Showing 162001 words to 165000 words out of 196754 words
Chapter 55 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
kalleta
“Toh me kike so nayi miki, na kula ki na saka miki cuta?”
“Eh ai gaskiya na fada, sai kaje ka saka matarka tayi abinda ya kamata.”
Har yanzu bata san me take yi ba don haka kawai ya tureta gefe ya wuce ya barta a nan tana ta kumfar
baki. Haka ya ci gaba da yin banza da ita domin tunda yake da ita bata taba bashi haushi kamar wannan
karon ba.
Sosai Mommy ta kula da abinda yake faruwa amma batace komai, ta dai ji dadi da bai dora mata bashi
abinci ba idan ba ranar girkin ta ba. Sai dai kawai ranar da ba girkin nata ba in ya shiga abinda ya samu
yaci, idan kuma ya sameta tana cin abinci musamman da safe toh sai ya ci. Da bai yi magana ba itama
bata tambayeshi dalili ba amma yara sun sanar da ita abincin dare ma siya yakeyi. Ita dai harkokin
gabanta takeyi don tun da ta dawo ta koma islamiyya, karatu duk an yi mata nisa don haka nan ta mayar
da hankali ga cinikin kayanta ana tayi da taimakon su Maman Farida da ragowar kawayenta irin su Hajiya
Salma. Don haka yanzu kam bata da lokacin wata Saudah tunda dama ta kula da yanda take mata wani
gani gani da ta shigo wajen nata.
……………
Tunda yara suka yi hutun makaranta ya daina ma shiga wajen nata da safe, sai dai da daddare yana
dawowa zai shiga. Idan itace da girki tana kallonsa zai shigo da abinci ya shiga daki ya cinye ya fito da
ledodin, sai ya wuce wajen Mommy har sai wajen sha biyu sannan zai dawo wajen kuma yana shiga
dakinsa sai ya saka mukulli ya rufe kofar. Tabbas wannan zaman ya isheta, ita da ta sa rai zai dinga binta
tana gudu amma shine shi harda wani kulle kofa kamar itace za ta saka masa cutar.
Yau din ma itace da girki don haka yana dawowa ya shiga wajen da ledar abincinsa, a kulle kofar take
don haka ya sa mukulli ya bude ya shiga yana mamakin inda taje da bata gaya masa ba ko don kudin
mota. A kan dining table ya ajiye kayan hannunsa ya karasa ya bude kofar dakinta ya leka, babu kowa a
dakin. Ya rufo kofar ya dawo kan dining table din sai da ya tsaya sannan ya kula da farar takardar da aka
ajiye, ya kai hannu ya dauka, rubutu ne a jiki ya karanta kamar haka
‘Na gaji da wannan zaman da nake yi a gidanka ni ba matar aure ba ni ba mara aure ba ban san matsayi
na ba. Saboda kawai na fadi gaskiya. Don haka na tafi gidanmu sai kazo kayiwa iyayena bayani.’
Yayi dariya a fili yace
“Ikon Allah, yaro yaro ne. Allah ya sauwake.”
Ya dauki takardar ya shige daki ya adana. Sai da ya canza kaya ya ci abincin da ya siyo sannan ya rufe
kofar ya wuce wajen Mommy. A falo ya samesu Khalifa da Auta suna kallon TV yayinda Salim da Madu
suke cin abinci a dining a table. Nan ya zauna wajensu suna hira, muryarshi ta jiyo ta fito don tayi masa
sannu da zuwa. Ta samu guri ta zauna suka hadu da yaran ana kallon TV ana hira. Yace zai sha shayi ta
tashi ta hado masa, bayan ta kawo ta ajiye masa ta koma dakin don tayi shirin bacci. Har wajen 11 tana
jiyo muryarsa kuma da yake kwana biyun nan haka yakeyi abun bai dameta ba, kawai sai jiyoshi tayi
yana cewa Ahmad ya rufe kofa kuma ta jiyo shi ya koma dakinsa. Tayi mamaki don ta san ba a nan ya
kamata ya kwana ba. Sai da ta tabbatar babu kowa a falon sannan ta fito ta tura kofa ta shiga dakin.
Yana zaune a kan dadduma ya idar da shafa’I da witri, ta wuce ta zauna a gafen gadon. Ya juyo ya zura
mata ido alamar yana sauraron tambayar tata, ta san ma’anar kallon wato ina sauraron tambayar taki
don haka tayi ‘yar dariya sannan tace
“Na ganka a nan.”
