Showing 63001 words to 66000 words out of 196754 words
Chapter 22 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
saura don haka sallar
azahar kawai yayi ya kirawo mommy a waya.
A zaune take a dining table tana cin dafaffiyar gyada yayinda Zulaiha take kicin tana wanke kwanukan da
suka ci abinci. Wayarta da take can kan kujera tayi waka don haka ta tashi ta dauka, sai da tayi murmushi
da taga Baba ne sannan ta dawo inda tashi ta zauna. Tana daga wayar bayan ta amsa sallamarshi tace
“Kardai sai yanzu ka sauka?”
Yace
“A’a Mommy tun dazu na sauka, wajen Barrister na tsaya sai yanzu na shigo gida.”
“Toh sannunka da hanya, iyalan barrister suna lafiya ko?”
A gaggauce ya bata amsa
“Lafiya kalau Mommy, kin san kuwa me Abba yayi?”
Sai da taji wani irin tana tunanin me kuma yayi tace
“Me yayi Baba?”
“Mommy gida fa ya bani kyauta a gidajenshi na Maitama.”
Ta sa hannu ta rufe bakinta da mamaki tace
“Kai Baba, gida fa kace? Amma gaskiya Abba ya burge ka, kai Ma Sha Allahu. Toh kyauta ya baka ko dai
kawai ka zauna kafin kayi naka?”
“Wallahi kyauta ya bani Mommy?”
“Kai Baba?”
“Allah Mommy harma ya cewa Barrister a canza takardun a mayar sunana.”
“Lallai Amma gaskiya na ji dadi, ai kuwa bari ya shigo na yi masa godiya.”
“Eh wallahi Mommy, Nima yanzu zan kirashi don ce min kawai yayi na nemi Barrister ni na zata ma sako
zan karbar masa.”
Su kayi sallama tana ta murna da mamaki. Ta san Abba mutum ne mai tsananin son ‘yayanshi amma bata
taba zaton zai yi wa Baba wannan kyautar ba musamman da yake kwanan nan ya bashi mota. Sai da ta ji
motsin Zulaiha ta fito daga kichin sannan ta tuna akwai mutum a kichin din da yake kujerar da take zaune
ta bawa kichin din baya kuma inda Zulaihan ke wanke wanke can cikin kichin din ne.
“Mommy na gama wanke-wanken.”
Ta juyo ta amsa ta
“Toh sannu Zulaiha.”
Ta amsa ta huce dakinta. Jimawa kadan Mommy ta tashi ta kwashe bawon gyadar ta zuba a shara sanna
ta dawo ta huce dakinta. Baccin rana take son yi amma saboda murna ta kasa yi don haka sai ta kirawo
Yaya Shafa take bata labarin kyautar gidan da Abba yayiwa Baba. Tana shigewa dakin Zulaiha ta fito ta fice
ta nufi wajen Saudah. Duk da ranar aiki ce amma saboda an kusa fara jarrabawar yawancin malaman sun
gama lecture shi ya sa yau basu je makaranta ba ita da Zulaihan. A falo ta same ta ta baza litattafai a dinga
table tana karatu, bayan ta amsa sallamarta tace
“Ina mutane na.”
Tace
“Suna bacci, shi yasa na ke sauri na sami abinda na samu kafin su tashi.”
“Yan biyu kyautar Allah kenan.”
Ta ja kujerar ta zauna a kusa da Saudan ta ce
“Anti kin san Abba yayiwa Baba kyautar gida a Abuja?”
Sai da ta dan razana sannan ta ce
“Ke Zulaiha, gida ko dai mota?”
Ta tabe baki sannan ta bata amsa
“Wace mota tsohon zance, ba yau Baban ya koma Abuja ba?”
“Eh, ai nima shi na gani.”
“Toh yana isa aka bashi mukullan gidan kuma kyauta Abba ya bashi.”
“Uhhmm! Abban daman yana da gida a Abuja ne?”
“Nima dai ban sani ba, Amma kin san zai iya siya ya bashi ko?”
“Hakane.”
Ta fada a sanyaye sannan ta mayar da hankalinta ta ci gaba da karatun ta. Jimawa kadan Zulaihan ta mike
tace
“Hmm bari naje nima na fara karatu tun kafin yunwar azumi ta sa na kasa ganewa.”
