Showing 12001 words to 15000 words out of 196754 words

Chapter 5 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15349

yayinda shi kuma auta ya zaro ido tare da dafe kirji.
Ta na Bude baki za ta bashi amsa kwallar da take boyewa ta kwace.

“Subhanallah.”

Ta fada a fili.

Ta rungumo Khalifa ta kamo hannun auta suka fito falon suka zauna

“Kirawo min Madu da Salim, suna daki suna game.”

Ta ce da auta.

Da yake Baba karami da Ahmad mai binsa basu dawo daga makaranta ba.

Bayan sun fito suma suka zauna suka kewaye ta sukayi tsuru-tsuru ganin Mommy tana kwalla. Ta fara
binsu da kallo, hawayenta na kara yawa domin ta ma rasa ta inda za ta fara wannan bayani. Ta rike hannun
Khalifa ta ce
“Mutum baya kashe mutum, Allah ne kadai yake kashe bawa. Ka tuna lokacin da Anti Bahijja ta haihu babu
rai, har ka ce min da ku aka je aka binne yaron?”

Duk suka daga kai alamar eh.

“Toh wa ya kashe mata yaron da ta Haifa babu rai?”

Salim ne ya bata amsa

“Mommy ba fa kashe shi aka yi ba, haka Allah ya kaddara, dama ai ana yi ba wai sabon abu bane.”

Ta goge ragowar hawayen da ke fuskarta sannan ta cigaba

“Yauwa. Toh irin abinda ya faru da matar babanku kenan. Ni ban isa na kashe kowa ba, kuma ban san
yanda aka yi ba, amma ita da yan’uwanta suna zargin wai ni na yi musu asiri na kashe yaron. Allah ya sani
kuma ku ma kun sani ba na bin bokaye, amma suka kirikiri wannan sharrin suka ce nice. Ban ma san sun
gama bazawa a unguwa ba sai yanzu da Khalifa ya jiyo a islamiyya. Ban yi niyyar gaya muku ba amma
tunda an fara gaya muku dole na yi muku wannan bayani. Allah shine shaida ta kuma ku ne shaidata, Allah
nake roka ya bayyana gaskiya.”

“Mommy Inna Sa’a ce ko?”

Ahmad ya tambaya.

Kafin ta bada amsa Auta ya riga ta

“Harda wannan tsohuwar ma me kama da mayu da muka je tana miki kallon raini.”

“Ban San waye ba, amma Allah ya sani, kuma ban ce ku nemi fada da kowa ba ku bari Allah zai warware.
Kun ji ko. Gaya muku nayi saboda tunda an riga an fara gaya muku a unguwa toh gara nayi muku bayani
ku sami natsuwa. Ban yi ba kuma da izinin Allah ba zan yi ba har abada.”

Nan dai ta gama kwantar musu da hankali tare da nuna musu abun ba na fada bane su kyale kowa su
tayata addu’a.

“Daddyn ma shi ya sa ya daina kula ki ko Mommy?”

Madu ya tambaya da yaga tana shirin tashi ta koma kichin.

“Wannan kuma ba maganarka ba ce CID officer.”

Ta bashi amsa ta fice ta barsu.

Duk da bata ji dadi ba da maganar ta fita har aka fara tare yaranta ana tambayarsu, amma ta sami natsuwa
da tayi musu bayani kuma ta gaya musu su kara dagewa da addu’a.

Wasa wasa abu har ya dauki wata biyu an shiga na uku. A makontansu da suke mutuncin ma mutum biyu
sai da suka tambayeta, domin a fadarasu duk inda yan unguwar suka hadu toh gulmarta ake. Dama kuma
wasu na jin haushin ta wai bata kula mutane, kuma haka Allah yayi ta bata son shige-shige da surutu. Haka
har kowa ya gaji aka bar zance.
Ko da ta je ta gayawa Yaya Shafa ma kara kwantar mata da hankali ta yi. Ta che mata ta kara dagewa ta
samu ta shirya da mijinta a hankali ta wanke kanta, kada ta yi fushi saboda ba’a fushi da miji. Haka ta dawo
tayi ta neman shiri, duk abinda ta san yana so sai ta kara dagewa a kai Kuma tana yi tana addua. Haka za
ta yi girki ya ki ci, in take dakinshi kuma ya ce me ya sa za ta sa shi a gaba, haka za ta huce dakinta ta kwana
tana kuka. Duk hanyar da ta biyo sai ya kwace, da ya gane tana neman shiri ma sai ya kara sabon wulakanci.
Tun tana sharewa har ta gaji itama ta fita harkarshi, hawayenta ya bushe damuwar ma duk ta daina.
Hidimar gabanta kawai takeyi tana kara addu’a. Abu daya ne yake damunta rashin abun yi, karatu dama
iya sakandare tayi ya aureta, don haka babu maganar aiki Kuma babu sana’a. Amma da yake mace ce mai
son karatu sai ta zama karatu ne yake debe mata kewa.

