Showing 174001 words to 177000 words out of 196754 words

Chapter 59 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15403

shiru ne muka biyo sawu, Saude tana gida tun kafin sallah don ka ga ni ba a ma sanar da ni
tana gidan ba sai bayan sallah.’

Kafin Abban yace wani abu Baba Sule yace

‘I, ka san Alhaji sha’anin mata sai hakuri musamman yaro.’

Yayi gyaran murya yace

‘Hakane, ni kaina ina baku hakuri saboda rashin zuwan nawa. Amma abunda ya faru shine na barta a
gida na fita kasuwa kawai na dawo na tarar ta tafi ba tare da ta sanar da ni tafiyar ba ko kuma
takamaiman abinda aka yi mata, sai takarda da ta rubuta ta ajiye min wai ta tafi gida. To shi yasa nace ba
zan nemeta ba har sai ta dawo da kanta.’

Baba Sule yace

‘Ikon Allah, ai kuwa ka ga ta yi wauta da yarinta.’

‘Kwarai kuwa.’

Abban yace

‘To kuma ni babu abinda tayi min don haka ko yau ta shirya zata iya dawowa dakinta, bani da matsala da
ita.’

Baba Yahaya yace

‘To Alhamdulillah tunda ma haka ne, in sha Allahu idan bata dawo yau din ba kuwa gobe zata dawyac

Abba yace

‘To ma sha Allahu.’

Suka yi shiru na dan lokaci, Baba Sule yayi gyaran murya yace

‘Sai kuma maganar sammaci da aka kai mata, ashe haka ta zo tayiwa abokiyar zamanta wannan babban
kazafi.’

Abba ya jijjiga kai cikin yanayi na nuna rashin jin dadi yace
‘Hm! Eh, ashe ma har sun kai kotun? Matsaloli ne wallahi na wauta da yarinta ta fadi zance kuma yanzu
yana yawo a unguwa ana nunata, ko da yake ba wannan ne karo na farko da tayi mata kazafin ba shi
yasa itama tace bazata yarda ba. To idan na saka baki zai zama kamar na goyi bayan Sauden don wancan
karon da tayi mata kazafin kisan kai ni na hanata magana.’

Cikin mamaki Baba Yahaya yace

‘Kisan kai kuma?’

‘I, kisan kai mana. Cewa tayi itace tayi mata asiri ta kashe mata yaro a ciki ta haife shi babu rai, haka aka
dinga yada zancen a unguwarnan wai ta kashe yaro tun yana ciki.’

Baba Sule yace

‘Ikon Allah, wai me yake damun Saude ne? Ta san kuwa girman kazafin kisa da zina.’

Baba Yahaya yace

‘Rashin hankali da rashin sanin dokokin Allah.’

Ya dubi Abban yace

‘To don Allah Alhaji ayi hakuri, ina baka hakuri saboda kai din ma tayi maka ba dai-dai ba. Kuma ka duba
al’amarin nan saboda Allah ba saboda mu ba ka bawa ita babar su Muhammadun hakuri, don Allah suyi
hakuri da zuwa kotun nan in ya so ita Sauden da kanta za ta zo ta bata hakuri. Don Allah ayi hakuri, kuma
ni da kaina nayi maka alkawarin bazata sake rashin hankali irin wannan ba.’

‘Uhm, to Babu laifi.’

Baba Sule yace

‘Ai kayi mata magana ma don Allah mu bata hakuri da kanmu kafin Sauden ta zo, ai an yi mata ba dai-dai
ba don haka dole a bata hakuri ‘

Bai so suka ce ya kirawo Mommy ba don baya so taga kamar shi yake so ya hanata ta kwaci hakkinta,
gashi sun riga sun ganta tunda itace ta kawo musu ruwa. Haka ya tashi ya bude kofar dakin ya shiga. A
kwance take ta rufe kafarta da zanin gadon har bacci ya fara daukarta

‘Bacci kikeyi ne?’

Ta juyo tana muttsike ido

‘Kwanciyata kenan har bacci ya dauke ni.’

Ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ita kuma ta tashi zaune.

‘Iyayen Saudah ne suka zo.’

Tayi murmushi

‘Sun kyauta ai gara ku san abin yi, ta tafi gida kai kuma ka barta babu wani bayani.’

‘To ai na gaya miki ba ni nace ta tafi, yanzun ma kuma haka na gaya musu. Duk lokacin da ta shirya ta
dawo da kanta ni babu inda zani.’
‘Uhm…’

‘Ki zo suna son magana dake.’

