Showing 111001 words to 114000 words out of 196754 words

Chapter 38 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15372

ta hadu da wannan din.”

“Babu mamaki.”

“Ina jin shi yasa suka takura ni, toh da na turo iyayen nawa me za su ce musu?”

“Yaudara ce kawai abokina.”

Haka suka kare hirarrakinsu suka kwanta, ya so kiranta da daddaren amma dai sai ya bari gari ya waye
kafin nan ya huce saboda baya so ta gane yanda ranshi ya baci. Sai da yaje ya zauna a office dinshi wajen
goma na safe sannan ya kirawota, tana dagawa tace

“Ka bani mamaki Hussain.”

Sai yaji wani banbarakwai saboda bata saba kiran sunanshi ba sai dai tace mijin Khairy, yana jin haka a
ranshi yace lallai Khairy ta yi Sabon miji. Kafin yace wani abu ta fara fadan yayi mata wulakanci ranar
birthday dinta ko kiranta bai yi ba balle ma ya zo ya kawo mata cake don haka wanda yake sonta ya zo
ya kaita. Takaici ba zai barshi yace komai ba don haka sai kawai ya ajiye wayar. Tayi ta kira ya ki dagawa
har ta gaji ta hakura. Daga baya ta turo mishi sako kamar haka

‘sai jiyan na tabbatar soyayyar da kake yi min a baki ne kawai, ka batawa kanka lokaci.’

Yana gama karantawa yayi tsaki ya goge sakon. Yana sonta amma ya hakura da ita domin ba zai dauki
wulakanci ba. Tunda suka hadu duk shekara sai ya siyo mata birthday cake mai tsada ga kyaututtuka,
kuma sai ya kaita yawo duk inda ta zaba amma saboda guda daya tana neman ta zage shi. Ita bata yi
tunanin ma ta kirawo shi taji ko lafiya ba, musamman da yake ya tabbatar ta ga missed call dinsa. Tabbas
ya san hanyar rabuwa take nema kuma ta samu. In dai shine Hussain jikan Hussain ya hakura da ita ko da
ita kadai ce mace da tayi saura a duniya. Ya gaji da rashin ganin Mommy, an fi kwana talatin yau babu
labarinta kuma kusan tunda ta tafi suke ta shiga tashin hankali daga wannan sai wannan. Shi kanshi
Abban bashi da nutsuwa gashi a yanda yake ganin Auta shima yana cikin matsananciyar damuwa. Sai da
aka buga masa kofa sannan ya tuna a office yake, nan da nan ya wattsake kafin bakon nashi ya shigo.




An riga an fara lecture tun wajen sati daya da ya wuce, gaba daya bata son ma komawa makarantar sai
dai da yake tayi alkawari sai ta bawa marada kunya dole ta daure ta cigaba. Toh ya zata yi da su Hanan,
yanzu kam tsoron ma ta kaisu ko ina take yi, gaba daya tunaninta ya kare bata da wani zabi da ya huce ta
kaisu gidan Ummanta ta wuce makaranta, idan ta taso ta biya ta dauko su ta hado da su Nawwara su
dawo gida. Ranar alhamis ne kawai Zulaiha bata da lecture don haka sai ta bar mata yaran a gida, amma
duk sauran ranakun haka take hadawa. Ta so kwarai ta dinga barin su Hanan a wajen Ummanta su yi
kwana biyar in ya so duk sati sai kawai ta dauko su suyi weekend a gida amma sam Abba ya ki amincewa;
ya ma ce kada ta sake yi masa wannan zancen, don haka ta hakura. Ranar da ta fara kai su Hanan Kaka ta
saka ta a gaba tana son ta ji inda aka tsaya aikin maganinta, ta gatsine baki tace

“Ai da tuni kunga sauyi, babu abinda yayi aiki shima wanda kika ce za a dauke yana nan sai ma karo
wulakanci da yayi.”

Ta bata labarin yanda aka yi da Madu da kuma yanda tayi barin abinci da kuma yanda akayi ta saka
wancan amma tayi asararshi. Yaya Ummu tace

“Kai Amma fa za ki sa kwabar mu tayi ruwa, wannan wane irin abu ne sekace wadda aka sawa hanntac

“Toh ai sauran yana nan sai ya kara samun lafiya zan yi amfani da shi don ma kar na kara asarar.”

