Showing 171001 words to 174000 words out of 196754 words

Chapter 58 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15369

fado daga tsakiyar rigar, da yake da wuta tar take gani. Kudine ‘yan dubu-dubu suka tarwatse a
kafarta, ta tsuguna tana murmushi da mamakin yanda Kaka ta sami wannan kudin don bata wata sana’a.
Tana kwashewa tana kirgawa

‘Dubu sittin da uku.’

Ta mike da niyyar ta mayar da kudin cikin sif din sai kuma kamar an tsikareta wani tunani ya zo mata

‘Wannan ai kudin wayata ne wanda Kamilu ya kawo.’

Ta juya kudin a hannu ta sake kare musu kallo, tabbas wannan sune kudin iphone dinta. Ba wai wata
alama ce a jikinsu da ta ganesu da ita ba amma tabbas wannan kudin nata ne. To ba ayi aikin ba kenan?
Ko kuwa kudin aikin ba yawa shine kaka ta cika mata kudi haka? Ta dora hannu a ka, ko ma dai garin yayi
kawai kaka ta samu ta bata ta zubawa mijinta a abinci. Tunani kala-kala suke shiga kanta a lokaci guda
don haka ta fara jinkanta ya chushe.
‘Saude.’

Ta jiyo Yaya Ummu tana kiranta daga waje. Kamar wadda aka tunkudo ta fito daga dakin rike da kayan
da kudin a hannu. Ta nunawa Ummu sannan tayi mata bayanin abinda take tunani, Yaya Ummu ta
kyalkyale da dariya

‘Tab! Lallai Kaka.’

Ta tabe baki tace

‘Hmm! Kana kallonta kamar bata san me duniya take ciki ba. Toh wallahi kudin nan baza su koma
hannunta ba kuma idan ta warke akwai case.’

Ta mikawa Ummu kayan tana fadin

‘Ki kai musu kayan kawai ni ba zan je ba ma wallahi.’

Ta mika mata kayan ta wuce dakin Umma ta barta a nan a tsaye. Haka Yaya Ummu ta hada kayan ta tafi
ta kai musu asibitin, daga baya ta baro Umman a can ta dawo gida.

………

Bayan Sallah da kwana uku itace ranar da ma’aikata suka koma aiki Kuma a ranar ne bayan lawyer din
Mommy ya gama waya da ita ya wuce kotu ya sake shigar da kara. Da yake ya san kan aikinsa nan da nan
aka rubuta sammaci aka bawa dan aiken kotu ya kai wa Saudah, a mota lawyer ya dauki dan aiken kotu
don ya nuna masa gidan daga kwatancen da Madu yayi masa. Suna isa suka tsaya a bakin kofa suka tura
yaro suka ce ya kirawo Saudah matar Alhaji Usman.

Ita da Yaya Ummune a gidan sai yaranta, duka su biyun sai da suka yi mamakin wannan kiran amma da
yake an hada da sunan Abban sai suka zata ko aike ya yiwo mata. Ta saka hijabinta ta bi yaron a baya,
suna fitowa kofar gidan yaron ya wuce ya barta da su. Suka matsa daga inda ta tsaya suka gaisa tana
shirin tambayesu daga ina suke dan aiken kotun yayi gyaran murya yace

‘Hajiya kece Saudah matar Alhaji Usman Usaini ko?’

‘Eh nice.’

‘Ni dan aike ne daga kotu, alkali ya aiko ni na kawo miki wannan takardar ta sammaci ranar Talata mai
zuwa in sha Allah.’

Baki bude take kallonsa, ya mika mata takardar ta mika hannu a hankali ta karba har yanzu idanunta
suna kan fuskarsa

‘Sammaci fa kace! To me nayi kuma?’

Ya mayar da hannuwansa cikin aljihun wandonsa yace

‘Abokiyar zamanki Hajiya Rabi’a ta yi kararki a kan bata mata suna da kika yi kina jifanta da Zina.’

Ta dafe kirji da hannuwanta biyu

‘Ni? Yaushe aka yi haka.’
‘Idan kun je kotu da ita za ku yiwa alkali bayani, na barki lafiya.’

Ya juya suka wuce shi da barrister suka shiga mota suka kama hanya.