Yace
“Ni ma na ganki.”
Ta sake yin dariya tace
“Don Allah ka bari, ina Umman Nawwaran.”
Yayi yar dariya ya tashi ya nade daddumar ya koma kan kujera, sai da ya zauna sannan yace
“Ta tafi gidansu.”
Ta zaro ido tana dan binshi da kallo alamar tambaya
“Ba ni nace ta tafi ba kuma ban yi mata laifi ba, itace ma tayi min laifi kuma tana jin ta fi karfin ta bani
hakuri. Don haka yanzun nan nima dawowata na tarar bata nan.”
Ta sunkuyar da kai
“Allah ya sauwake, mu din ne ka san sai hakuri.”
Yayi dariya, ya gyara zama
“Muma din sai hakurin, duk lokacin da ta dawo dakinta yana nan ta zo ta shiga.”
Ta mike za ta fita ya bita da kallo yana fadin
“Ina za ki kuma?”
“Ban kaso fitilar dakin ba kuma wayata tana can.”
Ta fita ta ja kofar.
EPISODE 35
Kawai sai ganinta suka yi da yara ga akwati tana ja, da gudu yaran suka shige ita kuma Yaya Ummu da
take zaune a tsakar gidan ta tashi ta karbi akwatin tana fadin
“Lafiya sai kace masu barin garin.”
Bata ce komai ba ta sakar mata akwatin ta wuce cikin falon inda ta tarar da Umman a zaune.
“A’ah, lafiya dai haka.”
Tuni su Nawwara sun haye kafafun Umman, ita kuwa tana karasawa falon ba tace komai ba ta wuce
dakin. Tana shiga ta jefar da jakar hannunta ta fada kan gadon ta sa kuka. A haka Umman ta shigo ta
tarar da ita, ta karasa ta zauna a kusa da ita ta dafa bayanta tace
“Ikon Allah, lafiya kuwa Saude?”
Bata ce komai kuma bata motsa ba sai kukan kawai da take yi, ahaka har Umman ta gaji da tambaya ta
taso ta fito daga dakin. Ta kalli yara taga su walwalarsu kawai sukeyi don haka ta zauna jiran ta gama
kukan tayi musu bayani. Sai da aka yi kiran sallar azuhar sannan ta taso ta fito, ta wucesu a falon ta yiwo
alwala a tsakar gidan, sai da ta dawo sannan ta tsuguna a gaban Umma
“Umma ina wuni.”
“Au ashe za mu gaisa? Ai na zata kuka kawai kika zo yi gidan.”
“Uhm.”
“Toh lafiya kalau, ya maigidan naki lafiya dai yake ko?”
“Eh.”
Ta mike tana fadin
“Bari nayi sallah Umma.”
Sai da ta idar da sallar sannan Umman ta samesu a dakin ita da Yaya Ummu, suka saka ta a gaba suna
tambayarta ko sakinta yayi
“Ni ba sakina yayi ba, bai ma san na fito ba fa na dai rubuta masa a takarda na ajiye masa idan ya dawo
zai gani.”
“Toh me yayi miki?”
Yaya Ummu ta tamabaya don ta kosa taji abinda ya faru.
Ta tabe baki tana duban Umman tasu tace
“Kawai gajiya nayi Umma, tunda aka ce an ga matarsa bakiga wulakancin da yake yi min ba wallahi.
Kuma matar da aka ce ba a san inda ma ta tafi ba kawai daga ta dawo ace a raba kwana, Umma idan
yawon barikinta ta tafi ta dawo fa ta kwaso cuta ta zo ta raba mana a gidan. Shine daga na yi masa
magana a kan ya kamata ya sa ta taje asibiti ayi mata gwaje gwaje a tabbatar da lafiyarta kafin ya fara
mu’amala da ita ya daina kulani. Yau sati wajen uku kenan tunda ta dawo ya daina cin abincina kuma ya
daina kulani kwata kwata, don ko kallona baya yi sai ma yaga dama yake shiga wajen kuma da ya ga
fuskata kamar wanda aka yiwa asiri sai ya bata rai ya fita. Ba kigaba yanda ya ture ni jiya saboda ina
tsaye a gabansa ina yi masa magana ya wuce ko amsa bai bani ba.”
