Showing 180001 words to 183000 words out of 196754 words

Chapter 61 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15363

fara maganar janye kara amma wai har ya sani. Tayi murmushi tace

‘CIA officer! Haka yace akwai matsala ne?’

‘Um um!’

Suka sake yin shiru na dan lokaci tana kallonsa yana satar kallon fuskarta, ya juyo ya fuskanceta gaba
daya ya marairaice ya ware tafukan hannunsa kamar mai bara

‘Mommy don Allah kar ki janye.’

Ta dan zare ido tana murmushi tace

‘Muhammadu kai baka son zaman lafiya ko?’

Ya kawar da kai yana shafa keya

‘Wallahi Mommy kin san ba haka bane amma yarinyar bata da mutunci ne ko kadan ya kamata a ja mata
kunne taji zafi.’

Ta bata rai

‘Matar uban naka ce yarinya?’

Ya kauda kai yana tunanin ta inda zai cigaba, kafin yayi magana aka sake buga mata kofa tace a shigo.
Salim ne yana shigowa kafin ya rufe Auta ma ya biyo bayansa inda ya bar kofar a bude suka zauna a
gabanta suka zuba mata ido. Madu yace

‘Mommy don Allah kar ki janye.’

Salim yace

‘Ai ba za a janye ba Mommy ki barta kawai taje tayi bayani.’

Ta bi su da kallo daya bayan daya ta ma rasa me zata ce, kafin tace wani abu Ahmad ya shigo da kofin
shayi a hannunsa bayan sun amsa sallamarsa ya zauna a gefen gado saboda kusan sun cike kasan.

‘Mommy secret meeting akeyi ne ba’a kirawo mu ba?’

Ya fada kafin ya gama zama.

Tayi dariya tace

‘A’a kannenka ne suke zugani nayi shari’a da matar ubanku.’

Yayi dariya yana dubansu yace

‘Me kuke ci na baka na zuba, ai jibi ne ranar da za a tsine uwar me karya a bainal-jama’a ai babu fashi.’

Ta bishi da kallo gaba daya yaran suna bata mamaki, Ahmad din ma da take jin shi zai bi layin masu bata
hakuri yau shine yake wannan maganar. Sukayi dariya gaba daya, Salim yace
‘Mommy wallahi ba zaki gane wulakancin yarinyar nan ba, da ba kya nan fa bakiga rashin mutuncin da ta
dinga yi ba.’

Auta yace

‘Sosai kuwa, ga satar tsiya.’

Ta juya zata yi magana Khalifa yace

‘Kwarai kuwa nan aka kama yaro da suga da kaji harda fulawa ta kunsa masa wai ta kaiwa Ummanta.
Wallahi a tsakar gida yayi bari Abba ya kamashi.’

Ta kama haba tana mamaki, kafin tace wani abu Ahmad yace

‘Kuma mu dinma ba barinmu tayi ba don wallahi da ta sami dama bazaki dawo ki tarar da mu ba. Shi
Madu kam har aljanu ta turo su tafi dashi.’

Ta kama baki ta zaro ido, maganar Maman Farida ta tabbata kenan

‘Kai Ahamdu yaushe akayi haka kuma, wa ya ce maka itace.’

Nan suka labarta mata yanda abun ya faru da kuma abinda aljanin ya fada ta bakin Madun, Khalifa yace

‘Kinga kuwa wace mace ce a rayuwarsa da zata turo aljanu su tafi dashi kan dutse a wannan lokacin idan
ba ita ba.’

Ta bude baki zatayi magana Ahmad yace

‘Itace kawai saboda tana jin haushinsa yanda suke da Abba, tunda ko me zata ce a siyo mata ko a bata
kudi sai dai ace Madu ya bata.’

Tace

‘Uhm, Allah ya kyauta koma wacece ta gani a kanta. Idan kuka biyewa irin wannan sai a zo a bata goma
daya bata gyaru ba.’

Madu yace

‘Shi kanshi Abban fa saura kadan ta kaishi lahira bakiga yanda ya dinga amai da gudawa ba saida ya
kwana a asibiti.’

Ahmad yace

‘Sai ma kinji daya tsiyar da tayi masa.’

Shi da Madu suka kyalkyale da dariya. Tace

‘Uhm! Ai ni ban ce muku zan janye ba, ko da za ayi sulhu to sai dai ayi a kotun amma ba a gida ba. Ayi
kowa ya shaida tunda itama ba a daki ta yi min sharrin ba.’

