Showing 45001 words to 48000 words out of 196754 words

Chapter 16 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15365

kamar wani bakon ‘barawo.”

Salim yace

“Ka san kuwa tun yaushe Abba yake neman ka, kai kuwa don Allah ina ka shiga?”

Yace

“Toh ba gani ba.”

Auta yace
“Tab! Yau za ka sha fada.”

Ya talle masa keya yace

“Da kai za mu raba fadan ai.”

Da sallama suka shiga falon gaba dayansu. Kafin suce komai Mommy tace

“Kai kuwa Madu ina ka shiga ake ta nemanka wayarka a kashe tun safe?”

Yace

“Uhm.”

Kafin ya karasa Abban ya daka masa tsawa yace

“Ina ka shiga tun safe ka bar mutane a asibiti?”

Yace

“Abba gidan wani abokina na shiga nan Nassarawa GRA na bashi handout dinshi ko minti goma sha biyar
ban yi ba na dawo ba sa nan sai na zata sun tafi don haka na huce wajen Adil muka yi karatun test.”

Daga Abban har Mommy babu wanda ya kama zancen don haka Abban yace

“Wayarka kuma me ya kashe maka ita?”

Yace

“Uhmmn dama Abba kwana biyu haka take in na ajiyeta sai ta kashe kanta sai dai na sake kunnawa ina ga
shi yasa aka rasa ni.”

“Kuma yanzun daga ina kake?”

“Daga wajen Adil din nake.”

Takaici ya kama Abban ya ma rasa mai zai cewa Madun yake tsugune a gabansu yana ta wasu muzurai
kamar shi aka yiwa laifi. Ya nuna shi da yatsa yace

“Kada ka sake yi min irin wannan, ka ji na gaya maka.”

Ya sunkuyar da kai yace

“Toh Abba in sha Allah ba zan sake ba.”

Ko kallonshi bai sake yi ba ya tashi ya shige dakinshi. Itama Mommy ta tashi za ta shige daki yace

“Mommy.”

Ta juyo a fusace tace

“Me za kace min, tun safe anata neman ka. Don rashin mutunci ka ajiye matar ubanka a asibiti kayi
tafiyarka ka kashe waya ba tare da wani bayani ba. Baka kyauta ba wallahi.”

Yace
“Don Allah Mommy kiyi hakuri ba zan sake ba wallahi.”

Ta dube shi yayi kalar tausayi takaici ya kamata. Ya iya yin laifi da gan gan kuna gashi da saurin ba da hakuri
don haka shi ba ya ma bari a yi fushi da shi. Ta nuna shi da yatsa tace

“Ka ma sake don ubanka ka ga yanda zan yi da kai a gidan nan.”

Ya kara sunkuyar da kai, har ta juya zata huce ta tsaya ta ce

“Kuma da safe ka sameta ka bata hakuri kayi mata bayanin abun da ya faru.”

Yace

“Toh Mommy, kin hakura.”

Hararashi kawai tayi ta huce dakinta.

……..

Tunda Abban ya shiga daki yake jirata ta biyo shi ta bashi hakuri amma yaji shiru, ita kuwa da ta shiga nata
dakin sai ta hau shirin bacci tunda ba itace da girki ba. Da ya gaji da jira bata biyo shi ba gashi yana so ya
huce inda zai kwana sai shi ya biyota. A kan dadduma ya sameta ta idar da shafa’I da witri. A tsaye ya tsaya
a kanta ya fara fada

“Bana son irin wannan, na aiki yaro kin sa ya baro su don ya zo ya kai ki unguwa.”

Da mamaki ta dube shi tana nan daga zaune da carbi a hannunta tace

“Ni kuma? Saboda me zan yi haka mun gama magana da kai na gaya maka da Salam muka tafi muka
dawo?”

“Toh in ba ke ya dawo kaiwa ba ina ya tafi? Allurar da tace ba suyi minti talatin ba ma an gama.”

Ta tabe baki tace

“Ai da yake mai gaskiya ta yi magana zancenta ne abun yarda ba nawa ba, ita ka yarda da tace kafin minti
talatin sun fito amma ni da ban fita ba sai da na nemi izinika na gaya maka da wadda za mu tafi ba ka yarda
ba ka zo kana tuhumata. Toh me zan ce, ai duk yanda ta gaya maka shine gaskiya ni ko na bude baki ma
‘karya zan yi maka.”