Ya katseta kafin ta karasa. Ta kalle shi da alamar tambaya a fuskarta, ya kauda kansa yana fadin

‘Suna jiranki ki taso muje.’

Ya mike tsaye ya nufi kofa ita kuma ta sauko daga kan gadon ta dauki hijabi a kan dadduma ta saka ta
biyo bayanshi. Bayan ta zauna ta sake gaishe su bayan sun amsa Baba Yahaya yayi gyaran murya yace

‘Zuwa muka yi daman mu roki arziki a wajenki Babar Muhammadu, wallahi duk munji rashin hankali da
tozarci irin wanda Saude take yi miki. Amma don Allah kiyi hakuri, za tazo da kanta in sha Allahu ta baki
hakuri. Ni da kaina kuma nayi miki alkawarin haka bazata sake faruwa ba, don Allah ki yi hakuri ki janye
karar a samu ayi sulhu a gida.’

Ta dago kai ta kalleshi kawai ta mayar da kanta ta sunkuyar ba tare da tace komai ba, Baba Sule yace

‘I don Allah ki yi hakuri, in sha Allah itama bazata sake yi miki irin wannan ba don ba karamin tashin
hankali take ciki ba sakamakon wannan sammaci da aka kai mata.’

Ta bude baki da kyar tace

‘Um, Allah ya kyauta.’

‘Gobe zata dawo dakinta in s3ha Allahu zata zo da kanta ta baki hakuri.’

Baba Yahaya ya dubi Abba yace

‘Idan ma ta kama Alhaji a tasa ta a gaba duk inda taje ta fada ta koma tace musu karya takeyi, wannan
shine zai sa ta san girman abun da ta aikata.’

‘In Sha Allahu.’

Abban yace

‘Toh bari mu tashi Alhaji mu barka ka tafi kasuwarka.’

Suka mike tare da Abban suka yi musabiha suna sake bawa Mommy hakuri tare da jadadda masa lallai
gobe Saude zata dawo dakinta. Ya bi bayansu yayi musu rakiya kofar gida, bayan ya sallamesu ya dawo
ciki. Bata falon don haka ya wuce ya bita dakin. A kwance ya sameta ya zauna a gabanta ya dubeta yace

‘Har kin koma baccin ne.’

‘A’a sai dai niyya.’

Suka yi shiru na dan lokaci kowa da abin da yake tunani. Baya son ya bata hakuri don ya fahimci bata son
ya dinga bata hakuri idan an cuceta, sai dai da yake shima din bayan an shigar da karar lokacin zuciyarsa
ta huce yaga rashin dacewar kai karar. Kawai dai ya rasa yanda zai yi ta bata hakuri musamman da yake
Saudah din itama bata nuna zata bada hakurin ba don haka ya saka musu ido. Yace

‘Uhm, kin ji me suka ce ko? Gobe zata dawo.’

‘To Allah ya nuna mana ai dama nan ne gidanta.’
‘Yaushe ne zaman kotun naku.’

‘Talata me zuwa.’

Ya danyi shiru

‘Uhm to za ki janye din?’

‘A’a, ba zan janye ba.’

Ya kalleta da baki a bude don bai zaton zata ce haka ba, jim kadan ya rufe bakinsa yace

‘Uhm, bari dai ta dawo din mu gani.’

Ya mike tsaye tace

‘A dawo lafiya.’

Ya amsa ya fito ya rufe mata kofar. Ta bi bayanshi da harara tayi kwafa. Tuntuni ta fuskanci yana so yace
tayi hakuri ta janye karar kasawa yayi, kuma bazata janye ba. Ba zai yiwu ba a dinga cutarta yana bata
hakuri, yanzuu a unguwar nan tana fita ake fara nunata. Mutane da dama da take harka da su sun yi
mata zancen don har mamaki take yanda zancen yake yawo a gari; wai ita ta tafi yawon bariki. Ai ko ta
yafe komai bazata yafe wannan ba don haka babu gudu babu ja da baya. Ta juya ta gyara kwanciyarta
don ta cigaba da baccinta, haka tayi ta juyi ba tare da baccin ya dawo ba don haka sai tashi tayi kawai ta
dauko littafi ta fara karatu.