Haka dai ta cigaba da hakuri.

……….

Wajen amarya kuwa rayuwarta take yi, tunda yanzu ta samu komai a wajenta Abban Khalifa yake yi. Zuwa
yanzu mafi yawancin kayansa ma da na sawa da na amfani ya dawo da su dakinsa na bangarenta. Duk da
dai har yanzu yana rabon kwana da Rabi, amma hankalinshi duk yana kan amaryarsa.

Da taimakon Yaya Sa’a sun gamsar da shi cewa shi kanshi wasu abubuwan asiri Rabi take masa, shi yasa
take yawan yi masa zobo da shayi mai ganye kala kala. Don haka shi yanzu Rabi ta sane masa, tsoron
sharrinta kawai ya ke yi. Duk da wasu lokutan yana shakkun yanda za ayi Rabi ta cuce shi, amma ya san
dan Adam yana canzawa.Da wannan damar amarya ta yi amfani ta tuna masa alkawarin da yayi mata na
zai sa ta a jami’a ta ci gaba da karatu.Matsalar da aka samu SSCE dinta ba tayi kyau ba, don haka ya ce
yanzu ana farkon zangon karatu ta bashi lokaci zuwa karshen zango za a samar mata makaranta ta sake
SSCE din.Nan da nan ta cigaba da shirye shiryenta da Kuma tanadin wadda za ta zauna mata jarrabawa.

Haka kawai ta tsiri wata sara, sai yamma ta yi sai ta kunna rediyo ta sa wakar gwanja “Allah ya aika
munafikinmu karshen nesa….” Ta kure volume sosai da yake ba fili tsakanin su kamar a falon Rabi aka
kunna. Haka tayi ta danne zuciyarta tana bawa yara hakuri. Haka dai rayuwa ta cigaba har kawo wannan
lokacin.

…..

Da yamma ya dawo dai dai lokacin Rabi ta gama gyaran dakinshi, ta saka turaren wuta ta janyo kofar. Ya
shigo Baba karami yana biye da shi ya riko masa jakarsa da mukullin mota. Yana Bude dakin ragowar
hayakin yana yawo a dakin ita kuma tana kawo kai

“sannu da zuwa.”

“Wannan hayakin na meye, bana so, a daina sa min shi a daki.”

Ya fada ba tare da ya amsa ba. Baba karami ya ajiyye masa jakarsa ya fice.

“Turaren wuta ne fa da na saba sakawa.”

Ta bashi amsa.

“Toh Kada a sake saka min shi a gida.”

“Toh.”
Ya huce ta ya shiga bandaki, nan ta tashi jiki babu kwari ta fice. Tun abubuwa suna saka ta kuka har
hawayenta sun bushe, don haka ta ci gaba da harkokinta.

………….

“Mommy idan an idar da sallar isha’I za mu je unguwa ni da Buhari.”

Baba karami ya gaya mata lokacin da zai tafi masallaci.

“Toh Baba, amma don Allah kada a huce tara da rabi ba’a dawo ba.”

Ta bashi amsa.

Ana idar da sallah kuwa ya nemi achaba ya haye sai gidan Baffa Hassan. Sai da suka gaisa sannan ya yiwa
Baffa Hassan bayanin abinda ya kawo shi. Baffa Hassan da Baba Yalwa duk sun sha mamaki. Sun bashi baki
kuma Baffa ya yi alkawarin lallai zai yi wa Abban nasu magana.

Kafin Baffa ya sami damar kiran Abban jinya ta kwantar da shi, hawan jininshi ya tashi har sai da aka
kwantar da shi a asibiti.Bayan ya dan farfado Abban Khalifa na gefensa da shi da Baba Yalwa, ya tashi ya
zauna ya jingina da kan gadon.

“Sannu Baffa.”

“Yauwa Alhajin Allah sannu da kokari. Ya iyalan naka?”

