Showing 36001 words to 39000 words out of 196754 words

Chapter 13 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15381

ku kuke saka sunan don haka sai dai na tambayeku.”

Ta kyalkyale da dariya tace

“Ohh mu sarakan shisshigi, wannan suna kam ai da shi aka haifo yaro, Alhamdulillah.”

Saura kwana biyu suna sai ga Abbati, shine telan da yake yiwa Mommy dinki Kuma itama Saudan tunda ta
zo shi yake mata dinki tunda daman Abba ne ya kawo shi kuma in dai shi ya sai musu kaya toh Abbati ne
zai dinka. Malam Bala yayi masa iso wajen Mommy ya shiga ya zauna a falo. Bayan ya gaisheta ya mika
mata ledar dauke da kaya yace

“Ga wannan.”

Ta Bude ledar ta leka ciki atamfa ce da aka dinka, ta ajiye a kusa da Abbatin tace

“Ka yi makuwa ai na Umman Nawwara ne bari Auta ya raka ka ka kai mata.”

Ya turo mata kayan kusa da ita yana fadin

“Naki ne Hajiya ai Baba karami ne ya bayar a dinka miki kuma yace min in na dinka na zo da kaina na kawo
miki.”

Ta karba ta yiwa Abbati godiya. Yana fita ta dauko waya ta kirawo Baba, kafin su gama gaisawa tace

“Kayan menene Abbati ya kawo min?”

Yace

“Mommy dinka miki nayi saboda za a yi taro kya saka.”

Tace

“Toh Baba na gode, Allah ya kara arziki ya kawo mace ta gari.”

Suka yi sallama ta zauna tana daga kayan. Atamfa ce super me ruwan shudi da yellow kadan me kyau,
kafin ta gama warware dinkin kuma mayafi ya fado daga ciki irin mayafan nan yan Dubai ya sha sequin sai
kyalli yakeyi kuma ya shiga sosai da atmafar. Dinkin doguwar riga aka yi mata irin babbar rigar nan gashi
daga can kasan rigar sai aka dora leshi aka jere shi da duwatsu masu kyalli. Kawai sai ta ji idonta ya ciko
da kwalla, ta sa hannu ta share. Tana kara godewa Allah da ya bata Baba domin shi din daban ne a cikin
‘yaya, yana da matukar kyauta kuma ya iya zabar lokacin da zai yi kyautar. Ga shi kullum tana ransa, bata
jin yanzu a fadin duniyar nan akwai wanda yake sonta fiye da yanda Baba karami yake sonta.

Abba yana dawo bayan ya huta ta dauko kayan ta nuna masa, bayan ya sa albarka yace

“Ai Baba ya dauko halin Mai sunanshi (Hussain, mahaifin Abban), kyautar yaron nan har ta yi yawa. Kin
san Ina zaune a kasuwa naga ya turo min naira dubu ishirin na daga waya zan kirashi nashi kiran ya riga
nawa shigowa wai babu yawa turo min yayi a sayi goro da dabino saboda suna jibi. Wallahi sai da naji
kamar zan yi kwalla saboda dadi, ya san ina da kudin amma duk da haka yana jin sai ya yi, ka samu ‘dan
da yake tausayinka tausayinka kamar haka ai sai ka godewa Allah.”

Tace

“Gaskiya ne Allah ya kara arziki.

Yace

“Amin, Kinga yanzu ‘dana yayi miki kayan fitar sunan ya fanshe ni ko? Don kin san ke Auta ne kawai danki
fa a gidan nan.”

Ta tuntsire da dariya tace

“Ai duka har su Nawwara da Yan biyun nawane kai ne dai baka da ‘da sai dai kayi ta addu’a Allah ya sa
Umman Nawwara ta sake haifo maka naka ‘dan. Wannan haihuwar ma da Autana ya yi kudi ai a Saudi za
mu yo sunan.”

…..