‘Yauwa Mommy.’

Nan suka zauna sunata bata labarin abubuwan da suka faru da da basu gaya mata ba, har saida Salim ya
nuna mata video din damben Saudah da Zulaiha suka yi ta dariya. Tace
‘Amma don Allah Salim ka goge wannan video din ka ji ko? Bana son lalata.’

Ya mayar da wayarsa aljihu yana fadin

‘Ai zan goge Mommy.’

………….

Shi kuwa Abba a hargitse ya fito daga wajen Mommyn, yanda yaji tana fadin wai har ana cewa kanjamau
ce da ita abun ya firgita shi. Wato yanzu kenan shima kallon da ake masa kenan, wannan wace irin
masiface. A haka ya koma falon Saudah. Babu kowa a falon don haka ya wuce daki ya shiga wanka, yana
yi yana ta tunani. Kwakwalwarshi ta kasa hutawa, wai menene zancen da me aikin Saudan ta ji tana fada
ne har ake wadannan maganganun? Jiya ta gaya masa wasu sun daina kulata yau kuma ana gaya mata
wai tana da kanjamau shi yasa ta tafi, kardai Saudah abunda ta cewa mai aikinta kenan kafin ta tafi?

Yana fitowa daga wanka ya shirya ya fito falon, zuwa lokacin ita da yara duka suna falon suna cin abinci.
Ya wucesu bayan ya gaisa da su Nawwara da suketa yi masa magana ya zauna a kan table ya fara cin
abinci. Kafin ya gama cinye abincinsa yaran sun gama duk sun fice tsakar gida, ta kwashe kwanukan ta
dawo kan table din ta zauna a kujerar da take gefen wadda yake kai. Kallonta kawai yayi sau daya ya
mayar da hankalinsa kan kwanon abincin da yake ci, suka yi shiru na dan lokaci. Ya gama cinye burodin
da shayin saura farfesun kifi ya dauki cokali ya fara shan farfesun. Ta dan yi gyaran murya tace

‘Uhm, Abban Nawwara kunyi magana da Mommyn kuwa?’

Ya kalleta suka hada ido, kafin ta gane me hakan yake nufi ya ajiye cokalin da yake hannunsa a cikin
kwanon kamar wanda cokalin yayiwa zafi ya tsattsareta da ido

‘Wai wannan maganar da ake yi yaushe ita mai aikin naki da kika ce ita ta fitar da maganar taji? Na san
dai lokacin da kika yi min maganar da daddare ne bata gidan, da kika maimaita da safe kuma ma bata zo
ba. To a ina taji?’

Taji tambayar kamar daga bakin dan sanda ko lawyer, ta dan diririce musamman da yake ya tsattsareta
da ido. Ta sunkuyar da kai tana sosa keya tace

‘Ai ba a lokacin taji ba.’

Mamaki ya bayyana a fuskarsa

‘To a yaushe taji?’

Addua kawai takeyi Allah ya kawo wani abun ya dau hankalinsa saboda bata son ta bashi amsar shi kuma
ya ki ya daina kallonta. Bai bata kofa tayi masa karya ba don haka da ta gaji da shirun tace

‘Um, dama ina waya ne nake tunanin taji um don a kicin nake wayar ita kuma tana wanke-wanke a
bayan kicin din.’

Tsananin mamaki ya karu a fuskarsa yayinda kansa ya kara kullewa, ya gyara zama ya jingina da bayan
kujerar har yanzu idanuwansa a kanta
‘Au ashe ma ke kika dauki waya kika dinga yayata zancen da kanki, haka kawai ki tsarawa kanki zance
kuma ki hau yadawa ta waya. To ai kece kenan kika fitar da zancen kika bayar da shi a matsayin abinda
kike da tabbas a kai. Ai Mai aikinki ma bata da wani laifi tunda….’

Tayi sauri ta katseshi saboda yanda yake neman yace ita kadai ce mai laifin

‘Wallahi itace, nifa babu wanda na gayawa.’

Hawayen da take ta rikewa suka kufce, ya harareta

‘Kika ce min waya kike yi taji, to wa kike gayawa zancen a wayar? Bayan kuma saida na ce da ke ki bar
wannan maganar amma saboda ban isa ba kin saka sharri a zuciyarki har waya kika dinga yi kina
yadawa.’

Ta ja shassheka ta share fuska

‘Ni fa ba yadawa na dinga yi ba, Yaya Ummuce fa kawai na gayawa a waya kuma daga ita ban sake
gayawa kowa ba.’

