Showing 81001 words to 84000 words out of 196754 words

Chapter 28 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15384

gida amma babu wanda yake cewa komai har
suka zo, sai da suka shiga gidan sannan Abban ya dubi Ahmad yace

“Kun sami abincin buda baki kuwa?”

Ba tare da ya kalleshi ba ya bashi amsa

“Za mu samu.”

Ya shige falo shima Abban ya huce wajen Saudah.

Ko da Ahmad ya shiga har Auta ya dora musu indomie, yacewa Salim da yake kwance a falo

“Me kuke dafawa ne?”

Yace

“Indomie da tea.”

“Jeka store ka debo kwai ku hada ku soya.”

Ya tashi ya fita don debo kwan, a nan Madu ya fito daga daki ya zauna a kusa da Ahmad ya dube shi yace

“Ka sami Mommyn kuwa?”

“Wallahi ban same ta ba, har yanzu wayarta a kashe.”

“Nima haka sai kira nake, a kashe.”

“Bari na kirawo Baba.”

Yana dauka yace

“Hello Ahmad ya kuke? Ina Mommy ne ina ta kiran wayarta a kashe.”
“Maigidan ya kore ta?”

“Kamar yaya ya kore ta babu dadin ji?”

Nan ya bashi labarin kamar yanda su Auta suka bashi.

“Lallai, yanzu kawai saboda tace ba zata yi raino ba yace ta bar masa gida? Lallai. To yanzu ina Mommyn
take?”

“Toh muna dai tunanin gidan Anti Shafa ta tafi amma bamu kirata ba, sai bayan isha’I zan je na gani.”

“Toh shikenan in ka je ma yi magana.”

Suka ajiye waya. Abinci Baban yake ci take ya ji abincin ya isheshi. Ya za ayi ace mutum yana zaune da
mace shekara talatin yace wai ta fice masa daga gida ba ko dadin ji, toh ina yake so taje. Wannan rashin
adalcin ya ma yi yawa, shi dai idan haka ‘kara aure yake toh kada Allah ya bashi ikon karawa. Bayan
jimawa kadan kuma sai ya sake kiran Ahmad din kamar wanda, yana dauka yace

“Ahmad ka barshi ma kada kaje, ina ga ta kashe wayar ne don kar a dame ta. Ka san duk wata damuwa
da zamu shiga ta fi mu, gaba daya abun ma ruda ta zai yi. So let’s give her some time and space, may be
zuwa da safe sai ka je ko kai ko Salim.”

“Hakane. Ka san dama in ranta ya baci bata son a dameta.”

“Yauwa. Ina Auta?”

“Gashi nan sai faman koke-koke yakewa mutane.”

Auta ya matso kusa Ahmad ya mika masa wayar, yana karba ya kara fashewa da kuka yace

“Ya Baba kuka fa take lokacin da ta tafi, a gaban matarsa yake nuna mata kofa yana cewa ta fice nai daga
gida wai bata son ‘yayansa su gidan ubansu ne..”

Ya katse shi da yaji mitar bazata kare ba yace

“Ya isa! Kana ji na ko? Kayi hakuri ka ji?”

“Eh”

Ya amsa yana share hawaye.

“She’ll be fine and we’ll be fine too ka ji. Na san wajen yayarta taje so babu abinda zai sameta, kada ka
sake kuka ka ji ko, nima ranar Friday zan shigo maybe ma kafin nan ya je ya dawo da ita ka ji?”

“Ummm.”

“Yauwa, kada ka sake kuka.”

Ya mikawa Ahmad waya bayan ya tabbatar da Ahmad yake magana yace

“Ina Madu?”

“Yana kichin.”

“Sai ka kula da shi, ka san saitin shi yana gocewa kada yaje yayiwa mutane shirme.”
“Ba zai yi ba in sha Allahu.”

“Yauwa, sai mun yi waya gobe “

Suka ajiye waya. Shi Ahmad abinda ma ya fi tsaya masa a rai shine yanda Abba ko kunya bai ji ba a gaban
su Auta ya kori mahaifiyarsu.

Madu ya fito daga kicin da kofin zobo a hannunshi ya zo hucewa ta kusa da kafar auta ya ‘dan taka shi
yace

“Kai ba fa rasuwa tayi ba kake ta wani kuka gidan ‘yar uwarta ta tafi inda ake sonta.”

Ya karaso ya zauna a kusa da Ahmad, Ahmad ‘din ya harareshi yace

“Kai fa baka da mutunci ko? Nan ba’a sonta kenan?”

