Showing 78001 words to 81000 words out of 196754 words

Chapter 27 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15367

ma bata yi ba ta cigaba
da aikinta. Ta dai san ko me zai yi mata ba za ta karbi yaran nan ba sai dai ayi duk abinda za ayi, da ganin
mutuncin ta Saudan take yi ne ma da sai ta daure domin ita a yanda take tuno wahalar kula da yara ma
bata ko sha’awar ta sake yi. Sai da ya kira sau biyu ba ta dauka ba yana kan na ukun sai kawai ya dauki
mukullin mota ya kamo hanyar gidan. Ko wanne irin taurin kai Rabi take ji da shi lallai yau zai sauke mata
shi don sai ta rike yaran nan. Wannan wace irin fitina ce?

Tana na tsaye a kan baranda yara suna ta wasan su musamman Hanan wadda bata da wani ciwo, sai
kaiwa da kawowa takeyi tana neman fashewa da kuka. Ta taba wayarta ta kalli lokaci taga karfe biyu
saura minti biyar, ta sake danna masa kira. Yana dagawa kafin tayi magana ya ce
“Gani nan na kusa karasowa gidan.”

Ya katse wayar ya ajiye.

Sai da ta goge kwallar saboda takaici. Tana daga kai sama ta hango tagar gidan makota. Da mutunci suke
yi ma da ko a makota ai za a rike mata su sai dai ita tunda ta zo unguwar bata kula kaf matan layin. A
cewarta dukansu kawayen Rabi ne don haka babu gidan da take shiga. Wadanda take harka da su can
kasan unguwa suke Kuma ba irin wadanda za ta kaiwa yara bane. Tana na tsaye taji tsayuwar motarshi,
kafin wani lokaci ya turo gate din ya shigo rike da mukullin mota. Nan da nan ta nufi wajenshi yace

“Ina Mommyn.”

“Tana ciki.” Ta fada taba nuna wajenta.

Ya karasa ya sa mukullinshi ya bude kofar ya shiga. Tun daga nan bakin kofar yake kwala mata kira

“Rabi, Rabi.”

A kicin take tana aiki, ta ajiye aikin da ta jiyo kiranshi ta fito daga kichin din ta tsaya daga bakin kofa tace

“Sannu da zuwa.”

Bai amsa ta ba ya cigaba

“Wanne irin wulakanci ne na ce ta baki yara ta tafi makaranta za ki ce ba ke nace ta bawa ba?”

Ya juya ya dubi Saudah da take bayanshi tana ta wata rawar jiki yace

“Zo ki bata su mu je na kaiki.”

Ta nufo mommy da sauri yayinda Mommyn ta rungume hannanyenta tace ai na ce ba zan rike su ba, ta
tafi ds su ko kai ka zauna ka rike mata su.”

Kafin ta karasa wajen Rabin ta dakata, tuni hawaye sun wanke mata fuska saboda agogon bangon da
yake saman kofar kicin din ya nuna mata karfe biyu da kwata. Ya dubi Mommy a fusace yana nuna ta da
yatsa ya ce

“To wallahi baki isa ba Rabi, ko ki rike su ko ki zo ki bar min gidana don su gidan ubansu ne babu yanda
za ayi dasu.”

Gabanta yayi matukar faduwa saboda bata taba tsammanin zai iya furta mata kalami mai kama da
wannan ba, nan da nan idanuwanta suka ciko da kwalla. Ana haka Auta da Khalifa suka yi sallama suka
shigo suna kallon iyayen nasu, a hankali suka huce kusa da Mommy Khalifa ya kamo hannunta ya rike, da
kyar ta makale kwallar da ke idonta tace

“Duk abinda kace zan iya yi maka amma bazan rike mata yara ba, yaro yana cikinta ma na bi shi na kashe
balle an hada min biyu masu rai. Ba zan iya ba ta je da su kawai.”

“Toh kuwa wallahi sai dai ki bar gidan nan, don rashin imani awa biyu kawai ki rike mata yaran kin kasa
saboda tsabar kyashi.”

Maganganunshi sun yi matukar yi mata ciwo kuma sun tunzura zuciyarta. Kwallar da take makalewa sai
da ta fado tayi sauri ta fizge hannunta da yake cikin hannun auta ta share. Ya nuna Saudah yace
“Ki bata su mu tafi.”

