Showing 51001 words to 54000 words out of 196754 words

Chapter 18 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15362

ta yi sai washe gari za ta dawo. Bayan ta gama bayani ta Zulaihan
tace

“Umma me ya faru a Kadunan?”

Ta galla mata harara tace

“Ubanki me ya faru. Toh aikin da kika kasa zan je na sa ubanki Atiku ya yi min, da ke da su in kun san wata
ba ku san wata ba, daga nan ma na sami yan kudin da zan zo na karbo mana wani taimakon.”

Ta sallameta ta kama hanya sai Kaduna. Bata ita ta isa ba sai bayan azahar, ko da isa gidan babu kowa sai
‘yan aiki su biyu. Da yake sun santa sun yi mata tarba mai kyau suka kirawo matar gidan a waya suka sanar
mata. Anti Hauwa wato matar Atikun lauya ce kuma in ta fita aiki sai karfe hudu suke tashi don haka sai
ta tattara yaranta su biyar ta saka su irin makarantun da in an tashi daga boko za a zarce islamiyya har sai
biyar na yamma, don haka basu dawo gidan ba sai biyar da rabi na yamma. Bata da matsala da Sa’a amma
tana sane da yanda takewa Rabi domin ita suna shiri da Rabin, shi yasa itama duk yanda Sa’an ta so su
zama aminai bata bari ya yiwu ba. Ita Hauwan ta san Sa’an tana saurara mata ne saboda ita tana da kudinta
kuma tana yawan yi musu kyauta, sannan kuma sai su shekara basu hadu ba don haka da sun hadu sai ayi
ta barka kawai babu lokacin da za a zauna tare balle a samu sabani.

Suna shiga gidan suka gaggaisa Hauwa da yara suka huce sama suka barta a dakin baki. Sai bayan isha’I
Atikun ya dawo, nan ya tsaya suka fara gaisawa da Sa’an sannan ya huce saman. Sai da ya gama cin abinci
yana hutawa sannan Sa’an ta same shi a falon saman tace tana son ganinshi, nan da nan Hauwa ta tashi
ta basu waje ta koma dakinta ta cigaba da hidimominta.

Gyaran muray tayi tace

“Dama maganar yara ce ta kawo ni kuma na san kai kadai ne za ka sa ko ka hana saboda ko ba komai kaine
waliyyinsu.”

Yace

“Hakane. Wadanne yaran kenan?”

Tace

“Toh ka san yanzu aure shima ya zama sai da sanayya, tunda in ba haka ba sai a gurbata zuri’a. Zulaihace
dama mun gama magana da Babanta yake so ya bawa Baba Karami aurenta toh amma ka san ni ba shiri
muke da uwarsu ba, idan na je da zancen ma ko an yi niyyar sai tasa a fasa.”

“A’ah fa Sa’a, in dai Hajiya Rabin da na sani ce toh bana jin za ta bada matsala a irin wannan al’amarin. Sai
dai kuma toh shi Baban yana son ta ne kuma ita tana son shi?”

Ta gyara zama

“Toh Allah ya sa. Ba suyi maganar ba amma ai Zulaihan tana gidan tun tuni kuma na san in dai itace da an
ce mata ba za tayi musu ba.”

“Toh amma fa ni wancan satin Baban ya zo min da zancen yarinyar da yake nema a Abujan, kuma mun yi
magana da Yayan ya riga ya ce min na yi bincike a kan family din yarinyar.”

Yanda gabanta ya fadi sai da ta ji kamar zuciyarta za ta iya fasa kirjinta ta fito saboda firgici da takaici, sai
da tayi kokawa sannan ta samo nutsuwarta ta bashi amsa

“Toh ai ka ga ba ayi masa magana an gani ba, kuma gida bata koshi ba a kaiwa dawa? Musamman da yake
Zulaihan a gidansu take tana karatu, duka abinda yake nema a mace zai samu a wajenta sannan kuma a
kulla zumunci.”

Yana jijjiga kai ya bata amsa

“Da wannan don wannan, don kinga yanzu duk manyan families din nan irin haka sukeyi yasu yasu su aurar
da yaransu.”
“Toh nima dai shi na gani, shima kanshi Yayan zai ji dadi sannan Baffa Hassan ma na san babu wanda zai
kai shi farin ciki.”

“Hakane, toh yanzu ke yaushe za ki koma?”

