanda aka yi maka shida nima shidan zan yi ko ma bakwai, ‘dan rainin hankali.”
Karar rufe kofar da yayi shine ya tashi Ummi daga bacci ta tsanyara ihu “Ummana.”
Kafin ta gama saka rigar ta Zulaiha ta kwankwasa kofar dakin dauke da Ummi. Ta bude suka shiga ta karbi
Ummin tana fadin
“Don Allah Zulaiha ki kwana a nan, bari na bata nono ki koma da ita ku kwana a can dakin, zan yiwa
Mommyn waya nace ta rufe kofa.”
Tace
“Toh.”
Yanda ta kwana tana kukan takaici haka shima ya kwana bai yi bacci ba yana ta juyi yana sake-sake. Tun
tuni ya riga ya yanke in ya kara aure haihuwa daya amaryar zata yi don in dai yara ne wadannan shidan
sun ishe shi, daga mata kafa yayi kawai ta kara daya. Ya riga yayi mata bayani sosai kuma ya zata ta fahimce
shi, duk da lokacin da yake mata bayanin ta so ta turje amma da ya nuna mata so yake ta dan huta ai ta
fahimce shi. Ba wai baya sonta bane ko kuma yara ne baya so amma ya za ayi ace mutum yana dosan
shekara sittin ana haifar masa yara, rayuwar da binciken masana da hadisi ya nuna sittuna au saba’una ce.
Ko su Ummi da Nawwara ma shi tausayinsu yake ji don ya san su Baba Karami kawai aka haifowa su. Nan
yayiwa kanshi alkawarin lallai daga wannan cikin ba zai sake barinta ta haihu ba, kafin ma ta je asibitin zai
yi magana da likitan tun a labour room su yi mata family planning ko kuma ma su cire mahaifar gaba daya.
Lokacin da ya kawo mata zancen tayi family planning ta yarda da zancenshi don gaskiya raino yana
matukar bata wahala don haka nan da nan da suka karbo pills ta fara Sha. Wata rana da taje gida ne sun
hira da Ya Ummu taje bata labari, nan Ya Ummu ta dafa kafadarta tace
“Ke shashashace amma wallahi, ya ma raina miki hankali. Wato tunda matarshi da yake kauna ta haifa
masa wadannan samarin ke ba sai kin haihu ba ko? Toh ina fatan kin san ko yanzu ya mutu duk yawan
dukiyarshi abinda za ki samu da kadan ya ‘dara tumunin takaba don ita da wadannan yaran za su cinye
komai tunda bashi da uwa ko uba a raye.”
Kafin dai su rabu sai da ta zige ta tas, don haka tun daga wannan lokacin ta daina shan pills din. Ko wata
uku ba ayi ba kuwa gashi yanzu har ciki ya shiga, addu’a ma takeyi Allah ya sa ‘yan biyu ne tayi sauri ta
haife masa duk kwan da yake cikinta ko yana so ko baya so.
EPISODE 8
Dayake ta san yau ba wajenta maigidan ya kwana ba babu abinda ta dafa da safe, burodi da shayi kowa
ya sha sai dai da yake akwai ‘kwai duk wanda yake so zai soyawa kansa. Ya riga ya shigo ya dubasu tun
wajen bakwai da rabi na safe don ya tabbatar Salim, Auta da Kahlifa basu makara a makaranta ba, don
haka bata sa rai zai sake shigowa ba. Tana zaune a falo ta kunna rediyo kuma tana chatting yayi sallama
ya shigo. Bayan ta amsa sallamar da yayi sai ya nufi wajen dining table, kamar yana neman wani abu da
ya tabbatar ya ajiye a wajen. Binshi kawai tayi da kallo domin dama kwana biyun nan sai ya shirya zai fito
sai ya zo ya ce ta bashi abinda ta dafa da safe bayan ba a wajenta ya kwana ba, yau kuwa ko burodin ma
basu rage ba ita da yara. Da yaga bai sami abinda yake sa rai ba sai ya juyo ya dubeta
“Yau me kuka dafa ne da safen nan? Yunwa nake ji.”
Ta bar abinda take ta dube shi
“Shayi muka sha da burodin da ka siyo mana jiya, mun kuwa cinye burodin tas gashi kyuya ta sa yau ban
yi abincin rana ba sai an jima.”