Kaka tace

“Toh Kinga dai shine kawai damar mu, in ya so in yayi aiki su yaran sai ki sa uban yayi miki maganinsu
daya bayan daya.”

“Haka ne kaka.”

Suka yi sallama tana ji a jikinta lallai za ta sake shiryawa tayi amfani da ragowar maganinta, domin idan
ba samu tayi ta mallake shi ba toh menene ribar auren nashi? Mutumin da baya tabusa komai kuma
kudin ma da zai sakar mata taji dadin rayuwa duk ya barwa yaranshi. Haka dai ta cigaba da kula tana
jiran taga ranar da Abban yake walwala da yawa ko zata dace.
……

Da yake yau Talata ce sai da ta kai su Hanan gidan Umma sannan ta shiga makaranta, tana shiga aka
sanar dasu malamin da zai musu lecture 9 to 11 ya bugo waya ba zai sami damar zuwa ba daman ta 4 to
5 ba tabbas don haka ta dubi kawarta Halima tace

“Dan wulakanci, da ya gaya mana tun jiya me zai fito dani?”

“Wallahi nima haka, muje gidanki kawai da yamma na wuce gida.”

Daga nan suka hawo motar Haliman b

Suka nufo gidan, bata tsaya daukan su Hanan ba ta barsu a kan idan yamma tayi sai ta fito gaba daya ta
dauko su Hanan ta dauko su Nawwara. Sai da ta kama kofar zata bude tajita a bude sannan ta tuna ashe
Zulaiha tana gida domin ita sai 12pm za ta tafi makaranta. Tana kicin tana wanke-wanke, sai da suka
zauna sannan ta fito suka gaisa da Halima da yake ta san ta, suna gama gaisawa ta koma ta cigaba da
wanke wankenta yayinda Saudah ta dauko ruwa da lemo ta cewa Halima

“Taso mu shiga daki kawata.”

Suka shige dakin Saudah suka turo kofar. A nan suka baje suka zauna suna ta hirarsu suna shewa don
wani lokacin idan suka kyalkyale da dariya har kicin din tana jiyo su. Ta gama wanke wanke ta duba
agogo taga karfe goma da kwata don haka sai ta dauko tsintsiya ta kama shara. Ta zo daidai kofar dakin
Saudah ta jiyo muryoyinsu kasa-kasa ta mike daga sharar ta kara kunnenta jikin kofar kamar yanda ta
saba don taji hirarrakinsu. Ta jiyo Saudah tana fadin

“Ta ce min kema fa kina siyanshi wani dan brown gari a leda bashi da wari kuma bashi da dandafadi

Halima ta bata amsa

“Ah, na gane shi kawata, ai wannan na maza ne shi za ki zubawa a miya.”

“Shine abinda nake gaya miki ai, wallahi ranar da na zuba masa wannan garin ko minti talatin bai yi ba da
cin abincin nan da ya dinga amai da gudawa sai da ya fita daga hayyacinsa. Ni ban karbi wata harka ba
sai tsabar fargaba shi kam a asibiti ma ya kwana.”

Ta zazzaro idanu ta kama haba tana mamaki

“Allah kawata?”

“Wallahi kuwa, ai wannan abun saura kadan ya sa ni takaba. Ai bazan ma kara siyan kayanta ba dama na
gaya mata babu harka, ko babu komai akwai tsufa don haka koma me na sha ko ya sha wasu lokutan
abun ba yiwuwa zai yi ba.”

“Kuma kin ga ni ina ganin aikinsa, musamman idan mukayi fada tunda baya wuce abinci wallahi
gumbuda masa nakeyi. Nan da nan zai Nemo ni ya bani hakuri har da tukwici.”

Saudah ta tabe baki

“Tab, toh ke kenan da kike auren yaro mai jini a jika wannan da dama kadan ya rage jinin babu karfi ai
kinga ya kusan shekawa. Ai ni nayi hankali ‘dan ba ‘kara mu ci gaba da baccinmu da minshari.”
Ta matsa daga jikin kofar a hankali ta ci gaba da sharar tana yi kamar ta fita da gudu saboda sauri kawai
take yi take ta kai rahoto. A gurguje ta karasa takwashe sharar ta shiga daki ta rufo kofar. Ta dauki
wayarta ta shige bandaki ta turo kofa; dama ita haka take yi indai za tayi wayarta ta gulma toh sai ta
shige bandaki saboda bata so wani yayi mata labe balle a ji me take fada. Ummanta ta kirawo, tana
dagawa bayan sun gaisa tace

“Umma kin san amai da gudawar da Abba yayi wancan satin ko?”