“Gobe in sha Allah ni karfe bakwai ma a hanya za ta yi min.”

Yace

“Toh shike nan, goben ki shirya in naje office ba zan huce awa daya ba sai na dawo mu tafi Kanon na je
naga Yayan.”

Tace

“Toh shikenan, ai kuwa Madallah ka ga sai mu yi abun mu tuwo na mai na.”

Nan sukayi sallama kowa ya shiga makwancinsa. Bai samu yayi maganar da Hauwa ba har gari ya waye.
Kafin dai ta fita aiki ya gaya mata zai tafi Kano in ya mayar da Sa’a sai ya samu ya ga Yayan shi, ba ta kawo
komai ba sukayi sallama, ta kawo naira dubu daya ta bawa Sa’a tace ta yi tsaraba kowa ya kama hanya.

Kafin su isa Kano ta gama zugeshi a kan yanda auren Baba da Zulaiha zai gyara musu zumunchinsu. Suna
isa Kano ya sauke ta a daidai inda za ta sami motar Bichi don shi a kasuwa zai sami Abba da sun gama
magana ya koma Kadunan. Bayan sun gama gaisawa da Abba suka matsa gefe tunda daman Abban ya san
sun yi maganar Khairiyya harma ya ce Atikun yayi masa bincike a kan family dinta. Yayi gyaran murya yace

“Yaya yaron nan Baba ni ina ga Mai zai hana ba za a hadashi da Zulaiha ba, ‘yar wajen Sa’a tunda daman
tana wajen ka, itama za a iya cewa rainon Rabin ce.”

Ya dan yi jim yana kallonshi yace

“Ita waccan yarinyar akwai wata matsala ne a tattare da ita?”

“A’ah ba wata babbar matsala bace sai dai gani nayi gida bata koshi ba a kaiwa dawa? Sannan kuma ita
yarinyar nan uwarta ce ma nake da ta cewa kan ta, ka san kuma mace yanda ta ga uwarta na yi da ubanta
toh haka za tayi da mijinta, in ko hakane toh gaskiya sai yanda uwarta tayi a gidansu uban bashi da wani
tasira.’

“Uhhmm?”

“Eh Yaya, in kuwa haka ne ka ga gara mu yi tuwo na mai na yarinyar da take da jininmu ka muka san
tarbiyyar da aka yi mata.

“Hakane, ban ki ta taka ba. Amma fa ka san ‘dan yau, in ba su suka ce suna son junansu ba sai fa su bamu
kunya.”

“Da wannan, sai dai ita Zulaiha Sa’an ta tabbatar min bata da wani manemi a kasa kuma ubanta za ji dadi
in aka yi hakan. Shi kuma Baba ai yaro ne mai jin magana, na san da zarar ka gaya masa ba zai yi wani
taurin kai ba.”

Abba yace

“Hakane, toh bari ya zo mu gani. In sha Allah za muyi magana duk yanda muka yi kuma zan gaya maka.”
“Toh Allah ya nufa Yaya, don wannan abu ne da za mu yiwa Inna da Baffa, Allah ya ji kansu kuma Baffa
Hassan sai ya fi kowa jin dadi.”

Suka yi sallama ya kama hanyar Kaduna.




Tafiyar su Mommy da sati daya aka saka su Nawwara makaranta, lokacin Nawwara ta shekara hudu ita
kuma Ummi uku. Nawwara kadai ya so sawa saboda shi baya son saka yara a makaranta sai sun shekara
hudu, amma da ta sa shi a gaba da naci sai da ya hadasu. Makarantar bata da nisa sosai daga gidan don
naira talatin ake biya aje, dukansu su biyun aji ‘daya aka saka su wato pre-nursery. Kafin ya saka su saida
yayi mata bayani dalla dalla cewa ita ce za ta dinga daukosu in an tashi, shi kaisu kawai zai dinga yi don
haka sukeyi shi da Rabi. Duka yaran gidan kowa yana da tashi makarantar, gashi ba makarantarsu daya da
su auta ba sannan kuma su auta sai 2:30pm suke tashi subkuwa su Nawwara 12pm ake tashi don haka
babu ma wanda za a iya dorawa daukosu sai ita. Da yake dai lokacin da aka saka su ‘yan Jami’a suna hutu
toh zuwa daukan nasu baya damunta, harma wani lokacin in ta fito taga Salim a kofar gida ta kan hada shi
da Allah ya dauko mata su ko kuma Jamila ta dauko mata su. Tana dai tunanin yanda za ta yi dasu in an
koma makaranta, ga shi level 4 za ta shiga kuma tana da carry overs da take so lallai ta gyara ba sai sun
zamar mata spill over.