Yace
“Toh yanzu me za ki bani na ci don so nake nayi sauri na fita.”
Ta dube shi cikin mamaki tace
“Wai kwana biyu Saudan bata da lafiya ne ko bata nan, ya akayi bata yi abincin safen ba?”
Ya bata rai
“Ba nata nake son ci ba naki nake son ci, ko kuwa ni da gida na bazan ci abinci a inda nake so ba.”
“Gani nayi ai….”
Kafin ta karasa ya katse ta
“Kinga don Allah kar ki makarar dani ki tashi ko indomie ce ki dafa min bana son wani neman magana.”
Ta kalleshi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa, ta tashi ta shige kichin, shi kuma ya shige dakinshi. Nan
da nan ta dafa masa indomie harda kwai ta hada masa shayi mai kayan kamshi, sai da ya ci ya koshi sannan
ya fice ya tafi kasuwa. Da yake washegari zai kama kwananta sai ta barshi a kan lallai kuwa gobe sai ta ji
dalili don bazai yiwu ba kura da shan bugu gardi da kwace kaya.
…….
Masa da miyar taushe ta dafa ga kuma lafiyayyan kunun aya; domin tun lokacin da aka yi mata sharri a
kan asiri ta rage yin zobo, tafi gane ta yi abubuwa kamar kunun aya, madarar waken suya ko pineapple
juice. Saida ya ci ya koshi sannan ya zauna kallon labarai tare da yaranshi a falo harda Nawwara wadda
Auta ya dauko ta. Bayan yaran duk sun tashi sun tafi bacci ne ita kuma ta fito ta zauna a gefenshi, suka
fara hirarsu kamar kullum yana bata labarin kasuwa. Bayan sun dan taba hirar tace
“Abban Khalifa.”
“Uhmn.”
Ya amsa ba tare da ya daina kallon TV din ba. Tace
“Don Allah ranar girkin Umman Nawwara ka daina zuwa kana yin breakfast a nan, ka ga ai bazata ji dadi
ba ko ba komai nima lokacin da ka yi min haka na shiga damuwa sosai. Na San dai ba za ta kwana gidanka
ta kasa tashi ta girka abinci safe ba.”
“Mtseww.”
Yayi gajeren tsaki sannan ya cigaba
“Kawai kice ba za ki dinga bani abincin safen ba na san yanda zan yi.”
Tace
“Ya za ayi na ce ba zan dafa maka abinci ba kai da gidanki bayan ka yi cefanenka kuma ina zaman matarka.
Kawai dai kada aje a shiga hakki ne.”
“Toh ba za a shiga ba.”
Ya bata amsa.
Daga nan ta bar zance sai dai ta sami yanda take so don daga wanna lokacin bai sake zuwa cin abinci ranar
da ba ita ce da aiki ba.
….
Yau sati na uku kenan da ya daina kulata akan kawai tana da ciki, kuma wannan banzatarwa da yake mata
ya kaita bango don tunda ta shigo gidan bai taba yi mata haka ba. Tunda taga ya haura sati baya kulata ta
fara tunanin ko gida za ta tafi, tunda ko ta zauna a nan din ma ba kulata yake ba abincin ma da take
daurewa ta dafa kwana biyu ta daina dafawa tunda ba ci yake ba. Kullum sai dai kawai ya shigo ya huce
dakinshi ya kulle kofa in gari ya waye ya fice ya barta. Ta san cewa wasu lokutan idan bai ci abincinta ba a
wajen Rabi yake ci domin Zulaiha ta gaya mata komai harma da karin gishiri. Takaicin duniya duk ya ishe
ta, gashi wannan cikin ya zo da saukin laulayi amma fa yana sa mata kunci da bacin rai duk da ita kanta
bata gama fahimtar cewa cikin ne yake sa ta damuwa ba.
Yau ma kwananta ne kuma tana jinshi tun da wuri ya dawo amma don wulakanci har yanzu wajen awa
daya bai shigo ba. Sai wajen 10:30pm sannan ya shigo lokacin tuni yaran sun yi bacci ta kwantar dasu. A
zaune ya sameta a falon TV tana kunne duk da ba kallon take ba, saida ta kai zuciyar ta nesa sannan ta iya
bude bakinta da kyar tace
“Sannu da zuwa.”
