Showing 120001 words to 123000 words out of 196754 words

Chapter 41 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15410

babu wanda ma ya san inda na taho, don na ma kashe wayata. Na san idan naje
gidan Yaya Shafa nan da nan za su hadu da Yaya Munzali su ce za a bashi hakuri ni kuma ban ga laifin da
nayi masa ba.”

“Gaskiya ne, ke kika haifar mata yaran ko kuwa ke wa ya taya ki rainon naki yaran?”

“Nima shi na gani.”

“Bari in an jima zan kirawo Yaya Shafan.”

Ta ajiye kofin shayin dake hannunta tace

“Babu wanda za ki kirawo ki rabu da su kawai, na fiso babu wanda zai san inda nake har sai na huta sosai
in ya so sai a yita ta kare.”

Tayi dariya tace

“Allah Bibi, toh amma dai sai ki gayawa ko da Baba ne saboda kar ki tayar musu da hankali.

“Babu wanda zan gayawa, ke ma ba za ki gaya musu ba. Ki bari sai sun duba basu gan ni ba kya je musu
jaje.”

“Allah Bibi?”

Ta gyara zama ta kalleta sosai tace
“Na gaji Baraka, bana so kowa ya dameni. Yanzu ina gayawa Baba inda nake zai gayawa Ahmad shi kuma
ya gayawa Madu haka kowa zai gayawa na kasa dashi. Kuma ma idan ba a ga sun shiga damuwa ba za a
gane dole sun san inda nake. Ki bari kawai sai na huta na sami natsuwa watakil sa gane mahimmancina
gaba daya.”

Suka dan yi jim, ta sa hannu ta share hawayen da yake kan fuskarta tace

“Babu wanda ya damu da damuwa ta Bibi, me na kulla a rayuwarta in banda hidimar shi da ta yaranshi.
Kalleki kina aikin ki itama Yaya Shafa tana nata amma ni na hakura ina ta hidimarsa da yaransa baya
gani. Ya auro matarsa so yake dole sai na so ta, so yake dole sai na tayata hidimar da ni bai samar min
wadda ta tayani ba. Sadaukar da rayuwarta da nayi don shi da yaranshi su ji dadi bai ishe shi ba yanzu so
yake na kwanta matarshi ta bi ta kaina. Ba zai yiwu ba Baraka, gara ya sake ni ya zauna da matar da ya fi
so. Alhamdulillah yarana sun girma kuma ma duk maza ne bani da damuwa da yawa.”

“Gaskiya ne Bibi, babu damuwa in Sha Allahu haka za ayi. Nan gidanki ne duk yanda kike so haka zakiyi
babu wanda zai ji har sai lokacin da kika so.”

Bayan sallar isha’I Rabi ta gama sallolinta na tarawih da tulawar kur’ani lokacin Baraka bata dakin, tana
zaune a kan dadduma Zahra ta shigo dakin da sallama, bayan ta amsa sallamarta ta rage tsaho tace

“Inna barka da shan ruwa.”

Da fara’arta ta amsa mata

“Yauwa, ina Innar taki?”

“Tana can tana kalo.”

“Kice ina kiranta.”

Ta amsa sannan ta duba kan gado ta dauki wayar Baraka ta juya ta fice. Jimawa kadan Barakan ta shigo
dakin da sallama ta zauna a gefen gadon tace

“Kin idar da sallar?”

“Na idar. Kin san fa ban taho da kaya ba sai na jikina.”

“Baki da matsala bari na baki na bacci, akwai wasu dogayen riguna na kuma na Saudiyya na san za suyi
miki in ya so da safe sai na bayar da wasu a dinka miki kafin mu samu muje shopping.”

Ta zaro mata doguwar riga irin ta yadi mai laushin nan mai hade da mayafi na tsakar gida ta bata, sannan
ta bata abaya baka guda biyu da kuma wat guda daya pink. Ta daga rigar yadin tace

“Duk sababbi ne, wannan ne kawai ba sabo ba.”

Ta karba tace

“Na gode.

Ta bude wani wardrobe din ta zaro fallen zani ta bata tace

“Towel dina yana toilet din idan kina bukata.”
Ta nuna mata wata durowa tace

“Ga undies ko za ki sami wanda za kiyi maleji kafin gobe tunda na san na fi ki ‘kiba. Pants din ma saura
uku da underwear guda daya.”