Ya dubi Auta yace

“Rabu da shi ka ji, in sha Allahu ma gobe Abban zai je ya dawo da ita ka ji, ka ci gaba da addu’a kar ka
saurare shi.”

Saida Madu ya tashi daga kusa da Ahmad sannan yayi magana saboda ya san zai iya kai masa duka

“In Sha Allahu baza ta dawo ba, ko za ta dawo ma zuga ta zan yi. Ya zauna shi da rabin ranshi su ci kansu
su sha bakin ruwa, tunda duk cikinmu babu mai shan nono.”

Yayi sauri ya shige daki da yaga Ahmad din ya mike. Ya dawo ya zauna yacewa su Auta dake zaune

“Ku rabu da shi mutumin wofi, in sha Allah sai ta dawo, in ta dawo ma sai ya fi kowa jin dadi dan rainin
hankali.”

Ya dauki remote ya kunna musu TV. Ranar dai haka aka kwana gidan kowa zuciyarshi babu dadi, Abba
ma ko bi takan Saudah bai yi ba ya shiga dakinshi ya kwanta, bai dai kulle kofa ba amma ita ma bata zo
ba domin itama abinda ya dameta ya ishe ta.

Lokacin sahur da Abba ya fito ya zata zai ga Saudah ta fito amma bata fito ba, sai da ya shiga dakin ya
taso ta. Ta fito tana muttsike fuska. Bata ma san me zata dafa masa ba don ita shayi kawai za ta sha ya
isheta na sahur. Tana tunanin dafa masa indomie sai ta tuna bai ci macaroni da ta dafa masa jiya ba ya
kwanta don haka ta dauko macaroni ta dumama masa sannan ta hada masa shayi. Yana zaune a falo kan
kujera ya kunna TV tashar Saudi TV ana karatun kur’ani ta doro abincin a tray ta kawo masa, da yake
abincin a bude yake yana kalla yace mata

“Bakiyi tuwo bane?”

“Ban yi ba wallahi, ban jin dadi shi ya sa.”

Ta ajiye masa abincin ta koma kicin din ta dauko kofin shayinta ta fito ta zauna a kujerar kusa da shi. Ya
dubeta yace

“Ke ba za ki ci abincin ba?”

“Um, shayin ya ishe ni.”
Ya dauki waya ya kirawo Ahmad

“Kun tashi sahur kai da kannenka ko?”

“Eh mun tsahi.”

“Kun dafa abincin sahur ko?”

“Eh, mun dafa indomie.”

Suka ajiye waya, so yayi ya je da kansa ya tashe su amma ya kasa hada ido da yaran. Shi kanshi ya fara
nadamar abinda yayi, ko da yake Rabi ta fiye taurin kai don haka tana bukatar ya koya mata hankali
yanda ba za ta sake yi masa irin wannan rainin ba. Ya kalli farantin abincin da ke gabansa yayi tsaki a
ransa, ya dauki cokali ya fara cin abincin kamar wanda aka yiwa dole. Babu abinda yake son yin sahur da
shi kamar tuwo, kadan ya dan taba macaronin ya tashi ya dauko burodinshi ya kara da shi sannan ya sha
shayin.

Gari na wayewa Khalifa da Auta suka yi shirin makaranta shi kuma Ahmad yayi shirin tafiya aiki suka fita
tare. Suka bar Madu da Salim suna karasa gyaran gidan domin su sun gama jarrabawa da yake ‘yan
jami’a ne. Madu kuma sai Abba ya fito za su fita.

Suka karasa ayyukan Salim ya kwanta a falo ya kunna TV, shi kuma Madu ya koma daki.

Sun saba tafiya da su Nawwara su ajiye su a makaranta amma yau sai sukayi tafiyarsu, shi Ahmad da
yake ba shi ya saba tafiya da su ba yau din ma don ya ga suna cikin damuwa ne ya sa su a gaba, don haka
bai ma san ya kamata su tafi da su Nawwara ba shi ya ma manta dasu gaba daya.

Wajen karfe takwas saura Saudah ta sami Abban a daki ko wanka bai yi ba tace masa

“Sun shirya wa zai kaisu makaranta?”

Yace

“Su jira ni ina zuwa.”

