Showing 105001 words to 108000 words out of 196754 words

Chapter 36 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15389

ita kawai zai yi a banza.”

Suka kyalkyale da dariya a lokaci guda.

“Sharrin ki yana da yawa kawata, toh yanzu wanne zan ajiye miki?”

“Allah kawata duk abinda na sha kaina zan wahalar.”

“Toh Kinga akwai wani abu da zan baki, ki zuba masa a miya za ki ga aiki kawata za ki zo ki bani labari.”

“Toh bari sai mun hadu.”

Sukayi sallama suka ajiye wayar ta cigaba da aikinta.

Da kyar ya karasa dakin kamar wanda ake tunkudawa, a hankali ya bude kofar don baya so ya janyo
hankalinta ya mayar ya rufe a hankali. Ya jefa hularshi kan gadon sannan ya bita ya zauna. Ya rufe
fuskarsa da tafukan hannunsa. Wato yanzu har an kai lokacin da Saudah zata fara nadamar aurenshi?
Shine ma tsohon kenan, wato babu abinda yake mata sai bacci da minshari? Duk da yake shi din ma ya
san mafi yawancin lokuta bacci da minsharin yake yi amma ai bata taba gaya masa ba. A takaice dai so
take tace baya gamsar da ita, toh da wa ma take wayar? Tana sane da cewar ba cikakkiyar lafiya ce da
shi ba ma a halin yanzu toh me take so yayi mata. Ya tuno hirarsu da Aliko lokacin da ya ganta yake ce
masa shi sam ba zai iya auren yarinya karama ba kamar yanda ya san ba zai iya bawa me shekarunsa ‘yar
da ya haifa ba saboda za su zauna ne shi yana wata duniya da ban itama tana tata duniyar. Sai yanzu ya
fahimci maganar Aliko. Toh shi ya ma akayi ya auro ta ne?

Ya tuno lokacin da suka hadu, wani mutum ne yake gina gida a unguwarsu Saudan. Da yazo saka kayan
lantarki irin su AC da sauransu sai yace kayan Japan yake so don haka aka hada shi da Abban. Shi yayi
masa order ya shigo masa da kayan kuma suna da yawa da yake gidan ma gari guda ne. Kamar yanda ya
saba in dai ya samu irin wannan kwangilar da shi ake kai kayan a kunna a gabanshi ya tabbatar suna yi
sannan ya tafi. Suna tsaye a kofar gidan mutumin su Saudah suka zo wucewa ita da kawayenta sun dawo
daga makaranta, da suka zo gabansu kawai sai suka gaishe su harda rage tsaho. Washegari ma aka sake
haka, ranar kwana na uku kuma zuwan su Alhaji na karshe sai yaran suka wuce amma babu Saudah
kuma basu gaida su Abba ba. Da yake suna tsaye da megadin gidan ne da abokin kasuwancin Abba Alhaji
Balarabe da leburori kawai sai Abba ya dubi maigadin gidan yace

“Yaran nan yau ina jin mai hankalin cikinsu itace wadda bata je makaranta ba don gashi yau ko kallonmu
ba suyi ba suka wuce.”

Maigadin ya dan rankwafa yace

“Saude ce ai bata zo ba yau, nan bayan layin gidan su yake ai tana da hankali sosai.”
“Wai islamiyya suke zuwa ne?”

“A’a Alhaji ai boko ce, jarrabawar fita suke shi yasa kake ganinsu da yamma.”

“Allah sarki.”

Suka dan taba hira, leburori da maigadi suka koma suka zauna Abba kuma da Alhaji Balarabe suka cigaba
da hirarrakinsu suna jiran Lalo. Alhaji Balarabe ya kara matsowa yace

“Alhaji ai sai a nemo gidansu tunda ka yaba da hankalinta.”

Suka kyalkyale da dariya Abba yace

“Kai rigimarka ta fiye yawa Balarabe, ina ni ina auren yarinya karama haka? Wannan shekarunta basu fi
goma sha ba fa.”

Yayi dariya sannan yace

“Ni tsiyata da kai boko yayi maka yawa a ka, ba ga ta nan ba ‘yar shekara goma sha din a gidana kuma
lafiya muke zaune. Wani lokacin ma har sun fi saukin sha’ani a kan na gidan.”

“Allah Bala.”

“Ai sosai kuwa Alhaji, yanzun nan za ta dawo maka da kuruciyarka.”

Suka yi dariya suka tafa, kafin su sake cewa wani abu Lalo ya dawo daukansu. Tun daga wannan lokacin
ya kasa cire Saudah a ransa, baya tunanin kara aure amma wani abu ya dinga jan tunaninsa har sai da ya
gamsar da kansa cewa za auri yarinyar nan. Da kanshi ya nemo Alhaji Balarabe suka koma suka nemo
gidan su Saudah da taimakon me gadin nan.