“Eh ai ya samu lafiya ko?”

Cikin yanayi na zakuwa ta amsa

“Eh Umma, kin san ashe magani Umman su Nawwara ta saka masa a abinci.”

Cikin yanayi na mamaki tace

“Ke Zulaiha, maganin me ana zaune lafiya?”

“Wallahi Umma da bakinta naji tana fadawa kawarta, irin magungunan nan ne na karfin maza ta saka
masa saboda tace baya komai sai bacci da minshari.”

“Laaa! Yanzu yayan takewa wannan wulakancin? Lallai yarinyar nan bata da kunya bata da hankali.”

“Wallahi Umma haka tace, na ma san kawar tasu mai sayar da magungunan ‘yar Sokoto ce.”

“Uhmn lallai ne. Toh shi yayan ya san ta saka masa wani abu.”

“Wallahi Umma bai sani ba, don ko abincin da likita yace ta bayar ayi gwaji canza miyar tayi sai yanzu na
fahimci kan zancen.”

“La ilaha illal Lahu, kashe shi za ta yi?”

“Wallahi dai Umma in bakuyi da gaske ba za ta baku mamaki.”

“Ai kuwa zan yi maganinta don ubanta, mu ba a yi mana wannan haukan.”

Suka yi sallama suka ajiye waya sannan Zulaihan ta fito ta ajiye wayarta ta koma ban dakin don tayo
wanka ta yi shirin makaranta. Itama Saudah a nan suka wuni ita da Halima suna hirarsu har sai hudu da
rabi sannan suka fito a motar Haliman don ta sauke Saudah a makarantar su Nawwara ta wuce gida.
Suna cikin tafiya a mota ta dubi Halima tace

“Ko ‘yar motar nan mutumin nan ya kasa saya min yana kallona Ina ta faman yawo.”

Tayi yar dariya sannan tace

“Haba kawata komai lokaci ne, ki bishi a hankali zai yi ne.”

“Hmmn, baki san mutumin nan ba ne idan banda ‘yayanshi fa babu wanda yakewa kyauta a duniya,
‘yayan ma na uwar gidanshi.”

Haka har suka karasa makarantar su Nawwara ta sauke ta sannan ta wuce.
Ita kuwa sa’a suna gama waya da Zulaiha ta shiga damuwa. Yanzu ashe wannan Saudan ma da takewa
kallon me hankali ashe idonta a bude yake. Yanzu ita har ta kai ta sawa miji magani a abinci, lallai dole ta
dauki mataki saboda ba za ta bari suna ji suna gani ta kashe musu dan uwa ba. Nan da nan ta dauki waya
ta kirawo Atiku, bayan sun gaisa tace

“Ka san amai da gudawar da Yaya yayi a karshen satin can ashe da dalili.”

“Kamar yaya da dalili, daman mana akwai dalili ai munyi waya da Baba Karami ya ce min likita ya ce food
poisoning ne sai dai an kasa gane a inda yaci abinci me guba.”

“Toh in gaya maka dai matarshi ce Saudah ta zuba masa.”

“A’ah wai me kike fada ne, guba ta zuba masa a abincin? Toh kashe shi tayi niyyar yi kenan?”

“O’oh, wai tace baya aikata mata komai da daddare sai bacci da minshari don haka ta sayi maganin
karfin maza ta zuba masa a abinci shine fa jikinshi bai karbi abun ba ya ci yayi ta wanna aman da
gudawan.”

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Kin ga illar auren kananan yaran nan masu budadden ido ko? Wadda
bata sami maganin mazan ta zuba maka ba sai ta je ta nemi maigadinka ko direba ta haifa maka ‘yayan
shegu a gida.”

“Shine fa, toh ai dole ayiwa tufkar hanci don in ba ayi mata da gaske ba zata kuma, ni kiranka nayi don ka
san yanda za kayi ka gaya masa don in ba haka ba wataran sai ta aika shi lahira sannan za muji garin
shegen barbade barnaden tsiya.”

