Showing 114001 words to 117000 words out of 196754 words
Chapter 39 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
kudi kawai nake tura musu amma kullum babu wani labari.”
Ya jijjiga kai ya cire tabaron dake idonsa ya rike a hannunsa
“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun. Yanzu don Allah ya za ayi ka dube ta kace ta fice maka gida, ni da ka
gaya min ka daina sonta wallahi zan zo har gidan na dauki ‘yar uwarta baza ka sake ganinta ba am….”
“Mubarak.”
Abba ya katse shi ta hanyar kama hannunsa, yace
“Wallahi ina sonta, Allah shine shaidata. Iyayen da suka haife ni duka su biyun sun rasu don haka yanzu
duk duniya wanda zan so bayan Rabi da ‘yayanta ne. Yanzu haka da kake ganina ina yawo wallahi saboda
ina kallon ‘yayan Rabi ne, sune strength dina. Wannan abu da ya faru tsautsayi ne Allah ya aiko mana
shi, ni kaina ban san me ya shiga kaina na ce mata haka ba. Kuma wallahi na zata gidan Shafa za ta tafi,
da na san za ayi haka babu inda zance Rabi ta tafi saboda Rabi ko zama tayi a gidan na dinga kallonta
kawai ya isa ya sani walwala ba sai ta yi min komai ba. Ni ai na Rabi ne kuma Rabi tawa ce har abada
kuma kai ma ka san haka.”
Ya tsagaita ya share kwalla, shima Mubarak ya zare hannunsa ya kauda kai ya share tashi kwallar yace
“Toh ina take?”
“Kullum sai na biyawa kaina wannan tambayar kamar wani azkar, ina Rabi take?”
Suka yi jugum kowa da abinda yake tunani, jimawa kadan Mubarak ya mike yace
“Ai shikenan, ni zan koma. Amma dai gaskiya ya kamata ace ayi wani abu a kai, mace babba ta bata
kamar wata kaza.”
Abban shima ya mike ya mika masa hannu yana fadin
“Wallahi kullum a kan neman Rabi nake, mu dai cigaba da addu’a in sha Allah za a ganta cikin koshin
lafiya.”
Sukayi sallama Madu ya raka Baba Mubarak mota suna mayar da zance. Kafin Madu ya dawo shagon
Abba ya goge fuskarsa, amma zuciyarshi ta kara shiga damuwa duka da daman kullum a cikin damuwar
yake. Jimawa kadan kuma yace Lalo ya zo ya kaishi gida yana so ya dan huta, duk da ya saba tafiya gida
kafin a tsahi amma yau Madu ya san maganar Mommy ce ta sa ya kara shiga damuwa. Shi din ma da bai
tafi gidan ba haka ya wuni a kasuwar zuciyarsa babu dadi.
Shi kuwa Mubarak yana barin kasuwar ya wuce gidan Shafa, da yake ya riga ya kirawo ta tun yana hanya
ta sanar dashi tana gidan. Ga mamakinsa sai ya tarar da Baraka a gidan, ta zo zumunci ne kuma dayake
tun sallah rabonta da garin tana so taje ta dubo su Madu. Aka yi masa iso ya karasa cikin falon da suke
zaune, bayan sun gaggaisa ya dubi Baraka yace
“Saboda nace zanzo shine kema kika zo?”
Ta harareshi
“Kai dai ka ji na zo ka zo, ni wajen yarana na zo gidan Bibi.”
Ya jijjiga kai
“Ni ma daga wajen Usman din nake, har yanzu babu wani labari.”
Shafa tace
“Wallahi babu wani labari, abun yana daure min kai kuma yana bani tsoro sosai. Kuma har makarantun
allo na jajje duk na bayar da sadaka ayi mana rokon Allah, ko ina sai dai kawai ace tana nan lafiya za a
ganta. Ni na kasa ganewa wallahi.”
Suka dan yi shiru, Mubarak yayi gyaran murya ya dubi Shafa yace
“Toh in Allah ya sa ta dawo ina da shawara. Kinga tunda Inna ta rasu muka zuba ‘yan haya a gidanmu a
kan Yaya ya dinga karbar kudin yana raba mana. Ni dai na manta ma shekara nawa rabonda na karbi
kaso na ban san ko ku ba ke da Rabin? Toh ni dai a sayar da gidan nan a bani kaso na itama a bata mata
sai na hada da nawa na cika na saya mata gida. In ya so in zama ya kama sai ta shiga in ba haka ba ma sai
ta saka ‘yan haya ta dinga karbar kudin da kanta tana hidimar gabanta.”