Ta fice ta barta a nan. Tana fita kuwa ta mike tsaye tana zancen zuci
‘gida fa? Ya za ayi ya bashi gida kuma a Abuja? Bayan kwanan nan ya bashi mota. Haka zai ta rabon
kadarorinshi kenan kafin a zo kan su Nawwara sun kare ko kuma ya muta bai basu komai ba. Ai kuwa dole
a ba wa yaranta itama gida ko da kuwa a Kano ne. In hakane tunda an bawa babban ‘dan Rabi gida ai kuwa
itama dole a bawa Nawwara, idan kuma ma maza ake kaiwa toh dole a bawa Baffa Karami.’
Abin da ma yake kara daure mata Kai shine, ita bata ma taba sanin yana da gida a Abuja ba tunda ta
aureshi sai dai da yake Zulaihan ta ce mata watakil yanzu aka siya gidan.
“Mtsewww”
A fili ta ja tsaki da ta tuna yau ta fita daga girki don haka sai bayan kwana biyu zai dawo, gashi kuma bata
son fara maganar in ba a wajenta zai kwana ba don yanzu ya tsiri da ta fara magana in baya son ji sai ya
fice ya barta don haka gara ta hakura sai kwana ya zo kanta in ya rufe kofa sai ayi ta ta kare.
Haka ya shigo ya sameta tana ta bata rai, da yake ya riga ya san babu wani abu da ya hadasu shi ma sai ya
shareta. Yana tunanin duk cikin shirin jarabawa ne don har hana kanta bacci take ta zauna karatu, shi yasa
ya rabu da ita. Dakinsa ya shiga yayi abinda zai yi ya fito ya sameta a falon yace
“Su Nawwara har sun kwanta.”
Tace
“Uhm.”
“Toh nima bari na je na kwanta, Allah ya bamu alkhairi. Ki taso ki rufe kofa.”
Ta bi bayansa ta rufe kofar bayan ya fita. Ya huce wajen Mommy.
Bayan ya gama duk abinda zai yi da yake ba shi yake kulle gidan ba Ahamd ne sai kawai ya shige daki. Sai
da ta gama nata shirin baccin sannan ta same shi a daki yana zaune a kan dadduma inda ya idar da shafa’I
da witri. A gabanshi ta zauna kamar wadda za ta dauki karatu tana kallonshi. Ya dubeta yayi murmushi
yace
“Yau kuma na zama kallo-kallo kenan?”
Tayi dariya ta sunkuyar da kai tace
“Furfurar gemunka nake kirgawa.”
Shima dariyar yayi yace
“Ki gama ni kuma sai na ‘kirga ta kanki.”
Suka kyalkyale da dariya gaba daya. Tace
“Baba yace min ka masa kyautar gida.”
Yace
“Eh, toh kinga ai kwanannan zai angwace.
“An gode, Allah ya kara arziki da rufin asiri Allah ya ja kwana. Allah ya sa su ji tausayinka fiye da yanda kake
tausayinsu.”
“Amin ya Allah. Ce minyayi a nan zai ajiye matar ya dinga tafiya Abuja aiki, ai kinga gara a bashi a can ya
zauna a nutse in an kwana biyu sa dinga zuwa.”
“Hakane, Allah ya kara arziki.”
Yana matukar jin dadin yanda take yawan yi masa addu’a Allah ya kara arziki Allah ya ja kwana, musamman
idan ya ji tace Allah ya sa su ji tausayinka fiye da yanda kake tausayinsu. Yana da yakinin bata cikin matan
da suke haduwa da ‘yayansu su juya wa miji baya. Nan suka yi ta hirarrakinsu kafin daga baya ya duba
waya yaga ana sanarwa an ga watan azumi. Ya dube ta yace
“Kin yi mana abincin sahur ko.”
“Eh, akwai dumamen tuwo duka shi zamu ci.
Yace
“Yauwa.”
Tunda Zulaiha ta ji labarin gidan nan hankalinta ya kara tashi, da yanzu ita za a saka a gidan. Ta so matuka
ace an dauketa daga Bichi a gaban kowa a kaita Abuja. Ga shi tana ji tana gani damar tana neman ta kubce
mata. Tana fitowa daga wajen Saudah ta shiga daki ta dauko wayarta ta kira Ummanta. Bayan ta gaisheta
tace
“Ya aka yi?”
“Uhmmn Umma kin ji wai an bawa Baba Karami gida a Abuja, shine na bugo in gaya miki.”
“Mtseww, toh yanzu me kike so nace miki? An baki kayan aiki kin je kin zubar, ai sai ki zauna kina kallo ya
kai wata Abujar.”