Umman ta jijjiga kai tare da kama haba
“A’ah.”
Yaya Ummu tace
“Tab, lallai matar nan, a shirye ta dawo miki.”
Umma tace
“Kwaria kuwa.”
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Umma tace
“Toh ai wannan da ma baki taho ba saboda ba lallai mu iya yin wani abu ba tunda ba kya gidan. Kuma
wannan maganar ma ta zancen gwaji da kin sani baki fara ta ba.”
“Toh Umma duk ciwon da ta kwaso ai debowa zai yi ya saka min. Yanzu kuma da kika ga na taho kawai
gajiya nayi, suna nema su saka min ciwon zuciya. Shi da matarsa da yaransa sai walwalarsu suke yi ni
yana kunsa min takaici, kuma wallahi Umma in dai yana so ya rabeni toh sai ya saka ta tayi wannan
gwajin kuma shima yanzu sai yayi don ba za su saka min kanjamau ba.”
“Ikon Allah, nan kuma fa da gaskiyarki amma dai da kin bi a hankali duk da haka.”
Suka sake yin shiru na dan lokaci, Umma tace
“Toh bari Kaka ta dawo muji abinda za tace.”
“Ni dai kada ta je ta yi min wani aiki ta dora min bashi don bani da ko sisi wayata ma da na siyar ban
gama jinyarta ba. Kawai dai ko su Baba Yunusa ne kiyiwa magana su nemeshi a yi magana da shi.”
“A’a bari dai ta zo din, itama yanzu ai ba zata soma karbo miki wani bashin ba.”
Su Baba Yunusa ‘yan uwan mahaifinsu ne, lokacin da ya rasu sun so su dauki su Saudah amma
mahaifiyarsu ta ki. Haka suka hakura suka dinga kawo mata kayan masarufi da abubuwan da yaran suke
bukata amma a haka ma sai ta dinga fitna tana maganganu wai ba sa bata kudi. Yayar Saudah din yarta
ta ta fari suka kulla soyayya da dan wan baban nasu, ai kuwa a nan ta dire tace ba za ayi aure ba. Ita
kuwa Yaya Maryam din tace tana son saurayinta don haka dangin uban suka hadu sukayi auren. Lokacin
da bikin Yaya Ummu ya tashi sosai tayi musu wulakanci da bakaken maganganu, tana cewa ta bar musu
Maryama da suka mallake amma ba za su yi mata shisshigi a kan sauran yaran ba. Sai da auren Ummun
ya mutu sannan ta fara shiga hankalinta. Da Saudah ta samu Abba kuma suka fara murnar sun samu
saniyar tatsa za su warwasa gashi har kawo yanzu hakan bata samu ba. Yanzu da yake sulhu suke so ayi
shine suka fara maganar a nemo su.
Sai bayan la’asar sannan Kaka ta dawo daga unguwar da ta tafi, nan suka zauna suka karewa Rabi da
zuri’arta zagi. Don su a tunaninsu asiri tayi ta sa Abba yake neman juyawa Saudah baya. Kakace tace
“Ni dama na san babu alkhairi ko daya a cikin dawowar matar nan, wannan shu’uma ce wallahi.”
Umma tace
“Toh yanzu dai sai mu saurara muga lokacin da zai zo, ko bai zo don komai ba ai zai zo don yaransa ai.”
Tun lokacin da Abba suka yi maganar auren su Ahmad da Aliko sati yana zagayowa suka hadu shi da
Abban su Ummi da abokinsa a Abuja, daga nan suka wuce Dukku don neman auren Zahra. Sosai aka
karramasu, kakan Zahra shine wanda ya karbe su tare da ‘yan uwan ubanta. Suka zauna aka yi magana
ta mutunci kakan Zahra ya nuna Abban su Ummi yace
“Toh ai ga ubanta nana duka mu ‘yan gayya ne.”
Yace
“Hakane, mun dai zo ne don muga gida kawai.”
“Toh ma sha Allah.”
Suka kawo kudin aure naira dubu dari suka bayar. Kafin su fito an zubo musu nono a manyan jarkoki biyu
ga fura cikin bokiti aka hada musu kuma da dabino da cukwi masu yawa. Aka zuba musu a mota suna ta
godiya. Sai da suka koma Abuja sannan Alikon ya kirawo Abba ya sanar da shi sun kai kudin aure don
haka a bawa Atiku ma kudin auren Fathiyya su kai.