Takaici ya sa ya kasa magana yayinda ita kuma ta kawar da kanta gefe bata ko son kallonsa. Ya bude baki
muryarsa da alamun ya sauko daga fushin yace

“Kada ki fassara min magana ba daidai ba Rabi, kin san ba haka bane. Amma dole na bincika dalilin da yasa
yaron nan yayi haka.”

Inda ta kawar da kanta ko sake kallon inda yake bata yi ba har ya gaji da tsaiwa ya juya ya fice. Ko da ya
koma wajen Saudah ma haka ta kwana mita duk da ya gaya mata ya dau mataki. Ita mataki daya take son
ya dauka ya siyo mata mota kuma ya ‘ki.

----------
Ta yarda za ta auri Baba karami domin shi din ma bashi da makusa, amma har yanzu zuciyarta na son
Ahmad. Ko bai kulata ba in dai ta ganshi toh ranar da walwala zata wuni. Tana sa ran in dai Baba ya fara
nuna mata soyayya za ta iya hakura da Ahmad din tunda daman babu wanda ya san tana yi.

Tana kwance a daki tana karatu ta jiyo muryarshi a falo. Tun jiya ya zo weekend daga Kaduna, sun hadu
har ma ta yi masa sannu da zuwa. Yanda ya saba haka ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. Yanzu da
take jiyo muryarshi gaba daya hankalinta yana wajenshi, tana sha’awar ace yanda yake hira da dariya da
auta itama ya dinga yi mata haka amma ya ‘ki. Ji take kamar ta tashi ta fito ta taya shi hirar amma ta san
da ta saka baki a zancenshi zai gwaleta ko ma ya bar mata wajen. A hankali ta tashi ta leka ta hudar mukulli
ta hango shi yana ta murmushi don har gani tayi kamar sai da ya kalleta ya yi murmushin. Ta juyawa kofar
baya ta tsaya a jikinta tana murmushi kamar wadda take a gabanshi. Kafin ta yi wani tunani ta huce ta
bude wardrobe ta dauko ledar da ta ajiye kwallinta da turare. Ta saka kwallin a idonta ta murza sosai don
ta tabbatar ya shiga sosai, ta Bude kwalabar ta kalato digo daya da kyar ta shafa a jikin hijabinta da niyyar
in ta zo kusa da shi sai ta hura masa iskar hijabin.

Ta bude kofar da dan karfi don ta janyo hankalinshi ta fito tana satar kallonshi. Ta huce su ta shiga kichin
ta tsaya a tsakiyar kichin din ba tare da ta san me zata yi ba. A hankali dabara ta fado mata. Ta samu kofi
ta hada shayi ta fito tana yauki, sai da ta zo daf da su sai ta yi kamar ta gurde kofin ya dan yi tangal tangal
shayin ya ‘dan zuba a kafarta. Ta yi ‘yar kara

“Wayyo.”

Duk suka bar abinda suke suka kalleta. Ahmad din shi kadai ne yayi jinkirin kallonta yana kokarin jona
wayarshi a computer din da take gabansu.

“Me ya faru?”

Khalifa ya tambaya.

Tana dago ido za ta bashi amsa Salima ya tuntsire da dariya ya tari numfashinsa yace

“Me ye haka kamar an yi barin kwalli a idonki?”

Ta sunkuyar da idonta tana kallon kasa yayinda a daidai lokacin Ahmad ya dago ya dubeta don ya ga kwallin
amma ta riga ta sunkuyar da kai. Auta ne yayi kasa da murya yana makale dariya yace

“Zulai sunan wata.”

Harararshi Ahmad yayi yayinda ita kuma Zulaiha tayi sauri ta shige daki ta bar musu wajen. Tana shiga ta
huce kan mudubi ta ajiye shayin nata wanda dama babu sugar a ciki. Ta juyo za ta fada kan gadon hijabin
jikinta ya janyo kwalbar da kwallin duka suka fadi gaban mudubin, kwalbar turaren tana dukan tiles din ta
fashe. Tsayawa kawai tayi tana kallon fasassun kwalaben suna sheki. Nan da nan hawayen takaici ya wanke
mata fuska ta fada kan gadon ta fashe da kukan takaici.