Duk wani abinci da za’ayi a wajen suna maijego ya bawa kamar yanda ya saba yace idan an dafa Rabin ta
bayar da kula a zubo mata saboda masu zama a dakinta. Itama da ‘dan tanadinta don gashi dama watan
da ya huce Baba ya bata dubu ashirin don haka ta hada kudinta wajen dubu arba’in ta bawa kawarta Anti
Amina; wadda makociyarsu ce kuma tare suke zuwa islamiyya lokacin da Rabin tana zuwa; sannan ta hada
mata da shinkafar tuwo kwano biyu wadda za ayi masa da kuma wadda za ayi fried rice itama kwano biyu,
Ai kuwa Anti Amina ta sa aka yi lafiyayyar masa da miyar taushe da kaji ga kuma fried rice da salad da
kunun aya sannan da cake guda dari don duk abinda kudin bai kai ba ma cikawa tayi.

…..

Tun ana gobe suna gidan ya dinke, kusan gaba daya ‘yan uwan Abba da suka zo kwana a wajen Saudah
suka sauka domin har a falo wasu suka kwana. Wajen Rabi kuwa sai yan mata kadan wadanda Zulaiha ta
ja. Gari na wayewa yan uwan mai jego suka hau dora tukwane. Abinda suka yi mata a sunan Ummi shi
suka maimaita, da ta bayar da kular da za a zubo mata abinci sai aka ajiye kular a gefe suka cigaba da
kwashe abinci ana kaiwa wajen Saudah, sai da aka gama sannan wata yar’ uwarta ta dauko kular suka
zuba shinkafar rabin kula aka bawa yara suka mika mata. Azahar na yi aka hau rabon abinci, su Inna Hajara
sune a falon Rabi don haka Sa’a ta karbo abinci ta kawo musu har nan. Shinkafa ce da nama ga alala da
zobo da kuma ruwa.

Sai da aka gama rabon abincin kashi na farko sannan Anti Amina ta bugawa ya yaranta waya sai gani sukayi
ana shigo da kuloli, aka huce dasu wajen Mommy. Sai wajen la’asar sannan ‘yan unguwa suka shigo. Nan
da nan aka fara rabon abinci da kunun aya a wajen Rabi, Anti Amina da kanta ta tsaya a kan rabon abincin.
Sai da aka bawa su Inna Hajara sannan aka fara bawa bakin Mommy. Jimawa kadan sai ga Sa’a da kanta
saboda ta turo yaro a bata kunun aya an hanata. Tana zuwa Anti Amina ta debo guda takwas ta bata tace
sauran akwai bakin da za a bawa, tace a bata cake din aka ce mata ya kare. Da taga ba fuska wajen Anti
Amina dole ta hakura ta fice.

Sai bayan la’asar Mommy ta canza kaya ta sa na wajen Baba, ta kawo warwaron da ya bata da zobe ta sa
a hannun hagu, hannun dama kuma ta saka zobenta na Dubai gold wanda tun bayan haihuwar Ahmad da
suka je Hajji ita da Abba ta siya da wata siririyar sarkar hannu itama ta gold da sarka da dankunnesu. Kwalli
kawai ta saka a idonta sai Vaseline a lebenta amma ta yi fes da ita.

Bayan ta gaisa da mutanen da ke falon ta huce wajen Saudah domin su gaisa da ‘yanuwan Abban da mafiya
yawancinsu suna can.

Itada makotansu suka shiga wadanda suke kawayenta ne suka zo suna, tun daga falon suke gaisawa da
mutane har suka karasa daki wajen mejego. Suka gaggaisa wadanda suka kawo abun barka suka bata.
Suka yi mata sallama suka fito ta biyo su don tayi musu rakiya. Da yake tana bayansu a falon sai Zulaiha ta
zagayo ta rada mata a kunne

“Anti kin ga zoben a hannunta ko?.”

Ai kuwa nan da nan ta yi sauri ta sha gabansu ta dawo gefen mommy ta dubi hannunta na dama tana fadin

“Na gode Mommy, Allah ya bar zumunci.”

Mommy tace

“Amin. Allah ya raya mana.”

Suka yi mata sallama suka fice.