“Hakan yayi daidai ko ni ma sai na bar mata nawa tunda duk cikinmu itace bata da wani abun kirki na
kanta.”
Baraka tayi gyaran murya tace
“Amma kuwa gaskiya kun kyauta sai dai nace Allah ya bar zumunci, kuma na san Bibi za ta ji dadi. Allah
ya sa dai a ganta.”
“Amin.”
Dukansu suka amsa suka koma suka yi jugum. Sai bayan la’asar sannan Baraka ta shirya ta tafi gidan Rabi
saboda ranar aiki ce kuma tana so ta samesu a gidan. Ta tarar da Salim, Khalifa da Auta, cikin murnar su
suka taryeta a nan falon Mommy din. Bayan sun gaggaisa suka kawo mata ruwa suka kewayeta, ta bude
baki zata yi magana Auta yace
“Anti har yanzu ba a samu labarin Mommy ba ko?”
Ta kalleshi cike da tausayawa tace
“Hmn, har yanzu dai shiru munata addu’a in sha Allah za a ganta.
Kawai sai ya kifa kansa a kan cinyarta yanda yake yiwa Mommy in yana jin rigima ya sa kuka, ta dafa
kanshi dake cinyarta amma ta kasa ce masa komai. Khalifa shima da yake gefenta ya juya baya ya kifa kai
a kujera ya sa kuka, ta dubi Salim ta ga Shima yana goge hawaye. Duk yanda ta so ta daure zuciyarta sai
da hawaye suka kwace mata. Gaba dayansu suka yi shiru kowa yana share hawaye sai shesshekar kukan
Auta kawai ake ji. Suka dauki lokaci a haka sai da taga dai kukan ba zai kai su ba sannan tayi karfin hali ta
goge fuskarta ta sake shafa kan auta tace
“Ku daina kuka in sha Allah za a ganta, Mommy bazata bata ba kuma in sha Allah babu abinda ya
sameta. Mu dai ci gaba da addu’a gaba daya.”
Da kyar suka tattara nutuwarsu, tayi musu sallama, ta kamo hannun auta suka rakota mota tana cewa
“Zo shazumamun Mommy na siyo maka tsaraba.”
Ta dauko ledar cike da chocolates da biscuits kala kala ta mika masa. Sukayi sallama ta shiga bayan mota
direbanta ya ja suka kama hanyar Jigawa. Sai da suka kama hanya sosai sannan ta dauki waya ta kirawo
Ahmad, bayan sun gaggaisa tace
“Ahmadu na je wajen kannenka duk na basu kuka, muna ta jajen Mommy. Don Allah in ka koma ka kara
tausonsu musamman Auta.”
Shima murya cike da damuwa ya amsa
“Uhm, in sha Allahu Anti.”
Damuwar da yake ciki ta kara mata tata damuwar tace
“Shi ya sa bana son zuwa wallahi, amma ya zamu yi ne. In sha Allahu za a ga Mommy.”
Bata son ta ja hirar don haka ta yi masa sallama ta ajiye wayar kowa da damuwar da take ransa.
Tare suka dawo daga kasuwa da Madu da Salim kamar yanda suka saba, suka rabu a tsakar gidan ya
shige wajen Saudah su kuma suka wuce wajensu. Sai da ya kintsa sannan ya fito, da yake ya riga yayi
sallar isha’I a masallaci kafin ya shigo sai kawai ya zauna ya ci abinsa. Wake ta dafa masa da salad ta dan
watsa masa macaroni kadan da miyar hanta. Bayan ya gama cin abincin ya dawo ya zauna ya kunna TV
yana yi yana kallon waya. Tana zaune a kusa da shi itama da tata wayar a hannunta da yake yaran duk
sun yi bacci.
Whatsapp ya budo ya shiga group nasu na ‘yan kasuwa masu kawo electronics yana duba sakonni. Ya zo
kan wani video wanda tun kafin ya buda video din yaga ana ta rubuta Allah ya kiyaye wasu kuma suna
rubuta subhanallahi a kasa. Ya kai hannu ya danna video din, nan da nan ya zabura ya gyara zama ya
kara kankame wayar. Matar da take cikin video a zaune take a wani fili yansanda da ‘yan jarida sun
kewayeta ana mata tambayoyi tana amsawa
“Hajiya yaya akayi aka sace ki?”