Jikinta na rawa ta kara matsawa ta nufi Mommy, cikin hanzari ta daga mata hannu tace

“Ba zan karba ba ki je da su kawai.”

“Sai dai ki zo ki fice min daga gidana Rabi don bazai yiwu na zauna da ke kina kyamar ‘yayana ba.”

Ta sake share kwallar da taki daina fitowa ta kawar da kanta daga kallon Auta wanda ya dawo gabanta
yana mata alamar ya karbesu.

“Ki zo ki fice min daga gida nace yanzun nan.”

Ya sake fada a fusace.

Saudah da ta koma bayanshi ta tsaya ta dan ja rigarshi ya juyo ya dubeta a fusace ta ma rasa me za ta ce
masa. Da kyar ta Bude bakinta tace

“Na makara ka zo mu tafi kwai.”

Ya juya ya dubi Mommy

“Baki ji me nake ce miki bane?”

Ta sa hannu ta share kwalla ta fizge hannunta daga hannun Khalifa ta ratsa su ta huce ta shige dakinta.
Gabaki daya tunaninshi ya tsaya, bai taba tunanin Rabi zata iya barin gidansa ba ko me za ayi mata. Kafin
ya gama wannan tunanin ta fito sanye da hijabinta da jakarta a hannu ta ratsa su ta huce ta nufi fita.
Tuni Auta da Khalifa suka sa kuka. Auta ya nufo ta da gudu yana

“Mommy.”

Abba ya daka masa tsawa ya dakatar dashi

“Koma ciki.”

Binta kawai yayi da kallo har ta fice daga falon, idonshi har rufewa yake saboda kaduwa da takaici.
Saudah ce tayi sauri ta dubi agogon bangon taga karfe biyu da rabi ta tabo shi tace

“Ni dai na makara, an riga ma an shiga.”

Ya wuce ya nufi kofa yana fadin

“Kwaso su muje.”

Nan da nan ta kamo hannun Hanan dama shi Baffa yana hannunta. Kafin su fito tsakar gidan tuni
Mommy ta fice. Ko da suka fito bakin gate inda mota take ma yana ta waige ko zai hango inda tayi amma
bai hangota ba. Saudah ta zuba yaran a bayan mota ya fizgi motar suka kama hanya. Duk yanda suka kai
ga sauri sai da suka sami cunkoson motoci a hanya don haka kafin su kai BUK new site karfe uku ta riga
ta yi. Suna shiga ta nuna mishi inda ake jarrabawar ya kaita har bakin kofa. Yace

“Ki barsu a nan kije ki yi ki fito mu tafi.”

Kafin ta bashi amsa ta hango mutum biyu ‘yan ajinsu sun fito daga dakin jarrabawar da takarda a
hannunsu, nan da nan hawayen ya wanke mata fuska tace
“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, shike nan ma ai tunda wasu suka fito ba za a barni nayi ba. Absent
kawai za a sa min.”

Yayi tsaki yace

“Ki je dai ki gani kin tsaya kina wani koke koke.”

“Ba za su ma saurare ni ba.”

Ya sake yin tsaki ya fice daga motar ya nufi dakin jarrabawa. Jimawa kadan ya fito ya tashi motar tana
fadin

“Sunce kin makara sai dai ki sake course din next year.”

Wani malolo ne ya tokare mata makogoro saboda takaici. 3 credit course ya zamar mata kaya, ga shi
sauran ma da tayi jarabawar ba wai tana da tabbas bane amma wannan wane irin abu ne. Dama ta san
yanda yakewa wannan karatun nata diban albarka sai ya janyo mata. Sai da suka kusa isa gida sannan ta
ta da su Nawwara don haka ta gaya masa ya tsaya a makarantar ya dauko su sannan suka huce gidan
tana share kwalla, ta kwashi yaran ta fito daga motar shi kuma ya juya kan motarshi ya koma kasuwa.
Rasa jarrabawar da Saudah tayi bai dameshi ba kamar yanda tafiyar Rabi ta dame shi, sai yanzu ne ma ya
tabbatar bai san Rabi ba don kafin yanzu ko a mafarki ya zata idan ya koreta hakuri za ta fara bashi don
ya barta ta zauna, ko ba don shi ba don yaranta. Amma babu komai ya san ba za ta huce wajen Shafa ba,
sai zuwa jibi idan basu kirawo shi ba shi sai ya je a yita ta kare. Ya san idan aka mayar da maganar a
gaban shafan ma suyi mata magana ta bari a zauna lafiya, ko shafa bata ce komai ba ya san Yayanta
Munzali zai sa baki don shi ma matansa biyu. Haka har ya isa kasuwa.