Kafin girki ya zagayo kanta ta gama cika fam saboda a ganinta ya raina mata hankali, ya siyo wa matarsa
gwal an ‘bige da cewa Baba ne sannan kuma ya sako mata atamfa Cote D’Ivoire a kayan fitar suna ya
sayawa matarsa Babbar super. Dama kafin a tashi daga sunan sai da kawarta Jamila ta gama zugeta a kan
atamfar, tare da cewa an yi haka ne don a fita haskawa. Sun manta a daidai lokacin da Rabin ta saka
atamfar Saudan leshi ne a jikinta wanda kudinshi zai kai wajen dubu arba’in. Ta riga ta san in ta haihu baya
yiwa Rabin sabon dinki domin a haihuwar Nawwara da Ummi kayan da ta saka itama tana da su saboda
shi kaya iri daya yake musu. Ko ba a sai mata atamfa ba sai an siya mata gold don ga kawayenta nan
mazansu ba su kaishi samu ba amma suna shigar gwala gwalai ita tana fama da fashion.

A zaune ta same shi a falo bayan ya gama cin abincin dare, rimi rimi suke hirarsu ta duniya yana mata ban
gajiya. Tace

“Wai ina alkawarin gold din da akayi min ne, ai ko tukuicin haihuwar Baffa da Inna Hajara a bani gold ring.”

Ya gyara zama yana murmushi yace

“Dadina da ke rashin hakuri.”

“Haka ma zaka ce, toh ai na ga ita Mommy ka sa Baba karami ya siyo mata nata kaga dole na tambayi
nawa ko?”

Ya tashi zaune kafin ya amsa

“Yaushe akayi haka ban sani ba?”

Ta daure fuska tace

“Ya za kace baka sani ba bayan gashi nan har ta saka gold din da sunan ‘yan biyu?”

“Toh gaskiya sai dai idan tsohon gold dinta ta saka amma babu wani gold da Baba ya siya mata.”
Da yaji shiru kuma sai ya ci gaba

“Toh Baba karami ma ko me ya siyawa uwarsa ai babu laifi ko? Tunda shima da albashinsa.”

Tace

“Amma yaushe ya fara aikin da za a ce har ya siya mata wannan gold din.”

Ya gyara zama sosai ya fuskanceta yace

“Wai ke me yake damunki ne? Kina maganar abun da babu shi har kina son kafa hujja.”

“Uhmmn.”

Sai da suka dan yi shiru sannan tace

“Toh shine kuma ka saya mata super ta fitar suna ka barni da Cote D’Ivoire ko? Bayan kuma ni na haihu.”

Kallonta kawai yake yana mamaki don kawo yanzu ya gane fitna kawai take nema. Yace

“Toh ban yi mata kayan fitar suna ba, idan kin ganta da kaya bani na siya mata ba sai dai ko Baba ko kuma
a yan uwanta. Na gaya miki ne ba don ina tsoronki ba sai don na ja miki kunne, ba zan dauki wannan aikin
banza ba. Wato nan titsiye ni kika zauna kiyi ko? Mtsewww.”

Kafin tace wani abu ya tashi ya bar mata falon. Dolenta ta hakura ta bar wannan zancen don kwata kwata
Bai bata fuska ba, ya nuna mata kamar yanda da bata saba wannan halin na gasa da Rabi ba toh kar ta
fara. Ta dai yo shiru me kawai amma tana jiran lokacin da za a yita ta kare domin ita duk abinda ta gani a
wajen Rabi tunaninta kawai Madu ne yake dauko musu kudi a kudaden Abba tunda ta san duk wani
account na Abban ya san pins da passwords din, kuma duk wani ciniki da Madun ake kullashi.
EPISODE 10



Kwanci tashi Madu ya shiga shekarar karshe a jami’a yayinda Ahmad yake bautar kasa a Kaduna. Da yake
akwai kanin Abba wato Baffa Atiku da kuma kanin Mommy Baba Mubarak duk a Kadunan sai da ya zabi
masauki ya darje. Gidan Baba Mubarak ya zaba saboda ya fi kusa da inda yake bautar kasar. Ita kuma
Zulaiha da Salim suna biye da su a level 3, Khalifa da ya kamata ace yana level 1 yanzu Amma bai fara
karatun ba saboda bai ci English a SSCE ba don haka sai computer school kawai yake zuwa kuma yana
shirye-shiryen gyara jarabawar. Shi Auta da yake akwai tazara sosai tsakaninshi da Khalifa har yanzu yana
secondary school. Ranar da Zulaiha ta gama jarrabawar 1 st semester ranar ta tafi gida, don bazata iya jira
su Madu su kaita ba don su basu gama jarrabawa ba ita kuma ana bikin kanwarta Maryam a gidansu,
wannan satin za a sata lalle.

