Showing 153001 words to 156000 words out of 196754 words
Chapter 52 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
amma dai yaki yayi mata maganar kuma
ya hana ‘yanuwansa. Nan suka zauna gaba daya suna ta murnar kujeru. Ahmad ya ce shi dai da safe zai
je siyo labule don na falon sun tsufa, Salim yace ai harda carpets a kayan don haka idan Abban ya shigo
zai ce masa saura carpet. Shi kuma Baba karami yace zai canza TV stand da kuma TV din saboda wajen
ya fi kyau sosai. Sai can bayan magriba Abba suka dawo tare da Madu, yana fita daga motar ya shige
wajen Mommy don ya ga motar Baba Kuma yana so yaje yaga yaya yaran za suyi da suka ga yayi haka. Ya
shiga su Auta suna biye da shi, bayan ya amsa gaisuwar Baba karami wanda yake zaune a kan kujerar
yace
“Babana kujerun sun yi ko.”
Yana dariya yace
“Sunyi sosai Abba, Allah ya kara arziki.”
Salim yace
“Don ma babu carpet.”
Abban ya dube shi yace
“Kuma fa hakane, toh gobe a dauko carpet a store wanda ya dace a zo a saka.”
“Yauwa Abba an gode.”
Auta da baiyi magana ba yace
“Abba yaushe Mommyn za ta dawo?”
Ya jijjiga kai yace
“Toh ina sa rai dai ko zuwa cikin sati me zuwa.”
Suka dan taba hira yana daga tsaya sannan yayi musu sallama ya wuce wajen Saudah. Bai sameta a falon
ba amma dai ta jera abinci a table, tana can daki ita da yaran ya san yanzu haka lallabarsu takeyi suyi
barci. Sai bayan ya shiga daki ya canza kaya ta sameshi a dakin tayi masa sannu da zuwa ta sanar da shi
abincinsa yana kan table, sannan ta koma daki ta cigaba da lallaba yaranta. Sai can wajen tara da rabi ta
sameshi a falon lokacin har ya gama cin abinci yana kallon labarai. Bayan ya amsa sallamarta ta zauna
daga gafe inda zata dinga hango fuskarsa. Jimawa kadan tayi gyaran murya ya kalleta tace
“Ya kasuwar.”
Ya mayar da hankalinsa ga kallon TV sannan ya amsa mata
“Alhamdulillahi.”
Suka yi shiru na dan lokaci sannan tace
“Kuma sai naga kujerun an kawowa Mommy, na ma zata nan din za a kawo da yake mun yi maganar.”
Sai yanzu ya gane dalilin da yasa tunda ya shigo take cika tana batsewa, shi ya ma manta da wannan
maganar da suka yi. Ya tashi daga kashingidar da yayi ya zauna sannan yace
“Dama ba muyi magana dake ba, tunda ai ce miki nayi ba zan canza miki kujeru yanzu ba ko.”
Ta kalleshi ta kawar da kai
“Toh amma ita ai gashi nan ka canza mata, ita da bata ma cikin gidan.”
“Eh ai na gaya miki ko da wane lokaci za ki iya ganinta ta dawo.”
“Toh yanzu ni ina nawa kujerun, tunda ai kamata yayi duk abinda kayi mata kayi min.”
Ya kalleta da mamaki
“Amma ai na gaya miki bazan sake miki kujeru yanzu ba ko, toh haka za ki hakura sai dai idan kina da
kudinki ba zan hanaki sakewa ba.”
Ranta ya gama ‘baci, wannan wane irin rainin hankali ne ya sakewa matarsa kujeru ita kuma yace in tana
da kudi ta sake.
“Toh ai kuwa wannan ba ayi min adalci ba don adalci shine raba daidai. Ta tafi yawonta amma har wasu
kujeru ake sake mata ni da nake cikin gidan ace wai idan ina da kudi na sake, gaskiya ba zai yiwu ba. Ni
bance ka bani komai ba amman gaskiya nima ka sake min kujeru don shine adalci.”