Tunda su Baba Yahaya suka dawo suka ce zata koma gobe take ta shiri, ta sa aka wanke musu kayansu
tsaf ta bi dare ta goge su. Suna ta kus-kus da Yaya Maryam tana sake jaddada mata yanda zata bi ta
gyara zaman aurenta. A daren Yaya Maryam ta sa aka kirawo yarinyar makotansu wadda take gyaran jiki
ta tambayeta idan zata iya shigowa bakwai na safe tayiwa Saudah gyaran jiki sharp-sharp, ta ce zata iya.
Daga baya kuma ta sa aka jika kanunfari ta dubi Saudan suna zaune su biyu a daki tace

‘Don ma bani da kudine da har kunshi zata yi miki, amma babu komai. Ga kankana can an siyo da
madara tunda babu lokacin da za mu nemi kayan gyara don haka da safe sai a hada da kanumfarin ki sha
ki tafi da sauran ki saka a fridge.’

Ta dubeta tace

‘Nagode Ya Maryam.’

‘Kiyi hakuri ki kwantar da kai ki zauna da mutanen gidan lafiya wallahi za ki ji dadi sosai.’

Ta yi kasa-kasa da murya ta dan matso kamar me rada tace

‘Kuma dole ki daina biyewa Yaya Ummu da Umman ma, ba wai za su cutar dake bane da niyya amma kin
san kowa da tunaninsa. Idan dai ba wata cutarwar ake miki a gidanki ba toh duk wata matsala ma ba sai
kin kawo musu ita ba, kiyi addu’a kiyi sadaka ki fuskanci matsalarki idan ba haka ba wataran za su kashe
miki aure.’
Ta jijjiga kai alamar to.

‘Yauwa, don Allah ki kula. Ki dinga yawan addua da azkar babu abinda Allah ba zai yi miki ba. Kinga idan
yaga ma kin kwantar da hankali ki da kin gama karatun sai ya barki ki fara aiki.’

Tayi murmushi tana jijjiga kai

‘Hakane.’

…………..

Kafin karfe tara an gama yiwa Saudah gyaran jiki tayi wanka ta shirya ta shirya yara, farin ciki take ji ko
kuma tsoron abinda zata je ta tarar bata sani ba amma ko abincin safe ma kasa ci tayi. Karfe tara saura
Baba Sule yazo da mota aka zuba kayanta, suka fito ita da Yaya Maryam wadda ita kadai Baba Sule ya
yarda ta rakata don yace ba rashin hankali za aje ayi ba. Ta sami Umma da Kaka suna zaune a tsakar gida
suna shan Koko da kosai ta tsuguna gabansu tace

‘Umma mun tafi.’

Kafin Umman ta amsa Kaka tace

‘To Saude kina ji dai uwarki ta hanani rakaki, nace mata kafar da sauki amma dai ta kafe. Idan na sami
mai kawoni na zo na duba ku da yaran. Ki gaida mijin naki kin ji.’

‘Toh Kaka.’

Umma tace

‘Ai ba haka nayi ba Kaka, za muje daga baya ni dake.’

Yaya Maryama ta dubi Yaya Ummu tace

‘Kema da kin shirya mun je wallahi ai komai ya wuce yanzu.’

Ta tabe baki tace

‘Um, rabani da zuwa inda ba a gayyata, ku dai kuje Allah ya bada zaman lafiya.’

Saudah ta karasa wajen Yaya Ummu wadda take zaune a tabarma ita da Najwa da Hafsa da Abdulhakim
suna cin abinci ta tsuguna a kusa da Yaya Ummu tace

‘Ya Ummu na gode, Allah ya bar zumunci sai munyi waya.’

‘Amin.’

Ta Sako su Nawwara a gaba suka fito inda suka tarar da Baba Sule a mota.

Sun yi sa’a suna zuwa Abban yana bakin gate da su Madu za su fita kasuwa, don haka a tsaye ya gaisa da
Baba Sule wanda ya ce shima sauri yake zai tafi office don haka yana jiye su ya wuce. Kamar yanda Baba
Sule ya umarcesu suna shiga gidan suka wuce wajen Mommy, tana kichin tana gyarawa ta jiyo
sallamarsu bayan Auta ya bude musu kofa sun shigo. Suna shiga da gudu Nawwara ta karasa ta rungume
Auta, bai so ya kulata ba amma ya kasa shareta ta sakeshi tace

‘Auta na dawo.’
Ya harareta ta sa hannu ta rufe bakinta tace

‘Yaya Auta Yaya Auta.’

Yasa hannu ya lakace mata hanci suka kyalkyale da dariya a tare. Ummi ta kamo hannunsa tace

‘Yaya ka dade baka bani alawa ba, Yaya Alifa (Khalifa) ya shanye ko?’

Yayi dariya yace

‘Bai shanye ba yanzu zan dauko miki ita shazumamun Abba.’