Su Abba suna fita daga gidan Auta da Khalifa suka runtumo da gudu ko za su hangota, amma babu ita
babu alamarta. A rude suka koma cikin gidan gashi kuma dukansu basu da waya, don haka suka zauna
suka yi jugum jugum. Daga baya dabara ta fadowa Auta suka sake fitowa suka duba basu ga Malam Bala
ba, da alama ya tafi wani wajen da sai su ari wayarshi su kirawo Madu ko Ahmad. Haka suka sake
komawa dakin suna fargaba auta kuma yana ta share hawaye.




Mommy tana fitowa daga gidan ta nufi titi don ta hau tasi ta tafi gidan Yaya Shafa. Tana tafiya zuciyarta
tana yi mata kuna, bakinta har ‘daci yake yi saboda takaici. Tana cikin tafiya ta juyo ta kalli gidan, hawaye
suka kara wanke mata fuska. Addua kawai takeyi kada taga wanda ta sani ya tsayar da ita. Gabaki daya
duk wani ragowar so da takeyiwa Abban Khalifa ya zube yau, wannan shine karo na karshe da zai yi mata
wulakanci. Ta tuno wani lokaci bayan ta haifi Madu da suka sami sabani a kan tana son ya daukar mata
mai aiki. Ya sa ta a gaba da fada, yana gamawa kuma ya fice ya barta. Gaba daya zuciyarta tayi kunci
saboda a lokacin yaran su uku ne a tsaye take wuni, in ta kwanta da daddare kuma haka zata dinga yi
tana tashi ta sa su fitsari, su sha ruwa ko ta gyara musu kwanciya sannan kuma ga bukatarsa shima, don
haka bacci baya isarta haka za ta wuni ta kwana da ciwon kai. Don haka yana fita itama ta shirya yaran
suka nufi gida, sai da suka je Baffanta ya sa ta a gaba da nasiha Inna tana tayashi sannan ta sami
natsuwa. Inna ta karbar mata yaran tace ta kwanta a dakinta tayi baccin. Baffanta kuma ya kirawo
Abban yace masa in ya tashi kasuwa ya biyo ya tafi da ita. A kan hanyarsu ta komawa ne ya dube ta yace
“Ni kika yiwa yaji don rashin kunya ko.”

Tayi murmushi ta kawar da kai tace

“Ba yaji nayi ba kuma ba zan taba yin yaji ba. In dai ka ga na bar gidanka toh kai kace na tafi ko kuma ka
nuna hakan idan ko na tafi toh ba zan dawo ba. In ba haka ba aure ni da kai mutu ka raba.”

Wannan kalamin shi ya fado mata taji a ranta bata kaunar ta sake dawowa gidanshi, bata dai ji ya furta
mata saki ba amma ko a kotu sai ya saketa. Ta gaji da wannan auren da ake tauyeta a cikinshi. Toh ai ma
idan taje gidan Yaya Shafa ta san kafin a sha ruwa Yaya shafan za ta kirawo shi ko ta gayawa Yaya
Munzali ya kirawo shi su saka ta a gaba ta koma, ko kuma ma suce ita ke da laifi sai ta bashi hakuri,
musamman ma Yaya Munzali. Don haka sai ta tsallaka titi ta ta koma baya tana neman tasi, sai da ta
tsayar da guda uku sannan a ta hudun ta sami wanda zai kaita inda za ta. Tana zama a bayan tasin
wayarta tayi kara alamar sako ya shigo. Ta zaro wayar ta duba taga sako ne daga MTN, bayan ta duba sai
kawai ta danne wayar ta kashe ta gaba daya domin batan son yin magana da kowa a halin yanzu kuma
bata son kowa ya san inda za ta tafi. Gaba daya duniyar ta yi mata kunci, sannan ga azumi. So take kawai
ta tafi inda babu wanda zai dameta har sai ta saita tunaninta.
EPISODE 19