Tayi murmushi ta matsa kusa da durowar tana fadin

“Kin kama Baban su Ummi kina masa wayo ai dole ki fi ni kiba.”

Sukayi dariya gaba daya, Rabi tace

“Toh a ina zan yi wankan? Ina ne dakin bakin?”

“Ke me yayi miki zafi da dakin baki ai nan ne masaukin ki.”

“Baraka dakin ki ne fa, idan Baban su Ummi ya zo za ki hanashi shigowa ai shi da dakin matarsa.”

“In dai wannan ne kada ki damu idan dai ba kasa tashi nayi ba ba za ki ganshi a nan ba, ga nashi dakin
can sai dai ni naje.”

Ta nufo kofa tan fadin

“Idan kin fito daga wankan muna nan falon sama ni da Zahra.”

Ta fice ta barta tana shirin shiga wankan.

….

Ta dawo falo ta zauna, inda ta bar Zahra tana karatu a dining table. Ita Zahra da mahaifinta da Baraka
‘dan wa da ‘yar kanwa suke. Da yake mahaifiyarsu wanda ta aura bayan rasuwar mahaifinsu dan uwansu
ne a can garinsu yake wato Dukku, jihar Gombe, shekarar da wuce ita da ‘yar kanwar mahaifiyar tasu
wadda ke aure a Kano suka shirya suka kaiwa Innar tasu ziyara can Dukku. Bayan sun huta take sanar da
su akwai yarinyar dan uwansu Zahra wadda za a sa ta lalle gobe don haka idan gari ya waye sai su shirya
su je bikin kafin su kamo hanya. Haka kuwa aka yi. Ko da suka je gidan bikin bayan sun gaggaisa ba
jimawa yara suka shigo da guda suna ihu amaryar ta fada rijiya. Nan da nan mata suka yi waje aka bar su
Baraka da uwar amarya wadda saboda kunya ba za ta wajen ba. Halima da suke tare Baraka ta tambayi
uwar amarya

“Wace irin Rijiyar ce wannan kuma a rasa wanda zai fada sai amarya?”

Ta share kwalla tace

“Dama jiya ai ta fada tace da a kaita gidan Mamman gara ta fada rijiya ta mutu shine taje ta aikata duk
nasihar da na yi mata.”

Baraka tace

“Ikon Allah, bata son shi ne?”

“I, bata sonshi. Yaron sarkin kasuwa ne shi kuma ya ce sai ita, toh mahaifinta dai ya gama magana yace
in ba a yi wannan auren ba sai dai ni da ita mu bar masa gida. Ya riga ma ya karbi sadaki da kudin auren
duka fa ya cinye.”
Yaya halima tace

“Toh ba sai a barta ba, na ga kuma yaranku suna karatun Boko a barta ta gama secondary mana kafin
nan wani mijin ma ya fito wanda take so.”

“Tab, ita kam za ta so haka don tana son karatun amma babu yanda za ayi Malam ya yarda sai dai ko mu
bar masa gidan kam.”

Kafin su gama wannan zance sai ga su nan da gudu wani mutum ya tallafo Zahra a sume, shi ma duk
kayansa a jike daga gani shi ya cirota daga rijiyar. Suka tashi ya shimfide ta a tabarmar da suka tashi, ya
dubi uwarta yace

“Ta auna arziki ina kusa da ko gawarta ba lallai a samu ba.”

Kafin a bashi amsa mahaifinta ya shigo a fusace da sandarshi yana dagawa yane

“Ina take na bugeta ta karasa kowa ya huta fitinanniyar banza da wofi kawai.”

Gadan gadan ya nufo ta sandar tabbas idan an barshi bugetan zai yi, Yaya Halima tayi sauri ta Sha
gabansa tace

“Haba Idi, ka bari mana kada kayi kisan kai.”

Bai san da zuwansu ba don haka sai ya dan dakata yana huci, Baraka ta nuna masa daya shimfidar dake
tsakar gidan tace

“Don Allah mu zauna mana.”

Bayan sun zauna ne Halima da Baraka suka sa shi a gaba suna ta bashi hakuri da magiya, ya nuna musu
ya riga ya karbi kudin aure naira dubu arba’in don haka sai dai ita da uwarta su biya. Yaya Halima tace za
ta biya yanzu kafin su tafi yayi caraf ya dubi innarta yace

“Idan ta biya kuma ki tattara yarinyarki ku bar min gida don wallahi in dai ban isa ba toh kuma baku isan
ba.”