Saida su Mommy suka yi sati biyu da tafiya sannan Baba Karami ya zo gidan, shima ya zo ne don yana so
yacewa Abba suje gaisuwa gidansu Khairiyya.

Sai bayan isha’I Abba ya dawo kamar yanda ya saba, bayan ya ajiye kayanshi a wajen Saudah ya fice ya
koma wajen su Auta; haka yake yi tunda Mommy ta tafi sai wajen 11pm sannan yake komawa wajen
Saudah yace su rufe kofa wata rana kuma ma a wajensu yake kwana. Yana shiga falon Abban ya amsa
sallamarsa yace

“Mutanen Habuja yaushe a Kano.”

Yace

“Dazu na zo Abba.

“Toh sannunka da zuwa, baka taho mana da kaninka ba yau.”

“Eh Abba ya ce next week za su gama sai ya dawo gaba daya.”

Bayan sun dan taba hira Baba karami ya dubi Abba yace

“Abba mota ka siya ne na ga wata sabuwa a gidan?”

Ya gyara zama yace

“A’ah ba tawa bace taka ce Babana.”
Duk suka bude baki suna kallon Abban cike da mamaki. Ya yi murmushi ya gyara zama yace

“Taka ce Babana, bari a dauko maka mukullinta.”

Nan da nan ya dauki waya ya kirawo Saudah yace mata ta dauko mukullin mota a cikin durowa Auta zai
shigo ya karba. Nan da nan kuwa Auta ya tafi yana ta tsalle. Gaba dayansu suka taya shi yiwa Abba godiya.
Auta ya shigo da mukullan yana fadin

“Ni zan fara tukata Yaya.”

Madu yace

“Toh bari mu yo alwala.”

Suka sa dariya yayinda Auta ya mikawa Abba mukullin, yana karba ya mikawa Baba yana cewa

“Allah ya tsare hanya.”

“Amin Abba na gode, Allah ya kara arziki.”

Suka tashi gaba daya har Abban suka tafi wajen motar, Baba ya bude motar suna ta tsalle suna dubawa.
Salim yace

“Abba ku tsaya in yi mana selfie.”

Suka gyara tsaiwa suka jeru suka dauki hoton. Madu ya dubi Abba yace

“Abba ai dare be yi ba za mu ‘dan iya zagayawa ko?”

Ya duba wayarshi karfe tara da rabi yace

“Za ku iya amma kada kuyi nisa don dare ya fara yi.”

Madu ne ya karbi mukullin motar ya karkadasu a fuskar Auta yana fadin

“Ni zan fara tuka ta.”

Suka sa dariya Baba ya zagaya ya shiga gaba, su kuma suka shige bayan. Salim ya tabo Baba yace

“Ka dauko ATM card ko?”

Ya juyo da alamar tambaya a fuskarshi, Salim din yace

“Toh ai ko dajaja ka saya mana saboda farin ciki.”

Suka kyalkyale da dariya Madu ya ja mota suka fice.

Ba ta san me yake faruwa ba kawai sai jin hayaniyarsu tayi da ficewar motar wadda ta leko ta taga ta
tabbatar da wace mota ce. Yana shiga wajen ta jefo masa tambaya

“Lafiya na ji fitar yara a daren nan, ko motar za su kaiwa mai ita?”

Yace

“A’ah. Ta Baba ce dama mukullin na bashi shine suka sa shi gaba sai sun yi dani.”
Tace

“Baba Karami? Motar ya sake siya ne?”

“A’ah ni na siya masa tunda ya siyar da waccan.”

Yanda ya tsare ta da ido ya sa ta kasa bayyana ‘bacin ranta, da kyar ta daure tace

“Toh suma duka yaran naka haka za ka bi su da motar kenan?”

Yace

“A’ah mai rabo dai ya samu, motar sai kace wata alawa za a hau bin kowa da ita.”

“Ai shikenan, Allah ya sa albarka, ka ga nima da ka bani ko baka bawa su Baffa Karami ba ta ishe mu.”

