Showing 69001 words to 72000 words out of 196754 words

Chapter 24 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15373

su, idan kuma suka ga dama tun
karfe 3pm sai su gudu masallaci sai bayan 5pm za su dawo.

Sai da suka yi jarrabawa hudu a jere babu fashi, duk wannan lokacin Abba baya kulata kuma abun baya
damunta saboda ko ba komai babu Mai damunta da girki, karatunta kawai take yi. Ta barshine a kan in ta
gama jarrabawa sai ta neme shi su shirya duk da bai taba dadewa yana fushi da ita kamar wannan karon
ba. Ranar da suka yi jarrabawa ta hudu ne bayan an sha ruwa tana zaune a falo tana karatu ya shigo wajen
nata. Ta yi mamaki da yake ba itace da girki ba. Ko kallon inda take bai yi ba ya shige dakin, da alama akwai
abinda yake nema a dakin. Sai da ya fito daga dakin ya nufi kofa zai fita sannan ta ce

“Abban Nawwara.”

Ya tsaya sannan ya juyo ya dube ta yace

“Menene?

“Ka zauna mana, ina da magana da kai ne.”

“Ba sai na zauna ba ina sauraronki.”

“Yanzu haka za mu zauna kana gaba da ni, ko don watan azumin nan ai ya kamata ace duk wani hakki dake
kan mutum ya sauke shi.”

“In kuma ya kasa saukewa ai sai a murdeshi a sauke masa ko?”

Ta sunkuyar da kai sannan tace

“Toh ni dai dan Allah na gaji da wannan zaman, ko ma me nayi maka kayi hakuri.”

“Ai na zata bakiyi min komai ba.”
Ta sake sunkuyar da kai tana murmushin tace

“Toh ai dai nace kayi hakuri ko?”

Ya juya ya fice ya barta, yanayin da ta gani a fuskarsa shi ya tabbatar mata da cewa ya hakura. Yana ficewa
ta murgudawa bayanshi baki tace

“Kuturun danja kawai, don kar kayi min shirme a kayan Sallah ne in banda haka kayi ta fushin mana.”

Sai da ya gama cin abincin sahur dinshi sannan yacewa Mommy

“Kada ki yi min abincin buda baki Saudah za ta yi girkin ta. Idan ina bukatar wani abun zan miki magana.”

Da murmushinta tace

“Kai Madalla, in sha Allah ma baza ka bukaci wani abu ba.”

Binta yayi da kallo har ta shige kicin, yana mamakin kishi ko kuma rashin kishi zai ce irin na Rabi. Wasu
matan har so suke a sato kwanan wata a kawo musu Amma ita murna take an ce za a koma wajen kishiya.
Ko kuma tsabar rashin wayo ne shi bai ma sani ba, shi dai kawai ya san tunda ya kara aure gaba daya ta
canza ko kuma watakila shine bai karanceta sosai ba dama.




Yau jarrabawarta 2pm to 4pm ce don haka sai da ta gama duk abinda take yi tayi sallar la’asar sannan ta
kama hanya. Kamar kullum su Nawwara suna makaranta don haka ta biya ta kai su Hanan gidan da ta saba
kaisu, daga nan ta hau tasi ta huce makaranta. Sai karfe hudu saura sannan suka fito daga jarrabawar don
haka ita da kawayenta su ka yanke shawarar su shiga masallaci su jira ayi sallar la’asar idan suka yi Sallah
sai su huce gida. Ana tayar da Sallah wayarta ta fara waka daga cikin jakarta, tayi ta waka har ta gaji ta
tsinke kafin wani lokaci kuma aka sake bugawa. Haka aka yi ta yi har aka idar da Sallah. Liman yana
sallamewa ta janyo jakartata tana mitar waye yake ta yi mata waya kamar wanda yake binta bashi. Tana
dauko wayar ta duba taga lambar Anti Hadiza wadda take kaiwa su Hanan idan za ta taho makaranta,
gabanta ya fadi saboda kiran bai yi kama da na lafiya ba. Kafin tace wani abu kiran ya sake shigowa nan
da nan ta amsa ta kara wayar a kunnenta. Kukan da Baffa Karami yake tsalawa shi ta fara jiyowa ta wayar
kafin ta yi ko da sallama Anti Hadizan ta fara magana cikin rawar murya

“Sai waya nakeyi miki, Hassan ne ya kone a hannu, gara ki zo a kai shi asibiti.”

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, wace irin konewa kuma. Gani nan zuwa.”