“Lafiya kalau suke Baffa.”

“Toh ma Sha Allah.”

Ya dan yi gyaran murya sannan ya ci gaba.

“Game da iyali Alhajin Allah. Duk lokacin da ka zargi wani abu game da iyalinka, toh ka yi bincike kafin ka
yanke hukunci. Ina sane da abubuwan da suke faruwa a gidan naka.”

Ya Bude baki zai yi magana ya daga mishi hannu alamar ya tsaya, sannan ya ci gaba.

“Ka zurfafa bincike, kuma kayi kokarin yin adalci. Mutumin da ka dade da shi ya kamata a ce ka san abinda
zai iya sai idan ba ka mai da hankali ba. Ina goyon bayan adalci ko a kan waye, amma uwargidanka da tana
bin bokaye da yanzu ta kassara ka, kai hatta mu ma da tuni ta raba mu da kai. Usmanu idan matar mutum
tana yi masa asiri toh wannan mutumin ba zai taba samun natsuwa ba, kuma duk wani makiyin shi sai yayi
nasara a kansa saboda mafi kusancin mutane a gareshi ta bude wata rufaffiyar kofa. A ce kana zaune da
mace shekaru 25 amma bata taba yin wani abu nai kama da wannan ba sai yanzu, matar da aka yiwa
kishiya ba tare da ta tada wata fitina ba.

Anya kuwa? Ko da dai mutum yana canzawa toh a tsananta bincike kafin a yanke hukunci. Ka san mata
suna da yafiya amma fa ba su da mantuwa, idan wannan abun ya tabbata sharri ake mata toh lallai sai ya
taba alakarka da ita. Hakan ba zai maka dadi ba, domin hausawa sun ce ba’a bari a kwashe daidai.

Don haka a sake duba al’amarin nan. Ita Kuma Sa’a idan ka biye mata toh tsaf za ta rusa maka gida ita
kuma tana nata gidan.”

Ya Bude baki zai yi magana Baffa ya dakatar da shi
“Ba sai ka ce komai ba, amma ka sake bincikawa.”

Haka suka yi sallama Baffa yana ta

Kara yi mishi nasiha. Tukin kawai yake ya kasa yanke inda zai nufa. La’asar batayi ba don haka kasuwa ya
kamata ya koma don yana ma da baki bayan la’asar din. Kafin ya gama wasi wasi a ranshi sai ya tsinci kan
shi a hanyar gida.Maganganun da Baffa ya gaya masa suna ta yi masa yawo a zuciya har yayi parking a
bakin gate.

“Toh me ma zan yi a gidan?”

Ya tambayi kanshi tare da yin tsaki.

Ya fito ya tura gate din ya shiga gidan, Bala megadi yana ta baccinsa a kan benci.Yana shiga gate din ya
dauke hanya ya yi bayan gidan. Akwai wani waje a bayan falon amarya da Bala ya ce masa ruwa yana
tsattsafowa a jikin bango har ya fara kwanciya, yana tunanin famfon kitchen ne ko na dining area ya fashe
a cikin bango; don haka nan ya nufa don ya duba in ya koma kasuwar sai ya turo musu plumber ya zo ya
gyara.Wajen kusa da tagar falo ne don falon a jikin kitchen din yake. Tun kafin ya karasa wajen yake jin
maganganu, ya dauki muryar Kaka don haka ya zata hirarsu ce ta zumunci; yana tunanin sauri zai yi ya fice
kafin Amarya ta ce ya Kai kaka gida.Ya karasa wajen ya tsuguna don ya ga inda ruwan yake fitowa.

“Wannan za kiyi wanka da shi wanna kuma ki zuba masa a abinci na tsahon kwana uku.” Kaka ta ce.

“Tuwo miyar kuka za kiyi ko zobo, sun fi dauke wadannan abubuwan.”

Yaya Ummu ta ce.

“Ba fa wani abu bane wannan din rubutu ne da kika ganshi baki, na wankan ma ruwan zamzam ne fa aka
yi aikin a ciki, kike wani zumbura baki. Ni ba zan saka ki kiyi shirka ba, amma kina bukatar kariya. Kuma
wannan aikin malam sai da ya rantse ya ce in dai kika bi ka’idarsa toh sai yanda kika yi a gidan nan. Babu
wata a gabanki babu wata a bayanki.”

Aka dan yi shiru, sannan Kaka ta ci gaba.