Haka kuwa aka yi, daga Kaduna Atikun ya zo suka hadu da dan wajen Inna Hajara da suke kira Baba
Muhammadu da kuma Baban Nafisa Abban ya kawo dubu dari ya basu su kai kudin auren Baba da
Fathiyya. Su ma an karramasu sosai kuma an basu Fathiyya, cartons din lemon kwali da ruwan roba aka
zuba musu a bayan mota suka kamo hanya. Bayan sun dawo gida Abba yace Atiku ya dauki lemo carton
daya sauran kuma yace Salim ya dauko mota ya mayar da Baba Muhammadu Bichi, yace ya tafi da
ragowar lemon da ruwan ya kaiwa su Inna.
Da yake da safe ne lokacin da suka je kafin sallar la’asar zancen ya karade dangi a Bichi, kudin auren
Baba karami naira dubu dari. Sa’a ta ji kishin-kishin din Fathiyya za a kaiwa amma bata tabbatar ba don
haka ta dauki waya ta kirawo Atiku. Bayan sun gama gaisawa tace
“Wai kudin auren wa kuka kaine Baba ko Ahmad?”
“Na Ahmad ai tun wancan satin aka kai, Dukku aka kai. Yau na Baba muka kai da yake yarinyar ‘yar wajen
yayar Rabin ce ai dukansu na gida suka aura.”
“Au Ahmad din ma ta gidan ce?”
“Eh, akwai ‘yar uwar mahaifiyarsu Baraka, ‘yar wajenta ce ai. Kowa an kai kudin aure dubu dari an bamu
don inaga ma fa kafin karshen shekarar nan za mu sha biki.”
Dif ta dauke wuta saboda takaici, sai yanzu ne ma ta gane lallai Rabi so take ta mallake duk wata dukiya
da Abba ya mallaka. Kenan yaran ‘yan uwanta zata sa yaranta su aura duka sai yanda suka yi. Lallai Rabi
ta raina mata hankali.
“Kina ji na?”
Ya katse mata tunani da ya ji shirun yayi yawa.
“Uhm, au shikenan Allah ya sanya alkhairi.”
“Amin ya Allah.”
Ta ajiye wayar kamar ta hadiyi zuciya a fili tace
“Kuma har dubu dari.”
Lallai an raina mata hankali, shi yasa dama tace mata yaranta baza su auri nata ba. Bata gama ciwon
zuciyar mayar da Zulaihan gidan Baffa da aka yi ba yanzu ga wannan. Muntarin ma da ake maganar
aurensa da Zulaihan tun bayan karamar Sallah ake sa ranar kawo kudin aure amma har yanzu shiru. Ta yi
tsaki ta kawar da kai, wani turiri ne yake tasowa yana tokare mata zuciya ji take kamar zata yi bindiga. Ta
gyada kai ta cije lebe, tabbas sai ta ruguza wannan auren in ba haka ba toh bakin ciki yana daf da
kasheta. Dole ma ta wargaza wannan shirin na Rabi.
Tun daf da lokacin rasuwar Baffa ta kula da wasu canje canje daga wajen Muntari. A da kullum sai ya
kirawota wajen sau hudu a rana amma yanzu wataran ma baya kiranta, sai dai idan ita taga shiru ta
kirawo shi. Wani lokacin ma ko ta kirawo haka take jinshi sama sama ba kamar da ba. Ta sha
tamabayarsa idan akwai wata matsala amma ya ki gaya mata, sai yace babu komai. Da kanshi ya fara
maganar kawo kudin aurensu har yasa ta sanar da Ummanta zuwa karshen wata za su kawo amma gashi
har an shiga wani watan an fita basu kawo ba. Kuma idan tayi masa magana sai yace ta dan yi hakuri
akwai shirye shiryen da yake yi. Da farko yace sai ya gama sabon gidansa kuma ya gama din don har ya
kaita ta gani don haka ta kasa gane wanne shirye shirye yake yi. Ba ita ta nemi ganin gidan ba shi ya
dameta har sai da ta shirya suka je, gida ne matsaikaici yayi kyau sosai, har sai da ya nuna mata
dakunanta. Sosai take shirin aurensa don kawo yanzu ta kamu da sonsa, sannan kuma gashi mutum ne
mai kyauta. Ta matsu ayi aurensu ko don ta huta da wannan zaman na gidan Baffa. Yau ma shi take jira,
wajen sati daya kenan rabon da yazo wajenta amma dai yau yace zai zo don haka ta shirya zuwanshi
kawai take jira. Mutumin da a da kusan kullum in ya tsahi daga kasuwa sai ya tsaya ya ganta yake
wucewa gida amma yanzu sai da kyar da magiya yake zuwa inda take. Karar shigowar sako a wayarta shi
ya katse mata tunaninta, ta tashi ta dauko wayar daga kan akwatinta inda ta ajiyeta. Ta danna ta bude
sakon ta karanta kamar haka
‘ki yi hakuri sai gobe zan zo mun fita da madam.’