“Toh, ni dai tasi na shiga zani wajen ‘yaruwata, mata biyu ne a bayan tasi din da na shiga muka yi uku, da
kuma wani mutum a gaba. Ban Dade da zama ba wanda yake gaba ya juyo ya feso wani abu, shikenan
ban kara gane me nake yi ba.”
“Ina suka kai ki.”
“Bude Ido kawai nayi na gan ni a wani daki tare da wasu mutum kusan ashirin, da gani su sun dade a
wajen don duk ga kashinsu nan da fitsari dakin sai wari kawai yakeyi. Kana ganinsu ka san ba sa samun
abinci yanda ya kamata.”
“Me suke yiwa mutanen da suka kama?”
“A yanda dai na sami labari wajen wata da na tarar a dakin tace tsafi sukeyi, kullum kwana biyu za a zo a
dauki mutum daya a je a yanka kuma ana kawo sababbin mutane.”
“Ya aka yi kika gudo?”
“Zuwa akayi aka dauke mu mu biyu, bayan an daure mana hannuwa aka tasa mu a gaba. Aka kai mu
wajen wani mutum cikin wani daki mai kyau sosai, muka tsaya ya kare mana kallo ya dubi masu kawo
mu yace sunyi. Sai aka tasa keyar mu aka kai mu wani dakin aka aske mana gashin kai kuma aka tube
mana kaya aka saka mana jar rigar da aka tsince ni da ita kuma aka bamu wani abu mai wari a kofi muka
shanye sannan aka tasa mu a gaba aka nufi wajen da za a yanka mu. Muna cikin tafiya kunama ta harbe
ni ai kuwa na kwalla kara na kasa daga kafar. Da masu rakiyar mu suka matso suka gani sai suka yiwa
junansu rada suka bawa mutum daya suka ce ya koma dani ya dauko wata. Haka kawai muna cikin tafiya
jiri yana ta diba na ya kalleni ya nuna min hanya yace bi nan kiyi ta gudu ko na harbeki, shine nayi ta
gudu ban san lokacin da na suma ba, ina bude ido na ganni a hannun mutanen kauyen da suka tsinceni.”
Ta share hawaye za ta sake magana video din ya kare.
A nan wayar ta subuce daga hannun Abba, ya sa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa. Saudah ta kai hannu
ta dauke wayar tana fadin
“Lafiya kake kuwa?”
Kafin ya bude fuskarshi ya amsa kawai sai ta ji ya fara numfashi da kyar, ya sauke hannunshi guda daya
ya dafe kirji shi gefen hagu. Ya fara hada wani gumi me saurin tsattsafowa duk da AC da fanka duk suna
kunne. Ta kwalawa Zulaiha kira wadda ta fito daga daki da gudu, kafin ta tsaya tace
“Kirawo Ahmad bashi da lafiya.”
Zulaiha ta fice ita kuma ta dawo gabanshi ta tsuguna tana kokarin dauke daya hannun nashi daga kan
fuskarshi tana fadin
“Abba me ya ke faruwa ne?”
Ta fara kokarin kwantar da shi ta ji kamar ya tokare a zaune. A nan Ahmad da Madu suka shigo suka
samesu. Sukayi kanshi suna tambayarta
“Me ya same shi?”
“Kawai yana zaune ya fara wannan abun.”
Suka kwantar dashi a kan kujera Madu ya zagaya ya dauki filon kujera ya saka masa. A hankali ya dauke
hannun nashi daga kan fusakar sai kuma numfashin ya fara dawowa daidai. Ahmad ya dubi Madu yace
“Juya mota mu kai shi asibiti.”
Nan da nan ya fice don juya motar. Kafin Madu ya gama juya motar numfashinsa ya dawo dai dai kuma
ya daina gumin. Ahmad yace
“Abba.”
Ya dubi Ahmad din sannan ya mike daga kwanciyar ya gyara zamansa yace
“Na’am.”
“Bari Madu ya kawo mota sai mu tafi asibiti.”
“Wai ni, ah ba sai mun je ko ina ba.”
Ya sake gyara zama yana mayar da maballan rigarsa da Ahmad ya bude masa, ya dubi Saudah yace
“Bani ruwa na sha.”
Ta tashi da sauri ta tafi kawo ruwan yayinda Madu ya shigo rike da mukullin mota. Ta dawo da ruwan ta
mika masa, Ahmad ya dube ta yace
“Wai me ya faru ne?”
