Showing 117001 words to 120000 words out of 196754 words
Chapter 40 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
tace
“Saukar yaushe Yaya ko unguwar tamu baka karaso ba?”
Kallon da yayi mata ya sa ta shiga hankalinta ta daina wani wage baki da takeyi. Ta san dai ba zai wuce
don ta tura masa Atiku bane a kan maganar da Zulaiha ta fada kuma babu yanda zai yi da ita. Shine
babba a cikinsu kuma ya fi kowa kudi sai su bari wata ‘yar mitsitsiyar yarinya ta zo ta kasheshi, idan ba’a
gaya masa ba ya za ayi ya san me ta saka mishi ya sa shi gudawar. Ta san halin mata babu yanda za ayi
ita da ta aikata ta fada sai dai kawai ta canza dabara. Ta dubi Inna tace
“Inna bari naje gidan Batula yanzu zan dawo.”
Ta yiwa Inna sallama ta fice ta bar Abba da Salim a nan. Ya tsani dabi’un Sa’a, tunda mahaifiyarsu ta rasu
take jin kanta kamar dole sai ta maye musu gurbin Innan, sai dai ta manta shi Yayanta ne. So take kawai
ta dinga kula da su kamar wasu kananan yara tana sa duk abinda za suyi sai ta sani, duk da cewa shi
Atiku wasu lokutan yana biye mata amma shi Abba baya sauraronta. Abinda ya fara hada ta fada da Rabi
kenen; tunda aka aurota ta so ace duk abinda zai yiwa Rabi yayi shawara da ita saboda ta riga shi aure da
shekaru; a take ya nuna mata ba zai yiwu ba, don haka ta tsani Rabi take cewa Rabi ta mallake shi. Ita
kanta Zulaihan yanzu haka ya tsani ganinta a gidan nashi sai dai ba zai iya korar ta ba, shima wan Uba ne
ya rike su bayan uban ya rasu toh ya za ayi shi kuma ya tozarta zumunchi. Shi yasa ya barta a kan da
zararr an yi hutu zai ce ta dinga tafiya Bichin. Allah ne ma ya san iya zantukan da ta kwaso ta kai Bichin.
Nan ya zauna suka dan taba hira da Innan sannan yayi mata sallama suka koma wajen Baffa. Sai bayan
sallar la’asar sannan suka kamo hanyar dawowa gida.
…………….
Suna ajiye Baffa suka wuce kasuwa sai bayan isha’I sanna suka koma gida. A gajiye yake sosai don haka
bayan ya kintsa ya fito sai kawai ya zauna a kasa kan kafet yacewa Saudah ta ajiye masa abincin a kasa
zai ci. Ta kwaso daga dining table ta ajiye a gabansa, ta bude kwanukan ta fara zubawa. Sai da gabashi ya
fadi da yaga tuwon alkama da miyar kuka. Sai da ta gama zubawa ta tura masa kwanon ya kalli abincin
ya kalleta, tace
“Ya ne? Ko yau baka son cin tuwon ne?
Ya kalleta yana kura mata ido yace
“Kin san idan miciji ya sare ka ko tsumma ka gani sai ya baka tsoro ko. Karon mu na karshe da tuwon nan
ban ji da dadi ba.”
Tayi murmushi tace
“Toh ai wancan ma likita ya gaya maka babu komai a ciki matsala dai kawai aka samu.”
Yayi dan gajeren murmushi sannan ya bata amsa
“Wanda kika bawa likita babu komai a ciki amma kin san wanda na ci a ciki kika zuba maganin.”
Ta ji matsanancin faduwar gaba, tayi sauri ta kalli kasa don kar su hada ido tace
“Magani kuma, ni kuwa maganin me zan zuba maka a abincin haka?”
Ya tsattsare ta da ido
“Maganin karfin maza da kawarki ta kawo miki mana, ko ba shi bane?”
Gabanta ya fadi bugun zuciyarta ya kara gudu, ta sunkuyar da kai ji take kamar kasa ta tsage ta shige ciki
don kunya.
“Tun lokacin da kaka ta kawo miki kaya tsafe tsafe nace miki bana son barbade ashe baki daina ba ko?