Binta kawai yakeyi da kallo tana magana tana jefa hannuwa kamar wadda takeyi da ‘danta, sai da ta
gama ta ja numfashi sannan yace
“Idan dai a wajenki wannan shine adalci to bazan yi miki adalci ba Saudah. Ita Rabin da kika raina kin san
ban taba saya mata kujerun ba ko? Da kujerunta aka kawota daga gidansu mukayi ta zama a kan
wadannan kujerun har zuwa lokacin da na yi wannan gidan da zamu taso na zuba gadaje a dakunan nace
bani da kudi don haka a kwaso tsofaffin kujerun a wankesu a saka a wannan falon. Ita ta fitar da kujerun
ta siyar yayarta ta cika mata ta sayi wadannan da kika ga an cire muka cigaba da zama har kawo yanzu
shekaru kusan ashirin. Lokacin da zan aureki ta san ni na sayi komai don yaranta ne sukayi sayayyar
amma ko labule bata ce na canza mata ba, iya abinda na bata shi ta karba. Amma yanzu ke kina da bakin
cewa ba ayi miki adalci ba. Baki ma da lissafi wallahi, kada ki sake yi min zancen wasu kujeru don ba zan
canza ba sai dai in akwai abinda za kiyi a kai toh kiyi.”
Kafin tace wani abu ya tashi ya wuce daki. Ta zauna a nana tana cika tana batsewa, saboda an yi mata
rashin adalci tayi magana shine yake nema yayi mata gorin kujeru. Dadinta dai suma ba rokonsa suka yi
ba shine da rawar kansa yace suyi kayan kicin kawai zai yi sauran. Wayarta da take ajiye a kusa da ita tayi
kara alamar shigowar sako, ta kalli wayar ta dauke kai. Yanzu ta san dole zuwa ranar litinin ta rabu da
wayar nan, a halin da ake ciki ma bata san ko zai sake mata wata wayar ba idan tace an sace wannan
don ta ga yanzu ta matarsa kawai yake yi sai kace wanda zai yi sabuwar amarya. Ta ja tsaki a fili ta fizgi
wayar ta shige daki ta turo kofar. Haka ta kwana da takaicin gorin da yayi mata gashi kuma dole ta bayar
da iphone dinta a sayar.
Ranar Asabar kafin azahar sun hado sayayya da yake inda suka sayi labule nan aka dinka musu suka hado
da tv stand din da sabuwar talabijin din da Baba ya saya harda wani frame me kyau an yi rubutu Home
Sweet home a jiki. Nan da nan suka gyara falo yayi fes. Duk kayan nan da suka shige da su a kan idon
Saudah tana lekensu ta taga, haka ta dinga ji kamar za ta hadiye zuciya don gani takeyi duk Abban ne ya
sa aka siyo. Sai wajen la’asar sannan Yaya Munzali ya kirawo Ahmad yazo su je an sami gida za a sayawa
Mommy. Suka tafi shida Baba karami, an sami gida mai daki uku da falo sai tsakar gida da kicin da
bandaki. Duk da gidan yana bukatar gyare gyare amma haka suka siya saboda yayi kyau kuma wajen da
yake bai shiga loko da yawa ba. Ahmad ya dauki video na gidan ya turawa Mommy itama tace yayi. Nan
da nan aka fara ciniki, cikon da ya kama za ayi Yaya Munzali yace zai cika. Ahaka aka gama magana a kan
zuwa sati mai zuwa za a kammala takardun gidan a basu.
Bai san ta dawo Kano ba don haka yana zaune a kasuwa ranar Asabar da rana yaji kawai yana son
ganinta. Ya kirawo Lalo yace za su je unguwa, sai da suka shiga mota suka hau titi sannan yace masa
Dutse za su je. Yana sanar da shi kuma ya dau waya yake gaya mata gashi nan a hanyar Dutsen.
“Ai ina gidan Yaya Shafa.”
Ji yayi kamar wanda aka daukewa wani dutse daga ka, yace
“Shine baki gaya min ba? Toh gani nan zuwa yanzu kuwa, amma ina jin zan fara tsayawa wajen Baba
Yalwa kwana biyu ban je ba.”
Yana ajiye waya ya dubi Lalo yace
“Muje gidan Baffa in ya so daga can sai na baka kudin mota ka koma kasuwa ni na dawo idan na gama.”
Nan Lalo ya karkata mota sai gidan Baffa, ya karbi mukullin motarsa ya bawa Lalo kudin mota sukayi
sallama. Tun daga bakin kofa ya ga motar Tijjani don haka ya zata shine sai da ya shiga sannan ya samesu
tare da Aliko shima ya zo. Suka zauna a nan suka gaggaisa suka dan taba hira a wajen Baba Yalwa, sai da
aka fara kiran sallar la’asar sannan sukayi sallama da ita gaba dayansu suka fito don suyi sallah a
masallaci sannan kowa ya wuce inda za shi. Suna fitowa daga masallaci suka kamo hanya zuwa wajen
motocinsu Tijjani yana binsu a baya Aliko ya dubi Abba yace
“Wai ya madam kuwa, ta dawo ko?”