A zabure ta mike Amina dake kusa da ita ta riketa

“Me ya faru? Ina za ki?”

Hawayen da take rikewa ya kwace ta dora hannu a ka tace

“Baffa Karami ne ya kone tafiya zan yi.”

Ta nufi hanyar fita daga masallacin yayinda duk kawayen nata su uku suka rufo mata baya suka fito daga
masallacin. A harabar masallacin Amina ta riketa tace
“Bari in dauko mota sai muje tare.”

Ta dubi dayar tace

“Halima bari mu huce daga can sai nayi gida ma hadu next week kawai.”

Suka shiga motar Amina suka kama hanya sauran suna yi musu Allah ya sauwake.

Tafiya suke amma gani take kamar Amina bata sauri, ji take kamar tayi tsuntsuwa. A firgice ta dubi Aminan
tace

“Ammi Allah ya sa ba duk jikinshi ya kone ba, kin ji kuwa ihun da yake yi.”

Amina ta dafa cinyarta tace

“In Sha Allahu kadan ne.”

Cikin kanakanin lokaci suka iso kofar gidan. Tun kafin motar ta gama tsayawa suka fara jiyo kukan Baffa,
muryar shi har ta sauya alamar ya dade yana kukan. Sai da suka shiga sannan suka gane ashe har Hanan
din ma kukan take. Kafin su karasa cikin gidan Anti Hadiza ta fito daga dakin da gudu dauke da Baffa suna
haduwa a tsakar gidan ta mika mata shi tana fadin

“Wallahi a ruwan damun kunu ya tsoma hannunshi ban kula ba.”

Ta karbeshi jikinta na rawa yayinda Hanan ma ta karaso jikinta ta tsaya. Ta dubi hannun nashi ta gani daga
wuyan hannu zuwa yatsun gaba daya ya tashi sai kace wanda aka wankewa hannu da ruwan zafin, gashi
yayi fari-fari alamar an saka masa gasara a kai duk da wannan bai hana ya tashi ba. Nan da nan ta
rungumeshi yana ajiyar zuciya hawaye suna bin fuskarta. Amina ce tayi karfin hali tace

“Ke kuwa garin yaya ya kone haka?”

A gigice ta bude baki jikinta har rawa yake yi ta na nuna mata inda murhunta yake a tsakar gidan kusa da
inda suke tsaye

“Wallahi daga in dama kunu, na zuba ruwan na mayar da ragowar kan wutar na shiga kicin dauko flask
wallahi kafin na fito yaron nan ya tsoma hannunshi cikin ruwan sai ihunshi na jiyo. Kuma sun saba ganin
murhun basa zuwa inda yake wallahi tsautsayi.”

“Allah ya kyauta.” In ji Amina, ta sa hannu ta dauki Hanan tana fadin

“Muje na kaiku asibiti, idan kika kira babansu ya zo sai na huce gidan.”

Ba tare da tace komai suka juya suka fice suka bar Anti Hadiza a nan itama ranta a jagule, bata san da
wane ido za ta dubi yarinyar nan ba ta kona mata yaro.

Suna zama a mota Amina ta ce

“Ki kirawo babansu ki gaya masa. Wanne asibiti za mu je?”

Ta dafe goshi tana matse hawaye ga Baffa a hannunta har ya gaji da kuka tace

“Rigima sabuwa ban ma San ta ina zan fara yi masa bayani ba don dama ya tsani kaisu gidan nan da nake
yi da karatun nawa ma baki daya. Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.”
Ta yiwa Amina kwatancen asibitin da suke zuwa sannan ta kirawo Abba. Wayar tana fara ringing Hanan
da take zaune a gefen cinyarta kusa da Baffa ta tsanyara kuka, shima Baffan ya cigaba. Yana daukar wayar
yace

“Me kika yi musu haka suke wannan kukan?”

Ta share kwalla a idonta kafin ta bashi amsa

“Uhhmm, Baffa Karami ne ya kone.”

“Subhanallah, ya Kone? Garin yaya? Kina me kika barshi ya kone, duk jikinshi ko a ina?”

“Hm! A hannu ne, amma ta tashi sosai muna hanyar zuwa asibiti.”

“Toh zan turo Madu.”

Kafin tace wani abu ya ajiye wayar. Suna isa asibitin suka shiga nan da nan likita ya duba su, ya dube ta
yace

“Garin yaya ya sami wannan kunar?”

