Showing 186001 words to 189000 words out of 196754 words
Chapter 63 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
nufi
wajen Mommy. Abban yana shiga falon ya tarar Mommy ta kawowa Baba ruwa tana zaune a kan kafet
gefen kafar Baban suna sake gaisawa. Su Baraka kuma suna zaune a kan kujera mai zaman mutum biyu
ita da Maman Farida yayinda shi kuma Mubarak yake zaune a kan mai zaman mutum daya wadda take
kan hanya. Bayan ya gaida Baba Yalwa ya zauna a kan daya kujerar mai zaman mutum daya sannan suka
gaisa da su Baraka, ita dai Maman Farida ya san dalilin zuwanta don ya san zata bada shaida amma
Baraka da Mubarak bai aan me ya kawo su ba; sai dai ko rakiya. Su kuwa su Ahmad shi da kannensa
bayan su gaisa da Baba sai suka koma kan dining table suka zauna. Sa’a ce ta fara shigowa wadda kowa
sai da yayi mamakin ganinta, musamman Mommy wadda tun kafin barinta gidan rabonda su hadu.
Bayan ta gaida Baba Yalwa suka gaisa da su Mommy, baba Yalwa tace
‘Nan kika kwana ne Sa’ade?’
Ta jijjiga kai tana ‘yar dariya
‘A’a Baba da safen nan nazo wajen Yaya, yanzu ma babu dadewa zan tafi.’
‘Allah sarki, ko Zulaiha ta san da zuwanki ne take ta fama nacin sai ta biyoni.’
Cikin sauri tana jijjiga kai tace
‘A’a, ai mun kwana biyu ma bamuyi waya da ita ba bata ma san zan zo ba.’
‘Allah sarki, ai can na barta saboda bana son barin gidan babu kowa gashi har na fito mai wanke wanken
bata zo ba.’
Shigowar Saudah da Ummu ne ya katse musu zantukan wadanda suma suka nemi waje a kan kafet suka
zauna gaban su Baraka. Cikin girmamawa suka gaida Baba Yalwa ta amsa babu yabo babu fallasa. Bayan
kowa ya zauna Baba Yalwa ta dafa kafadar Mommy wadda take kusa da ita ta sunkuyar da kai tace
‘’Yata wajen ki na zo, na ji duk abubuwan da suka faru amma ina rokon ki arziki ki janye karar nan kuyi
sulhu a nan.’
Tunda taga Baban daman jikinta yayi sanyi, ta faki ido ta share hawayen da suka kwace mata ba tare da
tace komai ba. Wato ita dai ba za’a barta ta kwaci hakkinta ba kenan? Baba Yalwa ta sake dafata
‘Don Allah kiyi hakuri da zuwa kotun nan kinji ‘yata.’
Da kyar ta bude baki tace
‘To Baba.’
Ta daga kai ta dubi Ahmad da suke zaune a kan table tace
‘Ahmad kace Barrister ya shigo.’
Ya tashi ya fice ba tare da ya amsa ba, Baba Yalwa tace
‘Bari mu jirashi ya shigo muji idan za a iya janyewa yanzu.’
Jimawa kadan Barrister ya shigo Ahmad yana biye dashi, Ahmad ya saka masa kujerar dining table a kusa
da Mubarak ya zauna. Bayan ya gaisa da su Baba tace
‘Barista za a iya janye karar nan yanzu?’
Yayi shiru ya kalli mommy, ta gyada kai tace
‘Za mu iya janyewa yanzu Barrister? Ina so na janye.’
Ya gyada kai yace
‘Eh mana, babu wata damuwa shikenan kawai zan je kotun yanzu in dai kin tabbatar kin janye.’
Tace
‘Na janye Barrister kaje kawai za muyi magana.’
‘Toh ma sha Allahu, babu wata damuwa.’
Ya mike ya zaro waya ya fara dannawa ya nufi kofa yana fadin
‘Bari nayi sauri naje don lokacin mu ya kusa.’
Da yake Bala mai gadi baya nan a nan suka jiyo ana buga gate din da karfi, Madu ne ya mike da sauri ya
je ya bude. Balaraba ce mai aikin Saudah ta ga kwana biyu da dawowar Saudah bata nemeta ba shine ta
zo taji ko za a cigaba da aikin. Bayan ta gaishe shi ta kama hanya ta nufi wajen Saudah, yace yana nuna
mata wajen Mommy
‘Tana nan ki shigo.’
‘To madalla.’
Ta wuce wajen Mommy ya bita a baya. Barrister yana fita suna shiga, ta dan yi turus yanda taga zaman
kafin ta juya Madu yace
‘Ga Balaraban nan Abba ta zo.’