Me kike so ki mayar da kanki ne? Haka kawai ki dauki abinda ke kanki baki san menene shi ba ki zuba
min a abinci saboda zalunci ko? Ko da yake in na mutu ai baki da asara sai kawai ki auri saurayi wanda
yake da karfin da zai iya biya miki bukata ko?”
Tuni hawaye sun riga sun jike mata fuska, ita kanta bata san kukan me take ba. Kunya taji ko kuwa
takaici, toh wa ya gaya masa? Wannan abun kunya da yawa yake? Toh amma ai akwai bukatar wadda
don ita aka yi auren amma baya biya mata, toh ya yake so tayi? Duk wasu maganganu da take neman
irin wannan damar ta gaya masa yau sun bace daga kwakwalwarta. Sai da ya ji shirun nata yayi yawa ya
cigaba
“Na san cewa akwai tauye hakki, amma ke kin san komai karfina bani da natsuwa sanan ga rashin lafiyar
da wani lokacin ke ma bakya yin abinda ya kamata don ganin blood sugar din nawa ya sauka. Ko ba haka
ba ai wannan matsala ce tamu ni da ke ba wai ke da ‘kawa ko wata can ba, gashi nan yanzu zancen har
Bichi. Don ni a can na jiyo wai babu abinda nake miki sai bacci da minshari; ko da yake dama da kunnena
ma na ji kina gayawa kawarki illar auren tsoho.”
Ta dago ta kalleshi a firgice, suna hada ido tayi sauri ta sunkuyar da kanta. A Bichi? Toh wane munafikin
ne ya kwashi zancen nan har Bichi? Zancen da suka yi a dakinta ita da Maman Surayya? Zulaiha! Tabbas
Zulaiha ce tayi mata labe, ai kuwa sai ta gurje mata baki kuma in bata yi wasa ba sai ta koreta daga gidan
nan. Toh amma shi a iba yaji tana bayanin illar auren tsoho? Kai! Da kyar ta nemo muryarta tace
“Kayi hakuri.”
“Ke zan bawa hakuri saboda ke aka tauyewa hakki, amma gashi nan saboda mugun hali da wauta kin
kwashi zancen da ya kamata ayi a daki kin rabar a gari kowa ya ji.”
Ta share guntun hawayen da yake fuskarta tace
“Kayi hakuri, nima ai tun daga shi ban sake zuba maka komai ba. Na wajen kaka kuma wallahi ban sake
karbar komai ba.”
“Ya za ayi na sani? Yanzu kinga kin saka min zargi a cikin zuciyata ko me kika bani sai na ji fargaba kafin
naci, wani abun ma bana iya ci. Wallahi ko abinci kika zuba na tafi da shi kasuwa idan zuciya ta tayi wasi
wasi a kanshi bayarwa nake na sayi na kasuwa. Lokuta da dama har tsoronki nake yi, garin son zuciya ki
bata tsakaninki da Allah da bayin Allah. Shekaru sama da ashirin da biyar ina zaune da Rabi bata taba
zuba min wani abu a abinci ba ko don wane dalili amma ke gashi a tsakanin shekaru basu fi shida ba
Allah ne ya san yawan gubar da kika zuba min na cinye.”
Ta sake share hawayenta, maganganun shi sun mata tsauri da yawa duk da ta san ta aikata. Ita Rabin da
yake cewa bata taba zubawa in ta zuba gaya masa zata yi, kawai don an fi ta iya dabara. Ta bude baki da
kyar tace
“Ka yi hakuri, ba zan sake ba.”
Ya kalleta ya dauke kai, sai taje ta aikata barna da an yi magana ta sa mutane a gaba da kuka. Gaba daya
ma shi mamaki take bashi, yanzu wannan yar yarinyar har ta san ta bi boka kuma ta san ta bi masu
magani kala kala. Tunda suka yi na Kaka ya hana su zuwa gidan ya zata ta daina ashe bata daina ba.
Tunda Atiku ya zo ya same shi da wannan zancen kullum sai yayi auzu billahi yake iya cin abincin da ta
dafa masa, duk da shima Atikun ya bashi haushi amma ya dade da sanin fitnar Sa’a. Duk wani abunda
babu ruwanta shi tafi son shiga kuma da yake ta raina Atikun sai ta sashi yayi ta shirme irin wannan. Da
ta ji shirun nashi ya tsawaita ta sake cewa
“Kayi hakuri, in sha Allahu bazan sake ba.”