“Ruwan zafin ne a wuta yana tafasa ya sa hannu a ciki.”

“Subhanallah! Bamu da kayan aikin da za mu duba shi yanzu amma ku kaishi asibitin Murtala ko Nassarawa
emergency don sai an bare wannan hannun.”

Ta sake shafe kwalla tace da Amina

“Ki tafi kawata idan ya zo sai mu huce Murtalan.”

“In na tafi wa zai rike miki wannan?”

Ta bata amsa tana nuna Hanan da take bacci a kafadarta.

Don haka sai suka koma gefe ta dauki waya ta sake kiran Abban ta gaya masa abinda likita yace.

“Kunar da yawa kenan.”

Da yaji bata ce komai ba ya cigaba

“Idan Madu ya zo ki gaya masa ku huce zan sameku a can.”

Kafin ta gama amsa wayar Madun ya shigo wajen da suke zaune, kafin ya karaso inda suke sun mike sun
nufo shi.

“Ance mu tafi Murtala.”

Duk yanda yake jin haushin ta saida ta bashi tausayi, ya kalli hannun Baffa yace

“Kai! Haka hannun yayi.”

Kafin ta bashi amsa Amina ta duba agogo tace

“Ni bari na tafi Saudah.”
Ta mika mata Hanan Madu ya sa hannu ya karbeta ya sakata a kafadarsa ya huce gaba suka bishi a baya.
Suna fitowa Amina ta huce ta shiga motarta ta tafi. Suka karasa wajen motar da yazo da ita. Ta Bude bayan
motar ta shiga ta zauna ya zagaya ta daya gefen don ya kwantar da Hanan, yana sauketa daga kafadarshi
ta tsanyara ihu don haka ya mayar da ita yana shafa mata baya. Ta dube shi tace

“Yunwa suke ji ma.”

“Toh bari na samo abinci.”

Cikin asibitin ya koma da yake suna da wajen sayar da abinci, ya siyo ruwan roba da fresh yo guda biyu da
biskit. Ya dawo ya mika mata sannan ya zaunar da Hanan a gaban motar ya bude fresh yo ya sa mata straw
sannan ya mika mata. Shima Baffan tashinsa tayi ta saka masa madarar a baki. Nan da nan ya kama sai dai
yana zukewa ya saka kuka har suka karasa asibitin. Suna shiga aka nuna musu emergency suka huce.
Mintuna kadan suka ci sa’a aka dubasu.

“Ruwan zafin ne ko?”

Ma aikacin lafiyar ya tambaya. Bayan ta bashi amsa ya ci gaba

“Kada ki damu in Sha Allah ba ta ci jikinsa ba, da wuri za ta warke in Sha Allah.”

Ya rubuta musu allurai yace a siyo, ta leko ta bawa Madu ya dauki Hanan suka je suka siyo, kafin wani
lokaci sun dawo. Aka ce ta rike shi ayi masa allura, jikinta har rawa yake da kyar ta samu ta rike shi. Wanda
yayi allurar ya dube ta yace

“Hajiya ki gyara zamanki sosai za ki rike mana shi mu bare wannan kunar.”

Ta kalleshi idanuwanta suka kara ciccikowa. Yayi murmushi yace

“Ina wanda kuka zo tare ko ke kadai kika zo?”

Tace

“Yana waje.”

Ta fito ta kirawo Madu ya shigo da Hanan. Ma aikacin lafiyar ya dube shi yace

“Mai gida rike mana yaron nan zakayi za a bare kunar nan.”

Ya amsa, ya bata Hanan ya karbi Baffa yace

“Ki fita da ita ku danyi nisa in an gama za mu fito.”

Ta rungumeta suka fito. Duk yanda ya so ya dake sai da yaron nan ya saka shi kwalla, tun yana kuka har
ya kasa. Jikinshi rawa yake yi kamar mai zazzabi, kara rungumeshi yake yana ta kokarin fizgewa haka dai
aka bare ta tas aka goge aka shafa magunguna sanan aka yi ta motsa yatsunshi har sai da Madu ya fara
tunanin anya ba mugunta sukeyiwa yaron ba.

Tana fitowa daga emergency din aka kira sallar magriba, ta ma manta azumi take yi. Nesa tayi da wajen
sosai sannan ta sami inuwa ta tsaya, gaba daya kamar wadda aka dauke wuta a kanta domin ta kasa tunani.
Tana nan tsaye Abba ya iso shi da yaronsa Lalo

“Ina Baffan?”
Ya tambaya a razane.