Duk suka juyo suka dubeta yayinda Saudah ta zaro ido, Abba yace
‘Au, ai sai ki karaso Bismillah.’
Ya nuna mata wajen ta zauna tana zare ido da mamakin yanda ta ji kamar dama ita ake jira, ya dubi Baba
Yalwa yace
‘Ta ce itace ta fita da zancen itace mai wanken wanken Saudah din.’
Baba tace
‘To faduwa ta zo daidai da zama.’
Ta gaisa da Baba da su Baraka da suke zaune suna kallon ikon Allah.
Baba Yalwa ta sake dafa Mommy tace
‘Allah yayi miki albarka kuma Allah ya kareki da zuri’arki daga duk wani abu da ake zarginki da shi. Ki yi
hakuri, ki yi hakuri! Tabbas na san wannan ba karamim abu bane kuma dama duk wanda aka cewa yayi
hakuri an cuceshi. Kiyi hakuri saboda Allah ba saboda mu ba kinji ‘yata, in sha Allahu komai zai wuce.’
Ta juya ta dubi Saudan tace
‘Baki kyautaba Saude, abinda kika yi zaluncine babba wallahi. Idan dai ban bata a lissafi ba yarinyar nan
tun kafin a haifeki take gidan aure bata tafi bariki ba sai yanzu, ki dubeta kice wai ta je yawon bariki!
Haba ke kuwa. Ai ko babu komai ka fadi alkhairi ko kayi shiru, ko ma me tayi miki ai wannan ba sharrin
da zaka yiwa mumini bane.’
Ta share hawaye tace
‘Wallahi kuskurene Baba, kuma ba zan sake ba. Wallahi Baba nima tsautsayi ne amma na san ba haka
take ba wallahi.’
Ta dubi Mommy wadda har yanzu kanta yana kasa tace
‘Kiyi hakuri don Allah Mommy, wallahi kuskurene da tsautsayi. Kuma wallahi na san ba haka kike ba don
Allah kiyi hakuri.’
Shiru tayi ba tare da tace komai ba, ta sa gefen mayafinta ta share hawayen da ta kasa hana shi fitowa.
Shirun ya tsawaita kowa yana saurarensu, da taga dai bazata amsaba ta dan matsa kusa ita ta dafa
hannunta wanda yake ajjiye a kan cinyarta tace
‘Kiyi hakuri Mommy kin ji.’
Ta dago ta dubeta suka hada ido kowacce da hawaye a makale a idonta tace
‘Na hakura, amma zan cigaba da yi miki addu’a abinda kika yi min Allah yayi miki.’
Kafin ace wani abu ta zare hannunta ta mike da sauri ta wuce dakinta ta shiga ta turo kofar. Gaba daya
suka bi kofar da kallo Abba ya mike zai bita kafin ya yi taku biyu Madu ya wuceshi ya bita dakin ya turo
kofa, don haka Abban ya koma ya zauna jikinshi babu kwari. Ya kalli Baba yana nuna Balaraba yace
‘A fadarta dai ga wadda ta fita da zancen nan kuma itace take ta yadawa a unguwa.’
Ta dago kai firgigit tace
‘Wallahi Alhaji ba ni bace.’
Maman Farida tace
‘To wacece? Ba ke kika gayawa su hajaraye ba da sauran ‘yan unguwa.’
Ta koma ta sunkuyar da kai da suka hada ido da Maman Farida don sai yanzu ta gane ta. Baba ta dubeta
tace
‘Baiwar Allah kin cutar damu matuka kuma kin cutar da kanki, ina fatan dai yanzu kinji daga wadda kika ji
zancen a bakinta tace karya takeyi ko? Allah ya sa ba dake za mu je kotun ba.’
Ta karkada da kai cikin rawar murya
‘Wallahi na ji Hajiya dama tsautsayi ne wallahi.’
Abba ya dubeta yace
‘Ita wadda tace miki za a saka mata kanjamau din gata nan ta dawo sai dai ko kece yanzu kike fama da
kanjamau din baki.’
Ta sake gurfana
‘Allah ya huci zuciyarka Alhaji, wannan ma kuskurene in sha Allahu ba za a sake ba.’
‘Idan kika sake shigo min gida kuma hukumace zata rabamu dake, tashi ki tafi.’
Ta tashi sumi-sumi ta fice zuciyarta na dakan uku-uku, lallai yau an yi mata tonon silili. To amma ai ba
laifinta bane fada akayi ta ji, ta fice daga gidan cikin sauri ta bar wajen.