Yana jin lokacin da su Auta suka fita ya zata ma tare da su suka fita, kamata yayi yanzun ma yace Madu
ya kai su makarantar amma ba ya jin zai iya, ko ba komai ma ya san taurin kan Madu tunda aka taba
uwarsa toh in aka biye masa yau babu abinda zai tafi daidai. Don haka sai ya saka jallabiya ya dauko
mukullin mota ya fito. Itama a shirye ya sameta a falo yana fitowa tace

“Ni ma na shirya, bari na fito sai ka ajiye ni a gidan Ummanmu idan lokaci yayi sai na bar mata su naje
jarrabawa in na dawo sai na dauko su mu dawo.”

“Toh tashi muje.”

Suka fice gaba daya.

Bayan ya ajiye su gidan ya dawo ya shige daki ya kwanta. Sai wajen tara da rabi sannan ya fito tafiya
kasuwa, ya leko falon bayan Salim ya amsa sallamarsa ya gaisheshi yace

“Kirawo yayanka mu tafi.”

Ya tashi ya shiga daki, a kwance ya sami Madun ya gaya masa sakon Abban, gyara rufarshi yayi yace
“Kace masa bani da lafiya.”

Ya juya ya bawa Salim baya, Salim ya kyalkyale da dariya don ya san karya ne amma da yaga Madun bai
ce masa komai ba sai ya fito ya zo ya sami Abban yace

“Abba bashi da lafiya fa.”

“Subhanallah, tun dare dama bashi da lafiya ko kuwa yanzu ne?”

“Tunda aka sha ruwa ne amma ya sha magani da muka tashi sahur.”

“Bari na je na gani.”

Abban ya shige ya bude kofar dakin ya hango Madun a kwance.

“Madu.”

“Na’am.”

Ya amsa da kyar sannan ya juyo, Abban ya kalleshi yaga idonsa yayi ja don haka yace

“Sannu, ka lallaba ka tashi ku je asibiti. Idan ba zaka iya ba Salim ya karbo muku mukullin mota wajen
antinku ni na fita.”

“Toh Abba, a dawo lafiya.”

Yana fita daga gidan Madu ya taso ya fito falon ya dauki remote yana canza channel. Salim ya dube shi
yace

“Ka samu lafiya kenan?”

Ya dubeshi yace

“Dan sa ido, na samu ya ranka?”

“Ba ni na kar zomonba, bari ka ga ma na tashi nayi sallar walaha na yi addu’a Allah ya yafe maka
Muhammadu.”

Ya fada yana kyalkyala dariya. Madu ya kai masa duka da kafa ya goce ya doki iska.




Idan an fito sallar azahar ana bawa su Ahmad break na minti talatin a wajen aiki, don haka ya yanke idan
ya fito zai yi sauri ya je gidan anti Shafa wajen Mommy da yake kusa ne sosai da bankin nasu. Yana
fitowa ya sami Dan achaba ya haye, kafin minti biyar ya tsaya a bakin kofar gidan ya sallami mai babur ya
shige. Babu kowa a gidan sai Anti Shafa ita kadai da masu aiki kowa ya tafi makaranta, manyan kuma
Najib da Habib sun tafi aiki, itama sa’a yaci yau sai dare take da aiki can zata kwana, shima din tahowa
yayi saboda yana tunanin ko ta tafi aiki zai sami Mommy a gidan.

Bayan sun gaisa a falo ta kalleshi tace

“Ma’aikatan banki ashe kuna fita da rana?”
Yayi murmushi yace

“Ai break muka fito, wajen Mommy nazo dama.”

Ta kalleshi da mamaki tace

“Wace Mommy kuma, Mommynka?”

“Eh, ai na zata tana nan.”

Mamaki ya kara cikata tace

“A’ah, ban gane ba fa, tana nan kamar yaya?”

Ya kalleta shima mamakin yake ciki da kuma tsoron abinda zata ce yace

“Jiya ne suka sami sabani da Abban yace ta fice masa daga gida, toh shine muka zata nan ta zo.”

“Ban gane ba Ahmad.”

Ya bata labarin duka abinda ya faru, ranta yayi matukar baci tace

“Toh yanzu Ina Mommyn? Don bata zo nan ba, ni rabo na ma da ita tun kafin azumi. Baku sameta a
waya ba?”

Ta fada tana dauko wayarta dake kan kujerar tana kokarin kira

Yace

“Tun jiyan muke kiran wayarta a kashe.”

Ta riga ta kara wayar a kunnenta don haka ya dan saurara

“Ikon Allah, a kashe wayar take. Toh ita kuwa Rabi ina zata da ya fi nan din harda kashe waya, Allah ya sa
dai lafiya.”