‘Ummu! Ummu!’

Ya fada cikin yanayi na mamaki da daga murya, kukanda take yi ya kara yawa. Kafin tace wani abu ya
cigaba

‘Sai da nace miki ki bar maganar amma saboda ki nuna min ban isa ba saida kika kirawo Ummu kika gaya
mata. Kika gayawa Ummu matata taje karuwanci ta debo kanjamau? Wato dama Ummu ce ta ce ki tafi
gida ke kuma kika tafi ko? Wai sai yaushe za ki gane Ummu so take kawai ta kashe miki aure ne?...’

Cikin shessheka ta katse shi

‘Wallahi ba ita tace na tafi ba Allah!’

Ya harareta

‘To ni nace ki tafi kenan?’

Ta sunkuyar da kai tana shesshekar kuka tana kokawa da malolon da ya tokare mata makogoro yake so
ya sa zuciyarta ta fashe. An riga an gama magana da shi an bashi hakuri amma yanzu yana nema ya
mayar da magana baya, to me yaje Mommyn ta gaya masa. Maganarshi ce ta katse mata tunani yana
magana cikin dacin rai

‘Sai da na gaya miki ki bar maganar nan amma saboda kin raina ni baki bari ba, ai gashi nan kin gayawa
Ummu ta yayata a gari ko? Sai ta zo ta rakaki kotu ta kareki ko kuma idan an yanke miki hukuncin bulala
a raba muku ke da ita.’

Cikin shesshekar da murya kasa-kasa tace

‘Wallahi ba ita ta kawo zancen unguwarnan ba Balaraba ce, Allah itace.’

‘Sai kuma ke da kika fara shi ba, to kya je kotun kya yi musu bayani.’

Ya mike a fusace ba tare da ya karasa cin abincin ba, ya wuce daki. Kafin tayi wani yunkurin ya fito a
shirye ya wuceta ba tare da ya ko kalli inda take ba. Da yake Madu da Salim sun riga sun fito suna jiransa
mota kawai ya shige suka fice. Ranar haka ya wuni a kasuwa cikin yanayi na rashin jin dadi; dukansu su
biyun iyalansa ne, ya za ayi a ce yana nan da ransa da lafiyarsa matansa na shari’a a kotu? Kamar shi ace
ana nuna matarsa a unguwa ana mata kallon lalatacciya? Kuma ace wai daya matar tasa ce ta fadi
zancen har aka ji? Bai taba jin takaicin rashin daukan maganarshi da Saudah takeyi ba kamar ya da yake
ji a halin yanzu. Yana so yaga laifin Ummu amma zuciyarsa tana tuna masa da cewa Saudah ce ta fara
fitar da maganar bayan shi da kansa sai da yace ta bar maganar. Ya san ba’a yiwa Mommy adalci ba duk
da a can kasan zuciyarsa yana so ta hakura, sai dai idan ya tuno wai ita ake tambaya tana da kanjamau
sai yaji gaba daya kwakwalwarsa ta daina aiki. Yanzu kenan shima kallon da ake masa kenan? Bai taba
nadamar korar Mommy daga gidansa ba kamar yanda yakeyi yanzu, tabbas wannan abun da ya aikata
guda daya shi ya janyo wannan matsalar. Da zai iya da ya mayar da hannun agogo baya ya share wannan
abun a labarin rayuwarsu duk da cewa ya kasa gane dalilin da yasa su biyu matansa suka kasa fahimtar
juna. Har suka isa kasuwar bai samo amsar tambayoyin da kwakwalwarsa take biya masa ba, ba tare da
yace musu komai ba ya fice daga motar ya shige kasuwar ya barsu suna tunanin ko ya shiga damuwa ne
saboda Mommy ta ki yarda ta janye kara.

.......…..

Yanda ya barta haka ta wuni cikin matsananciyar damuwa, bata taba zaton zai dau zafi haka ba. Yana
matukar son farfesun kifi amma haka ya tafi bai karasa cinyewa ba saboda ya rufe ido yana ta yi mata
fada. Ba wai fadan ne ya bata takaici ba saboda kawo yanzu ta riga ta gane tayi laifi, amma ya ma ki ya
saurareta so yake kawai yace laifintane ita da Yaya Ummu. Har azahar tana share hawaye tana ajiyar
zuciya, Nawwara sai faman tambayarta takeyi

‘Umma idonki yana ciwone?’