“Allah ya sauwake.” Kawai yace.
Ya dai ji abinda tace amma ko duk jikinshi kunnene ba zai yarda ba. Haka ta saba duk lokacin da tayi wani
abu ba daidai ba ta iya bada hakuri amma ko ta bayar da hakurin sai ta sake irin wannan laifin. Ya rasa
wacce irin kwakwalwa ce da ita, kayi ta yin abu ma ana kamaka ai ya kamata ace ka hakura ka san babu
riba.
Ta tashi jiki a sanyaye ta dauki farantin abincin za ta fice da shi ya dube ta yace
“A’ah! Wannan din ma kin zuba wani abun kenan a ciki.”
Ta tsaya ta juyo ta kalleshi tana rike da farantin tace
“Wallahi ban zuba komai ba, na zata ba za kaci bane babu abinda na zuba.”
“Toh ajiye na ci, in ma kin zuba ke da Allah don sai Allah ya bi min hakki na.”
Ta tsuguna a gabanshi ta ajiye tray din ta juya jiki a sanyaye ta shige dakinta. Ya bi bayanta da kallo
“A haka kamar mutuniyar kirki.”
Ya fada a fili yana gatsine baki.
Tana shiga dakin ta dora hannuwanta a ka, so tayi ta kurma ihu ko za ta samu malolon da ya tokare mata
makogoro ya fada. Da yake ta tabbatar idan tayi ihu za a ji sai tayi shiru kawai tana shassheka. Sai da tayi
me isarta sannan ta karasa ta zauna a gefen gadon, ta share ragowar hawayen da yake fuskarta sannan
ta cije yatsa. Wato haka Zulaiha ta yi mata, kwata kwata ta manta ma Zulaiha tana gidan lokacin da
sukayi wannan maganar amma shine za ta kwashi wannan zancen don wulakanci ta kai Bichin, lallai sai
ta koya mata hankali don ubanta. Sai ta nuna mata ita karamar ‘yar iska ce. Ta tashi ta shige bandaki ta
wanko fuska ta fito tana goge fuska da tawul, wato har wani yabon matarshi yake a gabanta, wai ita bata
taba yi masa barbade ba har wanibgaya mata yake itace mai mugun hali saboda cuta. Ita duk cutar da
ake mata a gidan nan ba ta magana amma ita daga an sami matsala sai ya sa ta a gaba da fada. Haka dai
da kyar ta samu ta shirya ta kwanta a kusa da yara, da yake bacci barawo ne ba jimawa ta dauke ta.
EPISODE 27
INA RABI TA SHIGA? ME YA FARU DA ITA?
Sai da suka kama hanya sannan direban ya juyo ya dubeta yace
“Hajiya cikin Kano line za ki shiga ko bakin titi za a sauke ki?”
Tace
“Ciki.”
“Drop kenan fa Hajiya naira dari biyu da hamsin.”
“Muje babu damuwa.”
Sai a lokacin ta tuna bata ma san ko da kudi a jakartata ba ko babu. Ta zuge zip din jakar ta zaro wallet
dinta ta duba ta sami naira dubu biyar a ciki; tun zuwan Baba ne da zai tafi ya bata naira dubu goma, ta
kashe dubu biyar sauran ne wannan; ta mayar da wallet ta duba aljihun ciki na jakar inda a nan ma ta
samu kusan naira dubu amma duka ‘yan canji wato ‘yan hamsin da ashirin. Ta mayar da jakarta ta rufe ta
cigaba da kallon hanya. Sun shiga Kano line direban yace
“Hajiya motar ina za ki hau sai na sauke ki a daidai.”
Tace
“Jigawa, Dutse zan je.”
Kafin ta kai ga fitowa daga tasi din an samar mata guri a motar Dutse. Mutum biyu ne a cikin motar ta
zauna suka yi uku, direban ya leko bayan motar yace
“Saura mutum uku, in sha Allahu yanzu za mu tashi.”
