Showing 129001 words to 132000 words out of 196754 words
Chapter 44 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
bari ma ayi sallar asuba tunda yanzu bacci yake yi, don Baba ce ma tace na sanar da kai
yanzun.”
“Toh, Allah ya kara lafiya ina tafe dai in sha Allahu.”
Ya ajiye wayar ya dubi Saudah wadda itama ta tashi ta zauna tun lokacin da ya fara wayar, yace
“Baffa ne bashi da lafiya.”
“Allah sarki, Allah ya bashi lafiya.”
“Amin.”
Ya amsa yana mikewa tsaye
“Nima alwala zan yi kawai na tafi idan na je can na yi Sallah.”
Sai da ya kirawo Madu sannan ya shiga alwala. Yana fitowa ya karasa shiryawa sannan ya fice. A tsakar
gidan ya tarar da Madu, nan da nan suka kama hanya. Suna isa Madu ya kirawo Tijjani ya shigar da su, da
yake likita yace kada suyi hayaniya saida Baba Yalwa ta janyo su suka fito sannan suka zauna a kofar
dakin suka gaisa.
“Jinishi ne yake ta hawa tun shekaran jiya.”
Abba yace
“Yana shan maganin kuma?”
“Wallahi yana sha, amma ka ganmu tun jiya da jinin ya haye ya ki saukowa, ban sani ba ko idan ya farka
da yake an yi masa allurai kafin ya kwanta.”
Jimawa kadan suka jiyo kiram asuba don haka suka fita don su sami waje suyi Sallah suka barshi da Baba
Yalwa. Jirgin karfe bakwai da rabi Aliko ya biyo daga Lagos don haka kafin karfe tara yana asibitin, kuma
har lokacin Baffan bai farka ba. Nan suka zauna a waje da su Abba suna Dan tattaunawa da hirar yaushe
gamo. Sai wajen karfe goma saura Baffa ya farka, Baba Yalwa da take bakin kofar dakin itace ta jiyo
muryarshi. Nan da nan Tijjani ya kirawo ma’aikatan jinya suka taho da kayan aikinsu. Bayan sun gama
gwaje gwajen Aliko ya dubi nurse din yace
“Hajiya jinin ya sauka.”
“Toh, yana dai sauka. Ya dan sauka kadan amma still yana bukatar ya kara hutawa don haka kada kuyi
masa surutu da yawa.
Tayi musu sallama ta fice.
Aliko ne ya fara matsawa yana gaida Baffa, bayan ya amsa gaisuwar ya fara kokarin tashi zaune. Abba ya
matsa ta daya gefen shi da Alikon suka taimakawa Baffan ya zauna. Ya dafa hannun Aliko yace
“Sai da Tijja ya taso ka ko?”
“Babu komai Baffa ai da yake yau Juma’ah sai ma ranar Lahadi zan tafi in sha Allahu.”
Ya nemi ruwa aka bashi ya sha, bayan ya ajiye ya sake dubanshi yace
“Ka dinga kular min da kannenka ka ga dukansu mata ne ka ji Aliko.”
“Ai ana kula da su Baffa.”
“Toh Allah yayi muku albarka, Allah ya sawa ‘yayanku da dukiyoyinku albarka.”
“Amin.”
Gaba dayansu suka amsa har Baba Yalwa da take zaune a kan tabarmar dake shimfide a dakin. Jim kadan
Baffa ya sake dafa hannun Abba da yake ajiye a gafen gadon yace
“Alhajin Allah baka nemo min ‘yata ba.”
Ya sunkuyar da kanshi idonshi ya fara kokarin cika da hawaye, a gajiye Baffan yace
“Za’a ganta in Sha Allah, sai dai kawai nace ka rike ta amana.”
Ya dubi Aliko da su Madu daka zazzaune a gafe yace
“Ku dinga jin tausayin matanku, wallahi sune rufin asirinku. Wata matar ba za ka gane itace bangon da
ka jingina a jiki kake jin dadin rayuwa ba sai bayan ta barka don haka ku yi hakuri ku zauna lafiya da
iyalanku. Har ku da bakuyi auren ba, mace idan ta haifar maka da ko daya ne hakuri kake da ita in dai ba
wata alfasha ta zo da ita ba.”
Duka suka yi tsit, ya juya ya dubi Madu yace
“Madun Kano za a ga Mommy in sha Allah, ku cigaba da addu’a”
“In sha Allahu Baffa.”
“Allah yayi muku albarka gaba daya, Allah ya baku arziki da rufin asiri da iyalai na gari.”