Mommy ta karaso daga kicin da murmushi a fuskarta, ta dauki Hanan kafin ta karaso tana musu sannu
da zuwa ta zauna. Suka sake gaisawa da Maryama.

Ta bude bakinta da kyar kamar wadda aka cusawo goro tana ta wani sunkuyar da kai kamar wadda take
gaban suruka

‘Mommy in wuni.’

Fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa

‘Lafiya kalau, ya su Nawwara da mutanen gidan?’

‘Lafiya kalau.’

Maryama tayi gyaran murya tace

‘To Mommy ga yaranki nan mundawo dasu na ga har sun shige wajen ‘yanuwansu, itama gata nan ta
dawo in sha Allah.’

‘Toh ma sha Allahu, Babu laifi.’

‘Uhm sannan kuma ta zo ne ta baki hakuri a kan abinda tayi miki. Ni yayarta ce na san baki san ni ba don
zuwana gidan nan ba yawa, ba a gari nake ba shi yasa ban san abubuwan dake faruwa don wallahi da ina
nan da tuni na taka mata birki. An kawo mata sammaci daga kotu, amma ina rokonki saboda girman
Allah kiyi hakuri. Tabbas na san ta cutar dake don wannan kazafin da ta yi miki ba karamin abu bane,
amma don Allah ki yi hakuri ki taimaka mana kuyi sulhu a gida.’

Ta harari Saudan, nan da nan kafin Mommy tace wani abu tace

‘Don Allah kiyi hakuri Mommy, wallahi rashin fahimtane Balarabace ta kulla wannan gulmar don Allah ki
janye karar.’

Da ace Saudance ita kadai take bata hakuri tabbas da sai ta ci mata mutunci, amma yanda Maryama ta
kwantar da kai ya sa ta ji nauyinta. Ta dubi Maryama tace

‘Uhm, case din yana hannun lawyer na don haka za muyi magana da shi tukunna, yanda muka yi za ku ji.’

Da raunannar murna Maryama ta kawar da kai tace

‘Kuma don Allah ba za mu iya magana da lawyer din ba shima mu bashi hakuri.’

‘A’a ki barshi sai munyi magana tukunna.’
Yanda ta tsuke fuska ta fadi zance bai bada damar a cigaba da zancen ba don haka Maryaman tace

‘Toh ni zan koma, don Allah bani lambar wayarki don mu dinga magana.’

Ta biya mata lambobin ta shigar a waya suka tashi suka fice. Tayi tsaki ta mike tsaye a fili tace

‘A daki mutum a hanashi kuka.’

Ta wuce ta koma kicin inda Auta yake cigaba da gyara mata.

……

Falon Saudah din suka wuce suka saka mukullin wajenta suka bude, wajen yayi matukar kura alamar ko
shi ma baya shiga. Ta samu waje ta zaunar da su Nawwara, Yaya Maryama ta ajiye jakarta a dining table
tana fadin

‘Tab, wannan ai karshenta sai an nemi taimakon mai aikin taki wajen yayi kura da yawa.’

Ta kama haba

‘Tab! Ai wallahi ba zan kuma shiga shirgin matar nan ba yanzu tana zuwa zata kwashi sabuwar gulma ta
shiga yayatawa.’

Tayi dariya tace

‘Kin fara hankali kenan, bari nayi sauri na tayaki mu gyara falon ko da kicin din don kin san nima yau za
mu wuce gidan su Baban Najwa.’

Nan da nan suka shiga aiki, kafin wani lokaci sun gyare kicin din da falon. Bayan ta wanke jikinta ta shirya
ta dauki mayafinta suna tsaye a bakin kofa suna sallama da Saudan. Ta dafa kafadarta tace

‘kina ji ko? Idan ya dawo shima ki bashi hakuri duk wani taurin kai ki sauke shi ba a yiwa miji. Ki saka shi
a gaba ya raka ki kije ki sake bata hakuri a gabansa ta hakane kin ga sai ya tabbatar kinyi nadama kin ga
ko umarni sai ya bata ta janye karar.’

‘To.’

Har zata fita tace

‘Kuma don Allah ki san maganganun da zaki dinga fada in ba haka ba sai ki saka kanki a fitnar da ta fi
wanna.’

Sukayi sallama a nan ta leka wajen Mommy ta sanar mata ita tafi sannan ta fice ta tafi.

…………….