Yanzu me za ta cewa Umma, wanda ma ya kamata ta yiwa amfani da kayan bai zo ba ba gashi har ta fasa
turaren da dama ta san sai tayi da gaske za ta samu na shafawa idan ya zo. Yanzu ya za tayi da Ummanta,
ta riga ta yi mata alkawarin za ta yi yanda tace amma gashi ta yi shirme. Sai da ta gama kukanta ta tashi ta
wanko fuskarta tana fitowa daga bandakin ta kula da dan wani bakin gari kamar an barbada shi a gaban
mudubin, ko da ta tsaya ta duba kwallinta ne ya barbade a kasa lokacin da kwalbar turaren ta fashe. Ta
kara dora hannu a ka tana jijjigawa, tabbas za suyi rigima da Umma don ta jinjina kudin da ta kashe kafin
ayi wannan aiki. Haka ta gama bakin cikinta ta zubawa sarautar ido, addu’a kawai takeyi Allah ya sa kada
ta yi ba wan ba kanin.




Babu wanda ya sanarwa zuwanshi kawai sai ganinshi suka yi. Motar da ta sako kai cikin gidan bayan
magriba basu santa ba don haka sun zata Abba ne ya zo da wani. Kirar Honda ce me ruwan gwal, kafin ya
gama shigowa gidan surutun Bala me gadi ya tabbatar musu chewa Baba karami ne. Nan da nan Auta da
Khalifa suka sheko da gudu suna masa oyoyo. Bayan ya gaisa da Mommy take tambayarshi

“Motar wa ka aro daga Abujan.”

Murmushi yake ta faman yi yace

“Mommy tawa ce siya nayi.”

Murmushinta ya kara fadi yayinda murnarta ta bayyana a fili ta ce

“Ma Sha Allah, kai na ji dadi wallahi. Allah ya sa albarka Babana Allah ya tsare hanya.”

Duka suka amsa da

“Amin.”

Khalifa ya zare mukullin motar daga hannun Baba suka fita shi da auta suka bude motar suna kallo. Ko da
Abba ya dawo ma murna yayi ya nuna jin dadin shi sosai. Ya dai yi korafin da ya gaya masa zai sayi mota
da ya cika masa ya sayi ta zamani wadda ta dace da shi. Dariya kawai yayi yace

“Na gode Abba Allah ya kara arziki, in zan canza ai sai a cika min.”

Yace

“Toh Allah ya nuna mana, Allah ya sa albarka.”

Gaba daya hankalin Zulaiha ya kara tashi musamman da ta ganshi da motar nan, ta rasa ma ta yanda za
ayi ta gayawa Umma kayan sun lalace balle ta samo musu mafita. Haka ta hakura take ta dan shisshigi.

Ranar Lahadi da safe ya sami Mommy a daki yana rike da mukullin motarshi yace

“Mommy in an jima zan bi jirgin 12pm na koma, sai an kwana biyu kuma.”

Tace

“Toh Babana Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bada sa’a.”

“Amin Mommy.”

Ya mika mata mukullin motarshi yace

“Mommy a nan zan bar motar in za ki unguwa Salim ya kai ki, ki ajiye mukullin a wajenki.”

Tace
“Toh Baba kai kuma fa, a motar wa za ka dinga zuwa aikin, ga tahowa daga Abuja zuwa Kano.”

“Mommy ai ina da lifan a Abujan, duk shi muke hawa tunda ba wani yawo muke ba kuma unguwar mu
kusa ne da office.”

Tace

“Toh zuwa Kanon fa, ai duk rintsi a motarka ya fi dadi. Ka ga in dai don ni ce sai nayi wata ma ban fita ba
kuma babanka yana sawa a kai ni.”

“Ba komai Mommy a nan din dai zan barta ko Ahmad ma in ya zo ya samu ta zaga gari. Kuma fa yanzu
yawanci a jirgi nake dawowa.”

“Toh mun gode Baba Allah yayi maka albarka Allah ya kawo mata ta gari.”

Yayi ‘yar dariya ya amsa

“Amin. Bari naje wajen Abba kafin ya fita.

Yayi mata sallama ya fice. Ta tashi ta adana mukullin motar tana mamakin saukin kai irin na Baba da yanda
yake kaunarsu gaba daya.