Haka kawai ya tsinci kanshi yana ta faman duba wayarshi kamar wanda yake sa ran wani zai kirawo shi,
ba kiran kowa yake tsammani ba na Yaya Shafa ne ko Yaya Munzali. Har aka tashi daga kasuwa babu
wanda ya kirawo shi. Suna tare da Madu amma bai san me yake faruwa ba ya dai kula Abban bashi
natsuwa. Wajen karfe biyar da rabi suka baro kasuwar suka nufi gidan. Abban da ya saba da hira idan
suna hanya shi da Madu yau sai ga shi kwata kwata ya kasa cewa komai. Haka suka ci gaba da tafiya
babu mai cewa komai.




Sai wajen karfe biyar da rabi Salim ya dawo daga makaranta, tun kafin ya ajiye jakarsa suka taso suka
nufo shi.

“Ina Mommy?” Ya tambaya kafin su karaso.

Suka yi cirko-cirko suna kallon juna, shima ya bi su da kallo. Khalifa yace

“Ta tafi.”

“Ta tafi ina?”

Auta ya matso jikinshi ya fashe da kuka yana fadin

“Abba ya koreta, ya ce ta fice masa daga gida.”

Ya razana ya ‘daga Auta daga jikinshi yace

“Ban gane ya koreta ba.”

Khalifa ya share kwalla yace

“Ya ce ta fice masa daga gida shine ta tafi, kuma bamu san inda ta tafi ba.”

“Subhanallahi! Me tayi masa?”

Khalifa ne ya bashi labarin abinda ya faru domin shi auta kuka ya riga ya ci karfinshi. Bayan ya gama jin
bayaninsu ya ja kujerar dining ya zauna da yake suna kusa da dinning din. Ya zaro wayarshi ya kirawo
Ahmad ya gaya masa abinda ya faru. A tsaye yake a kofar bankinsu yana jiran tasi sai da ya ji kamar zai
fadi, da kyar ya rike wayar da take barazanar faduwa daga hannunsa yace

“Kuma kun tabbatar ba ta cikin gidan.”

Salim yace

“Eh mana, ga mu a cikin gidan Kuma na ma kirawo wayarta a kashe.”

“Toh bari na karaso gidan, ina bakin titi yanzu zan zo.”

Suka ajiye wayar.
Salima ya sake daga wayar yace

“Bari na kirawo Ya Baba.”

Khalifa ya ce

“Ka bari Ya Ahmad din ya zo tukunna.”

Sai wajen shida da rabi sannan Abba ya iso gidan shi da Madu, haka kawai gabanshi yake faduwa tunda
suka nufo gidan. Madu na tsayar da mota Abban ya fito, kafin Madun ya shigo ya karasa falon Mommy.
Yanda ya gansu a falon cirko-cirko sai suka bashi tausayi, babu wanda ya amsa sallamarshi balle ayi masa
sannu da zuwa. Jikinshi babu kwari ya juya ya fito suka hadu da Madu a bakin kofa ya shigo shi kuma
Abban ya fice. Yana shiga ya dubesu yace

“Ku kuma lafiyarku, ina Mommy?”

Auta ya sake fashewa da kuka yace

“Abba ya ce ta fice masa daga gida ta tafi.”

Kafin ya basu amsa Ahmad ya shigo, Madu ya dube shi yana fadin

“Wai da gaske suke ko wasa ne?”

“Nima haka suka ce min, ba kuna tare ba a kasuwa dawowa yayi ya baro ka ko waya yayiwo mata?”

“Wajen karfe biyu dai na ga ya fito daga kasuwar kuma wannan matar tashi ce ta kirawo shi, ina jin a
lokacin ne.”

Nan suka sake bawa Madu da Ahmad labari. Suka hadu suka zauna a dining table din, kafin wani lokaci
suka ji kiram magriba. Salim ne ya tashi ya debo musu pure water a fridge suka karya.