Da farko kamar baza ta saurareshi ba don haka sai Alhaji Balarabe yace ayi mata kyauta. Da kanshi ya
zabi agogo mai kyau da turaruka kala biyu masu tsada aka hada da kudi sababbi kar naira dubu biyar,
bayan sun gama hira Alhaji ya bata. Tun daga wannan lokacin ta fara saurarensu har ta kai idan tana son
wani abu sai kawai tayiwa Abban waya ya saya ya kai mata. Tana gama jarrabawa kuwa aka gama
magana aka daura aure.

Sai yanzu sannan ya gane baya ma bukatar aure ko da lafiyarshi kalau, shi kanshi bai san me ya kai shi ya
kara din ba amma a lokacin tabbas ji yayi ya kamata ya kara din. Gashi yanzu ko shekara goma ba’ayi da
auren ba har ta fara nadama don daga maganganunta da yaji tana yi ya san nadama takeyi. Sosai yaji
tausayinta ya lullube shi, ya tabbatar da Baba da Ahmad duk sun girme mata shi kanshi ya bata kusan
shekaru arba’in. Su Nawwara daman tuntuni yake tausayinsu idan ya tuna ba lallai ma su gama primary
yana raye ba, gashi su Baba da yake saka ran za su kula da yaran ita bata son zaman lafiya da su. Yana
kifta idonsa kwallar da take makale a idon ta fado, ya sa hannu ya goge. Ita kuwa Rabi ina ta tafi haka ne
ta barshi? Gaba daya al’amura sun cabe masa. Wai me ma yasa ya cewa Rabi ta tafi ne? Toh ai ta bakin
Baffa ne ina yake so ta tafi da yace ta fice masa daga gida? Yanzu ga shi ta barshi da matar da baya ma
iya gamsar da ita harma ta zama mai bawa mata shawara kada su auri tsoho. Lallai zai sameta su zauna
suyi wannan maganar. Toh amma in an zauna maganar ma me zai ce mata? Maganganunta babu karya a
ciki kuma babu abinda zai iya yi a kai don yanzu ma ta lafiyar jikinshi yake yi. Allah ya sa dai a sami Rabi
kafin Babbar sallah, ita kadai ce yake jin tana da maganin duk wata matsalarsa domin komai girman
damuwa idan ya shigo gida ya ganta sai ya ji ya sami natsuwa, kuma Sai ta mayar masa da komai ba
komai ba. Yana son Rabi, in dai tana duniya ba ya jin zai iya rayuwa babu ita.

Ta turo kofar ta shigo tana dauke da tsintsiya da abun kwasar shara, ta dan ci burki da ta ganshi a dakin.
Yayi sauri ya faki idonta ya goge guntun hawayen da yake fuskarshi. Tace

“A’ah, Abban Nawwara ashe ka dawo?”

“Uhm, bana jin dadi ne wallahi shi yasa nace Lalo ya kawo ni gida na huta.”

Ya mike yana fadin

“Bari na shiga bandaki na fito bacci zan zo nayi.”

Ya shiga bandaki ya barta, nan da nan ta gyara gadon ta kama shara tana tunani.

Toh me ya dawo da shi yanzu, kuma taga kamar yana da damuwa. Toh ko Madun ya gudu ne? Gashi
kuma bata son ta tambaye shi saboda yanda yake yawan bagarar da ita idan tana zancen.

Kafin ta gama sharar ya fito daga bandakin, ya canza kaya ya haye gado. Ta kwashe sharar ta fita ta rufe
masa kofa.




Yau ma kamar kullum da Baba yaje zance wajen Khairiyya zancen kenan ya turo a sa rana. Tare suka je
da abokinshi Abdallah, sai da suka kusa gama zancen Daddy ya dawo. Suna nan suna hirar ya kirawo ta a
waya yace idan ta gama hirar yana son ganin saurayin nata. Tana gaya masa yace

“Ai sai mu tashi kawai muje mu ga Daddy in ya so daga nan sai mu wuce.”

Haka aka yi tayi musu iso suka shiga suka zauna, bayan sun gaishe shi ya amsa ya dubi Baba yace

“Kai ya muka ji ku shiru ne. Ka san an sa ranar auren yayyenta su biyu, yanzu haka saura abinda bai fi
wata biyu ba. Kai muke jura ku fito kuma mu hada bikin gaba daya.”

Ya sunkuyar da kai yayinda Abdallah ya bada amsa

“Mahaifiyarsu ce har yanzu ba a sameta ba ga shi Abban nasu ma ba lafiya ce da shi ba.”

“Eh ai haka dai za ku daure ayi a wuce wajen ka ji, in ka je ka sami manyan naka su zo muyi maganar.”

Yace

“Toh in Sha Allah za su zo.”