Ya dubeta sosai yace

“Ba za a baki ba su kuma mai rabo ya samu, Baffa Karamin kam ai wata kila ma Baban ne zai siya mishi
mota.”

Ta tabe baki ta gyara zama. Nan Kuma suka ji shigowar yara Auta ya shiga wajen bayan an amsa sallamarshi
yace

“Abba mun dawo.”

Ya mika mata leda dauke da rabin kaza da kuma ice cream roba uku yace

“Ga shi na su Nawwa ne.”

Kafin ya ji mai za ta ce ya juya ya fita da guda, jimawa kadan ya dawo da wata ledar ya mikawa Abban yace

“Abba ga naka da na Anti inji Ya Baba.”

Ya kuma juyawa ya fita da gudu. Nan ya sauka kan kafet ya kama kazarshi da ci ga sassanyan yoghurt. Ta
tashi za ta huce daki ya mika mata kasonta da na yara yace ta sa musu a fridge da safe sa ci. Ta karba ta
huce kicin. Haka ta kwana tana lissafi, a ganinta ba ayi adalci ba tunda ko za a bawa kowa mota ma kafin
a zo kan yaranta gani take abun ya kare ita dai ta fi so kawai a raba yanzu a basu ita da yaranta. Ta yi
nadama da tayi rigima aka kori waccan motar don tana tunani fushi suka yi su da uwarsu shi yasa ya huce
musu takaici da wannan da tafi waccan komai. Shi kuwa da kawo yanzu ya riga ya fahimci halinta burus
yayi da ita kuma bai bata fuska ba balle tayi wani korafi, don haka sai dai kawai tayi ta muzurai ita kadai
har gari ya waye.

Ranar Lahadi da safe Baba karami ya shirya zai tafi ya sami Abban a falonsu. Bayan ya gaishe shi ya zauna
a gabanshi yana shirin yacewa Abban za a je ayi gaisuwa gidansu Khairiyya Abban ya riga shi yace

“Babana yau za ka tafi ko.”

“Eh Abba yanzu ma kuwa in sha Allah.”

“Toh Allah ya tsare hanya. Yauwa maganar yarinyar nan da kayi nace maka Babanka Atiku zai bincika ba,
toh ina ga baza ta yiwu ba.”
Da sauri ya dago kai ya dubi Abban suna hada ido kuma sai ya yi kasa da nashi idon zuciyarshi na nan ta
daina aiki yace

“Abba matsala aka samu ne?”

Yace

“Toh shi dai a bincikensa ya ce bata dace ba, amma kuma nima ka turo min details din mahaifinta zan
duba.”

“Toh Abba don Allah a sake dubawa.”

“Toh ka ga tunda ka shirya mai zai hana ka raya mana zumuncinmu ka auri ‘yaruwarka Zulaiha ka ga…”

Firgigit ya dago kai ya katse Abban yace

“Abba bana sonta.”

Abban yace

“Ikon Allah, toh shi kenan ai ba a yiwa namiji auren dole. Wannan din zan kara dubawa.”

Ya sallami Abba ya shiga motarsa ya kama hanyar Abuja zuciyarshi a jagule. Ya tabbatar wannan tsarin na
Sa’a ne ta kullawa Baffa Atikun, shi bai ma yadda Baffa ya wani bincika ba so ake kawai ayi masa dole shi
kuma ko mata sun kare a duniya ba zai auri Zulai ba, to ya auri jinin Sa’a ma yace ya auri wa? Ga shi kuma
Mommy bata nan duk da suna magana ta waya amma baya son ya dora mata wata damuwa tana
hutawarta. Haka ya hakura bai gayawa kowa ba, don ko Ahmad bai gayawa ba saboda baya son a gayawa
Mommy sai ta dawo. Ba wai zai yiwa Abba taurin kai bane amma tabbas ba zai auri Zulai ba.

“Allah ma ya kiyaye.”

Ya fada a fili.
EPISODE 13



Satinsu uku a Saudiyya suka hau jirgi sai Dubai, duk yanda take tunanin garin nan ya huce haka. Sun huta
sosai sannan suka fara yawo, kasuwanni da guraren shakatawa kala kala suka dinga zuwa. Ga abinci nan
sai wanda ta zaba. Sayayya kuwa ta yi ta daidai gwargwado, kowa ta siyo masa tsaraba har da su Nawwara
ma. Kwanansu biyar a Dubai suka duro Abuja, Baraka ce ta canja musu ticket ya koma za su sauka a Abuja
domin ta ce ya kamata su tsaya a saloon su danyi kitso da kunshi domin ita duk lokacin da ta yi tafiya ta
dawo haka takeyi.