“Hakane, ai kuwa dole zan je har Kanon na same shi na gaya masa don wannan harkar cikin gida ce shi
kadai zai yiwa kanshi maganinta.”

“Hakane, toh sai kaje nan kusa don in ba haka ba har ta kuma baka je ba.”

Suka yi sallama ta ajiye wayar. Baffa Atiku shima ya shiga rudani, wannan wace irin yarinya ce. Lallai
ranar Asabar da safe zai je Kanon don ya ga Yayan. Har ya ya ajiye wayar ya cigaba da aikinsa sai kuma ya
daukota ya danna ya kirawo Baba karami. Bayan sun gama gaisawa yace

“Weekend mukayi magana da kai a kan an kai abincin da Abbanku yaci ya samu food poisoning asibiti
ko?”

“Eh Baffa, ai likitan ma yace bincikensu ya nuna babu komai a tuwon da miyar sai dai idan a kunun ayar
ne shi kuma ka ga kafin ta dawo an shanye so likitan yace da wuya ma idan a kunun ne.”

“Toh ita ta san abincin da ta baku domin dai na ji daga manjiya me tushe cewa maganin maza ta zuba
masa yaci yayi wannan gigicewar?”

Har zai tambayi Baffan menene maganin maza sai kuma kwakwalwarshi ta hasko masa amsar, a razane
yace

“Um!”
“Ai kwarai kuwa. Da banyi niyyar gaya maka na amma dai na ce bari na gaya maka ko za ka gayawa
likitan la Allah ya fahimci wani abu sannan kuma ku din idan akwai hanyar da za ku bi kusa ido in ba haka
ba sai tayi mana barna.”

“Uhm, in Sha Allahu zan gayawa likitan kuma za mu sa idon ma.”

Sukayi sallama ya ajiye wayar ya shiga mamaki. Yanzu wannan ‘yar ficiciyar yarinyar mai kama da abun
tausayi har ta san wani maganin maza. Sai kuma abun ya bashi dariya ya kuwa kyalkyale da dariyar,
dama dai an ce kaza garin kwadayinta take tono wukar yankata. Shi da ma Baffa Atiku ya sani bai gaya
masa ba don ba wani abu da zai iya yi a kai ba, ko da yake zai sanar da likitan. Haka ya wuni yana tuno
abun yana dariya shi kadai kamar mai hauka sabon kamu.

Ranar Asabar tun ana idar da sallar asuba Atiku ya kamo hanyar Kano don ya fi so ya sami Abban a gida.
Yayi sa’a yana shiga ya same shi a tsakar gida shi da Madu za su fita don shi Salim yana da lecture 8 am,
don haka yana makaranta. Yayi masa iso wajen Saudah ya nuna masa suje wajen Mommy don magana
yazo suyi. Shi kuwa Madu bayan ya gaishe da Baffa sai ya dauko kujera a nan tsakar gidan ya ajiye a
inuwa daidai bakin tagar falon ya zauna yana jiran Abban. Su kuma su Abba suna shiga suka zauna a kan
kujerar zaman mutum uku wadda take bakin wannan tagar dai. Bayan sun sake gaisawa yace

“Ya jikin naka?”

Yayi dariya

“Ah ai na samu lafiya, likata dai yace food poisoning ne duk da ma an kasa gane wane food din.”

“A’ah ba’a dai kasa ganewa ba, an dai bayar da abincin da ba a shi aka zuba maka binda ya janyo ba.”

“Ban gane me kake so kace ba?”

Nan ya mayar masa da zancen kamar yanda Sa’a ta sanar masa. Take ya shiga yanayi na kaduwa da
mamaki, lallai biri yayi kama da mutum. Dama ai kwanaki ta gama bayar da labarin shi tsohone baya iya
komai watakil shine ta shiga nemar masa magani. Ya ma rasa tunanin me zai yi, wai ya zai yi da wannan
yarinyar ne? Haka kawai ya kori matarshi ta rufin asiri yanzu gashi wannan din za ta kwance masa zani a
kasuwa. Ya dago ya dubi Atiku yace

“Ita Sa’an ce ta gaya maka wannan labarin.”