Baraka tace

“A’ah ni sai in tafi da Zahra mu je muyi zaman mu a birni, amma fa idan kayi min alkawari za ka bar
uwarta a dakinta.”

A nan aka yi yarjejeniya suka taho da Zahra suka taho da dan aike suka sami wajen cire kudi Halima ta
fidda dubu talatin ta bayar ita kuma Baraka ta bayar da goma suka hada arba’in suka bayar. Daga nan
suka taho da Zahra ta zama ‘yar gidan Baraka. Suna zuwa ta sami private school me kyau ta saka ta
sannan ta daukar mata lesson teacher, kuma da aka yi sa’a tana da kwazo da son karatun yanzu gashi
nan har an saka ta a SS 3 suna shirin SSCE. Sun shaku sosai da Baraka domin da yake su Umminta sun yi
aure ji take kamar haihuwa ta sake yi, aka yi sa’a kuma yarinyar tana da kyawun hali ga girmama
mutane. Tunda suka taho har yanzu wajen shekara daya da rabi bata je gida ba sai dai kawai takan yi
waya da innarta, amma shi babanta ma ta ki bari a kirawo mata shi.

…….

Sai zuwa jimawa can Rabi ta sakko ta samesu a falon, tana zama Zahra tace
“Sannu Inna.”

Bayan ta amsa Baraka tace

“Akwai abinci fa ko za ki ci.”

Tace

“Gaskiya na koshi, sai dai ko shayi idan akwai ruwan zafi.”

“Ah akwai sosai ma ko babu ma kuma Yalwa za ta dafa.”

Kafin su ce wani abu Zahra tace

“Inna irin naki shayin take sha na zubo mata?”

“Eh, irinshi za ki zubo mata.”

Ta fice ta barsu suna hirarsu.

Sai wajen sha daya sannan suka tafi don kwanciya bacci, tare suka kwanta a gadon Baraka ta kashe fitilar
ta kunna musu fitilar gefen gadon wadda bata da haske sosai. Ta dubi Rabi tace

“Bibi da fa haka muke kwaciya kai da kafa a gidan Umma.”

Suka kyalkyale da dariya gaba daya Rabi tace

“Ki yi min duka saboda buge bugenki ba, to Allah yanzu kina zuba min kafa kasa zan tura ki.”

Suka sake kyalkyale da dariya gaba daya. Baraka ta dauki wayarta ta fara duba Whatsapp, ta dubi Rabi
tace

“Yauwa, kin ga wadannan duba min su.”

Ta mika mata wayar, hotuna ne na atamfofin ta karba ta fara dubawa, Barakan tace

“Ki zabi kamar guda biyar gobe sai na bayar a dinka miki.”

Tana dubawa tace

“Kuma nawa ne kudinsu?”

“Ke ina ruwanku da kudinsu, ki zaba kawai.”

Tayi dariya tayi marking guda biyar ta nuna mata. Ta karbi wayar ta cigaba da dubawa. Jimawa kadan ta
sauke wayar ta dubi Rabi tace

“Wai ina wayar taki, ki daukota a sa chaji gobe sai muje ki sayi sim card kawai, in ya so wancan sa a ajiye
sai kin koma Kanon.”

Ta mika hannu ta dauko jakarta da take kan durowar gadon ta zaro wayar ta mikawa Baraka tana fadin

“Kin ganta nan amma bana ma sha’awar kunnata wallahi, barinta zan yi kawai sai na sami dama na cewa
Baba ya siyo min wata, dama rannan yayi maganar nace ya barta shine ya bani kudin na cinye.”
“Me tayi to, ta samu matsala ne.”

“Mtsew, kwancen ta Abbansu ce wadda ya canza lokacin da zai sayi Samsung ya bani ita, da yake ba
wani abun kirki nake yi da ita ba ba abinda ma tayi amma dai yanzu ta isheni.”

Ta karba tana dariya tace

“Toh ai kince min an baki iphone kin boye ta kin ki amfani da ita.”

“Kin san ni a rayuwa ta idan aka nuna min ban isa ba a kan abu toh ban fiya jin dadin amfani da shi ba
wallahi, amaryar shi ya fara sayawa wayar ya boye min sai da na nuna bacin raina sannan daga baya ya
siyo min ita a tsarabar Dubai din da ya tafi da amaryarsa ya ki tafiya dani.”