“Suna ciki ana wanke masa.”

Kwallar da take makalewa a idonta ta gangaro ta goge, Abba ya kalleta yana tsaki

“Mtsewww! Kukan me za ki yiwa mutane kin je kin bawa wata mara kula yaran, in banda sakarci ya za ayi
ta ajiye ruwa inda yaro zai iya sa hannu. Aikin banza kawai.”

Kafin ta bashi amsa Madu ya fito da Baffa a kafadarsa yana ta ajiyar zuciya. Yana ganin Abban ya mika
mishi hannu ya daukeshi , nan da nan ya kwanta a kafadarsa ya janyo hannun yana dubawa. Kafin yace
wani abu Madu ya mika masa takardu yace

“Abba wai kwantar da su za ayi.”

Ya karba yace

“A’ah, su bari muje gida idan akwai wani abu a dinga zuwa. Nuna min wajen ma’aikatan.”

Ya huce gaba Abban yana biye da shi har ciki, sai da Abban yaga ma’aikatan suna cin abinci sannan ya tuna
ya dubi Madu yace

“Na manta baku sha ruwa ba, akwai ruwa a mota ka dauko musu.”

Suka fice shi da Lalo suka tafi don dauko ruwan. Nan Abba ya gama magana, suka yi masa bayani a kan
dressing ne za a dinga yi da safe kullum shi yasa suke so a kwana amma idan za a iya zuwa karfe 7:30am
toh sai ayi dressing din su tafi. Aka sake yiwa Abban bayanin magungunan da aka rubuta ya fito ya same
su. Yanda suka zo haka suka koma wato ita da Madu, Abba Kuma da Lalo. Sun dauki hanyar gida a firgice
ta dafa kafadar Madu tace

“Su Nawwara suna makaranta, na manta da su. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.”

Yace

“Subhanallah.”

Ya dauki waya ya kirawo Abba ya sanar da shi za su tsaya su duba a makarantar su Nawwara. Hankalin
Abba ya kara tashi ya ce wa Lalo suma su tsaya a nan. Kafin su Madun su karaso har su Abban sun tsaya a
makarantar. Nan da nan maigadi yayi musu bayanin babu kowa a makaranta fa kowa ya tafi. Hankalin su
yayi matukar tashi, tuni Saudah ta fara Kuka. Abba ya dubeta yace

“Kukan me za ki dame mu dashi?”

Madu yace

“Bari na kirawo Mommy ko an kaisu gida.”

Yana kiranta kuwa ta sanar dashi cewa Auta ya dauko su, ta zata ma Saudan ce ta bar masa sakon ya dauko
su ashe haka kawai yana fitowa daga sallar la’asar ya huce sai ganinshi Mommy tayi da su don haka suna
wajenta. Sai da suka ji wannan bayani sannan suka dawo hayyacinsu suka shiga mota suka kama hanya.
Sai da suka zo gida sannan ya sallami Lalo ya tafi. Da yake kafin su dawo Madu ya riga ya sanarwa Mommy
halin da ake ciki ta riga ta yi musu abinci. Suna shiga gidan Abba ya bi bayan Saudah suka shige falonta,
gabanta har faduwa yake saboda yanda ta san zai yi mata fada. Suna shiga kuwa ya fara

“Kinga abinda nake gaya miki ko? Matar nan bata da kula amma ke kullum kin fi so ki bata yara. Kin kasa
samarwa yara natsuwa saboda kije kiyi karatu, toh haka masu karatun suke rashin hankali?”

Yana ta wannan fadan Auta ya shiga falon da abinci a tray wanda Mommy ta zuba ya kaiwa Saudah tunda
shi Abba a wajenta zai sha ruwa. Har ya shiga ya ajiye a kan dining table Abban bai san da shigowarshi ba
yana ta fada, sai dai ita Saudan ta ganshi. Nan a kan kujera ta shimfide yaran ta zauna ta dafe kai tana
sauraronshi.

“Mommy kinga kuwa yanda Abba yake ta yi mata fada, sai kuka takeyi bai ma san na shiga ba.”

Kallonshi kawai tayi ta sa hijabinta ta fice. A yanda ya barsu a haka ta same su, babu wanda ya amsa sai
dai shigarta ta sa Abban ya lafa da fadan. Ta dube shi tace

“Sannunku, Allah ya kiyaye gaba.”

Ta karasa kan Baffa da yake bacci a kan kujera ta duba hannun tace

“Subhanallah, har haka? Allah ya bashi lafiya.”