Suka dan yi shiru, Baffa ya fara kokarin zame filon ya kwanta, Madu ya taimaka masa. Jimawa kadan
likita ya zo ya duba shi, bayan ya gama gwaje gwajesa yace da su su fita don Baffa ya samu ya kara yin
bacci. Don haka duka sai suka fice suka barshi da Baba Yalwa. Nan suka samu inuwa suka zauna gaba
dayansu Abba da Madu sai Aliko da Tijjani. Basu dade da zama ba Baba Yalwa ta fito ta same su tace
“Ya yi bacci, ai za ku iya tafiya in ya so zuwa jimawa ko Khalifa sai ya kawo mana abinci don yanzu duk ga
kayan shayi nan Tijjani ya siyo ni ma yanzu zan karya.”
Aliko yace
“Da yake nima ba wani abu na zo yi Kanon ba in sha Allah idan na je gidan mota zan dauko na dawo.”
Ya dubi Tijjani yace
“Ka zauna ka Taya Baba zama idan na dawo sai ka wuce ka tafi office din.”
Suka yi mata sallama suka kama hanya. Aliko ya tafi gidansa na Kano shi kuma Abba da Madu suka tafi
gida.
Kafin su zo gidan ma Saudah ta fice don tana da lecture, itama Zulaihan ta tafi makaranta don haka babu
kowa a gidan. Sai da suka gama shiryawa sannan Abban yake tambayar Madu ya za su yi da abincin
Baffa, nan suka yanke shawara in an jima kadan Madu zai sayi abinci ya kai musu. Kafin su karasa kasuwa
sai ga wayar Tijjani yana kuka
“Abba Baffa ya rasu yanzu.”
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.”
Kafin ya gama magana Tijjani ya ajiye wayar. Sai da ya ji shiru sannan ya ajiye wayar, nan da nan
hawayen ya wanke masa fuska. Ya dubi Madu wanda shi ma ya riga ya fuskanci abinda yake faruwa yace
“Mu koma asibiti Muhammadu, Baffa ya rasu, ba ni da uba yanzu. Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.”
Ya karya kwana suka kama hanyar asibiti, kafin su isa har Aliko ya riga su isa. Cikin yanayi na jimami da
damuwa sukayi duk wasu cike cike aka saka gawar Baffa a ambulance aka kama hanyar gida kowa na
kuka babu mai rarrashin wani. Sai da suka isa gida sannan suka yanke shawarar tunda Juma’ah ce gashi
rana tayi to a kai jana’izar masallacin Juma’ah dake nan unguwar, nan da nan kuwa aka bayar da
sanarwa.
…………..
Da yake ranar Juma’ah ce tun kafin Sha biyu ta dawo daga aiki. Suna zaune a daki suna hirarrakinsu
yayinda Baraka take duba Facebook a wayarta. Kan post din Baba karami ta zo wanda ya saka hoton
Baffa da rubutu
‘Bango ya Fadi, Allah ya sa kana Aljannah Baffa, Allah ya baka ladan zumunci.’
Bayan ta gama karantawa sai kawai ta mikawa Rabi wayar tana fadin
“An muku rasuwa fa.”
Tana gani ta dafe kirji
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.”
Tuni hawaye ya fara bin idonta, sai da ta dau lokaci tana kallon hoton tana hawaye, ta mikawa Baraka
wayar tace
“Lallai an yi mana rasuwa, tabbas bangon zumunci da amana ya fadi.”
Baraka ta taso daga kan gadon da take kashingide ta dawo kusa da Rabin a kan kujera tana fadin
“Allah sarki, Allah ya sa ya huta.”
Ta share hawayenta tace
“Yanda kika san shi ya haifeni haka yake tattalina, ga shi da zumunci. Don ni duk dangi su Abban Khalifa
ko wadanda suke uwa daya uba daya basa kaunata da yarana kamar yanda Baffa da zuri’arshi suke
kaunarmu. Shi kansa Abban jin sa yake kamar ubansa. Allah sarki Baffa.”
Jimawa kadan ta sake share hawaye tace
“Allah sarki Baba Yalwa, Allah ya baki juriya.”
“Amin”
Sai can da aka jima bayan ta nutsu ta dubi Barakan tace
“Za mu iya tafiya Kanon da wuri gobe ko?”
“Kwarai kuwa, ai in sha Allahu karfe shida za mu kama hanya.”