“Mtseww, dan rainin hankali ba.”

Ta tashi ta bude wardrobe ta dauko kwalinta dawo ta kwanta, ta mikawa Rabin tace

“Toh ga wata.”

Wayace sabuwa kar a kwalinta kirar Samsung tace

“Ummi ce ta bani birthday gift, kin san mijinta dealer din Samsung ne shine a last birthday dina suka
kawo min ita.”

“Toh ke da aka bawa kyauta kema sai ki kyautar?”

“Eh, na baki. Ga tawa ni, sai dai kawai idan ba kya so gobe sai na siyo miki wata.”

“A’ah, ina so mana ba sai ki sake saye ba. Na gode sosai wallahi Allah ya bar zumunci.”

Ta tashi zaune ta zaro wayar daga kwallinta, Samsung ce galaxy baka sai kyalli takeyi. Ta jujjuya ta a
hannunta, sosai wayar ta burgeta. Baraka tace

“Ga socket nan bayan durowar gefenki ki sa chaji da safe akwai mai sim card a nan kusa sai na kirawo shi
ya kawo miki sim card ki dinga amfani da shi in ya so daga baya in komai ya daidaita sai ki mayar da
tsohon layin.”

Ta gatsine fuska tace

“Ba zan ma mayar dashi ba don Abban Khalifa ne yayi wa layin rijista gara na sayi wani nima nayi rijista
da kaina.”

“Haka ne wallahi in sha Allah toh gobe sai a yi miki rijista ta layin MTN da na Airtel.”

Suka kare hirarrakinsu har bacci ya dauke Baraka. Ita kuwa Rabi duk gajiyar da ta yi da yanda take jin
bacci amma ta nemi baccin ta rasa. Juyi kawai take yi, tana mamaki wai yau itace take kwana a dakin da
ba gidan Usman ba. Tunda tayi aure zata iya kirga sau nawa ta kwana ba a gidan ba, ko taron me ake a
gidansu baya barinta kwana. Haihuwar Baba Karami ne kawai taje wankan gida shima kuma da ya dinga
zarya a kwana talatin Baffanta yace ta shirya a mayar da ita. Daga baya ma kuma sai ta saba ko bikin wa
akeyi a gidansu bata ma shirin kwana tunda zai barta har sai wajen goman dare yaje ya dauko ta da safe
kuma in zai tafi kasuwa ya kaita, don haka ma sai ta daina tambayar kwana gaba daya. Amma yau gata
nan a gidan ‘yar uwarta tana shirin kwana ba iyaka. Sai can wajen ukun dare bacci ya kwashe ta ko minti
talatin bata yi ba Baraka ta tasheta don suyi sahur. Gari yana wayewa kuma kafin Baraka ta tafi aiki sai
da ta tabbatar an yiwa Rabi register din sim card guda biyu ta kunna wayar tace

“Na dinga jinki ni kadai in kina bukatar wani abu, ba ma dadewa zan yi a office din ba idan na dawo za
mu je mu kai dinki mu dan yi shopping.”

Sukayi sallama ta tafi aiki. Tana wajen aiki aka kirawo ta ana tambayarta Rabi tace bata zo ba. Ko da ta
dawo aiki a falo ta sami Rabi tana kallon fim din hausa, bayan ta yi mata sannu tace

“An fara cigiyarki ba, babu wanda bai kirawo ni ba yau din nan wai ko nan kika taho.”

“Kyale su kawai ki ce baki san inda nake ba.”

“Haka na gaya musu, gobe da safe ma Kanon zan je kafin wani ya biyo ki nan, nima naje jaje.”

Suka kyalkyale da dariya Rabi tace

“Kin yi min daidai wallahi.”

Gari na wayewa kuwa Barakan ta taho Kano suka hadu akayi ta jaje. Bayan ta dawo sun zauna suna shan
ruwa ta dubi Rabi tace

“Bibi baza a gayawa Baba karami inda kike ba kuwa? Baki ga fa yanda aka shiga damuwa ba.”