Cikin rawar murya tace
“Umma toh a sake yin kwallin mana Allah zan yi amfani da shi.”
“Toh ina naga kudi, na ce ki san abinda za kicewa Abban an ce ku siya a makarantar kuma kin kasa.”
“Hmmn. Umma level dinmu fa daya da Salim, ko na ce a bani wani abu Madu za a ce ya bani kuma in ya
gane karya nake ban san ya zanyi ba.”
“Ai shike nan sai ki yi addua Allah ya fito miki da naki mijin, na dai gaya miki idan ba wani tsayayye kika
samu kada ki zo don Habu yana nan yana jiranki da shi da ubanki.”
Suka yi sallama suka ajiye wayar. Sai da Sa’a ta share kwalla saboda takaici, dama ta riga ta san duk abinda
Yaya ya samo a kan Rabi yake karewa ita da ‘yayanta. Haka ta kwana tana lissafi dukiyar da bata da gado.
Ita kuwa Zulaiha damuwa kawai ta kara shiga musamman da ta kara jaddada mata in ta zo Habu zata aura.
Bata jin dadin zaman gidan sosai amma yanzu dole ta sa ta jima bata je gidan ba duk da yanda ta takura.
Ga shi ta rasa yanda za ayi ta sami kudi ta bawa Umma a sake musu aiki.
Ranar da aka tashi da azumi ya koma dakin Saudah, ko ‘daya bata nuna masa wata damuwa ba. Tun da
safe kafin ya fita ya sanar da ita ba a waje zai sha ruwa ba don haka shi kadai za ta yiwa abincin shan ruwa.
Da yake Zulaiha ma bata da abin yi a makaranta bata je ba don haka ita ta taimaka mata suka shirya abincin
shan ruwa. Kosai da kunun tamba tayi sai kuma farfesun kaza ga kuma fruit salad wanda babu suga.
Sannan tayi tuwon alkama wanda in yaci sai kuma ta dumama masa don sahur. Nan da nan suka jere
komai a kan tebur inda Zulaiha ta dauki nata ta shige dakin baki don a nan zata Sha ruwa. Da ya gama cin
abinci ya tafi masallaci sallar isha’I sai ya shigo da bako, yaronsa ne a kasuwa Muntari ya zo gaishe shi sai
suka shigo tare. Ya kirawo Saudah suka gaisa ita kuma ta turo Zulaiha ta kawo masa lemo da ruwa. Nan ya
zauna sukayi ta hira da Abba sai wajen goman dare sannan ya tafi. Kafin nan kuwa yara duk sun yi bacci ta
kwantar dasu tana dakinshi tana jiranshi. Sai wajen Sha daya da rabi ya shiga dakin bayan ya yi sallama da
su Mommy ya kulle gidan.
A dakin ya sameta a kashingide a kan gado tana duba wayarta, yayi sallama ta amsa sannan tayi masa
sannu da zuwa. Sai da ya gama abinda zai yi ya zo ya zauna a gefen gadon yana duba waya tace
“Ni kuwa wai daman kana da gida a Abuja?.”
Yayi mamakin tambayar tata amma sai yayi dariya yace
“Eh, akwai matsala ne.”
“Babu wata matsala, na dai yi mamaki da ban taba sani ba.”
“Toh dolene sai kin san duk abinda na mallaka?”
Ya bata amsa yana dariya.
“A’ah. Amma ina laifi ma idan na sani?”
“Toh ai yanzu kin sani ko?”
Ta yi shiru don haka ya cigaba da abinda yake yi a waya sai da ta dan nisa sannan tace
“Shine wanda ka bawa Baba Karami?”
Yayi matukar mamakin jin wannan tambayar, sai dai da yake ya dade yana zargin tana sa masa ido bai yi
mamaki ba. Yace
“Eh, shine.”
“Allah sarki, toh ina na Baffa Karami?”
“Wane Baffan, wannan da yake koyon tafiya?”
Ya kyalkyale da dariya.
Ta tsahi zaune ta ajiye wayarta a kan durowar gadon ta dube shi tace
“Toh ai tunda a ‘yan dakinsu ka bawa babbansu ai nan ma sai ka bawa Nawwara in ba haka ba kuma ka
bawa Baffa tunda shi ne namiji.”
Ya dubeta da mamaki a fuskarshi ya kara bata rai sannan yace mata
“Idan na bawa Rabi sai ki tambaye ni ina naki, amma ‘yaya duka nawa ne don haka duk wanda ya dace na
bawa wani abu ni zan bashi ba sai kin gaya min ba. Wai ke Anya kuwa za ki iya bari na mutu kafin ki raba
gadona.”