“Yauwa, ina so na je nayiwa Baba Yalwa da su Amina gaisuwa. Ko ban je wa kowa ba na je wa Baba
matar nan tana kaunata sosai.”
“Allah sarki, da wuri za mu tafi in sha Allahu. Amma fa sai mun fara zuwa gidan Yaya Shafa, don saboda
kada muje ki ruda min yara a gidan makoki.”
Suka yi dariya Rabin tace
“Sai an jima ma zan kirawo Mubarak, ya fara sanin inda nake na dan tsara mana shi don na san Yaya
Shafa da Yaya Munzali sai sun yi fada da mita. Idan ya goyi bayanmu ba zai bari su saka ni a gaba ba kin
san shi ‘dan darune.”
Tayi dariya tace
“Na wajena kenan, za ki sa ya yi min hayaniya kenan ‘dan kanina don na san sai yayi.”
Suka fashe da dariya. Yaya Munzali ne na farko a wajen iyayensu, sai Yaya Shafa daga ita sai Rabi sannan
Mubarak Dan auta. Tun suna yara yake da son girma don haka kullum cikin fada yake da Rabi a kan cewa
itace kanwarshi, daga baya ma da ya fi ta girma haka ya dinga cewa abokanshi kanwarsa ce. Bayan da
aka dawo da su Baraka gidan kuma sai ya ce toh ya yarda Rabi ta girmeshi amma dole Baraka kanwarsa
ce; da yake ita Rabi shekara daya ta bawa Barakan. Haka suka taso kullum drama don haka in Baraka
tana son tsokanarshi sai tace ‘dan kanina.
Yanzu da suke shirin zuwa Kano sun san tabbas sai sun sha fada musamman a wajen Yaya Shafa, duk da
ba wani sabon abu bane amma suna bukatar Mubarak ya goyi da bayansu. Musamman da yake shi in ya
tashi rigimarsa har Yaya Shafa da Yaya Munzalin ma saurara masa suke yi. Baraka ta nisa tace
“Gobe akwai drama.”
EPISODE 29
Sai can bayan la’asar suna zaune suna hirarsu sannan Rabi ta kirawo Mubarak, ta sa wayar a hands free
“Salamu alaikum.”
Tayi masa sallama bayan ya amsa wayar. Ya dan yi shiru kamar yana sauraron ta ta kara magana sai
kuma ya fara amsa sallamar kamar me koyon karatu
“Wa alaikum salam, Rabi.”
“Na’am Abban Sabir.”
Mamakinshi ya kara tsananta yace
“Rabi, daga ina kike kira na don Allah.”
Dariyar Baraka ce ta bashi amsa yace
“Baraka ce take dariya? La ilaha illal Lahu. Amma matan nan kun raina mana hankali, yanzu daman duk
abun nan kina gidan Baraka kuke raina mana hankali?”
Barakan ce ta bashi amsa tana dariya
“Toh da kai me ka zata, muna tare babu inda taje.”
Shiru yayi ya kasa magana, Rabi ce ta karya shirun
“Kana ji ko, ai gobe za mu zo Kanon. Na ga Baffa ya rasu in sha Allahu zan je gaisuwa.”
“Wallahi kuwa, ai Yaya Munzali da shi aka yi jana’izar. Ni ma da sai ranar Lahadi zan je amma in sha
Allahu Goben zan taho sai mu hadu a gidan Yaya Shafan.”
Baraka tace
“Yauwa dan kanina sai mun hadu.”
“Rabi, muna haduwa ki fara bani hakuri idan ba haka ba za mu dambace da Baraka.”
Tayi dariya tace
“Ni kam ai sai dai na matsa ‘yayanku sa raba ku.”
Shima dariyar yayi yace
“Amma gaskiya kun tayar mana da hankali kuma kun dauki alhakin mu wallahi, kusan kwana arba’in
baku bari mun huta ba. Ke Baraka harda wani zuwa jaje, sai kun nemi yafiyar mu wallahi.”
Suka kyalkyale da dariya, Rabi tace
“Kada ka gaya musu ka ganni, ka barsu kawai goben ma hadu.”
“Wato sai kun kara musu kwana daya na gashi kenan? Toh zan duba na gani.”
Tunda ya fadi haka sun san ba zai fada ba, Baraka tace
“Idan fa muka je goben za mu dawo tare ni da Bibi fa.”
Da mamaki yace
“Ah, me kuma Rabin zata dawo yi Jigawan, ai ko bazata koma dakinta ba sai ta zauna gidan Yaya Shafa.”