Jikinta a sanyaye ta koma ta shiga gidan, kamar wadda aka jefar ta zauna a kan tabarmar da Ummu take
kai. Ta jefa mata takardar akan cinyarta, ta kama hijabinta ta goge gumin da ya karyo mata tana bin
fuskarta da kallo. Yaya Ummu ta dauki takardar ta fara warwarewa tana tambayar Saudan

‘Takardar meye wannan?’

Da kyar ta bude baki tace

‘Wai sammacice aka kawo min, wai Mommy ce ta kai ni kara.’

Ta karasa bude takardar ta duba kamar me karantawa, babu abinda ta iya ganewa saboda hankalinta
baya wajen. Ta saki takardar a gabanta tana fadin

‘Kara kuma a kotu! Toh me kika yi mata kina daga nan. Da kika bar mata gidan ma bai isheta ba sai ta yi
miki bita-da-kulli?’’

‘Nima dai haka na gani, dan aiken dai yace wai nayi mata kazafin zina. Ni wallahi na ma rasa me zance,
kotu fa! Ni ko shaida bana fatan zuwa kotu balle shari’a kuma wai ni aka kai kara.’

Yaya Ummu ta kara daukan takardar ta mayar ta ninke ta mikawa Saudan tana fadin

‘To yanzu ya za ayi, ga shi su Umma suna asibiti?’

‘Ai dazu da kika fita munyi waya ta ce min gobe za a sallamesu, tunda a yanda takardar ta nuna da
sauran kwanan bakwai kafin ranar shari’ar in suka dawo ta ji.’

‘Hakane, Allah ya kyauta. Toh ke da gaske kin mata kazafin ko kuwa sharrintane ya tashi a kanki?’

Ta tabe baki

‘Toh ya za ayi na sani sai dai idan mijinta ne ya gaya mata don ni da shi kawai mukai maganar kuma ce
masa nayi wa ya sani ko barikinta ta tafi za ta dawo a ce mu raba kwanal ba tare da wani bincike ba.
Daman kuma sai da yace min wai ban san girman kazafin zina ba, in dai bashi ba na san ban yi zancen da
kowa ba. Sai dai kuma idan shi din ne zai gaya mata.’

Ta kama haba cikin mamaki

‘To shi kuwa me zai sa yayi haka?’’

‘Oho! Ba so yake yayi min wulakanci ba?’

‘Allah ya sauwake, bari Umman ta dawo muji.’

Ranar haka Saudah ta kwana cikin wata sabuwar damuwa. Tana tunanin komawa gidanta kuma sai ta ga
wannan, ya za ayi Abba yayi mata haka? Wai me yake faruwane? Duk wannan tsananin son da yace yana
mata har ya kare kenan ko me hakan yake nufi? Amma ita kuma Mommy ribar me zata ci idan tayi
shari’a da ita, wai ta yi mata kazafin zina? Lallai matar nana bata da hankali kuma azzaluma ce.
Washe gari bayan azuhar aka sallami su Umma da Kaka suka dawo gidan, an yi mata aiki a yatsun da da
doki ya take mata don haka da kyar take tafiya a hankali. Babu wata babbar matsala sai jinyar yatsunta
sai kuma rikicin tsufa da ya zo mata gaba daya, don kafin likitan ya sallameta musu sukayi tayi da shi da
ita; ya ce doki ne ya taka ta ita kuma tace mota ce ta taka ta. Duk yanda ya so ya tuna mata ta ki yarda
don haka sai hakura yayi, ya dai cewa Umma babu komai mantuwa ce kuma shekarunta ne ya sa.

Sai da suka yi wanka suka huta sosai sannan Yaya Ummu da Saudah suka sami Umma suka yi mata
bayanin takardar sammacin da aka kawo. Tunda suka fara zancen take maimaita

‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’

Ta dan yi shiru tana binsu da kallo, Jim kadan tace

‘Wannan wace irin masifa ce ni Rakiya! Kotu fa kuka ce ‘yayan nan. Ni ban taba zuwa kotu ba ko da
shaida bana fatan naje ta amma gashi yanzu an janyo mana. Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Wannan
kishiyar taki wai wace irin hatsabibiyar mace ce ne, ke bata barki kin sami mutsuwa a dakinki ba kuma
hakan ma bai isheta ba sai ta kai ki kotu. Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Yanzu ya zamu yi da wannan
fitnar?’

Ta karkata kai cikin sanyin murya tace

‘Ya zamu yi kuwa Umma? Haka za mu je kotun mu ga abinda hali zai yi.’