Maryam ubansu daya da Zulaiha sai dai ita uwarta ta fita. Bayan an haifi Zulaiha da ‘yan watanni babanta
ya auri uwar maryam din, bata yi shekara hudu ba a gidan auren ya mutu. Da farko ta tafi da Maryam din
amma da ta shekara shida ya dauko ta ya dawo da ita wajen Sa’a. Haka ake zaune da dadi babu dadi har
kawo wannan lokacin da ta gama secondary school. Mahaifinsu na fafutukar samar mata admission ‘dan
wan mahaifiyarta ya fito neman aurenta yace karatun ma a bari tunda shi a Sokoto yake aiki in sun je chan
ya samar mata a UDUS. Da farko Sa’a ta so a ‘daga bikin saboda a fadarta ai Zulaiha yayartace kuma bata
yi aure ba don haka a jira sai Zulaiha ta sami miji. Dangin baban su Zulaihan ne suka ce ba zai yiwu ba
tunda ita ta tura ‘yarta karatu wannan ta sami miji ‘dan mutunci toh babu abinda za a jira. Nan da nan
kuwa aka fara shirye-shiryen bikin gashi har lokacin ya zo. Don haka Zulaiha take ta sauri ta tafi gida kar
ayi ba ita.

Ranar Laraba ta isa gidan ana gobe kamu, da yake dangin ubansu sun karbe duk wata hidimar bikin a
wajensu za a yi bata sami mutane da yawa a gidan ba domin ko kannenta duka suna can gidan kakannunsu
inda ake bikin. Bayan ta gama gaisawa da babarta tace

“Umma bari na bisu gidan bikin na gani.”

Tace

“Ba fa rawar kai za ki je kiyi tayi ba don kin san bikin kanwarki ne ba na kawarki ba.”

Tayi dariya tace

“Haba Umma ni me nace miki zanyi.”

“Na dai gaya miki. Hutun naku kuma kwana nawa ne?”

Tace

“Sati daya ne fa Umma, shima don wasu sai gobe zasu gama exams ne da kwana biyar ne ma. Ai nima da
an gama bikin ranar litinin zan koma saboda wanki suna nan na tarasu da yawa gara naje na wanke na
goge kafin a koma na rasa na zuwa makaranta.”

Umman ta kalleta tace

“Au! Toh zo nan, matso ki zauna a nan muyi maganar nan don na san in aka shiga hidimar bikin nan ba zan
sami sarari ba sai dai kawai naji kina cewa za ki tafi, zo ki zauna ki ji.”
Inda ta nuna mata kusa da ita a kan kafet din da yake tsakar dakin nan ta zauna tana kallon mahaifiyar
tata tace

“Gani Umma.”

Sai da ta yi gyaran murya ta gyara zama ta karkato ta fuskanci Zulaihan sanna ta fara magana

“Wai ya batun naki auren ne, har yanzu baki hilato Baban ba? Kin ga an fara tsallake kanki ana auren
kannenki yanzu dangi ubanku za su ‘kara sa miki ido fa.”

Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta, da Umman ta ji shirun yayi yawa tace

“Baki ce komai ba, mun riga mun yi maganar nan dake fa don ni wallahi ban taba tunanin za a kawo yanzu
babu maganar aurenki da Baba Karami ba duk wani shirin biki na gama shi.”

Ta kalli mahaifiyartata ta ce

“Hmmn! Umma toh wa ma ya kulani? Kuma fa na gaya miki shi Baban nan ba wani zuwa ma yake ba, in
ma yazo wani lokacin kafin mu hadu ya koma.”

“Duk abubuwan da na gaya miki ba kya yi kenan?”

Ta tamabayeta tana me nuna mamakinta, ta jijjiga kai tace

“Hmmmn! Umma baza ki gane ba.”

Takaici ya kama Sa’a a fusache tace

“Wane irin bazan gane ba? Zancen banza kenan, shi Baban ba namiji bane ke kuma mace? Kin dai je kin
tsaya sakarci. In ma karatun kike ji ai kin san dai babu yanda za ayi ya hanaki ko? Ke da nake so ki ‘dan
karkato da tunaninshi kadan ni zan karasa aikin daga nan amman kinje kina ta bacci.”