“Wallahi waya kawai yake kallo sai ya saki wayar ya fara sankamewa yana numfashi da kyar.”
Ta dauki wayar da ta ajiye a kan kujera ta mikawa Ahmad, yana karba Abban ya mika masa hannu ya
bashi wayarsa yana fadin
“Abba ai gara muje likita ya duba ka, ka ga dare ne kada a zo a sami matsala cikin dare.”
“Kada ka damu babu wani abu in sha Allahu.”
Kafin suce wani abu Madu ya zaro wayarshi ya danna lambar likita, yana dauka bayan sun gaisa ya saka
ta a loud speaker sannan yayi masa bayanin halin da suka sami Abban. Likitan yace
“Yanzu ya dawo normal?”
“Eh, tunda gashi nan a zaune.”
“Zai kai minti talatin a yanayin da ya shiga.”
“Gaskiya ba zai kai ba, may be dai minti goma ko zuwa ashirin haka.”
Likita ya dan yi jim sannan yace
“In dai ya tashi lafiya toh ba wani abun damuwa bane, panic attack ya samu. May be abinda yake kallo a
wayar ya tuna masa da wani abu da yake bashi tsoro ko kuma dama anxiety da fargaba suna damunsa.
Ka rabu da shi sai da safe sai ka lallabashi ku zo na duba shi ko kuma ni nazo gidan.”
“Ok. Toh babu wani magani da za a bashi?”
“A’ah, in sha Allah baya bukata. Ku dai yi kokari ya sami bacci sannan kuma ya dinga shan ruwa sosai a
kai a kai.
Suka yi sallama ya ajiye wayar, kpafin yace wani abu Abban ya dube shi yace
“Allah ya sauwake, panic attack din ne ma amma yanzu na dawo normal.”
Dukansu suka yi shiru na dan lokaci, Abban ne ya mike ya nufi kofa yana fadin
“Ku zo muje.”
Suka bishi a baya suka bar Saudah da Zulaiha a nan zaune suna mamaki.
Falon Mommy ya nufa, yana shiga su Auta suka taso suna yi masa sannu. Ya amsa yana fadin
“Ba komai ma, gani lafiyata kalau.”
Ya wuce dakinshi dake nan wajen Ahmad da Madu suka bi bayanshi. Yana shiga ya zauna a kan kujerar
dake dakin yayinda Ahmad ya zauna a kan daddumar dake tsakar dakin shi kuma Madu ya juya da sauri
ya daukowa Abban ruwan roba a kicin. Sai da ya bude sannan ya mika masa yace
“Abba ga ruwa.”
Ya karba ya kurba ya mika masa ya rufe ya ajiye shima ya zauna kusa da Ahmad. Cikin damuwa Abban ya
dube su yace
“Yanzu don Allah baku sami wani labari ba na inda za a iya samun Mommy, shirun yayi yawa. Sama da
kwana talatin fa.”
Ahmad yace
“Wallahi Abba bamu samu ba, da mun samu ai da za kaji.”
“Babu inda ban duba ba, ka ga kawarta Salma ma da kaina na sake zuwa gidan last week amma ko daga
kawayensu basu ji labarinta ba. Ga ‘yan sanda ma sun kasa samota, suma last week da naje har cewa
DPO nayi in dai suka samo Mommy zan basu miliyan guda amma har yanzu shiru sai dai yayi ta kirana
yana damuna da tambayoyi don nace suna aiki.”
Nan Madu ya tashi ya fice daga dakin ba tare da yace komai ba. Ahmad yace
“Toh wallahi Abba muma dai bamu ji komai ba kuma muna ta kokari.”
Ya mayar da kanshi ya kwantar a jikin kujerar suka yi shiru. Haka Madu yake, tunda Mommy ta bar gidan
nan baya yarda suyi maganarta da Abba. Babu wanda yakai Madu jin haushinsa tunda abun nan ya faru,
ko da yake shima yanzu haushin kan nasa yake ji. Gaba daya ya kasa nutsuwa, ana kara dadewa ba’a
ganta ba yana kara shiga damuwa. Ahmad ne ya katse masa tunani yace
“Abba ko a nan za ka kwana a canza bedsheet din.”
Yace
“A’ah, a can zan kwana. Babu damuwa in sha Allahu za a ganta kwanan nan.”