“Hmm, bata dawo ba tana nan dai tana ja min rai. Sai faman zarya nake Kano to Dutse.”
“Allah mutumina, ya akayi haka ko ka kasa tsarota ne.”
“Toh, ina ma ta saurare ne. Ta dai ce za ta dawo. Yanzu ma kafin na zo nan sai da na kama hanyar Dutse
na kirawota sannan take gaya min tana gidan yayarta nan sheka, can zan je yanzu na ga ko Allah zai sa na
dace ta bini mu tafi.”
“Kace yanzu zance za ka ma.”
Ya harareshi yayi shiru, shi kuma Alikon ya kyalkyale da dariya yace
“Toh ai ba komai muje na raka ka, ko baza ka da ni ba?”
“A’ah ai wata kila ma ta ga girmanka ta saurare mu.”
Ya juya yacewa Tijjani ya tafi shi Abba zai dawo da shi gida. Suka shiga motar Abba suka kama hanyar
sheka, suna tafe suna hirarrakinsu.
Suna isa aka yi musu iso suka zauna a falon baki na gidan, sai da aka kawo musu ruwa da lemo sannan ta
shigo falon. Ta zauna daga kujerar da tafi kusa da kofar, bayan ta gaisa da su gaba daya ta yiwa Aliko
gaisuwar Baffa sannan tayi shiru tana kallon TV din da take kunne a falon. Aliko ne yayi gyaran murya
yace
“Ina kayan naki, ai ni nan zuwa nayi fa na daukeki mu koma gida. Kin tafi kin bar mana gida yana neman
rushewa haba ranki ya dade.”
Tayi murmushi tace
“In sha Allahu ba zai rushe ba.”
“Toh a gaskiya dai ni zuwa nayi na kara baki hakuri, wanda na san kin fini sanin rayuwar gaba dayanta
hakuri ce. Munyi kuskure amma ayi mana afuwa a koma in sha Allah baza mu sake ba.”
Tayi murmushi ta sunkuyar da kai tana wasa da zoben da yake hannunta. Tana ganin girman Alikon sosai
don haka bata ma san me zata ce masa ba.
Abban yace
“Rabi.”
“Na’am.”
“Ai dai na san kawo yanzu an sayi gidan ko, ya kamata ace yau ki taso mu tafi.”
Aliko yace
“Kwarai kuwa, idan ma akwai wasu abubuwa da kike so a gyara duk yanzu za ki yi bayani na shaida don
kin san ni ne lauyanki.”
Tayi murmushi tace
“Babu komai in sha Allahu.”
Yayi murmushi sannan yace
“Toh yanzu mu jiraki a waje kenan ki hado kayan.”
Tayi dariya tace
“A’a, ai nace zan dawo da kaina ba ma sai kun tafi dani ba.”
Abba yace
“Toh yaushe?”
“Kwanan nan in sha Allahu.”
Aliko yace
“A’a ai rana za ki saka mana saboda mu shirya, kin san fa yanzu kin fi amarya ai dole mu shiryyac
Dariya tayi tace
“Kwanan nan in sha Allahu.”
“Toh yanzu haka zan koma Lagos in bar mutumina yana hamma, da kuwa har ina cika masa baki da na zo
zaki koma.”
Tayi murmushi tace
“Zan koma ai.”
“Toh shike nan muna nan muna baza red carpet.”
Suka dan taba hira Abban yace za su tafi, ta yiwa Aliko sallama ta mike za ta koma ciki Abban yace
“Ki yiwa Yaya Shafan magana mu gaisa.”
Ta amsa sannan ta wuce. Jimawa kadan Yaya Shafa ta turo kofa ta shigo, ta zauna suka gaggaisa ta sake
yi musu gaisuwar Baffa. Aliko ne ya fara magana yace
“Za mu koma da sanyin jiki, Uwargida ta ki ta zo mu tafi amma dai tace za ta koma da kanta.”
Tayi murmushi
“Eh in sha Allahu daga yanzu zuwa kowane lokaci za ta koma, ta dai ce min ta fi so ta koma da kanta
kamar yanda ta fita da kanta.”