Dole haka ta amsa tace musu yaji ne ya shigar mata idon. Can bayan azahar wayarta tayi kara suna
zaune a falo itada yaran suna kallon cartoon, da gudu Nawwara ta tashi ta dauko wayar a kan dining
table ta kawo mata. Tana kallon screen din taga Yaya Maryama don haka ta tashi daga cikin yaran ta
shige daki. Bayan sun gama gaisawa tace

‘Ban jiki ba, Mommyn ta hakura.’

Kawai sai ta rushe da kuka

‘Subhanallahi me kuma ya faru kike kuka?’

Ta share hawaye ta nemo muryarta da kyar tace

‘Ta ce bazata janye ba, shima Abban Nawwaran yanzu ya gama yi min fada ya fita.’

‘Mtseww! Toh shine kike kuka saboda an yi miki fada? Ai dole ayi miki fada wannan aika-aikar da kika yi
wallahi gara ma ki share hawayenki ki nemi mafita.’

‘Baki gani ba fa Yaya Maryam kamar zai dokeni wallahi.’

‘Haka za ki hakura ki cigaba da bashi hakuri itama Mommyn ki kara bata hakuri don gaskiya bana so aje
kotun, ke ko a yaran nata ma in da wanda kike ganin zai saurareki ki sameshi kice ya bata hakuri. Kin san
uwa da da sai kiga ta janye.’

‘Uhm, baki san halin yaran nan bane.’
‘Naki halin kawai ma sani.’

Tayi shiru don ta gane bakar magana Maryam din take mata.

‘Kina ji ko, ki dage da addu’a ki bi dare kiyi nafila ki roki Allah ya basu hakuri gaba dayansu kuma ya sa a
daina yawo da maganar. Ke kanki ma ki roki yafiyar Allah don wallahi wannan abun da kika yi laifi ne a
wajen Allah. Kin ji ni ko?’

‘Eh, zanyi wallahi.’

‘Yauwa, Kinga jibi ne ki dage yau ki bi dare Allah ya saukar musu da hakuri in sha Allahu baza a shiga
kotun nan ba.’

‘In sha Allahu.’

‘Sai kuma ki kiyaye gaba, komai kiyayyarka da mutum ba komai kake jifansa da shi ba. Ka fadi alkhairi ko
kayi shiru.’

Sukayi sallama suka ajiye wayar, ta ajiye wayar a kan mudubin ta karasa ta zauna a gefen gadon kamar
wadda aka jefar. Hawaye ya sake kwace mata ta dora hannu a ka; yanzu kowa ma laifinta yake gani
amma gaskiya Balaraba ta cuceta. Toh ko ma Yaya Ummu ce ne ta yada zancen, kai amma ai Yaya Ummu
bata san kowa a unguwar nan ba don haka dole sai dai Balaraban. Ina ma bata furta wannan maganar
ba! A yanda ta zata daga wannan maganar Abba zai juyawa Mommy baya amma yanzu fata take ace
mafarki takeyi wanda zata farka yanzun nan, fata take ace bata yi wannan zancen ba wani kuskure aka
samu.

…………

Ko da Abba ya dawo daga kasuwa wajen Saudah ya fara wucewa tunda itace da kwana. Yanda ya amsa
sannu da zuwan da tayi masa yasa ta gane bai huce ba don haka ta shiga taitayinta. Bayan ya gama
shiryawa ya fito daga dakin, ta riga ta shirya abincin a dining don haka kai tsaye ya wuce ya zauna domin
cin abinci. Take ta tashi ta wuce daki saboda bata son wata hira ta hadasu don yanzu ta fara tsoron
abinda zai gaya mata. Shi kadai yaci abincinsa har ya gama sai yara da suke masa hira, yana gamawa ya
fice ya shiga wajen Mommy. A falo ya samesu ita da yaran don haka nan ya zauna suka dan taba hira,
jimawa kadan wajen karfe goma ya dubi Ahmad yyac

‘Gobe fa kannenka za su koma makaranta sun gaya maka ko?’

‘Na sani Abba.’

Yayi musu sai da safe ya wuce wajen Saudah.