Saudah ce da kwana don haka a falonta ya sami Abba yana zaune yana kallon tashar BBC su Nawwara
suna wasanninsu yayinda Saudah take zaune a dining table tana cin abinci. Bayan ya gaishe da Abban
itama ya gaisheta ya sami guri a kasa kusa da Abban ya zauna

“Abba in an jima zan bi jirgin 12pm na koma in Sha Allah.”

Yace

“Toh motar fa ai na zata da ita za ka tafi.”

“A’ah Abba na bawa Mommy mukullin motar idan za ta unguwa Salim ko Ahmad su kai ta, tunda in na tafi
da ita ma babu abinda zan yi da ita.”

Yace

“Toh shike nan, Allah ya kara arziki Baba Allah ya taimaka.”

“Amin, na gode Abba.”

Ya kamo Hannun Nawwara da Ummi suka fito, sai da ya bawa auta kudi ya siyo musu biskit sannan ya
mayar dasu. Da yake sha biyun da dan saura sai yayi zamansa a falon Mommy yqana kallon TV.

Baba yana fita ta taso ta dawo kusa da Abban tace

“Dama ba motarshi bace ta Mommy ce?”

Yace

“Ta Mommy kuma? Haka kika ji yace? Toh tashi ce ya siya da kudinshi, baya bukatar mota a inda yake shi
yasa ya bata mukullin yace in za a kaita unguwa ta bawa Salim ya kaita.”

Ta bata fuska ta zumburo baki tace
“Kun dai siya mata mota, ina ta faman yi maka magiya ka siya min motar ko karama ce ka ki yanzu kuma
ku bullo ta nan.”

Da mamaki ya ke kallonta yace

“Ta ina muka bullo? Ke wai me yake damunki ne?”

Nan da nan ta sa mishi kuka tana fadin

“Haka ya siyo zoban gwal ya bata na gani da idona an ce min ba haka bane yanzu kuma muna zaune mu
biyu matanka ka zagaya ka sa ya bata mota ni kuma ina nan. Wannan ai rashin adalci ne, nima ai mutum
ce in baza ka bani motar ba don me za ka bata? Ai ba fi na tayi ba don an ga ni yara na kanana ne sai a
dinga raina min wayo ana min rashin adalci.”

A fusace ya bata amsa

“Wai ba a gabanki yayi magana bane, shi da motarsa ki ce ba zai bawa uwarsa ba, toh da kin sani kin tsayar
da shi ki ce ya baki taki motar tunda shi kike aure.”

Tashi yayi zai bar mata falon ta mike tsaye da sauri ta rike rigarsa tana fadin

“Wallahi ba zan yadda ba, ita kenan in za ta fita sai dai kawai ta dauko mukulli ta bayar a kaita amma ni
sai na yi ‘yar murya. Kuma ita ina ma take zuwa ni da nake zuwa makaranta kullum a barni da bin titi.
Gaskiya nima sai dai ka bani motar ko bazan tuka ba in zan fita sai ka turo driver na san dai mota tawa ce.”

Da kyar ya fincike rigarshi daga hannunta ya tunkudata kan kujerar ya shige daki, ta bi bayanshi ta je ta
cigaba da tsiwa tana yi tana kuka tana nuna ba a yi mata adalci a gidan. Ya aiki Madu da motar da ya saba
fita don haka ya dauko mukullin wata motar ya nufo kofa ta sha gabansa ta tare shi tana fadin

“In dai adalci za ayi nima sai a ware mota daya a gidan nan a bani mukullinta na san tawa ce in za ni
unguwa sai na bayar a kai ni ko ma na dauki driver na.”

Hannu ya sa ya ture ta gefe har sai da ta fada kan gadon yana fadin

“Baki da hankali.”

Ya fice ya barta a nan.