Sukayi sallama ta rakosu bakin mota suka tafi. Suna mota suke tattauna abinda ya faru

“Na rasa da yaren da zan yi musu bayani, ba zan fa iya aure ba in dai ba a ga Mommy ba. Sun kasa
fahimta ta su dai kawai a zo a sa rana.”

Abdallah yace
“Ni wallahi ma sai na gama kamar akwai wata a kasa, kamar dai amfani da damar za ayi a raba ku ka san
yaran masu kudin nan sai a hankali yanzu haka an tanadar mata wani wanda za bawa ita.”

“Wallahi nima ina wannan tunanin, kuma ka ga yanzu da muka fara maganar rayuwar da zamu yi bayan
aure sai take fito da wasu abubuwa da ban.”

Ya dan dube shi da mamaki yace

“Allah ko mutumina?”

“Allah. Ka san abinda ya fi bani tsoro? Bata son haihuwa fa, wai ita in ta haihu sau daya shike nan sai
dayan ma kuma wai sai ta yi shekara biyar da aure.”

“Ka ji ba, ita a gidansu fa ce min kayi su bakwai ne amma ita tana maganar daya.”

“Wallahi kuwa, nima ba wai ina son tara yaran bane da yawa amma kai da baka yi auren ka ga kana ma
haihuwar ko ba ka yi ba amma ka fara tunanin daya za ka haifa.”

“Shine ai.”

Ya gyada kai yayi kasa da murya yace

“Kawai dai ina son ta.”

“Uhm! Allahu Akbar Sharuk Khan.”

Ya harareshi yace

“Bana son isakanci.”

Ya kyalkyale da dariya, haka har suka isa gida Abdallah yana yi masa dariya. Har dare yana cikin damuwa,
yana son Khairiyya amma zai iya hakura da ita in dai ba za suyi masa hakuri a ga Mommy ba. Yana ji a
jikinshi cewa Mommy tana raye kuma za ta dawo, ya za ayi yayi aure ba’a ganta ba. Yanzu ma babu
wanda zai gayawa a je ayi magana balle Abba yace a yi bikin, ba zai ma fara ba.




Bai saba zuwa gida duk sati ba amma da yake Baffa ya sanar musu cewa ranar Asabar Madu zai koma
gida sai yaji yana so shima yaje. Don haka ranar Juma’ah yana tashi daga aiki ya wuce airport sai Kano.
Babu kowa a gidan lokacin da ya shiga, su khalifa daga masallaci gidan Anti Shafa suka wuce shi kuwa
Salim dama suna kasuwa tare da Abba. Mukullin shi ya sa ya bude kofar ya shiga, haka kawai ya ji yana
son shiga dakin Mommy don haka ya bude kofar ya shiga ya zauna a gefen gadonta. Ina Mommy? Yau
wajen kwana talatin ke nan, duk inda suke tunanin za a ganta sun duba ba’a sameta ba. Gidajen radiyo
da talabijin, ofishin ‘yan sanda duk sun je amma shiru.

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Ina kika shiga Mommy?”

Ya fada a fili. Sai da ya dauki tsahon lokaci yana zaune a dakin ko tunanin ma ya kasa, haka ya hakura ya
taso ya fito daga dakin.
Jimawa kadan su Auta suka dawo suka zauna nan suna hirarrakinsu. Saudah bata ma san Baba ya dawo
ba da yake ba da mota ya zo ba har sai da Abba ya dawo yake gaya mata. Tun da daddare ya gama
magana da Baba a kan idan sun tashi su je su taho da Madu don shi ba zai je ba. Haka kuwa suka yi,
wajen karfe takwas suka shirya dukansu suka tafi. Ko da suka je can sai da Baffa ya sa su a gaba da
nasiha ya kara tuansar da su hanyoyin da za su tsare kansu sanna sukayi sallama da shi suka tafi har
Madun. Suna isa gidan ya shiga wanka, kocda yafito a dakin babu kowa sai Ahmad. Ya dube shi yace

“Baffa da Malam sun hada baki sun ki gaya mana waye ya turo min aljanu.”

Ahmad yana daga kwance yace

“Ba waye ba wacece?”

Ya juyo ya dubi Ahmad din

“Au mace ce?”

“Eh mana, ai tun aljanin yana jikinka da Malam ya tambaye shi wa ya turo shi yace bai santa ba amma
sarkinsu ya santa, shine ya turo su.”

“Uhmmn! Lallai.”

Ya cigaba da shirinsa, sai bayan ya sa riga sannan ya sake duban Ahmad yace

“Mace daya nake zargi wannan matar ta Abba.”

“Ka dai ji ai me Baffa yace shi da Malam din, duk sun ce a bar zancen.”

“Hmm! Ai an barshi amma idan halin mutum ne za a kama shi yana yi za ta gane kurenta. Kai ni na ma
tabbatar itace ba wani zargi.”