“Eh, itace ta fada mana ai da yake ita Zulaiha da kunnenta ta jiyo don haka ta fada don a dau mataki.”

Yayi shiru ya sunkuyar da kai, lallai idan dai Sa’a ta ji wannan maganar toh duk wani mahaluki da yake
Bichi ma ya dade da sani, yanzu kenan haka za su dinga kallonsa a matsayin wanda ya kasa. Amma kuwa
ba’a kyauta masa ba, toh waye ma bai kyauta masa ba Zulaiha da ta fita da zance ko kuwa Saudah. A
halin yanzu kam ai sai dai yace bai kyautawa kansa ba, amma zai dau mataki dole.

Shi kuwa Madu yana jin wannan labarin dariya ta kusa kwace masa sai rufe bakinsa yayi da hannunsa ya
lallaba ya fita baikin gate. Yana fita kuwa ya tuntsire da dariya kamar zai fadi kasa yace

“Kan bala’i.”
Wato ‘yar wannan matar da ya raina itace da wannan aiki, Allah sarki Abba ya dauko ruwan dafa kansa
tunda dai wannan zance ma babu wanda ya isa ya tona. Ya kara kwashe da dariya sai kuma ya fara
tausayin Abban.
EPISODE 26



Kamar yanda ya saba tun bayan da aka ce an nemeta an rasa duk safiyar litinin yana zama a office sai ya
kirawo Baba karami da Ahmad don ya ji inda aka tsaya, yau ma Baban ya kirawo. Bayan sun gama
gaggaisawa yace

“Baba wai ya na ji ku shiru ne?”

Cikin yanayi na kosawa da matsananciyar damuwa yace

“Baba Mubarak wallahi har yanzu shiru, kuma har yanzu bamu daina bayar da sanarwa da cigiyarta ba.”

“Ikon Allah, wannan abun ya fara bani tsoro fa. For over 30 days ace ba’a ga Rabi ba? Shi Abban naku me
yace.”

“Toh ai duk da shi ake ta cigiyar kuma har yanzu babu wani labari.”

Suka dan yi shiru kowa da abinda yake tunani

“Toh shi kenan za mu sake yin waya.”

Sukayi sallama suka ajiye waya. Wayar ya ajiye a kan tebur din da yake gabansa ya fada tunani. Ina Rabi
za ta shiga, Allah ya sa dai ba ‘yan yankan kai ne suka sace ta ba. Amma ya za ayi ace an rasa ta, jiya har
wajen sha dayan dare yana waya da Baraka amma duk tunaninsu ya kare basu samo inda take ba.

“Mtsewww.”

Ya ja tsaki a fili, ya mika hannu ya dauki wayar da ya ajiye ya kirawo mai dakinsa ya sanar da ita yanzu zai
tafi Kano.

“Lafiya dai ko, don naga baka fita da shiri ba.” Ta tambaya

“Sai in ga kamar babu abinda suke yi a kan batan Yaya Rabi, shi Yaya Munzali kullum sai dai yace min
suna kan nemanta. Nayi nayi da shi ya koma ya kara jawa Usman din kunne ya ki, gara kawai ni naje.
Gani nake kamar babu abinda suke yi a kai in ba haka ba an fi kwana talatin ana abu daya fa.”

“Haka ne kam, toh yaushe za ka dawo.”

“Yau din zan dawo sai dai in ta kama na kwana toh zan kirawo ki.”

Sukayi sallama suka ajiye waya, ya dauki mukullan motarsa ya rufe office din ya fice.

Yana isa Kano ya wuce kasuwa don ya san can zai sami Usman ya san in dai ya tsaya gidan Yaya Munzali
ba zai bari suje wajen Usman din ba. Kafin ya karaso cikin shagon Madu ya hangoshi, nan da nan ya fito
yana yi masa sannu da zuwa. Ya karasa cikin shagon inda Abba yake, aka saka masa kujera ya zauna
Abban yana yi masa maraba. Madu da sauran yaran shagon suka fice, ya dube shi yace

“Zuwa nayi naji inda aka tsaya, Rabi har yanzu shiru me kakeyi a kai ne?”

“Wallahi na fi ka tashin hankali Mubarak, babu inda bamu buga ba. Police station din da na kai rahota
har sun gaji da ganina,

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login