Shi kadai ya kwana a dakin don ita yanzu tsoronsa takeyi, da dai ta gama abinda take yi sai kawai ta rufe
daki tayi kwanciyarta a tsakiyar yaranta. Haka ya kwana shi kadai ba tare da yayi wani baccin kirki ba,
yanzu kamar shi ace matansa su biyu suna shari’a a kotu. Kuma idan fa hukunci za a yanke sai an yiwa
matarsa bulala a gaban mutane, idan muma ya tuna laifinta da yanda Rabin ta gaya masa zancen yana
yawo a unguwa sai yaji kamar yayi bindiga saboda takaici. Yana so ya gayawa Baraka amma yana tsoron
kada Barakan ta kara tunzura masa Mommy, ba zai gayawa Yaya Munzali ko Yaya Shafa ba saboda ba so
yake ayi mata dole ba ko ayi mata fada su kuma ya tabbatar sai sun yi mata fada. Ya gyara kwanciyarsa a
karo na babu iyaka, da Baffa yana nan ya san da yanzu wata maganar ake ba wannan ba. Ya rasa wanda
zai gayawa maganar nan ko bai sami wata mafitaba ya rage nauyin da take masa a kirji, haka ya kwana
juyi da tunani ba tare da ya sami wata mafita ba.

Itama Saudan haka ta kwana tana juyi saboda tunanin gobe ce kawai ranar da ta rage mata idan ba ayi
sulhu ba to tabbas sai dai fa ta hakura ta karbi bulalar nan. Domin bata da wata hujja da zata yi amfani
da ita ta kare kanta, gashi ita ko tunanin ma ta dauki lawyer bata yi ba don in ta daukeshi bata da kudin
da zata biya a lauye karar. Sai wajen ukun dare sannan ta tuna da maganar su da Yaya Maryama don
haka ta tashi ta dauro alwala ta fara Sallah.




Yanayin damuwar da Abba ya shiga saboda karar nan ya sa yaran suka fara tunanin zai sa Mommy ta
janye, don haka ranar litinin Ahmad yana shiga office ya dau waya ya kirawo Anti Baraka. Bayan ya sanar
da ita abinda yake faruwa ji tayi kamar a mafarki tace

‘Kasan ko jiya munyi waya da Mommy amma bata gaya min ba.’

‘Wallahi Anti, kin san halinta. Ina jin dai Anti Shafa ta sani.’

‘Shine Abban yace ta janye?’

‘A’a ba kai tsaye ba dai amma yana ta faman bata hakuri, amma Anti ai gara aje kotun yanda yan gulma
suka kwashi wancan zancen sai su kwashi wannan su bar wancan in ba haka ba haka za ayi ta yi mata
kallon lalatacciya. Kuma duk ai Abban ne ya janyo.’

‘Hakane, ba za a janye ba in sha Allahu, yanzu zan kirawo Mommy. Baba Mubarak ma yanzu zan kirawo
shi gobe kafin sha biyun mun iso Kanon in sha Allahu a gabanmu za ayi.’

‘Yauwa Anti, don wallahi yarinyar nan idan ba bulala ta sha ba bazata shiga hankalinta ba.’

‘Kada ka damu sai mun yi maganinta.’

Sukayi sallama suka ajiye waya. Nan take ta kirawo Mommy bayan ta gama yi mata mitar yanda za ayi
wannan babban al’amari ya faru bata gaya musu ba Mommyn tace

‘To don Allah ai ba sai na taso ku ba, ba gashi ma za a shiga kotun. Wai ma wa ya gaya miki?’

‘Ina ruwanaki, gobe in sha Allahu da safe muna nan zuwa da Mubarak, ai kema kina da dangi da za a
cuceki kuma a nemi a sa ki hakurin dole.’

Sukayi sallama suka ajiye waya.

Shima Abban haka ya wuni a kasuwar ba tare da walwala ba, sai ji yake kamar ana rada masa a kunnensa
gobe matansa biyu za su shiga kotu. Yana so a tabbatar da gaskiya a hukunta mara gaskiya amma ai
matansa ne duka su biyun, a sulhuta a gida mana ba sai an je kotun ba. Sai can da yamma an kusa tashi
daga kasuwa dabara ta fado masa, don haka nan da nan ya karbi mota suka fita shi da Lalo bayan ya
sanarwa su Madu idan an tashi su wuce gida. Suna fitowa suka kama hanyar gidan Baffa, duk Juma’ah
suna zuwa gaishe da Baba Yalwa shi da su Madu amma bai taba tunanin yayi mata zancen ba sai yanzu.
Yana kyautata zaton in dai Rabin da ya sani ce ko ta shirya zata tafi kotun idan Baba Yalwa ta sa baki zata
hakura.

Da sallama ya shiga gidan Zulaiha tana tsakar gida don haka tayi masa iso har falo inda Baba Yalwa

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login