Nan Abban ya fice, da yake ta jera masa duk wani abu da zai bukata a kan tebur bata bishi ba. Ta zauna a
kusa da Saudah ta dafa bayanta tace

“Kiyi hakuri kin ji, in sha Allah komai zai huce. An auna arziki ma da ba duk jikinshi bane, in Sha Allah kafin
sati za ki ga ta kame.”

Tunda konar nan ta faru babu wanda yayi mata kalami mai dadin wannan don haka ta kara fashewa da
kuka tana fadin

“Sai fada yake yi min kamar ni na kona shi.”

“Ki rabu da shi kawai, ya za ayi ki kona ‘dan da kika haifa? Kema kin san halin Abba, kar ki bari fadanshi ya
kara miki damuwa. Tashi za kiy ki dan ci abinci kiyi sallah sai ki ga kin sami natsuwa.”

Ta dubi Baffa tace

“An ce a bashi abinci ga allura nan an siyo ayi masa kafin ya kwanta.”

Mommy tace

“Toh ci naki abincin ki bani nashi yanzu zan bashi ya koshi.”

Nan da nan ta daukowa Mommy cerelac ta ajiye mata da kayan hadawa, Saida ta hada sannan ta tashe
shi a hankali yana yin ‘dan kuka bacci na kwasarshi. Da yake da yunwa a cikinsa nan da nan ya dinga karba,
har saida ya daina karba sannan ta bashi ruwa ya sha ta dubi Saudah tace

“Da da ruwan dumi sai ayi masa wanka a canza masa kayan.”

Ta mike tana fadin

“Ci abincinki bari nayi masa.”
Ta daukeshi ta shiga bandakin dake dakin Saudah din tayi masa wanka yana ta rigima sanan ta shirayshi
ta dawo kan Hanan. Kafin ta gama da Hanan bacci ya kuma kwashe Baffa yayinda itama Saudah ta shiga
wanka. Bayan ta shirya ta fito ta cewa Mommy

“Bari na kirawo Abban a kaishi allurar.”

“A’ah, bari na kirawo Ahmad akwai abokinshi da yake da chemist a nan bayan layin sai yaje ya dauko shi
yazo yayi masa allurar a nan, wahalar ta isa haka a barshi ya huta.”

Har cikin ranta ta ji dadin wannan maganar saboda yanda ita kanta jikinta ke ciwo. Nan Mommy ta fita ta
barta, bayan ta gama yiwa Ahmad bayani ya dau mukullin mota ya fice. A falo ta sami Abba yana zaune,
da yake an riga an tayar da sallar isha’I kafin ya gama cin abinci bai je masallaci ba. Bayan Ahmad ya fice
ta dawo ta zauna a kusa da Abban tace

“Sannu, Allah ya sauwake.”

Ya dubeta yace

“Tsabar sakaci me nata ita da matar da take kaiwa yara. In banda haka ya za ayi a ce yaro ya tsoma
hannunshi a tafasasshen ruwa.”

“Ai hakuri za ayi, tsautsayi ne. Itama tana cikin damuwa don Allah ka daina fadan.”

“Toh ai dole nayi fada.”

“Toh abinda ya faru ai ya riga ya faru, mun gode Allah ma da bai kone duka jikin ba. Ka daina fadan ka
barta ta sami natsuwa.”

Shiru yayi ya kau da kai, saida suka danyi jim ta fahimci ya dan sauko sannan ta cigaba

“Ka ga tana bukatar wanda zai tayata da yaran ga su Nawwara ga kuma jinya, ka yiwa Sa’a waya Zulaiha
ta dawo ko kuma ita Saudan tayi waya gida a turo mata mai tayata.”

Ya gyara zama

“Hakane, zan dai kirawo Baffan Zulaihan gobe sai ta dawo.”

Tace

“Toh hakan yayi. Uhmn, yau din ma sai ka kwana a wajenta don ciwo a cikin dare bashi da dadi Kada wani
abun ya taso.”

“To mai zan yi mata…”

Ya fada a fusace. Nan da nan ta tare numfashinsa tana fadin

“Don Allah dai nace ka taimaka ka kwana a can, ni da su Nawwaran sai mu kwana a nan. Saboda Allah ba
saboda mu ba.”

Kamar ba zai amsa ba daga baya kuma yace

“Toh.”

Sai da ta bari ya dan sake numfasawa sannan tace
“Don Allah kar kayi

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login