Sai da aka dan dauki lokaci sannan motar ta cika, nan da nan suka kama hanya. Tunda ta zauna a motar
take ta ambaton Allah don haka zuwa lokacin da suka dauki hanya sosai ta dan fara samun natsuwa. Ta
juyar da kanta tana kallon gefen hanya tana yaba halittun Allah na shukokin da take hangowa daga nesa.
Kamar wadda aka zungura kuma ta tuna ashe wai Usman korarta yayi daga gidashi, ba ma saki ba kora.
Gani takeyi kamar gara ma a sake ka akan abinda yayi mata. A gaban kishiya, a gaban yaranta ya dubi
tsabar idonta yace ta fice masa gida, lallai Usman. Ta tuna fuskar Auta da yake kallonta cikin zakuwa
yana mata alamar ta karba, kwalla ga kara taruwa a idonta ta sa hijabinta ta goge. Tabbas da ba don
yaranta ba da ba za ta sake bari Usman ya ganta ba, amma ‘yaya sun hada don aure dai kam ta gamashi.
Ta tuno loakcin da tana amarya kusan kullum in zai fita sai tayi ta magiya ya fita da ita ya kaita gida, ta
kan ce
“Don Allah ka tafi dani ka kaini gidanmu in ka dawo sai ka dauko ni.”
“Wai gidan su Mubarak.”
“Eh gidanmu.”
Yayi dariya yace
“Yarinya ke ai nine gidanki bayan ni baki da wani gida.”
“Kai ne ma gidan ba nan ba.”
“Eh, ai nan din ma ya zama gidan ne don ina cikinsa, duk gidan da bani a ciki ba gidanki bane Rabina.”
Ta cigaba da yi masa dariya
“Toh shike nan babu inda zan kaiki kuwa har sai kin yarda ni ne gidanki, bari ma ki gani na tafi.”
Ta karasa da sauri ta sha gabansa tace
“Toh na yarda, wallahi na yarda bani da wani gida bayan kai.”
Ta karkata kai tace
“In dauko mayafin ko nawan?”
Ya kalleta suka hada ido ya lakace mata hanci yana fadin
“Dauko ba don halinki ba, kar na tafi na barki kyankyaso ya baki tsoro.”
Duk da yanayin da take ciki sai da tayi murmushi da ta tuno hirar nan. Yau Usman ya manta shine
gidanta ita ya kora korar kare duk a dalilin kishiya. Ta share kwallar da ta sake fadowa idonta, ta mayar
da dubanta gefen hanya ta cigaba da kallon halittun Allah tana kuma yiwa Allah tasbihi.
Sai da aka kusan magriba sannan suka isa Dutsen, a hakan ma don direban yana gudu ne don ya sha
ruwa a Dutse. Suna sauka ta sake daukar shatar tasi zuwa gidan Baraka.
Dawowarta kenan daga aiki tana ta sauri kada a sha ruwa bata zauna ba. A rumfar da aka tanada don
motocin gida ta saka tata motar ta fito tana kwashe kayanta daga bayan motar kenan ta jiyo ana buga
gate. A ranta tace wa kuma na samu da magribar fari. Maigadin gida da suke kira Baba Habu ya bude
kofar ya ja baya yana rage tsaho alamar gaisuwa yayinda ya bata hanya ta shigo. Daga nesa bata gane
fusakar sosai ba sai da ta dan matso, tana ganeta mamakinta ya karu tace
“Bibi.”
To me Rabi takeyi a Dutse da yamman nan ga azumi. Nan da nan ta ajiye kayan da ta dauko a kan motar
ta nufo ta da sauri, suka hadu a tsakiya. Ta kama hannunta tana duban fuskarta da mamaki tace
“Bibi? Lafiya kuwa Bibi? Ina yaran na ganki ke kadai haka.”
Suna hada ido taji wani malolo ya tokare mata makogoro, nan da nan hawayen ya fara bin fuskarta.
Baraka ta kara firgita tace
“A’ah, Bibi wai ko hatsari kika yi ne a hanya?”
Da taga ta rude ta jijjiga mata kai alamar a’a. Ta dubi Baba Habu da yake tsaye a bakin gate tace
“Baba Habu kwaso kayan ka rufe motar ka bawa Zahra ta kawo min.”