“Hakane, babu laifi. Mu na zuba ido, a kara bata hakuri tabbas na san dan uwana bai kyauta ba amma in
sha Allahu irin wannan baza ta sake faruwa ba.”
“Babu komai ai ya wuce in sha Allahu.”
Suka dan yi shiru, suna shirin mikewa Yaya Shafa tace
“Akwai dai dan karami saye da sayarwa irin namu na mata da ta fara don ga kaya nan an saro har an fara
sayarwa, ina fatan hakan babu matsala.”
Abba yace
“Ai babu matsala wannan ba wani abu bane, daga can ma zata sayar da duk abinda take so Allah ya sa
albarka. Gidan ma tace min an samu wanda ake so.”
“Eh, dazu yara suka je suka gani. In Sha Allahu da an gyara za a saka ‘yan haya shike nan.”
“Toh Allah ya sa albarka, wannan ba wani abu bane.”
Aliko yace
“Kwarai kuwa, muna nan dai muna zuba idon dawowarta. Ni Allah ya sa ma ta koma kafin na tafi Lagos
kinga sai na bar danuwana cikin nutsuwa.”
Yaya shafa tayi murmushi tace
“In sha Allahu.”
Sukayi sallama suka barta a nan. Gidan Aliko Abba ya nufa don ya sauke shi, a kan hanyarsu ne yake
sanar da shi maganar neman auren da yake so suje wa Baba da Ahmad. Sai dai ita Zahra Abban su Ummi
yace Dukku za a je kuma a sanar da shi don shi zai wuce gaba, mahaifinta yace ya yi komai amma shi ya fi
so ayi a gaban iyayenta tunda itama ‘yar asali ce. Aliko ya karbi lambar Abban Ummi yace
“Za muyi waya sai mu wuce daga Abuja, in ya so shi kuma Baba idan na dawo Kano sai muyi waya da
Atiku, idan ma banzo a kan lokaci ba sai su je da wani don kada mu bata musu lokaci amma Dukku in sha
Allahu next weekend za mu je.”
“Toh hakan ma yayi, Allah ya nuna mana. Saura su Tijjani kuma.”
Yayi dariya
“Wadannan ai da dan sauransu, ka manta ne sa’an Madu ne fa karatun kawai ya gama da wuri.”
“Hakane fa, lokacine ai Allah ya nuna mana.”
Suka yi sallama ya ajiye shi ya kama hanyar kasuwa.
Yanda ya ji Rabi tana fadin za ta koma kuma da maganganun Yaya Shafa bai zata zai dawo gidan ya tarar
bata nan ba, don haka suna tsayawa da mota a tsakar gidan ya wuce falonta. Khalifa ne kawai da Auta a
falon suna kallo saboda har Ahmad ya yi musu subscription. Ya karasa ya zauna yana kallon falon yana
murmushi yace
“Iyye ‘yayan Mommy, harda wata sabuwar TV? Babana ne da Ahmadu ko?”
“Eh Abba.”
Auta ya bashi amsa
“Ai na san sai su, wajen yayi kyau kam.”
Ya jingina hannuwansa a saman kujerar ya dubi Auta yace
“Mommyn ta dawo ne?”
Suka ji banbarakwai, suka bi shi da kallo na dan lokaci Khalifa yace
“Abba yau za ta dawo ne.”
“Uhm, inaga ba yau bane tunda bata dawo ba zuwa yanzu.”
Nan Madu da Salim suka shigo suka same su, yayi musu sallama ya wuce wajen Saudah wadda take fushi
da shi tun a kan maganar kujeru. Kamar yanda ya zata haka ya tarar babu kowa a falon sai dai kawai ya
jiyo motsinta da yara a daki, kuma ya kula ta ajiye abincin a dinin table. Ya san yau ba lallai ta zo inda
yake ba tunda bai yi mata yanda take so ba. Yana shiga ya zauna a gefen gado ya cire hularsa ya ajiye a
kusa da shi, ya kwanta rigingine kafafunsa suna kasa. Yana shiga falon Mommy yaga yanda wajen yayi
kyau ya zata ta dawo, da yara suka ce masa bata dawo ba sai da yaji kamar ya yi bindiga don takaici. Har
yanzu baya cikin walwala saboda wannan sa rai da yayi. Toh yaushe Rabi za ta dawo gidansa? Matar da
da kafin ya gama bada umarni ta aikata amma yanzu sai binta yake tana zamewa, ya dai riga ya gaya
mata duk abinda ma zatayi sai da tayi don ba zai sake ta ba.