Ji tayi kamar ta maka wayar da bango, wannan wane irin iskanci ne? Kwanakin nan kullum akayi alkawari
da shi sai yace Madam tace, sun fita da Madam kullum dai Madam. Anya kuwa wannan shegiyar madam
din zata bari ayi auren?
Ta koma ta zauna jikinta babu kwari, ta fizge daurin dankwalin Dake kanta ta jefa kan gadon ta kwanta.
Kwalla me zafi suka biyo idanunta. Ya za ayi Muntari yayi mata haka? A final semester take, idan aka
gama exam bata auri Muntari ba ya zata yi? Tunda ta san dole ta koma gida don bata jin Baffa Aliko zai
bar Baba Yalwa a nan ya dai daga mata kafa ne kawai ta samu nutsuwa. Karar wayarta ce ta sake katse
mata tunani, ta kai hannu ta janyo wayar, Ummanta ce. Bata son yin magana da ita a yanzu amma haka
dai ta danna amsawa ta kara a kunnenta, bayan sun gaisa tace
“Ya na jiki haka bacci kike yi ne?”
“Eh, ina dai kwance.”
“Toh.”
Suka dan yi shiru daga baya Umma tace
“Wai ya na ji ku shiru ne Muntarin bai yi magana ba a kawo kudin.”
Ta juya kwayar idonta cikin kosawa tace
“Um, bai yi magana ba ya dai ce akwai shirye shiryen da yake yi.”
“Toh wane shiri ne haka, ki lallaba shi ya kawo kudin auren in ya so sai ya gama shirin daga baya mana.”
“Toh Umma za muyi magana.”
“Ke ni wace ‘ya ce ne ta Baraka da aka ce Ahmadu ya kai mata kudin aure?”
Ta tashi zaune a dan razane
“Wane Ahmad din Umma?”
“Mtsew, wanne kika sani na Yaya mana.”
“Au ai na zata kudin auren Baba karami a kaiwa Fathiyya?”
“Eh, na Ahmad din aka fara kaiwa sai da sati ya zagayo aka kai na Baban. An ce ‘yar Baraka ce.”
“Ni dai ‘yayanta biyu na sani kuma duk sun yi aure. Babbar ma fa sa’ar Ahmad din ce. Sai dai ko itace
wadda na gani a status din Salim kwanaki ita da Mommy da Barakan.”
“Saboda tsabar munafurci shine Rabi ta raba musu ‘yayan ‘yan uwanta don kada ma su auri jininmu, hm.
Don Allah ki maida hankali a kawo naki kudin a fara yin bikin ki kafin ma su shirya.”
“Toh Umma za muyi magana za ki ji yanda muka yi.”
Ta kagu sosai ta ajiye wayar taju Umman tace
“Toh kada dai naji shiru.”
Suka yi sallama suka ajiye wayar, ta jefa wayar bayanta ta gyara kwanciya. Basu taba haduwa da Zahra
ba amma tabbas ta ga wani hoto a status din Salim kwanan nan, Mommy ce da Baraka sun sa wata
yarinya a tsakiya. Tabbas wannan yarinyar itace Zahra. Kana ganinta ka ga bafullatana, ba wai fara bace
domin Ahmad din ma zai iya finta fari, amma fa babu karya kyakkyawace. Wani malolo ya tokare mata
makogoro, kwalla ta kwaranyo mata. Shi kanshi Muntarin a yanzu haushinsa take ji amma
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good