Ta bita da kallo na dan lokaci

‘To ke yanzu Saude yaushe kika yi wannan maganar da ita?’

‘Ni wallahi ban taba gaya mata ba sai dai idan shi ne ya gaya mata, don da shi kawai mukayi maganar sai
Yaya Ummu da na gayawa ta waya.’

‘Ikon Allah.’

Ta dan yi jim kamar mai tunani, jimawa kadan kamar wadda ta tuno wani abu tace

‘Sai dai ko idan Balaraba ce za ta yayata don lokacin da muke zancen da Yaya Ummu a waya; ana I gobe
zan taho; ina tsaye a kicin ita kuma tana bayan gidan tana min wanke-wanke. Tabbas wannan matar za
ta aikata don gulmar da take cikinta tana da matukar yawa, duk matar da take unguwar nan ta san halin
da take ciki saboda tsabar gulma.’

‘To ai kuwa ta jika mana aiki don kin ga idan kotun shari’ar musulunci ta kai ki idan ta gamsar da alkali
kin yi mata kazafin sai an yi miki bulala kuma a ciki tara.’

Ta kalli Umma idanuwanta sun ciko da kwalla, ta sa bayan hannunta ta goge tare da sunkuyar da kai.
Wannan wace irin musiba ce kuma shi Abban yana kallo za ayi mata wannan cin zarafin? Ya barta a gida
bai biyo sawunta ba kuma yanzu an kawo mata sammaci. Ta sake share hawaye, inama ace mafarki
takeyi yanzu ta farka daga wannan mummunan bacci sai dai ga dukkan alamu ba mafarkin bane idonta
biyu. Ta rasa me zata ce don haka ta mike ba tare da ta sake cewa kowa komai ba ta shige daki ta fada
gado tasa kukan bakin cikin da tunda aka kawo takardar sammaci take tareshi.

Suna zaune can bayan la’sar sai ga Yaya Maryama; wadda take auren dan wan mahaifinsu. Ita da mijinta
suka zo daga Bauchi inda yake lecturing a jami’ar ATBU. Bai dade da samun canjin aikin ba don haka
basu dade da komawa Bauchin ba, kafin ya sami wannan aikin malamin makarantar sakandare ne shi
yasa Umman ta raina shi. Amma da yake yanzu ta ga ya fara maiko an fara yi dashi. Tare suka zo da
yaranta ‘yan mata biyu Najma wadda take da sunan Umma sai kanwarta Hafsah sai kuma kannensu
maza Saifullahi, Tahir da Kuma Abdulhakim.

Bayan sun zauna sun gama gaggaisawa Yaya Ummu ta kawowa Baban Najma ruwa da lemo a falon
Umma, sannan ta zubo masa dambun nama a dan faranti. Bayan ta ajiye suka tashi ita da Maryam suka
shige daki inda suka samu Sauda tana kukanta. Maryama ta dubi Yaya Ummu tace

‘Me ya sameta haka?’

Nana ta zauna ta bata labarin halin da ake ciki, kama bakinta tayi tana mamaki tace

‘Ke Saude to wannan wane irin rashin hankaline za ki kalli mace da aurenta kice ta je yawon bariki.’

Bata bata amsa ba don haka ta dubi Yaya Ummu tace

‘To yanzu ya za ayi?’

‘To haka dai muke jira yau saura kwana biyar muje kotun mu ga yanda za ta kaya?’

Ta kama bakinta

‘Yanzu babu wani abu da za a iya yi a kai sai an je kotun? Idan fa aka je hukunci za a yanke mata kuma
dole tayiwa alkali biyayya, bulala za ace ayi mata a gaban mutane fa sannan kuma acid tararta. Ko da
mun iya biyan tarar ai ba kimarmu bace ayi mata bulala haka a bainannasi ai babu daraja.’

‘Nima dai haka na gani, to Amma ya zamu yi.’

‘Ina mijin nata?’

Ta tafa hannuwa

‘Hmm! Wanne miji? Nan fa da kika ganta yaji ta yiwo tun kafin sallar kuma ko waya bai yi ba balle ya zo,
sai bayan sallar nan ne ma Umma take cewa za a nemo su Baba Yahaya su neme shi suji halin da ake
ciki.’

Ta kama haba

‘Yaji Kuma.’