Kamar yanda ya saba sai bayan sallar isha’I suka dawo daga kasuwa shi da Madu da Salim. Tun kafin
motar ta tsaya su Nawwara suka sheko da gudu suna masa oyoyo, yana fitowa daga motar ya taresu ya
dauki Hanan da Baffa Karami. Yanda suka ji dadin ganinsa shima haka yaji dadin ganinsu don baya son su
dade a gidan su Saudah, bai yarda da tarbiyyarta ba don haka baya jin ko da wani abu zai faru zai iya bar
mata wadannan yaran. Wajen Mommy ya nufa suka biyoshi gaba daya tare da su Salim, ya ajiye su a falo
ya wuce daki. Jimawa kadan suma suka fice suka koma wajen Ummansu.
Sai da ya gama kintsawa ya fito falon ya zauna don cin abinci a dining table, ta tashi daga nan inda suke
zaune ita da Auta da Khalifa suna kallo ta karasa dining table din don ta zuba masa abinci. Ta dauko plate
ta fara kokarin zuba masa tana fadin

‘Su Nawwara fa sun dawo, ka san abincin nan ma dafawa kawai nayi saboda ka riga ka fita ban sanar da
kai ba amma fa a wajen Saudah ya kamata ka ci abinci don yau itace da kwana.’

Ya kalleta da fara’a yana jijjiga kai

‘Wannan shine kora da hali ko? Saboda ta dawo sai koreni bazama ki bari a zauna a sake rabon kwanan
ba.’

‘Wane kwana da yake a rabe, ai da ka gama cin abincin ma ya kamata ka wuce can.’

Yayi dariya yace

‘To ai sai ki korani.’

Itama dariyar tayi ta ajiye masa abincin a gabansa tana fadin

‘Bari ka koshi kuwa kaga yanda ake kora megida wajen amarya.’

Ya ja abincinsa ya fara ci ita kuma ta zauna tana masa hira. Bayan ya gama cin abincin ta kwashe
kwanukan kafin ta fito daga kicin shi kuma ya koma ya zauna yana hira da su Auta. Da ta gama tazo
itama ta zauna, bata Dade da zama ba yaran suka tashi suka fice. Ta dube shi tace

‘Amma dai wajen Saudan za ka kwana ko.’

Ya kalleta yana murmushi yace

‘Irin wannan korar da kike min ai dole ma na kwana a can.’

Tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tana fadin

‘Shine dai-dai.’

Jimawa kadan ya tashi ya shiga daki ya dauko duk wani abu da take bukata ya fice ya nufi wajen.

…………..

Ta riga ta gyara wajen tsaf har ragowar turaren wuta ta samu ta kunna don haka kamshi falon yakeyi
dama kuma ga wani kamshin da ya debo daga falon Rabi wanda shima baya rabuwa da turare. Da
sallama ya shiga tana zaune a falon ita kadai da alama yara sunyi bacci. Bayana ta amsa sallamarshi tace

‘Sannu da zuwa.’

Ya kalleta suka hada ido, tayi sauri ta sunkuyar da kai. Yayi murmushi yace

‘Ai ke zan yiwa sannu, kin sha gida kin huta da ni.’

Ta kawar da kai yayinda ya karaso ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku wadda take kai.

‘Yajin naki ya kare kenan.’

Ta dan rufe bakinta da tafin hannunta tana dariya, murya a can kasa tace
‘Kayi hakuri.’

Yana dariya yace

‘Na hakura, amma kin san abinda kika yi bai dace ba ko?’

Ta kalleshi suka hada ido ta marairaice tace

‘Ai na ce kayi hakuri.’

Yayi murmushi ya gyara zamansa ya zuba hannuwansa a saman kujerar. Suka yi shiru na dan lokaci yace

‘Yayarki tace yau zaki karbi kwana Allah ya sa dai kin gyara min dakin.’

‘Eh na gyara.’

Suka sake yin shiru, jimawa kadan tace

‘Abban Nawwara don Allah ka raka ni wajen Mommy na bata hakuri wallahi ban san yanda aka yi
wannan zancen ya fita ba wallahi babu wanda na gayawa sai kai.’

Nan da nan ya tsuke fuska ya kalleta yace

‘Ashe kin san kinyi ba daidai ba. Sai da na gaya miki ki bar wannan maganar amma sai da kika sami
wanda kika gayawa sannan kuma kika fice kukayi tafiyarki gidanku ko?’

Tayi narai-narai da idanuwa tace

‘Don Allah kayi hakuri kaima, wallahi na gaya maka ban san yanda aka yi zancen ya fita. Wallahi da kace
kada na sake ban yi magana da kowa ba.’

‘To ya akayi zancen yaje kunnen mai aikin ki.’

Ta sunkuyar da

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login