Ya mike ya fito Ahmad din yana biye dashi, suka fito falon ya dubi Salim da yake zaune da sauran ‘yan
uwan yace
“Ina Muhammadu?”
“Yana daki.”
Yayi musu sai da safe ya wuce wajen Saudah. Ko zama Ahmad bai yi a wajensu ba ya wuce daki ya sami
Madu a kwance a kan katifa, ya doki kafarsa yace
“Kana da damuwa wallahi.”
A fusace ya tashi zaune yace
“Toh duk ba shi ya jawo wa mutane ba zai zo yayi wani panicking, mun san inda Mommyn take zai
ganmu haka?”
Ahmad ya harare shi yace
“Sai ka maida hankali kai kuma ka sami anger attack ai tunda baza ka yi hakuri mu cigaba da addu’a ba.”
Ya koma ya kwanta ba tare da yace komai ba, shi kuma Ahmad ya fice daga dakin ya koma wajen su
Salim. Gaba dayansu haka suka kwana zuciyoyinsu babu dadi, dama kuma tunda aka ce ba a ga Mommy
ba duk lokacin da akayi zancenta toh sai sun kwana kuka sai a hankali suke dan warwarewa. Shima
Abban da ya riga ya san ko ya kwanta ba zai iya baccin ba sai kawai yayi alwala ya tada Sallah, bai kwanta
ba har sai wajen uku da rabi na dare. Da kyar ya tashi sallar asuba, yana dawowa daga masallaci ya koma
ya kwanta. Karfe bakwai da rabi Saudah ta tashe shi don yanzu tunda aka rasa Rabi shi yake kai su
Nawwara makaranta, ya kasa cewa yaran su kai su su kuma suna kallonshi basu ce komai ba. Haka ya
tashi da kyar idon sa yana yaji saboda bacci. Yana dawowa daga kaisu ya koma ya kwanta, sai wajen
goma saura sannan ya shirya suka wuce kasuwa shi da Salim da Madu.
Suna isa kasuwa suka ajiye Madu, Salim ya karbi tukin suka wuce gidan Baffa.
Tunda Mommy ta tafi haka yake yi, idan ya kwana da damuwar kewarta to sai ya je wajen Baffa, domin a
wajen Baffa ne kawai yake samun natsuwa da kuma maganganu na kwarin gwiwa.
Suna shiga suka tarar Baffa ya shirya tsaf zai tafi Bichi, bayan sun gaisa yake wa Abba bayani
“Ka san Gwani Hadi ko, abokinmu ni da mahaifinku.”
“Eh, na sanshi Baffa, wani abu ya same shi ne?”
“Mai dakinshi ce ta rasu jiya shine zan je masa ta’ziyya da ma abubuwa da yawa da suka faru a Bichin
ban je ba duk sai na je. Ga Kabiru nan a waje yaron makocina ne da yake direban tasi ne in ya kai ni
muka dawo sai na sallame shi.”
Abba yace
“Baffa ai sai a sallameshi mu je tare, kuma ga yara Baffa nace ka dinga waya ka ga Ahmad, Madu, da
Salim duk suna tuki ai za a samu daya da zai kai ka Bichi.”
“Na san da su Usamanu, suyi ta karatunsu shi kuma wannan ya sami na cefane ko? Ai duk daya ne.”
Suka sallami Baba Yalwa suka fito, Abba ya kawo naira dubu ya bawa Kabiru yace ya sha mai. Tun kafin
suyi nisa ya kirawo Saudah ya sanar da ita ya tafi Bichi. Haka al’adarshi take in dai kasuwa ya fita toh in
ta kama zai yi wata tafiya mai dan nisa toh sai ya gayawa matansa, wani lokacin kuma sai ya gayawa
Ahmad kawai.
Gidan gaisuwa suka fara tsayawa, a nan Baffa ya sami abokansu na kuruciya wadanda sukayi saura. Suka
zauna suna jajen mutuwa da kuma tuno baya. Bayan Abba yayi gaisuwa ya sanar da Baffa zasu je ya
gaisa da Inna Hajara, suka kama hanya shi da Salim.
A tsakar gida ta taryesu aka shimfida musu tabarma, ta sa aka damo musu nono da fura suka zauna suna
sha suna hira. Yana nan zaune Sa’a ta shigo gidan ta zo wajen Inna. Bayan ta gama gaisawa da Inna
shima Abba ta gaishe shi sannan
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good