Haka ya kwana shi kadai babu Saudah babu Rabi yana juyi, yana so ya kirawota amma a wannan Daren
idan ya kirawota Mai ze ce mata. Da yake bacci barawo ne a haka ya sace shi sai ji yayi ana assalatu.
Da yake ranar Lahadi ce bai je aiki ba aka kirawo shi daga tasha ana sanar da shi an kawo masa sako
daga Dutse. Mommy ta riga ta sanar da shi za a kawo don haka sai ya dauki mota ya tafi karbo sakon,
yana karba ya wuce gidan Yaya Shafa don ya kai mata. Dinkunan ta ne wajen kala biyar da ta bayar a
Dutse lokacin da ta taho ba a gama ba sune ana gamawa Baraka ta saka mata a motar haya aka kawo.
Bayan ya bata kayan sun gaisa ya zauna nan wajen ‘yan uwansa da yake duk suna gida, sukayi ta hira har
la’asar. Sai da sukayi sallah sannan ya shigo cikin gidan ya same su ita da Yaya Shafa a falo bayan sun
amsa sallamarsa yace
“Mommy zan wuce.”
Ta nuna masu wasu kaya akwati daya da kuma jakunkuna manya a gafe tace
“Ga kaya na nan saka a motar sai mu tafi.”
Bai fahimceta ba kuma yana so ya tamabaya amma da ya tuna ba su kadai bane a wajen sai yayi shiru, ya
fita ya kirawo Abubakar yayan Fathiyya suka kama kayan duka suka kai mota. Kafin su dawo ta shirya ta
yafa mayafinta ta dauki jakarta a hannunta.
“Mommy mun gama sakawa a mota.”
Ya karbi jakar hannunta yayi wa Anti Shafa sallama ya koma mota.
Yaya Shafa ta dafa kafadarta tace
“Toh Allah ya baki hakuri, ba sai nace miki komai ba saboda duk abinda zan gaya miki kin sani kuma
Usman din ba bakonki bane. Allah ya hada kayuwanku.”
Sukayi sallama tana yi mata godiya ta fito ta shiga mota. Sai da suka hau titi sannan ya dubeta yace
“Mommy ina zamu je?”
Tana murmushi ta dube shi tace
“Gidanku za muje.”
Yayi dariya ya mayar da hankalinshi kan hanya yana fadin
“Mommy kin dawo kenan.”
“Eh, ko kada na dawo ne?”
Ya dan zare ido ya kalleta sannan ya mayar da idonsa kan hanyar yace
“Ki dawo mana Mommy, wallahi mun yi kewarki. Mun sha wahala fa Mommy da kika tafi, gaba dayanmu
har Abban. Wallahi wani ma da sai dai ki dawo ki tarar da gawarsa saboda tasabar wahalar da muka
sha.”
Tayi murmushi tace
“Allah ya raba mu da wahala.”
Suka cigaba da tafiya suna hirarrakinsu. Karfe biyar da kwata suka tsaya a kofar gidan, Malam Bala baya
nan don haka Ahmad din ne ya fito ya bude gate ya tuka motar ya shigar. Auta da Khalifa ne a cikin gidan
suna TV game a falonta, sun ji shigowar mota amma da yake sun san ba Abba bane sai suka cigaba
kawai. Ita kuwa Saudah tana kicin, ta riga ta san wanda ya fita da motar don haka da ta ji dawowarsa
bata fito ta leka ba. Yana gama tsayawa ta dauki jakarta ta wuce cikin gidan ta barshi yana rufe gate din.
“Salamu alaikum.”
Gaba daya suka juyo bakinsu a bude suka bita da kallo, suka kalli junansu nan take kowa ya saki abun
game din da yake hannunsa suka kwaso da gudu. Suna karasawa inda take Auta ya fada jikinta, ta danyi
baya kamar za ta fadi tace
“Wai kai sai yaushe za ka san ka zama ‘kato ne, ko so kake ka kada ni?”
Suka saka dariya gaba daya, ta karasa ta zauna a kan kujera tana kallon falon da ya sauya mata. Auta ya
zauna a gefenta shi kuma Khalifa
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good