Ta kama hannun Rabi suka nufi cikin gidan. Suna shiga falon Uwani mai aikin Baraka ta leko daga kichin
inda take hada musu abincin buda baki tace
“Sannu da zuwa Hajiya.”
“Yauwa Uwani.”
Zahra ma ta fito daga kichin din itama tace a ciki hausarta mai kama da fulatanci
“Inna sannu da dawowa.”
“Yauwa Zahra, ki karbo kaya na a wajen Habu ki kawo min.”
Ta ja hannun Rabi suka haye sama, sai da suka kai dakinta sannan ta zauna a kan kujerar zaman mutum
biyu da take dakin ta zaunar da Rabi a kusa da ita. Kafin tace wani abu suka ji kiran magriba, dai dai nan
kuma Zahra ta turo kofar ta shigo da sallama, bayan sun amsa sallamarta ta shige ta ajiye kayan a kan
mudubin ta mikawa Baraka wayarta. Ta tsuguna ta gaida Rabi wadda ta amsa da murmushi. Baraka ta
dubeta tace
“Ki kawo mana zobo da ruwan sanyi nan.”
“Toh Inna.”
Ta mike ta fice. Baraka ta dubi Rabi zata yi magana Rabin ta sa dariya ta dafa hannunta tace
“Ki bari mu sha ruwa mana sai ki ji me ya kawo ni.”
Tayi murmushi tace
“Haka ne kuma.”
Zahra ta shigo da tray dauke da ruwa roba biyu da kuma zobo mai sanyi a jug da kofuna guda biyu da
kuma kankana a dan karamin faranti. Ta ajiye a kan kafet din dake gaban kujerar tace
“Inna har kankana na yanka miki.”
Tace
“Ai kuwa na gode Zahra, Allah yayi miki albarka.”
Ta fice ta barsu suna shan ruwa. Sai da sukayi alwala sukayi sallar magriba sannan Baraka ta dubi Rabi ta
ce
“A kawo mana abincin nan ko mu je kasa.”
“Duk yanda kika ce.”
“Toh gaskiya bari na sa a kawo mana nan.”
Ta kirawo Zahra tace ta karbi abinci ta kawo musu dakin. A nan suka zauna suka fara cin abincin, Baraka
ta kasa jurewa ta kurbi shayinta ta ajiye kofin ta dauki dan kwano ta fara zuba farfesun kaza tace
“Bibi kin barni a duhu, don Allah kowa dai lafiya kika taho da wannan yammar ba tare da kowa ya kawo
ki ba.”
Tayi murmushin bakin ciki yayinda Baraka ta cika cokali da roman kaza ta kurbe tace
“Koroni Abban Khalifa yayi.”
Ta kware da ragowar roman da take kokarin hadiyewa ta dan yi tari tace
“Kora kuma? Ban gane ba.”
Ta mayar da kwanon farfesun ta ajiye a kasa yayinda ita kuma Rabi ta sa cokali mai yatsun da yake
hannunta ta tsikari dankali da kwai ta kai bakinta, sai da ta hadiye sannan tace
“Yace na fitar masa daga gida.”
“Bibi kina kara sani a duhu shi Usman din ne yace ki fitar masa daga gida? To sakinki yayi ko me?”
Nan ta bata labarin yanda abun ya faru daga farko har karshe, tace
“Toh ya ce in fitar masa daga gida tunda bana kaunar ‘yayansa.”
Baraka da take mata kallon mamaki da baki a bude ta rufe bakin nata tace
“Amma ban taba sanin Usman dan iska bane sai yau, shi yanzu har yayi gidan dai zai ce ki fita saboda ya
auro wannan kucakar? Toh sakinki yayi ko me?”
“Bai sake ni ba amma zai sake ni don ba zan koma ba?”
Suka yi shiru na dan lokaci Rabi ta ci gaba da cin abincinta, ita kuwa Baraka ta kasa ci sai dai shayi kawai
da take ta korawa. Baraka ce ta karya shirun tace
“Lallai namiji sai a barshi, shekara talatin da aure amma mace bata wuce kora ba. To sai sai yaushe ne
mace za ta mike kafa a gidan miji?”
“Babu rana.”
Ta bata amsa tana tabe baki. Suka sake yin shiru na dan lokaci sannan Rabi ta ce
“Nan da kika gan ni
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good