Baba Yalwa ta mayar da kallonta kan Baraka tace
‘Ki bata hakuri kinji, abun da ciwo. Na santa tana da gudun magana kuma gwargwado tana da kiyaye
hakkin wani a kanta, amma ayi mata irin wannan babban sharrin kuma ace an fara gudun mutum a
unguwa kinga ai an cutar da ita da yaranta ba kadan ba. Ki sake tausonta don Allah, hakuri bai taba zama
sharri ba kin ji. In sha Allah komai zai wuce.’
Ta jijjiga kai tace
‘Hakane.’
‘Allah yayi muku albarka gaba daya.’
Suka amsa
‘Amin.’
Sukayi shiru babu abinda kake ji sai shesshekar kukan Saudah kasa-kasa. Baba Yalwa tace
‘Ai kuma shikenan, idan kika bari kika zauna lafiya komai zai wuce da ikon Allah. Amma don Allah ki
kiyaye bakinki.’
Kai kawai ta iya jijjigawa alamar toh. Baba Yalwa ta mike tana fadin
‘Ni bari na tafi don me tasi yana jirana a waje.’
Ta dubi Mubarak wanda tunda aka fara magana bai ce komai ba tace
‘Kuyi hakuri ka ji, Allah ya huci zuciyoyinku kuma Allah ya kara albarka a rayuwarku da ta iyalanku.’
Ya amsa
‘Amin.’
Baraka ta mike yayinda Maman Farida ma ta mike tayi musu sallama ta riga Baba Yalwa wucewa. Suna
gama yin sallama Baraka ta wuce dakin Rabi yayinda Salim ya rufa mata baya. Baba Yalwa ta dubi Sa’a
wadda gaba daya an manta da itama a wajen tace
‘To Sa’ade ni na tafi, Allah ya kiyaye hanya kya gaida mutanen Bichin.’
Ta mike daga inda take zaune a kan kafet jikin kujera tana fadin
‘To Baba ai nima tafiyar zan yi, dama munyi sallama shigowa nan nayi mu gaisa da Rabin na tarar da
wannan al’amari.’
Gaba daya a tare suka fice bayan Abba ya sanar da Mubarak zai raka Baba, Ahmad ya karbi jakar Baba
Yalwa suka rakata mota shi da Abban. Sai da ya bude mata kujerar baya ta shiga ta zauna sannan ya
mika mata jakarta, ta karba ta rike hannunsa don haka ya sunkuyo ya leka cikin motar sosai. Bayan sun
hada ido tace
‘Kuyi hakuri ka ji Ahmadu, komai zai wuce da ikon Allah. Ka sake bawa Mommy hakuri ka ji.’
‘To Baba.’
Yayi mata sallama ya wuce ya bar Abban a nan. Ya sunkuyar yace
‘Na gode Baba, Allah ya bar zumunci, sai na zo.’
‘To Usmanu kayiwa Rabi a hankali don gaskiya abun da ciwo kuma suma yaran ka bisu a hankali don
ransu ya sosu. Allah ya warware.’
Suka ja mota suka tafi yana daga mata hannu. Da sauri ya dawo cikin don ya bar Mubarak shi kadai a
falon wanda kafin ya shigo ma Ahmad yana zaune a wajen Mubarak din. Bayan Abban ya zauna Ahmad
ya tashi ya shige dakinsu, ya dubi Mubarak din yace
‘Na barka kai kadai, afuwan.’
‘Um babu komai ai, Allah ya kiyaye gaba.’
Baya son wani dogon surutu a halin yanzu don haka ya mike ya mikawa Abban hannu yace
‘Bari na wuce don Baraka ba yanzu zata tafi ba ina jin.’
Yayi masa rakiya zuwa kofar falon ya koma ciki ya zauna a jigace kamar wanda yayi wata tafiya mai nisa.
Kukan da Rabi takeyi ya daga masa hankali, yanzu ya zai yi da ita? So yayi ace Madu ya barshi ya bita don
ya lallasheta amma ya riga shi, yanzu ma so yake ya shiga dakin amma su Baraka da suke ciki ita da yaran
su suka saka ba zai shiga ba. Nan ya zauna a falon kanshi a jagule, kamata yayi ace yanzu yana cikin jin
dadi saboda sun fasa zuwa kotu amma kuma yanayin da Rabin take ciki ya hanashi sukuni ko daya.
………..
Tana shiga dakin ta zauna a gefen gadonta tana share hawaye, bata taba zaton Abba zai yi mata haka ba.