“A’a nan za mu taho, ai kaga cewa yayi ta fice masa daga gida. Sai dai kuma a zauna a mayar da magana
in ya nemi afuwa a duba a gani, ai ba neman kai muke da ita ba.”
“Kuma fa hakane, don wallahi ko ni ya ban haushi sosai. Ka kori mace da azumi sai kace wani jahili.”
“Toh ai shine. Dama yanzu idan munje ba wajen shi taje ba, kawai, ziyara muka kai gashi nan kowa ya
san inda take yanzu. Amma fa Usman sai ya yi biko in ta yarda ta koma idan bata yarda ba a murdewa
auren wuye tunda yanzu yana da amarya.”
“In sha Allah bama za a murde masa wuyan ba, amma dai kam sai yayi biko.”
“Yauwa mutumina.”
Sukayi sallama suka ajiye waya. Rabi ta dubi Baraka suka tafa tace
“Kinga yanzu da karfi na zan je, na san ko su Yaya Shafa sun so takura min Mubarak zai shigar min.”
“Haka ne.”
Dadin da Mubarak ya ji da ya samu Rabi ji yayi kamar ya tafi Jigawan yanzu, gashi yayi musu alkawarin ba
zai gayawa kowa ba da yanzu zai kirawo Yaya yayi masa albishir. Har ya dauki waya zai kirawo matarsa
Anti Hauwa ya sanar da ita sai kuma ya tuna, yaranshi suna waya sosai da su Khalifa don haka in ya gaya
mata sai ta gayawa yaran ba mamaki kuwa kafin gari ya waye labarin ya isa Kano. Don haka shi kadai ya
ke ta walwala da jin dadi bakinsa yana kaikayi amma ba halin ya fada.
Sai da dare yayi kafin su kwanta Baraka ta kirawo Yaya Shafa ta sanar mata za ta zo gobe wajen karfe
goma idan za ta sami lokaci tana so su je gaisuwar Baffa tare. Ta ce mata tana da aiki amma za ta dauki
excuse don haka su hadu a gidanta don Mubarak ma da Yaya Munzali duk nan za su hadu su je a tare
duk da ita da Munzalin sun je.
Suna idar da sallar asuba suka fara shiri, wajen karfe shida saura direban Baraka wanda yake kaita Kano
ya iso gidan. Sai da suka shirya tsaf sannan suka zauna Shan shayi a falo suna yi suna hira. Zahra ce ta
sauko daga sama inda dakinta yake, bayan ta gaishe su tace
“Inna fita zaku yi?”
“Eh, kin manta jiya na ce miki za muje Kano.”
Cikin yanayi na shagwaba tace
“Lah, Inna ai na zata sai da yamma shi yasa na kwanta bacci bari kawai na sa kaya sai mu tafi.”
Baraka ta kalleta cikin mamaki tace
“Au dama na ce dake za mu je ne?”
Ta langabe iai alamar magiya
“Inna ko jaka ma sai na rike miki fa, baki taba zuwa da ni Kano ba fa haba Inna ta.”
“Toh ai baki shirya ba, wani zuwan ma je dake.”
Ta dawo kusa da Rabi ta kwantar da kai a kafadarta tace
“Inna ai da ni za ki je ko?”
Ta kalleta da gefen ido tana murmushi tace
“Eh, je ki shirya maza ki taho mu tafi.”
Da gudu ta nufi benen don ta je ta shirya, Baraka ta dubi Rabi tace
“Kin san dadewar da takeyi a wanka kuwa, ai sai mun kusa azahar bamu tafi ba.”
Ta juyo kafin ta gama hayewa benen tace
“Ba ma sai na yi wanka ba Inna, riga kawai zan canzo.”
Kafin minti goma ta sauko tana dauke da wayarta ta dauki jakar Mommy tace
“Inna bari na rike miki jakar sai na sa wayata a ciki.”
Ta bude jakar ta jefa wayar tata, bayan ta rufe ta mika hannu tacewa Baraka
“Inna kema kawo sai na rike mana duka”
“A’a daya ta ishe ki, muje kawai.”
Karfe shida da kwata suka dau hanya suna ta hirarrakinsu. Sai da suka shigo garin Kano sun kusa
karasawa gidan Yaya Shafa Rabi ta kirawo Mubarak a waya
“Mu fa mun iso Kano mun ma kusa gidan Yaya Shafa, sai yaushe zaka taho.”
“Ai nima ina cikin Kanon, ba jimawa zan karaso in Sha Allah.”
“Toh sai mun hadu.”
……….