Yana fitowa ya nufi inda ake ajiye motoci ya shiga motar da zai fita da ita ya zauna ya kifa kanshi da sitiyari.
Gaba daya ya rasa ma yanda zai yi, wannan fitnar ta Saudah ta yi masa yawa domin shi ba haka ya saba
ba. Kullum bata da aiki sai dai kiran ba ayi mata adalci ba a inda bata ma da hakki. Har ya zura mukulli zai
tayar da motar sai ya fito ya nufo wajen Mommy. A falon ya same su ita da Baba Karami da Ahmad wanda
shi ma ranar asabar ya zo daga Kaduna. Bayan sun amsa sallamarshi ya zauna a kusa da Mommy yace

“Baba ka tafi da motarka Abuja ko ka kaita wani wajen ka ajiyeta, ko gidan Baffa ma za ka iya kaiwa akwai
wajen mota daya kuma ba komai a wajen.”

Dukansu binshi kawai suka yi da kallo basu ce komai ba, ya sake dubanshi yace

“Kaji ko?”

A sanyaye ya amsa yace
“Toh Abba.”

Ya shige dakinsa dake falon. Mommy ta tashi tabi bayansa. A tsaye ta same shi kamar dama ita yake jira.
Bayan ta rufo kofar tace

“Ya haka Abban Khalifa, ina Baba zai kai motarsa da yafi nan tunda nan ma akwai wajen parking din?”

Yace

“Motar tana neman zamar min fitna, tunda ya fito Saudah ke tsiwa tana kuka gani take wai ni na sa ya
baki mota itama sai na bata.”

Ta tabe baki tace

“Da ma ka barshi ya ajiye motarsa don ko nima da ya bani mukullin ajiyewa kawai nayi ban yi niyyar bari
kowa ya hau masa mota ba tunda duk inda zan fita kana sawa a kai ni, fitarma sau nawa nake yinta a
shekara da sai an bani mota ta musamman? Allah ya kyauta.”

Kafin yace wani abu ta fito ta barshi a dakin. Tana fitowa ta ji rufe gate shi da Ahmad sun fice da motar.
Ta dauki waya ta kirawo Baban yace mata Ahmad zai kaishi airport ya dawo da motar gobe zai huce da ita
Kaduna. Ta ajiye waya tana tunanin wanna wace irin fitna ce ace mutum ba zai ajiye mota a gidan ubanshi
ba, kenan ita da ‘danta ba zai yi mata kyauta ba sai kishiya ta yarda. A haka ta jiyo Abban shima ya fita.
EPISODE 12



Har Baba karami ya isa Abuja yana tunanin abunda ya faru, shi da gidan ubanshi ace ba zai ajiye abinda
yake so ba. Kenan ita Mommy ba zata samu wani abu na jin dadi ba in dai Saudah bata da shi. Ya tsani
polygamy, in dai haka karin aure yake mayar da mutum toh shi kam baya fatan ya auri mace sama da
‘daya. Ya ma rasa laifin wa zai gani, Saudah, Abba ko Mommy. Toh Mommy ma laifin me tayi, duk fadan
da kasan baza kayi nasara ba farashin bashi da amfani. Idan ta fara fada kowa sai ya ji babu dadi a gidan
don kuwa za su goyi bayan uwarsu, don haka sam bai ga laifinta ba. Amma ba komai ya san yanda zai yi.

Yana shiga daki ya ajiye jakarshi ya zauna ya sha ruwa, da yake ba yunwa yake ji ba sai kawai ya dauki
waya ya kirawo ta.

“My love ka dawo ne?”

Sai da ya saki murmushi ya gyara zaman shi ya kashingide sosai sannan ya bata amsa

“Me kyau, na dawo. Kin gan ni nan a cikin ‘daki. Toh ya kike?”

“Lafiya my love, ya Mommy da Abba?”

“Lafiyarsu kalau Alhamdulillah.”

“Ka ce wa Mommy ina gaisheta?”

Ya kyalkyale da dariya yace

“Na bari dai kya gaya mata in kun hadu.”

Itama dariyar tayi sannan ta cigaba

“Ka san wani abu?”

“Sai kin fada.”

“Daddy na yace ka zo yana son ganinka.”

Sai da ya tashi zaune yayi gyaran murya sannan ya bata amsa cike da jin dadi

“Don Allah da gaske kike?”

Ta yi dariya ta ce

“Allah kuwa Habibi, ya ce ka zo ranar Juma’ah ya ganka kafin ya baku dama ku turo.”

“Alhamdulillah, ki ce na kusa zama mijin Khairiyya?”

Ta yi ‘yar dariya tare da bashi amsa

“Habibi kenan, ka bari

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login