Su ka dan yi jim, Ahmad ya gaji da jira a shirun yace

“Ko Anti Baraka za a kirawo?”

“A’a. Bari na kirawo Yaya Munzali yanzu haka gidansa ta huce.”

Ya dauki waya suka gaisa sannan take tamabayarsa Rabi. Nan tayi masa bayanin abinda yake faruwa tace

“Na zata ma nan gidanka ta taho.”

“Bata zo nan ba amma bari na kirawo Mubarak muji sai dai har ta tafi Kaduna kuwa ga azumi? Amma
bari dai na kirawo shin?”

Suka ajiye waya kafin ta yiwa Ahmad magana ta kirawo Baraka ita ma tace bata ganta ba don haka suka
kara shiga rudani. Ita da Ahmad din duk sun kasa magana, AC ce a falon Amma Ahmad har gumi yake yi.
Ta ajiye waya tace

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, ka ga ikon Allah duk wani wanda nake tunanin za ta gidansu bata je ba.”
Ya dube ta idanuwanta sun riga sun yi jawur yace

“Bari na kira Abban ko ya san inda ta tafi.”

“A’a bari na kirawo shi.”

Ta danna lambarshi ta kirawo shi. Yana zaune a kasuwa wayar tayi kara, yana kallon screen din yaga
Shafa ce sai da yayi murmushi ya dauko wayar. Dama ya san za su neme shi, ce mata zai yi sai gobe zai
zo kuma lallai sai dai ayi a gaban Munzali don ba zai saurari mata ba ta goyi bayan kanwarta su raina
masa hankali. Yanda yaji muryarta shima sai da gabansa ya fadi domin ya san ba lafiya ba. A gurguje suka
gaisa tace

“Wai me ya faru me jiya, yara sun zo neman Rabi ni kuma bata zo min nan ba, rabo na ma da ita tun
kafin azumi.”

“Um mun ‘dan samu sabani ne nace ta taho gida ko ni din ma na zata nan wajenki ta taho.”

“Bata zo min ba, kuma na kira su Yaya Munzali har Baraka ma duk bata je wajensu ba.”

Gumi ya karyo masa, toh ina Rabi za ta

“Ikon Allah, toh ina za ta. Ko da akwai wata kawarta da kike jin za ta je wajenta?”

“Toh Rabi kawaye nawane ma da ita gaba daya balle har ta je wajensu, zan ma iya cewa fa bata da wata
Kawa.”

Yace

“Ikon Allah! Toh ita kuwa Rabi ina za ta. Umm, akwai wata kawarta makociyarmu bari na sa Salim ya
duba can don yana gida.”

Ta ajiye waya ta dubi Ahmad tace

“Ka koma office kada kayi laifi, in sha Allahu Rabi ai baza ta bata ba, za muyi waya.”

Ya tashi jikinshi babu kwari ya fice ya koma office.



……….



Abba ya kirawo Salim bayan ya dauka yace

“Kana gida ko?”

“Eh muna nan ni da Madu.”

“Kaje gidan Maman Farida ka tambayeta ko Mommynku ta je wajenta.”

Yayi jim sannan yace

“Abba ai Yaya Ahmad yace tana gidan Anti Shafa in ya je office zai karasa.”
“Ya je ai, bata je can ba. Kaje gidan Maman Faridan ka duba.”

Nan da nan suka jiye waya.

………..

Ahmad yana zama a office ya daga waya ya kirawo Baba ya sanar da shi halin da ake ciki. Ya shiga tashin
hankali ba kadan ba. Suna gama waya da Ahmad ya kirawo kanin Mommy Baba Mubarak, bayan sun
gama gaisawa yace

“Baba Mommy bata zo nan ba?”

“Bata zo ba Baba, ka gan ni nan a mota Kanon zan tafi na ga halin da ake ciki, tun dazu muke waya da
Yaya Munzali. Ya za ayi ace ba’a ga Rabi ba, sekace wata ‘yar tsana.”

Suka dan yi jim

“Kada ka damu ka zauna yanzu ni ina hanya in naje sai gobe zan dawo in sha Allahu duk ma inda ta shiga
kafin goben an same ta.”

Suka ajiye waya.