“Wannan kuma ki barbada a inda kika san tana bi, so ake lallai ko da sau daya ne ta bi ta kai ko ta tsallake,
shi ma kiyi haka kwana uku. In Sha Allah komai sai yanda kika ce za ayi a gidan nan. Amma ace kamarki
kina auren mutum da anyi magana ya ce Rabi ta ce… Rabi ta yi…”

“Ah toh.”

In ji Yaya Ummu.

“Toh Kaka ni da kin barni na yi ma wankan kadai, tunda ni za a tsare. In ya so ai ko ta yi wani abu ba zai
same ni ba.”

Amarya ta fada cikin yanayi na mita.

“Lallai ma yarinyar nan. Kina kallo dai kishiya ce ta fitar dani daga gidana, ni zuwa tai ma ta same ni amma
sai da ta yi waje dani. Ana kokarin a kafa ki kina wani korafi, za ki gane baki da wayo.”

Yaya Ummu ta fada.
“Ke rabu da ita, dolenta sai ta yi wannan abun duka, Wallahi idan kuma ba kiyi ba in zare hannuna daga
lamarinki. Dama uwarku ce ta shiga damuwa yanayin zama, shi yasa ta sa nake karbo taimakon amma kina
so ki sa kwabar mu tayi ruwa.” Inji Kaka.

Suna kawowa nan ya tashi jikinshi babu kwari ya fice daga wajen. Haka ya fita babu wanda ya san ya dawo.
Ya shiga mota ya zauna turus, ya kafa kanshi da sitiyari. Zantukan Baffa suka dawo masa. Da kyar ya samu
ya tashi motar don baya son ma wani ya san ya dawo gidan.Yana tuki yana tunani.

Menene ma’anar abinda ya ji? Wato dama nan ne inda ake masa barbade a abinci? Ya ma aka yi ya yarda
Rabi za ta iya yin wani asiri? Ko dama an gama mallake shi an batar masa da tunani? Toh maganin me aka
ce a barbada inda Rabi za ta tsallaka? Kada fa ya je kafin ya dawo sun kashe ta?

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.”

Ya fada a fili.

Nan da nan gumi ya rufe shi, ya cire hularsa ya ajiye a kan cinyarsa. Ya lalubo wayarsa ya buga kira.

“Hello, Baba karami. Kana Ina ne?”

Ya tambaya a kagauce.

“Ina gida Abba, yanzu na shigo da makaranta.”

“Ina Mommynku?”

“Yanzu ta shiga daki amsa waya takeyi.”

“Toh shikenan, ka zauna a gidan kada ka fita har sai na dawo, kannenka ma in sun dawo kada wanda ya
sake fita sai na dawo.”

Ya ajiye waya.Yana fatan duk abinda zai faru yaran nan ba za su bari a cutar da uwarsu ba. A daddafe ya
sallami bakinsa a kasuwa, kafin magriba ya dawo gidan. Duka yaran suka fito suka yi masa sannu da zuwa.
Ya dubi auta ya ce

“Ina mommynka?”

“Tana falo.”

Ya huce falon suka bishi a baya.

Ba ita ce da girki ba Kuma yanzu har ta saba idan ba ita ce da kwana ba baya shiga wajenta kwata kwata,
don haka bata sa rai zai shigo ba.Sai bayan ta amsa sallamar shi sannan ta gane muryarshi. Ta juyo ta kalle
shi, murya kasa kasa ta ce

“Sannu da zuwa.”

Ya amsa shi kansa a yanayi na dar-dar.

Ta tashi da nufin ta shige daki ya ce

“Komai lafiya dai ko?”

Ta ce
“Lafiya Alhamdulillah.”

Yayi shiru kuma don haka ta huce daki ta barshi tsaye shi da yaransa.

Ya huce dakinsa ya ajiye kayansa, yara kansu suna ta mamaki. Ya fito ya huce wajen amarya. A kichin ya
same ta tana dafa abincin dare.

“Sannu da zuwa. Yau da wuri haka.”

Ta fada bayan ta amsa sallamarsa.

“Yauwa. Mun tashi da wuri yau.”