Ta kalli Saudah da take kwance rub da ciki ta dada mata duka a baya tace

‘Da’Allah tashi malama wane irin hauka kike yi? Yaji sai kace wata ‘yar kauye? Tashi ki min bayani.’

Babu yanda zata iya haka ta tashi ta zauna ta sake fashewa da kuka. Maryaman ta harareta tace

‘Kukan me za kiyiwa mutane kin taro match?’

Suka jiyo Umma daga falo tana kiran Maryama tazo mijinta zai tafi. Ta dauko takardar sammaci ta fito da
ita a hannunta, ta mikawa Baban Najma takardar tana fadin

‘Wai Saude aka kai kotu har an kawo mata sammaci.’
‘Subhanallahi!’

Ya karbi takardar ya fara dubawa.

Umma ta bi Maryaman da harara don gani take zata tona musu asiri, ita kuwa tana kallon Umman ta
dauke idonta ta koma gefe ta zauna. Ya gama karanta takardar ya dubi Umma yace

‘Kazafi tayi mata a yanda aka nuna a takardar.’

Umma tace

‘I, haka aka ce.’

‘To ai Umma wannan baza a bari aje kotun ba, idan fa aka je za a iya yi mata bulala a gaban mutane
kuma a ci tarar ta in dai ta tabbata ta yi.’

‘To ya zamu yi tunda an ce aje, kuma idan ba aje ba ma an ce za a iya turo ‘yan sanda su tafi da mutum
ka ga ai gara muje girma da arziki ba sai an yi tonon silili ba.’

‘Hakane, amma Umma ai an ce abokiyar zamanta ce ina ga idan manya suka saka baki aka je aka bata
hakuri da kanta ma zata janye karar suyi sulhu a gida musamman ma idan aka bi ta hannun maigidan
nasu.’

‘To wane maigida, yaji fa ta yiwo nan daka ganta ko biyo sawunta bai yiwo ba.’

‘Ikon Allah, to ai duk magana ce da manya za su shiga a samu ayi sulhu. Amma gaskiya ina ganin wannan
maganar kazafin kada ma ku bari aje kotu, ku sameta duk yanda za ayi a bata hakuri ta janye karar suyi
sulhu a gida.’

Umma ta dan yi shiru kamar mai tunani, jim kadan tana jijjiga kai tace

‘Zancenka gaskiya ne, na kirawo iyayen naku su nemi maigidan sai muji ta yanda za ayi a nemi sulhun
don wallahi ka ga dazu muka dawo daga asibiti suka gaya min zancen nan na kasa nutsuwa.’

‘Ai shine kawai mafita Umma, su Baban su zo a nemo mijin nata ta koma dakinta. Kuma aje a bada
hakuri a nemi sulhu, duk yanda za ayi ma kada ku bari a kai ga zama a kotun nan gaskiya.’

‘To gamu ga Allah, hakan za ayi in sha Allahu.’

Ya mike yayiwa Umma sallama, Yaya Ummu ta rakashi dakin Kaka ya dubota sanna ya kama hanya shi da
Saifullahi da Tahir don shima zai je gidansu. Ita Maryama da ‘yan matanta da Abdulhakim mai shekaru
uku a nan za su kwana biyu sannan suje su samesu a can su koma Bauchin.

Yana fita Suka tashi gaba daya suka bar yaran a nan falon suka koma daki wajen Saudah, Yaya Ummuce
ta daka mata duka a baya tace

‘Tashi fa zakiyi tunda dai ba mu aka gayyata kotu ba, ah toh!’

Ta tashi ta zauna a kan gadon ta mike kafafunta idonta a kasa tana ta zumbura baki. Umma tace
‘Kin ji abinda Baban Najma ya ce ko? Manya za a samu aje a bata hakuri ta janye kara, shine kawai rufin
asirin mu tunda idan ma tarar ce yanda megidan naki yake tsula rashin mutunci ba biya zai yi ba kuma
nima bani da ko sisi.’

Maryama tace

‘A’a! Rashin mutuncin me kuma.’

Ta dubi Saudah tana sauraronta, a nan ta bata labarin abubuwan da suka faru har ta yo yaji. Da mamaki
a fuskarta tace

‘A’a to ai ni ban ga abinda aka yi miki na bacin rai ba a nan, ya kori matarsa kuma ya dawo da ita toh sai
me kuma?’