“Daga na yi magana sai kace zan raba gado, na ga dai ko a addini babu kyau mutum ya fifita wasu ‘yayanshi
a kan wasu suma ai adalci ake yi.”
“Toh bani da adalcin kin ji?”
“Ni ba haka nace ba, gaskiya na fada. Kwanan nan ka bashi mota kuma yanzu ka zo ka kara masa da gida
su wadannan da suke kanana ko tayar keke baka basu ba.”
“Mtseww, toh ba zan basu ba kin ji, duk abinda za kiyi ki je kiyi.”
Kafin ta ce wani abu ya juya mata baya ya kwanta yana fadin
“In kin gama ki kashe min fitila.”
Tana man zaune ta na mita a ranta sai munsharinss ta jiyo. Takaici ya kara kamata, wato yanzu har ta kai
matsayin da zai fara yi mata wulakanci yana gaya mata maganganu yanda ya ga dama. Ko da ta tashi kashe
fitilar sai kawai tayi ficewarta tana fadi a ranta ai kuwa lallai zai ga abinda za ta yi. Haka ta kwana tana
tunanin yanda za tayi da shi don tabbas ta gaji da wannan rabon dukiyar da ake yi babu ita babu yaranta.
Ko da ya tashi sahur kin tashi tayi, da kanshi ya tafi dakinta don ya taso ta ya ganta a kwance a tsakiyar
yara don haka sai kawai ya juya ya fice ya barta. Da kanshi ya dumama miyar kukar da ta saka a fridge da
yake tuwon yana flask kawai sai ya ci abinsa. Sai da safe sanna suka hadu, nan ma da yaga Taki kallonsa
ya san fitna take so don haka ya fita harkarta. Tunda ya fita take tunanin wanda ta sani da za ta sa yayi
masa magana amma ta rasa, sai kawai ta dauki waya ta kira kawarta Zahra. A makaranta suka hadu da
Zahra da yake yanayin da suke ciki a gidajensu ya zo daya sai suka yi kawance. Sai dai ita Zahra mijin nata
ya rasu kuma a yanda take siffantashi ma zai girmi Abban. A fadarta itama sai bayan rasuwar mijin ta gane
bata da komai domin yana rasuwa babban danshi ya kame duk wata dukiya tashi ko rabon gado ma ba
komai suka fito dashi aka raba ba, gashi nan yanzu dai dai da kudin makarantar yaranta sai ta gayawa
uwargidan itace take sawa manyan yaran suna biyawa nata ‘yayan. Wanna shi yasa itama Saudah ta tashi
tsaye don baza ta yarda da wannan cutar ba. Bayan ta labarta mata abinda yafaru tace
“Hmmm! Ai dama na gaya miki haka suke yi, sai a faro rabo ta sama kafin a zo kan yaranki babu sauran
abun bayarwa. Ki sami wani abokinsa wanda kika san yana dan sauraronshi kiyi masa bayani, watakila ki
samu ya canza ko bai baki na yaranki ba dai ya daina wannan rabon da ya fara.”
Tace
“Haka za a yi. In sha Allah kuwa za ki ji yanda ta kaya.
Suna ajiye waya ta lalubo lambar Alhaji Fatihu a wayarta, tun yana raka Abban zance ya bata lambar da
kanshi lokacin ana hidimar bikin. Tana kira kuwa ya daga, bayan sun gama gaisawa tace
“Karar abokin ka na kawo don na ga yana sauraronka sosai.”
“Toh me mukayi kuma?” Ya fada yana dariya.
“Duk abinda ya samu sai dai ya bawa su Baba karami, amma su su Nawwara ba zai basu ba. In nayi magana
sai yace wai ai Baban ne zai kula da su Nawwaran.”
“Eh gaskiya bai kyauta ba, ai daidai ya kamata ya raba.”
“Toh, kwanan nan ya dauki mota ya bawa Baba Karami kuma ga shi nan yanzu ya bashi gida a Abuja.”
“A Abuja kuma, lallai ne. Toh amma ai aurenshi naji ana magana ko? Kin ga kuwa ai yana bukatar gida.”
“Toh ai nima bance kar ya bashi ba amma sai sai ya bawa Nawwara ko kuma in Maza yake bawa ya bawa
Baffa Karami ko?”
“Haka ne, toh kinga in sha Allahu zan same shi. Za ki ga sauyi in Sha Allah.”