Ta kawar da kai tace

“Hmmn! Umma da ma Ahmad kika ce don kin ga shi na fi ganinshi kuma ina ga zai fi saukin hali mtac

Ta rike haba tana mamaki tace

“Wallahi zan bata miki rai Zulaiha, auren da ake so a yi miki shi ko gobe shine za ki tsaya jiran wani Ahmad.
Yaushe ya gama bautar kasar ya samu aiki ya zo ya aureki kina kallo dangin ubanku har sun fara yar min
da magana a kan ki, so kike sai zaman garin nan ya gagare mu ko? Don fitinar ubanki kawai ta ishe ni in
aka kai wani lokaci baki sami miji ba.”

Ta kawar da kai gefe tace

“Toh Umma zan kara dagewa, bari in je wajen bikin in na dawo ma karasa.”

Kafin ta ce wani abu ta mike tsaye ta fara gyara mayafinta. Kallonta kawai tayi tace

“Ai shikenan.”

Zulaiha ta fice ta barta nan zaune tana tunani kala-kala.
Tunda Zulaihan ta gama secondary Jibrin ya fito ya nuna yana sonta, yaro ne mai hankali kuma mahaifinshi
abokin mahaifin Zulaihan ne. Shima da karatunshi na NCE sai dai da yake bai sami aiki ba sai ya koma
kasuwa yana sayarda hatsi, wani lokacin in akayi girbi sai ya siya a hannun manoma ya taho birni ya siyar.
Amma da yeke Sa’a ta raina samunshi kuma tana ganin ga samari da take iko da su sai ta zuge Zulaihan.
Tun tana sauraronshi har ta daina kulashi, yayi naci sosai kafin ya hakura. Idan babansu yayi magana sai
Sa’a tace

“Ni bana son auren talauci, ga Ummi nan kullum chefane sai ka taimaka masa da wani mai hali ta aura da
ba ita ba har mu ma mun huta amma ka siyar da akuya ta dawo tana gogar muka danga. Yan matan nawa
su biyu kacal an sadakar da waccan wanna ma a kuma, gaskiya ba zai yiwu ba Zulaiha karatu zata yi kuma
in sha Allah zata samo mijinta daga can.”

Tun abun yana damun shi har ya gaji ya sa mata ido, shi yasa da ta ce auren Maryam a bari sai Zulaiha ta
samu miji a hada ya ce ba zai yiwu ba, da yaga ma kamar za ta yi masa wasa sai ya kaiwa Babbar yayarshi
bikin. A can aka karbi lefe aka yi duk wata hidima sai dai kawai a aiko Sa’an taje kuma da yake tana shakkar
yayar tashi haka ta hakura.




Ko da Zulaiha ta fito sai da ta biya gidansu wata kawarta dake jikin nasu gidan don su tafi cikin garin tare
amma bata sameta ba, don haka ita kadai ta kama hanya.

Ta rasa gane abinda ya sa Ummanta take so lallai sai ta auri Baba, ita ba ta son Baba, Ahmad take so. Ta
san bai san ma tana yi ba kuma bata jin zai saurareta a halin yanzu, amma gaskiya ita shi take so. Bata san
yanda akayi ta fara sonshi ba amma zuwa yanzu ta tabbatar lallai shi kadai take so da aure a duniya. Ahmad
yana matukar burgeta, komai nashi ma burgeta yakeyi. Ko a makarantar ma sai da ta bibiyeshi har
department dinsu a nan ta ji labarin ‘yan mata da yawa ma suna son shi amma ya ki kula su, duk da kin
kulasun da yake yi yayi mata dadi amma ya kara tabbatar mata da cewa tana da aiki. Gashi yanzu kuma
Umma tana ta wani zance, yanzu karshenta sai dai ta auri wa ta dinga kwana da tunanin ‘kani domin ta
ma ‘ki saurararta suyi maganar Ahmad din ita burinta kwai ta auri Baba. A wajen bikin ne take samun
labarin Jibrin din ma yayi aure ya gina gida a Kano inda ya zauna don yanzu hatsi har kudu yake kaiwa
sanna ya kawo kayan abinci irin na su ya sayar

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login