…………

Saida Salim ya gayawa Madu halin da ake ciki sannan duka su biyun suka kama hanya suka shiga gidan
Maman Faridan, kamar yanda suka zata kuwa haka akayi don Maman Farida ma tace rabon ta da Rabi
tun jiya da suka dawo daga islamiyya. Don bata ma nan an yi wannan rigimar ba. Suna fitowa Madu ya
kirawo Baba, bayan sun gama mayar da zance Baba yace

“Kana ji ko, kada kuyi panicking babu inda Mommy za ta shiga in sha Allah za a same ta before the end
of today, Kada kaje kayi wani rashin hankali kuyi hakuri komai zai warware in sha Allahu.”

Suka yi sallama.

Suna nan zaune a falo suna tunanin mafita Auta da Khalifa suka dawo daga makaranta. Tunda Auta ya ji
ba a ga mommy ba ya fara kuka, don ma yana tsoron Madu shi yasa bai yi hayaniya da yawa ba. Salim ne
kawai yake bashi hakuri.

………….

Duk wani wanda Abban yake tunanin kira ya kirawo shi gashi har la’asar ta yi babu wanda ya ji labarin
inda Rabi ta tafi. Toh ita kuwa Rabi ina za ta, ita ba ta da kawaye balle ma yace ta bi wata kawar. Wani
gefe na zuciyarshi yana gaya masa toh ko sace ta akayi? Amma baya so yayi wannan tunanin saboda
yanda yake firgitar dashi. Tun yana daurewa shi kadai har ya kasa don haka ya shiga shagon abokin
kasuwancinsa ya gaya masa halin da ake ciki

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Alhaji Usman ai hakuri ake da mata. Duk haka suke in ka biyewa fitnar
su kowacce ma ba iya zama za ka yi da ita ba, Banda abinka ma kuka shekara talatin tare kuma ai nan
gidan naka shine gidanta ita ma. Toh ita kuwa Ina za ta je da azumin nan?”

Ya share gumi yace
“Shine abinda duk muke tunani.”

“To kun duba asibitoci? Ko tasin da ta hau ce ta sami hatsari, ka san kwasarsu za a yi a kaisu Murtala
emergency.”

“Hakane. Bari na fita sai naje can in ya so daga can sai na huce gidan.”

Ya fice ya sallami yaranshi aka rufe shagon shi da Lalo suka kamo hanya don a yanda yake jin jikinsa ba
zai iya dogon tuki ba. Har cikin emergency suka shiga HOD yayi musu bayani

“Alhaji accident daya aka kawo mana jiya na mota karfe bakwai na safe, kuma daga gwammaja ne
victims din ma duk maza ne.”

Bayan ya tabbatar basa nan kuma ya huce Nassarawa nan ma ya sami rahoton babu wannan zancen.
Don haka jiki babu kwari suka nufi gida, tura kujerar motar baya yayi ya dan kwanta Lalo yana ta gudu.
Suna isa gidan falon Mommy ya shige, Madu ya fara gani a kujerar dining da kyar ya amsa sallamarshi,
kafin ya karasa ciki Salim yace

“Abba an sameta?”

“Bamu same ta ba Salim.”

Ya karasa wajen auta wanda yake zaune a kofar dakin Mommy ya hada kai da gwiwa yana ta kuka. Ya
tsuguna ya dafa kanshi yace

“Yusufa kayi hakuri za a ganta.”

Wani banbarakwai ma ya ji saboda ya manta rabon da yaji Abba ya kirawo sunan shi na gaskiya, har
garama yayyanshu in suna son tsokanarsa sukan ce Isuhu. Yana jinsa yayi shiru kuma ya ki dago kansa,
har Abba ya gaji da tsuguno ya tashi Auta bai ce masa komai ba. Ya bi fuskokinsu da kallo hawaye ne
yake bin fuskar Salim, shi kuma Madu idonsa yayi ja sai wani kallo yakewa Abban mai cike da alamomin
tambaya da yawa. Ya kasa jurewa don haka ya fice ba tare da ya ce musu komai ba.




Karfe goma da rabi Saudah tana cikin gidansu a falo suna hira ita da Umma da Yaya Ummu. Da kyar ta
samu ta lallaba Baffa yayi bacci saboda tunda ta fita yake kuka har ta dawo. Sai da kwantar dashi a dakin
Umman sannan suka dawo falo, a lokacin take bawa Ummansu labarin Abba ya kori Rabi. Kafin Umman
tayi magana Yaya Ummu tace

“Barkan ki.”

“Ba fa sakinta yayi ba.”

Kafin Ummu ta sake yin magana uammansu ta gyara zama tace

“Toh kin ga yanzu kafin ya je ya dawo da ita kina da dama hannunki. Duk yanda za kiyi kiyi

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login