Sukayi sallama suka ajiye waya ta barshi da mamaki. Bai taba sanin Abba yana da gida a Abuja ba sai yanzu
da ta fada, shi kuma Abban yayi shiru ne saboda ya kula kamar gasa Fatihun yake yi dashi sannan kuma
kusan komai yake da shi ya sani don haka yana so ya boye masa wasu abubuwan ko don gudun hassada.
Yana ajiye wayar ya kira Abba, bayan sun gama gaisawa yace
“Mutumina ina son ganinka ne fa, kana kasuwa yanzu?”
“Ina nan amma yanzu zan tashi, don haka ka bari tunda wajenka kan hanya ne sai na tsaya Allah ya sa dai
ba zai dau lokaci ba don ka ga ni yanzu dole ta sa a gida nake shan ruwa.”
“Hakane, Allah ya kara lafiya. In sha Allah minti uku ma ya isa.”
Da yake shi da Madu suka je kasuwa tare suka kama hanya Madun yana tukawa Abban yana zaune a gaban
motar suna hira.
“Kai kowa yana karatun jarrabawa banda kai, ina jin hutu zan baka daga yau har zuwa a gama jarrabawar.”
Yayi dariya yace
“Abba ai ina karatu, ka ga fa litattafai na a bayan mota duk inda na sami waje karatu nake yi.”
“Za dai a baka hutun saboda ka san bamu saba faduwa jarrabawa ba ko, in ka fadi Mommy cewa za tayi
ni ne da laifi tayi tayi mana fada.”
Gaba dayansu sukayi dariya. Da suka karasa Abba ya fito daga mota Madu yana biye dashi. Bayan ya gaishe
da Alhaji Fatihu ya mikawa Abba wayarsa da ya bari a gaban motar yace
“Abba ga wayarka kada a kiraka, bari na zauna na jiraka a motar.”
“Toh.”
Alhaji Fatihu ya dubi Abba yace
“Mutumina dole ka dinga walwala wallahi, baka da matsala da yaranka yanda kake so haka suke yi.”
Yayi murmushi yace
“Toh Alhamdulillah, gaskiya uwarsu bata yi min mugunta ba kuma sannan Allah ya amsa addu’a ta da ta
iyaye da muke ta fatan zuri’a ta gari.”
“Hakane kam, ka san ni yaran har yanzu sai a hankali. Babban ya girmewa Madu Amma duk shiriritarsu
suka sa a gaba, ga shi iyayen kowa zuga nata yaran kawai takeyi wai kar ayi musu wayo.”
“Allah ya sauwake, jajircewa za ka yi da addu’a da sadaka kana yi kana nuna musu abinda ya kamata, babu
abinda ya fi karfin Allah a hankali za ka ga komai ya zama daidai. Kuma ka dinga jansu a jiki, ka san in ba
sa tare da kai basu ma san me za su yi su taimaka maka ba.”
“Hakane kam.”
Suka dan yi jim sannan Fatihu yace
“Yauwa, kararka aka kawo shi yasa nake nemanka.”
Yayi dariya yace
“Toh ai gani wa ye ya kawo karar?”
“Saudah Amarya mana.”
Sosai mamaki ya bayyana a fuskarshi yace
“Toh me kuma nayi da aka kasa gaya min aka gaya maka?”
“Ta ce kana ta rabon kadarori, amma baka bawa yaranta komai ba kuma sune kanana. Tace baka
tausayinsu manyan kawai kake tausayi.”
“Ita Saudan ce ta gaya maka haka?”
“Kwarai kuwa.”
Shiru Abban yayi saboda ya ma rasa me zaice don takaici. Shi tunda yake matarsa bata taba kai kararsa ba
sai sau daya, kuma da ta tashi sai ta kai wajen wanda yake ubane a wajensa. Duk wani abokin shi ta sanshi
amma baya ma jin tana da lambarsu, amma ita wannan ya rasa wanda ya gaya mata aboki ake kaiwa karar
miji, abokin ma na kasuwa.
“Mtseww, ni da na san wannan maganar ce ma wallahi da bazan zo ba wallahi, kada ka kara sauraronta ta
bata maka lokaci.”
Yayi dariya
“Ni bani da matsala, amma dai ka duba abokina. Tace ka bawa Baba mota, ko wata bata yi ba ka bashi
gida a Abuja.”
“Mtseww.”
Ya mike tsaye sannan ya ci gaba
“Na
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good