“Wallahi nima a cikin damuwar nake Baraka, amma ina so na huta na sami natsuwa zuciyata ta huce
tukuna. Ko yau na koma hakuri za a bashi nima ace naje na cigaba da hakuri, kuma ba zai yiwu ba. Bari
su ji jiki tukunna musamman ma shi da su Yaya Shafan. Suma yaran yanzu basu ki su bani hakuri suce na
koma ba, nima ina son zama da su amma dole sai ubansu ya gane muhimmancina tukuna, in ba haka ba
kowa tashi ta fissheshi.”

“Hakane, kada ki damu nan za muyi zaman mu ina tare dake har sai lokacin da kika shirya.”




Kafin kwana biyu suka je shopping duk wasu kaya da take bukata suka siya Baraka ta biya kudin;
underwears, takalma, mai da sauran kayan bukata. Suna hanya a motar Baraka Rabi ta dubeta tace

“Kin kashe kudi da yawa fa in nace a bar wani abun kuma sai ki dauko.”

Ta bata rai tace

“Don Allah ki daina wannan zancen Bibi, kin san dai da bani da shi bazan boye miki ba don Allah ki daina
wani damuwa kudina naki ne kin ci bulus kawai.”

Tayi murmushi ta kalleta tace

“Toh Allah ya kara arziki.”

“Amin.”

Tabbas kaunarsu ita da Baraka daga Allah ne, yanzu gani take duk duniya babu wanda yake fahimtarta
kamar Baraka. Ta yarda Yaya Shafa ma tana sonta to amma da ita ce zama zata yi ta ce sai ta koma
amma Baraka itace wadda za ta bata dama har sai ta sami natsuwa kuma ba za tayi kokarin canza mata
ra’ayi ba. Ko da suna yara ma a gida Baffansu ya kan ce ‘ai da Rabi da Baraka bakin su daya, in abun kirki
ne suyi shi tare idan ma barna ce suyi tare babu mai kwabar wani.’ Kafin su karasa gida Baraka ta sake
dubanta tace

“Kin san jiya Abban su Ummi ma ya kirawo ni yana min jaje ya gani Baba ya dora a facebook suna
cigiyarki, yana yi min jaje sosai.”

Tayi dariya tace

“Ai kuwa in ya zo kya san yanda za kiyi ki boye ni wallahi don na san shima yana zuwa zai tona mana
asiri, kin san maza duka bakinsu daya.”

“Rabu da shi ba zan barshi ya zo ba, kawai dai zan tafi Abuja na barki ke kadai. Yanzu yana Umra sai
bayan sallah zai dawo, ana I gobe zai dawo zan tafi can mu hadu. Da an kwana biyu sai na dawo, tunda
kin san shi tunda innarshi ta rasu baya son zuwa garin nan tunda in ya zo ba barinsa ake ya huta ba.”

“Haka ne kam, toh ai shikenan.”

Saura kwana biyu Sallah suka shirya za su je saloon sai kuma Baraka ta sake tunani, ta dubi Rabin tace

“Ina ga fa baza ma mu fita ba, kin san su Baba duk sun baza hotunanki a facebook da instagram sun
cigiyar ki za a iya samun wanda zai gane ki tunda yanzu kowa yana social media.”

“Hakane fa, toh ke kije kawai.”

“A’ah ai kira zan yi a zo gida ayi mana kawai, na dai san baza su zo yau ba may be sai gobe.”

Nan suka zauna aka zo aka yi musu kunshi da gyaran gashi duk a gida. Ga dinkunansu na sallah wanda
Baraka ta sa aka yi musu. Haka suka yi hidimar sallah, idan aka yi baki dama Rabi tana daki sai dai kawai
su zauna da Baraka, kusan in banda ‘yan cikin gidan ma babu wanda ya san da zuwan Rabin. Idan Baraka
ta fita sai ita da masu aiki ko Zahra idan tana nan.

Sai da aka gama hidimar sallah sun shiga daki domin kwanciya bacci, bayan sun kashe fitilar sun kunna
karama Baraka tace

“Bibi kwanaki muna maganar business dake bamu gama ba, ai yanzu ne ya kamata ki nemi abun yi.
Business kike so na saye da sayarwa ko kuma na yin wani abu da kanki.”

Ta tashi zaune tace

“Wallahi abun yana rai na, ina son saye da sayarwar amma toh me zan sayar kuma wa zan sayarwa, wani
lokacin kuma sai na ji ina son na wani da zan dinga yi da hannu na ko babu

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login