Bata yi mamaki ba da ta ji an bude gate mota ta shigo ta san Baraka ce. Tana tsaye a kichin tana hada
shayi tana yiwa mai aikinta bayanin abinda za ta yi na aikin gida kafin ta dawo ta jiyo sallama an shigo
falon. Muryar Rabi bata yi kama da muryar Baraka ba da sai tace Barakan ce, nan ta bar hada shayin
cikin hanzari ta leko daga kicin. Tabbas Rabi ce, yanda ta ganta cikin walwala da koshin lafiya tayi haske
sannan ta na sanye da tufafi masu kyau ta san lafiya kalau. Bata ma kula da Baraka da Zahra ba ta karaso
cikin sassarfa da hannuwanta ta budesu sama kamar mai shirin rungumar wani, tana karasowa ta kama
fusakar Rabin kamar mai so ta tabbatar da wani abu ta kalleta suka hada ido. Sukayiwa juna murmushi
sannan Rabin ta fada jikinta suna kwalla tace
“Rabi.”
Tana daga kai sai ta hango Baraka a bayan Rabin don haka cikin gaggawa ta janye jinkinta daga na Rabin
ta kalli Rabin da har yanzu murmushi take da kwalla a idonta tace
“Wajen Baraka kika tafi kika buya ko?”
Rabi da Baraka suka kyalkyale da dariya, ta share kwalla tace
“Toh ba gani ba Yaya.”
Ta bata rai ta harari Rabin sannan ta juya ta harari Barakan, ta sunkuyar da kanta tana murmushi tace
“Tuba muke Yaya Shafa.”
Sai a lokacin sannan ta kula da Zahra da take tsaye rike da jakar Rabi tana kallon abun mamaki. Ta karasa
ta kamo hannunta tana ja tace
“Shigo ‘yata ki zauna kin ji.”
Ta sake banka musu harara tace
“In kun ga dama kar ku zauna.”
Suka kalli juna suka kunshe baki suka karasa suka samarwa kansu wajen zama, gaba daya suka yi shiru.
Zahra ce ta karya shirun ta hanyar gaisawa da Yaya Shafa. Mai aikinta ce ta shigo da ruwa da lemuka a
faranti ta kawo ta ajiye musu. Yaya Shafa ta dubi Baraka tace
“Yanzu don Allah duk wannan lokacin tana wajenki kika dinga zuwa ana jaje dake kina kallonmu muna
kuka, amma wallahi Baraka baki da tausayi.”
Ta sauka daga kan kujerar ta tsuguna kusa da gwiwarta tace
“Tuba nake Yaya Shafa wallahi ita tace kar na fada.”
Ta kawar da kanta ba tare da tace komai ba, ita ma Rabin ta sauko ta tsuguna kusa da Barakar tayi fuskar
tausayi tace
“Yaya Shafa don Allah kuyi hakuri, in sha Allah ba za mu sake ba.”
“Ai shike nan, Allah ya shirye ku tunda ku dai ba za ku girma ba. Allah ya ji kan Baffa dama yace Rabi da
Baraka idan abun kirki za kuyi tare idan ma abun tsiya ne tare kuke yi babu mai kwabar wani. Ai shike
nan.”
Suka zauna nan a kan kafet din, jimawa kadan Yaya Shafa ta dubi Rabi tace
“Yanzu ke ko tausayin yaranki baki ji ba?”
Ta dubeta kwalla ta cicciko mata ido tana murmushi tace
“Na ji tausayinsu mana Yaya, amma tunawa nayi ni din babu Mai tausayi na idan ban tausayi kaina na
kwatarwa kaina yanci ba. Da azumi fa a gaban yarana da matarsa ya dube ni yace na bar masa gidansa
harda cewa yanzun nan, Yaya ai ko mai aiki ce ta shekara talatin tana maka aiki bata cancanci wannan
korar ba.”
Ta jijjiga kai tace
“Hakane kam, amma dai ai da sai ku sanar da mu inda kike ba wai ku bar mu muna ta lalube a duhu ba.”
Tayi murmushi ta dafa Yaya Shafan tace
“Toh ba gani ba yanzu Yaya.”
Itama Yaya Shafan tayi murmushi tace
“Hakane, amma kuwa kin bamu kashi gaba dayan mu. Shima Usman din yana nan jiya da na ganshi duk
ya fita hayyacinsa sai kace wanda take tsomen shayi da shi.”
Daidai nan Mubarak ya shigo falon da sallama. Kafin a amsa sallamarshi
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good