Ta dai yi tunanin da Baffa yana nan da yanzu shi zai shiga maganar, bata zata zai kaiwa Baba Yalwa
zancen ba. Maganganun da suke cikinta wadanda take so ta gayawa Saudah din suna da yawa kuma
suna da zafi ba zata iya a gaban Baba Yalwa ba shi ya sa kawai ta taso ta bar wajen. Ita din ma a yanzu
yanda kowa ya riga ya bata hakuri ba zata bari a kai ga zane Saudah ba, ta dai so kawai aje kotun a yi
musu iyaka. Amma hakan ma babu komai kowa aniyarshi ta bishi. Abu dayane yake tsaya mata a rai
yanda labarin ya baza unguwa don kawo yanzu an canza labarin wai kishiyarta ta yi yaji saboda Rabin ta
dawo tana dauke da kanjamau shi yasa ita ta tafi. Amma duk da haka ta san akwai Allah kuma in sha
Allahu komai zai wuce. Shigar Madu ne ta katse mata tunani, ya karasa ya zauna a kusa da ita ya sakalo
hannunshi ta kafadarta yace
‘Kiyi hakuri Mommy, idan ta kara yi miki wani abu wallahi sai dai ta bar gidan nan ko mu mu bar masa
gidan.’
Ta dago ta kalleshi tana murmushi duk da hawayen da yake fuskarta ta lakace masa hanci tana fadin
‘To shugaban rigimammu.’
Yake kawai yayi saboda yanda zuciyarsa take suya, ta kwantar da kanta a kan kafadarsa suka yi shiru
kowa da abinda yake tunani. Suna nan zaune a haka Baraka ta shigo ta mayar da kofar ta rufe, ta karasa
ta zauna ta daya gefen nata yayinda ita kuma ta daga kanta daga kafadar Madu ta mayar kafadar Baraka
sukayi shiru. Jimawa kadan Salim ya shigo ya tsuguna a gaban mommy ya dafa gwiwoyinta yace
‘Mommy.’
Ta dago ta kalleshi, yayi murmushi ta mayar masa. Suka zauna a haka na tsawon wani lokaci sannan
Madu ya mike zai fita, Baraka tace
‘Ka cewa Baba Mubarak ya tafi zan taho.’
Yana fita Salim ma ya mike ya bi bayansa. Suna rufe kofar ta daga kanta daga kafadar Baraka tace
‘Kinga abinda yayi ko?’
‘Uhm, na gani Bibi. Ai idan bai yi haka ba bai cika namiji ba, kansu kawai suka sani.’
Ta share kwalla tace
‘Hakane kam, don shi cewa yake wai bai kamata ba ace kamar shi iyalansa suna shari’a shi yasa yake so
nayi hakuri ba don kada ayi mata hukunci ba.’
Baraka ta jijjiga kai tace
‘Hmm.’
Ta sake share kwalla tace
‘Shikenan ai sunyi yanda suke so.’
‘Allah ya kyauta.’
Suka sake yin shiru na dan lokaci, jim kadan ta dubi Barakan tace
‘Dama kin tsayar da Mubarak kun tafi.’
‘Babu damuwa yanzu zan je na tafi Bala yana jirana a gidan Yaya Shafa yanzu za mu wuce. Bari ma na
kirawota kada taje kotun ta tarar ba ma can.’
Sai da ta kirawo Yaya Shafa ta sanar da ita sannan tayi sallama da Rabin wadda ta mike zata yi mata
rakiya. Barakan ta dubeta tace
‘Kiyi zamanki Bibi, za muyi waya. Yanzu haka ‘yar tsurkunki Sa’a tana nan don ban san ma wa ya gayyato
muku ita ba.’
Tace
‘wallahi nima ina mamakin ganinta amma daga baya zan ji bayanin na san.’
Sukayi sallama Baraka ta fice, tana fitowa falon ta tarar da Abba shi kadai yana zauna. Kafin ta karasa
inda yake ya mike tsaye yana dan murmushi
‘Hajiya Baraka har kin fito?’
‘Eh, za mu kama hanya.’
‘To mun gode fa, a dai yi mana afuwa don Allah. Allah ya bar zumunci.’
‘Amin ya Allah, Allah ya rufa asiri.’
Sukayi sallama ta fice daga falon yayinda shi kuma yayi wuf ya fada dakin Mommy.