Kallonta kawai yayi ya dauke kai ya huce ya nufi dakinsa. Cikin hanzari tana hada taku ta tare shi a bakin
kofar yana daf da rufewa, ta rike hannun kofar kalleshi a tsiwace tace
“Inada magana da kai.”
Ya kalleta sama da kasa sannan ya shige dakin ya bar mata kofar a bude, ta bishi cikin dakin ta tsaya a
gefen mudubu tana wani yatsina fuska. Sai da ya ajiye kayan dake hannunshi ya saka wayarshi a chaji ya
juya ya ganta a tsaye sannan yace
“Ina sauraronki.”
Saida ta kare masa harara sannan tace
“Ina so ne inji matsayina a gidan nan, ka barni ni ba mai miji ba ni ba marar miji ba. Ita wadda kake zuwa
take baka abincin da kasan ita da ‘yayanta sun isheka kaje ka auro ni? A yi min ciki kuma a dinga cin zarafi
na, ciki kuma na halak ba shege ba? Gaskiya se an gaya min matsayin na in kuma ba ni da wani matsayi a
gidan nan toh na koma gidanmu tunda da gatana.”
Kafin ta gama wanna bayani har ya zauna a gefen gadon yana kallonta yana takaici hade da mamaki. Sai
da yaji tayi shiru alamar tana sauraranso sannan yace
“Kin gama rashin kunyar?.”
Tayi shiru bata bashi amsa ba, ya dube ta sai wani faman zumbura baki takeyi tana jijjiga ya sake cewa
“Nace kin gama rashin kunyar?”
Ya dan saurara ko zata amsa da yaji shiru sannan yace
“Toh ba za a gaya miki matsayin naki ba duk abinda za kiyi kiyi.”
Sai da ta zabga mishi harara sannan tace
“Toh wallahi zuwa da safe idan ban ga wani sauyi ba gidanmu zan tafi tunda dai ba daga sama na fado ka
dauka ba.”
Kafin yace wani abu tayi sauri ta juya ta fice daga dakin ta maka masa kofar. Ya zauna a nan yana mamaki
domin shi bai taba sanin ta iya tsiwa hakaba. Tana fita ta huce dakinta ta shiga ta sa mukulli ta rufe kofar
don a tunaninta kada ma yace zai biyota. Haka ta kwana tana kukan takaici, ta zata ba zai iya yi mata irin
wannan cin zarafi ba amma gashi nan yau saboda kawai tana dauke da cikinsa yana nema ya juya mata
baya.
Tun asuba ta tashi ta hada masa abincin safe ta jera a dining table, ta wanka ta shiga hidimar yara. Bata
da lecture yau don haka ba wani sauri take ta gama ayyukanta ba a hankali take bi. A shirye tsaf ya fito da
jakarshi wadda kullum da ita yake fita, nan da nan Nawwara ta tashi ta tare shi da surutu itama Ummi ta
karaso tana mika mishi hannu ya dauketa, ya dauketa ya kama hannun Nawwara za su fice ta mike tsaye
sannan tace
“Ina kwana.”
Ba tare da ya kalleta ba yace
“Lafiya.”
Ya cigaba da tafiya tare da yaransa ya huce dining table ba tare da ya kalli abincin ba. Ta yi sauri ta cimmasa
tana fadin
“Ga abincinka nan.”
Bai fasa tafiyar da yake ba wadda da ba don yana rike da Nawwara ba ma da tuni ya fice daga falon yace
“Na zan ci ba.”
A tsiwace tace.
“Toh a gaskiya tunda dai bani da wani amfani a gidan nan wallahi gidanmu zan tafi in ka shirya sai ka biyo
ni da takarda ta.”
Cak ya tsaya a daidai bakin kofa ya juya, tana tsaye tana masa kallon raini. Ya bude baki zai yi magana sai
kuma ya fasa ya ja tsaki
“Mtsewwwww.”
Ya juya ya fice da yaran ya barta a nan. Sai da ya shiga yayiwa Rabi sallama sannan ya fito ya bawa Bala
megadi yaran yace ya mayar dasu idan ya rufe gate sannan ya ja motarsa ya fita.
Bayan ya fita ya barta a tsaya ta kusan minti daya a wajen tana takaici kafin ta goge hawayen dake fuskarta
ta koma daki. Nan da nan ta dauki babbar jakarta
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good