Yaya Ummu tace

‘Ke ba zaki gane ba, nema fa sukeyi su cuceta kiri-kiri.’

Ta daga hannuwanta kamar mai shirin yin ruku’u tana fadin

‘Nema dai take ta cuci kanta.’

Ta mayar da dubanta kan Saudah tace

‘Ke aure fa ba wasan kwaikwayo bane da zaki dinga rashin hankali kuma ki zata za a dinga binki, ko bashi
da mata ba zai biye miki ba balle da matarsa kika ganshi kice za ki daga masa hankali. To yanzu ai ko
hakurin za aje a bata ai dole sai an bi ta hannunsa tunda ko ta ki hakura shine wanda ya san yanda zai yi
da ita ta hakura.’

Umma tace

‘Hakane Kam.’

Ta mike ta da wayarta a hannu tana fadin

‘Bari na kirawo Baban naku gara su zo a san abun yi, tunda auren ma gara ta koma idan dai kuma ba so
take a nemi saki ba.’

Ta fice ta barsu a nan, Yaya Maryama ta dubi Saudan tace

‘Saude.’

Ta dago ta kalleta suka hada ido

‘Kina son ya sakeki ne ko za ki koma?’

Ta bude baki ta dubeta da mamaki

‘Zan koma mana.’

‘Yanzu kika yi magana, ki koma dakinki kiyi zamanki da yaranki. Duk matar da kika ga ta ci ribar aure har
tana juya gida da maigida to hakuri tayi da biyayya ta kwantar da kai, kai da ba wata cutarwar ake maka
ba ai sai dai kayiwa Allah godiya. Ki cire komai daga ranki ki yi zaman aure saboda Allah.’
Ta sa bayan hannunta ta share hawaye. Tana son komawa gidanta don haka ta ji dadin wannan
maganganu na Yaya Maryama, sai yanzu ta gane da Yaya Maryama ta san yaji tayo ma watakil da yanzu
ta koma dakinta. Tunda Yaya Maryama ta auri Baban Najma bata zuwa gida sosai saboda Umma bata so
aka yi wannan auren ba, musamman da yake lokacin koyarwa yake a makaranta a babur yake kawota.
Duk lokacin da tazo sai Umma ko Yaya Ummu sun san abinda suka gaya mata tayi kuka don haka sai ta
hakura da yawan zuwa gidan sai da wani kwakkwaran dalili ko kuma da Sallah. Sai dai kwanan nan da
rayuwarsu ta fara canzawa saboda zamansa lecturer, tunda yanzu har ya sayi mota. Wannan rashin zuwa
gidan ya sa basuyi wani asabo sosai da Yaya Maryaman ba, sai ta fi sabawa da Yaya Ummu wadda da ita
take shawara. Haka suka kwanan ita da Yaya Maryaman tana bata shawara a kan yanda zata zauna lafiya
a gidanta.

………

Washegari da yamma sai ga kannen Baban su Saudah sun zo saboda kiran da Umma tayi musu, basu so
zuwa ba saboda yanda bata saka su a harkar yaranta ko daya kuma kiri-kiri ta gaya musu ta bar musu
Maryama amma basu isa suyi mata iko da sauran yaran ba. Haka ta saka su a gaba da magiya da lallami
dole suka kirawo Abban Khalifa suka sanar da shi gobe za su zo su same shi da safe a gida.
EPISODE 37

Da yake ya riga ya san zai yi baki da wuri ya gama cin abincin safe, ya zauna a falo ya kunna tashar BBC
yana kallon labarai. Ya riga ya sanar da Mommy zai yi baki duk da bai sanar da ita su waye za su zo ba, ta
dai tanadi ruwa da lemo da zata kawo musu. Wajen karfe tara saura suka iso, Malam Bala ya shigo ya
sanar da shi zuwansu. Take aka shigo da su falon Mommy suka zauna. Su biyune Baba Yahaya da Baba
Sule, duka su biyun kannen mahaifinsu Saudah din ne. Babu wanda ya girmewa Abban a cikinsu sai dai
ko su zo sa’anni da Baba Yahaya. Cikin mutuntawa suka gaisa, Mommy ta shigo ta kawo musu ruwa da
lemo itama ta gaishe su sannan ta shige dakinta.

Baba Yahaya ne ya fara magana bayan yayi gyaran murya

‘Alhaji munji

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login