…………
Baraka tana fita ta koma ta zauna a gefen gadon, hawayen da ta rike ta karfin tsiya suka kwace. Kenan
yanzu haka zata cigaba da shiga mutane ana nunata, wadanda suka zake ma har sunayi mata tambayoyi
na wulakanci. Abinda kawai yake tayar mata da hankali kenan, duk da ta ga Balaraban tana zaune aka yi
magana amma ai wannan abu ne na cikin gida ba kamar ace a kotu bane a gaban alkali. Amma babu
komai Allah zai saka mata. Gidan yayi mata kunci gaba daya, ina ma zata samu wani wajen da ba nan ba
ta dan huta ko zuciyarta zata sami hutu. Ba tare da tayi wani tunani ba ta mike ta janyo dan kit din
akwatunanta ta ajiye a kan gado, ta koma wardrobe ta fara zaro kaya tana sakawa. Set biyu kawai zata
dauka, gidan Yaya Shafa zata je ko kwana biyu tayi ko zata ji sanyi a zuciyarta. Tana tsaye a gaban
wardrobe aka bude kofar aka shigo, ta juyo don ganin waye. Ga mamakinta Abbane wanda ita ta zata ya
wuce kasuwa ko kuma yana wajen Saudah duk da ta san yau zata karbi girki. Da sauri ya karasa cikin
dakin a dan razane yana fadin
‘Ya naga kamar hada kaya kike yi?’
Bata san tana matukar jin haushinsa ba sai ya zu da ta ganshi, don wannan maganar da yake mata ji tayi
kamar ta rufe shi da duka. Ta bata rai kwarai tace
‘Gidan Yaya Shafa za ni ba wai yawon barikin zan kuma tafiya ba.’
‘Sub….’
Ya bude baki zai yi magana ta katse shi kafin ya karasa
‘Ba wai dadewa zan yi ba gobe zan dawo ina dai so ne na sami natsuwa kawai.’
Ta ajiye hijabin da ta dauko a kan gadon ta koma cikin wardrobe din ta cigaba da dubawa.
Da sauri ya karasa ya sha gabanta kafin ta karasa wardrobe din ya rike hannuwanta yana magana cikin
damuwa
‘Kada kiyi min haka Rabi, don Allah kiyi zamanki. Wallahi duk abinda kike so a nan din ma za ki samu
amma babu inda za ki.’
Ta zare hannanyenta daga nashi ta wuce wardrobe din
‘Ai gobe zan dawo.’
Ya karasa ya dafe kayan da take kokarin dauka
‘Babu inda za ki fa Rabi.’
Ya kama hannunta ya dawo da ita gefen gadon ya zaunar da ita ya tsuguna a gabanta
‘Kiyi hakuri Rabi, na san an yi miki ba dai-dai ba shi yasa nake baki hakuri kinji. Babu inda zaki sake fita
daga gidan nan ki tafi, don Allah kada ma ki sake wannan tunanin. Duk abinda ma kike so zan yi miki,
idan ma so kike na raba muku gidan ki gaya min kafin gobe in sha Allah za a raba. Ko ma me kike so ki
gaya min zan yi miki in sha Allahu.’
Ta kalleshi suka hada ido, nan da nan hawaye suka wanke mata fuska yayinda shi kuma ya kara rikicewa
jikinsa har rawa yake. Ya kasa cewa komai binta kawai yake da kallo yana rike da hannuwanta. Ta zare
hannuwanta ta rufe fuskarta da su tana ajiyar zuciya. Jim kadan ta sauke hannuwan idonsa a kan nata ba
tare da hawayenta ya daina zuba ba tace
‘Ka san me nake so Usman?’
Har tsakiyar kansa yaji wannan kiran don ba zai iya tuna lokacin da ta kirawo sunansa haka ba, sai dai
tace ‘man’. Ya jijjiga kai alamar a’a.
‘So nake da kai da matarka ku barni na huta don Allah.’
Mamaki ya maye gurbin firgicin dake fuskarsa ya cigaba da binta da kallo
‘Tunda ka kara auren nan ban huta ba. Shekara ashirin da hudu muna tare da kai baka taba yin gaba ko
fushi da ni ba sai da ka kara auren nan. Kai ka auro matarka amma ni kake so nayi mata hidima, ita kuma
duk wani sharri da fitnarta a kaina take juyewa ban san me nayi mata ba. Idan bata sani ba ka gaya mata
tun kafin a haifeta nake tare da kai bamu taba samun sabani ba sai da ka aurota, yarinyar da Madu ma
ya girme mata. Kada ka manta duk wani abu da nake so nake da buri a rayuwata na hakura da shi na zabi
zama da kai da hidimarka amma a ‘yan shekarun nan gaba daya nema kuke kai da matarka ku hana ni
sukuni. Ban taba yaji ba amma a dalilinta ka kalli tsabar idona ka koreni daga cikin gidanka Usman, kuma
ba ni
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good