Suna sauka a Abuja Mommy ta kirawo Baba tace

“Babana mun iso fa, amma muna Abuja Antin ka ta janyo ni sai dai in za ka weekend sai mu huce in ba
haka ba tace sai tai min booking flight na tafi don ka san ita tana da gida a nan.”

“Sannunku da zuwa Mommy, yau za mu tafi ko gobe.”

“A’ah ka bari dai sai ranar Asabar ka ga yau alhamis.”

Yace

“Toh Mommy, ki gaishe min da Anti Barakan.”

Suka yi sallama suka huce Gwarinpa inda a nan gidan Baraka na Abuja yake. Gari na wayewa suka tafi
saloon din da Barakan take zuwa domin kitso da kunshi. Ita Baraka halawa aka yi mata ga dilke, sannan
aka yi kitso aka ce kunshi sai ta kwana biyu. Ita kuwa Rabi da yake bata son halawa sai kawai akayi mata
dilke aka goge fatar sannan aka yi mata kunshi aka wanke kanta aka yi mata kitso.

Ranar Asabar tun wuri Baba ya Isa gidan Anti Baraka, sai da yaci abincin safe ya huta sanan ita da Mommy
suka fito. Bayan sun gaisa yace

“Mommy sai kyalli kuke yi ke da Anti Barakan lallai shinkafa kaza ta karbeku.”

Suka kyalkyale da dariya gaba daya. Suna karasowa waje Mommy tace

“Babana wannan motar fa?”

Ya fadada murmushinsa yace

“Abba ne ya bani bayan kun tafi.”

Fuskarta cike da farin ciki da mamaki tace

“Abba kuma? Cewa fa yayi motar ajiya ce.”

Baraka tace

“Toh wanda aka ajiyewa ya zo.”

Ta juya ta dubi Baba tace
“Idan ka je kace ina gaida Abba ka ji, kace na ce muna godiya Allah ya sa Amarya ta kara ‘yan biyu sau
biyu.”

Suka kyalkyale da dariya, Mommy ta shiga mota da kayanta suka kama hanya sai Kano. Tuki yake yi suna
ta hirarrakinsu in sun gaji da hira kuma su yi shiru. A nan yake bata labarin yanda suka yi da Abba a kan
neman aurenshi. Ranta yayi matukar baci don sai da yaji dama ya sani bai gaya mata ba saboda yanda
yaga fuskarta ta canza, amma shima abun ya ishe shi don haka ya kasa daurewa. Ta bishi da kallo sannan
tace

“Toh kai me kace?”

“Na gaya mishi bana sonta, in kin je kema Mommy don Allah kada ki saurara masa. Wallahi Mommy ba
zan taba auren yarinyar nan ba, ko ban auri Khairiyya ba toh ba zan aure ta ba. Don wallahi Mommy gara
na kare rayuta ban yi aure ba da na auri jinin Sa’a.”

Tace

“Hmmm. Ka min daidai, kuma shima ya san ba zai yiwu ba in haifi ‘da ya auri ‘yar Sa’a, idan ma bai sani ba
kuma zan sanar da shi. Itama Khairiyyan na san babu wata matsala da suka binciko a kanta tsabar sharrin
Sa’a ne kuma bata isa ba da izinin Allah.”

Suka yi shiru duka suka mayar da hankalinsu ga hanya. Kamar wadda ta tuno wani abu tace

“Dama ina ta mamakin dalilin da ya sa ta kawo ta nan, ashe dalili kenan saboda tsabar rashin kunya aka
fake da karatu. Lallai ‘dan Adam.”

Tayi ‘kwafa ta mayar da hankalinta ga hanya. Sai yanzu ne ma ta tabbatar da cewa Sa’a ta raina ta, amma
in sha Allahu an zo wajen da za ta nuna mata cewa ‘yaran nan jinin Rabi yana yawo a jikinsu ba wai jinin
Usamanu ne kawai ba. Ita bata taba ganin inda

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login