Shi kuwa Abba yana fita daga nan ya huce wajen Saudah, yana shiga babu kowa a falon sai dai ya jiyo
motsin yaran a dakinta don haka ya san suna ciki dukansu. Kawai sai ya huce dakinsa, yana shiga ya
zauna a kan gado ya zuba fuskarshi a tafukan hannayenshi. Gaba daya kwakwalwarshi ta daina aiki ya
kasa tunani don haka ya ma hakura. Yana nan a zaune sai ji yayi ana kiran Sallah, firgigit ya mike ya fito
don ya sami ruwa ya sha. Tun kafin ya karasa dining table din ya hango babu komai a kai, ya jijiga kai
kawai ya huce kicin ya dauko ruwan sanyi a fridge ya fito ya zauna a dining table din ya karya. Bayan ya
sha ruwan sai kuma ya koma dakinshi inda ya dauro alwala ya sako takalmi don tafiya masallaci, har ya
fito babu kowa a falon don haka ya huce dakin ya tura kofar ya shiga. Tana zaune a gefen gadon da ledar
pure water a hannunta, su kuma yaran suna wasansu a tsakar dakin. Ta dago fuskarta ta dube shi bayan
da ya shiga cikin dakin, fuskartata duk a jagule take da alamar hawaye ga idon yayi ja amma da yake ba
wannan ne ya kawo shi ba sai yace

“Kin san bata nan sai ki zo ki tanadar min abinci kafin na dawo daga masallaci.”

Da kyar ta bude bakinta ta bashi amsa saboda yanda kanta yake wani mugun ciwo, ya juya ya fice yara
suna yi masa a dawo lafiya. Ya saba idan zai tafi masallaci ya yi musu magana su tafi tare, amma yau sai
ya kasa, ba tare da ya kalli kofar ba ya fice shi kadai ya tafi. Suma duka suna jin motsin fitarsa binshi ne
ba za suyi ba don haka yana ficewa suma suka fito suka tafi masallacin.
Da kyar Saudah ta mike daga kan gadon ta dauko Panadol a kan mudubinta ta balli guda biyu ta sha da
ragowar ruwan dake hannunta, ta ajjiye ledar ruwan a kan mudubin ta shige bandaki. Ta san ya kamata
ace murna takeyi saboda ko babu komai an kori kishiyarta, amma ta kasa jin komai a ranta. Bakin cikin
yanda ta rasa jarrabawarta ya hanata walwala kwata kwata. Ta ja tsaki a fili sannan ta tuna a bandaki
take. Ta san ba komai bane ya hana Rabi ta rike mata yaran nan sai tsabar bakin ciki da take yi mata
saboda ita bata yi karatu ba don haka ta kara yiwa kanta alkawarin gama wannan karatun ta karbi
certificate dinta a hannu. Bayan ta idar da Sallah ta dauki Baffa Karami ta goya shi sannan ta ja sauran
suka fice daga dakin. Falo ta ajiye su Nawwara ta kunna musu cartoon sanna ta huce kichin. Ta fi minti
uku a tsakiyar kichin din tana tunanin me ma za ta dafa masa, lallai dole ta dage wajen girkin nan tunda
yanzu ita kadai ce a gidan, da gida da miji duka nata ne. Ko da dai ta san bai yi saki ba don haka ta san
yanda yake ji da wannan matar zai lallaba ya dawo da ita, amma tana so ya barta ta kwana biyu ta ‘dan
gwada zawarci ta ji ko babu komai yanda ta ja mata asarar jarrabawa toh ita ma ta raunana igiyar
aurenta. Da yake akwai burodinshi na alkama sai kawai ta soya kwai, ta dauko ragowar miya a fridge ta
dumama ta dora macaroni. Yana dawowa ta hada masa shayi ya sha da burodi da kwai, ta juye macaroni
a flask saboda cin an jima. Burodin ta dauko itama ta hada shayi sai dai da yake ita da yara ne ita sai ta
zauna a kasa suna ci da yara, har suka gama cin abincin babu wanda yace da kowa komai.

Su kuwa su Auta ana sallame sallah suka yi sauri suka fito daga masallaci suka kamo hanya, Ahmad ne
kawai ya jira Abban. Tare suka taho daga masallacin har

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login