Ya shige dakinshi ya barta a kicin din. Nan da nan ta sauke tuwon ta da miyar kuka. Duk da bata son yin
amfani da kayan da kaka ta kawo mata, amma haka ta daure ta juye na wankan a ruwan wankanta, da
yake ma kamar ruwa yake abun bai dameta sosai ba. Bata son amfani da kayan toh amma yanda aka ce
mata za ta sami kanshi tana son hakan, don yanzu har wasu muzurai ya ke son ya fara yi mata ita da da
yake zuwa kofar gidansu yana yi mata yar murya. Sai da aka yi sallar isha’I sannan ta gabatar masa da
abincin daren. Ta fara zuba masa a faranti kenan ya dakatar da ita, ya ce

“Bar abincin ma bari na je wajen Bala me gadi na dawo.”

Kafin ta ce wani abu ya fice daga falon. Ta rufe abincin tana jiranshi ya dawo ya ci. Ita kuma tayi amfani da
wannan damar ta zuba nata tuwon ta ci. Ya fito yana tunani: Maganganun da yaji sun tabbata, tunda ga
shi ta yi masa tuwo miyar kuka. Lallai dole ya dau mataki. Har ya nufi wajen Rabi sai kuma ya tuna me zai
ce mata? Yanzu ma bai ga alamar za ta saurare shi ba, shima kuma bai san ta ina zai fara ba. Don haka sai
ya juya ya fice daga gidan. Akwai wajen cin abinci nan kusa da su, ya karasa ya siyo kaza gasasshiya guda
biyu. Yana shiga ta karbi ledar hannunsa ta ajiye a kan tebur

“Na ga ka siyo kaza? Ba za ka ci tuwon ba?.”

“Uhm! Wallahi Ina fita kamshi kazar nan ya bugi hanci na, don haka na karats na siyo. Dauko plate mu ci.”

Ta tashi ta kawo plate din ta jiye masa. Ya dauka ya fara juye kazar. Sai da ta bata rai ta zumburo baki
sannan ta fara

“Yanzu wahalar banza na sha kenan na yi tuwon, da ka je ka siyo kaza?.”

Ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa

“A’a, a rufe shi ma ci dumame ko.”

Ta kara zumburo baki ta muskuta

“Ni bana ci don na riga na ci tuwo na da ka fita, saboda Ina jin yunwa.”

Kafin ta karasa magana ya mika hannunshi ya bude duka biyun flasks din.

“A’a baki ci ba, gashi nan ba’a diba ba.”

“Ai a kichin na debo wanda ya riga ya sha iska, ga ma plate din da na ci nan a gefenka.”
Ya juya ya kalli inda ta nuna ya ga plate din nata.Ya dan yi jim kamar mai saurare yana tunanin ta inda zai
fara domin rashin diban wannan miyar ta ci ya kara tabbatar masa da cewa tabbas an zuba masa maganin.

Sai da ya cinye guda a cikin kajin sannan ya dago ya dube ta. Ta janyo Kofi za ta zuba masa ruwa yayinda
ya mike ya nufi kichin don ya wanke hannu. Bayan ya wanke hannun Sai kawai ya tara hannunshi a fanfo
ya sha ruwan. Ya fito ya zauna, yana ta nazarin ta inda zai fara don dole ne a fito da wadannan tarkacen a
zubar in ba haka ba sai dai ta bar masa gidan.

“Yau su Kaka ne suka zo ko?”

Duk da bata sa rai zai yi mata wannan tambayar ba amma sai ta dake ta bashi amsa

“Eh, sun zo min zumunci ita da Ya Ummu.”

“Allah sarki.”

Suka dan yi jim.

“kulle-kullen da suka baki ki sassaka mana a abinci kuma na menene?”

Ya tambaya yana tsattsare ta da Ido.

Gabanta ya fadi, gumi ya karyo mata. Ta ce

“Wanne kulle-kulle Kuma, wane irin zance kake yi ne?”

Ta fada tare da dafe kirji. Sai wani kifta ido take tana waige-waige.

“Kulle-kulle mana. Wannan ki zuba min a tuwo miyar kuka, wannan ki barbadawa Rabi, wani kuma kiyi
wanka da na turawa da asuba?.”

Kafin ta ce wani abu hawaye ya wanke mata fuska, tana sharewa tana bayani

“Banyi amfani da komai ba Allah, ni ma ba so nake ba saboda na san babu kyau, jira nake yi gari ya waye
sai na sa a kona ko a zubar. Da ma…”

“Tashi ki dauko min su gaba daya.”

Ya katse ta kafin ta karasa.

Tana rawar jiki ta je dakin baki ta kwaso masa. Biyu a kulle a farar leda, yana

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login