“Ko ni ma haka nace, amma dai tunda an ce a bar zancen toh ka barshi kawai.”

Shiru kawai yayi ya gama shiryawa sannan ya fito falon ya zauna wajen su Baba karami.




A shirye ya fito ya samesu a falo ita da Zulaiha da yaran. Bayan ya amsa gaisuwar Zulaiha yana yiwa yara
wasa ya dubeta yace

“Madu bai shigo ba?”

Dukansu suka dube shi da mamaki Saudah tace

“Madu kuma? Ko ka manta yana asibiti ne?”

“Oh ashe fa ban gaya miki ai an sallameshi, dazu da su Baba suka fita shi suka je suka dauko fa.”

Ta gyara zama mamakinta ya karu, da kyar ta Bude baki tace

“Uhm, Allah ya sauwake.”
Ya wuce ya nufo kofa suna yi masa a dawo lafiya. Yana ficewa ta tashi ta shige dakinta. Wato saboda
tsabar wulakanci bata ma isa a gaya mata an sallameshi ba sai dai kawai a fito ana tambayarta ina yake.
Toh ya aka yi ya dawo, ita fa ba haka suka yi da kaka ba. Yanda ya fita gidan nan bata taba sa ran zai
dawo ba amma gashi yana gaya mata wai harma ya dawo bata sani ba. Har ta dauki wayarta za ta kirawo
kaka sai ta canza shawara, tunda gobe Lahadi in ya dawo za ta tambayeshi in ya so ita da yara sai su je su
yini a gidan Umman a yi maganar a zaune. Ta jefa wayar kan gado tayi sauri ta fito daga dakin ta wuce
yaran ta tsaya a bakin taga ko za ta hangoshi in zai raka Abban mota.

Shi kuwa Abba yana shiga falon Mommy ya gansu gaba daya suna ta hira da dariya don haka shima sai
kawai ya ja kujerar dining table ya zauna shima aka yi hirar da shi. Jimawa kadan ya dubi Salim yace

“Tashi mu tafi Salim kada rana tayi mana.”

Madu yayi sauri yace

“Abba ai da ni za mu tafi.”

“Au baza ka kara hutawa ba ko kwana biyu.”

“Haba Abba wallahi na gaji da hutun nan, mu je kawai in na ajiye ka sai naje makaranta na kwafo
timetable na dawo.”

Abba yayi dariyar jin dadi yace

“Toh ai sai mu tafi duka ka ga shi Salim sai ya zauna mana a shagon computer tunda na ga shi yana son
shan AC.”

Dukansu suka kyalkyale da dariya sannan suka mike suka fice.

Tana nan a bakin taga tana jiran fitowarsu. Abban ne a gaba da Salim da Madu suna biye da shi, suna
karasowa kusa da motar wadda Bala ya gama wankewa Abban ya dubesu yace

“Na manta bari na dauko takardu a daki.”

Ya juya ya koma dakinsa na wajen Mommy. Abban yana wucewa Madu ya zo gaban motar ya zauna
daga kan boot, ya san tana nan a bakin taga don haka ya zauna ta ganshi sosai. Bala da yake cikin
dakinshi ya fito ya karaso wajen da sauri yana fadin

“Bari na zo na kwashi gaisuwa na wajena.”

Madu ya mika masa hannu yana fadin

“Malam Bala namu na najeriya.”

“Na wajena ni kadai, Allah ya kare ka ya sa haskenka ya kashe idon makiya na wajena. Ka yi taka kayi ta
rago dakalin majina a hauka a zame ka hau mutum ka zauna dai dai ‘dan Alhaji, babu yanda za suyi da
kai na wajena ni kadai.”

Ya zaro gudar naira dubu yace

“Gashi ka sai alawa Malam Bala.”

Dama haka yake jira nan da nan ya karba ya mike ya daga naira dubun yana fadin
“Allahu Akbar, yaushe rabon da ayi min kyautar naira dubu da farar safiya, Allah ya kare gabanka da
bayanka na wajena, nan gani nan bari sadakin mayya.”

Nan Abba ya fito ya juya wajen Abba kuma ya zube

“Alhajin Allah, Allah ya kara lafiya da nisan kwana.”

“Amin Malam Bala.”

Abba ya amsa ya zagaya ya shige gaban mota, Salim da yake tsaye a jikin kofar motar ya bude kofar baya
ya shige. Bala ya dawo ta bangaren Salim yace

“Dan gidan Hajiya a dawo lafiya, Allah ya kau da idon makiya idan ka dawo ka bani na cefanen.”

“Ni bazan baka ko dari ba na wajenka ya baka.”

Ya ruga ya bude gate suka fice Abba yana musu dariya.

Ta ja tsaki ta juya ta koma daki, Zulaiha ta bi kofar dakin da kallo a ranta tace ikon Allah me akayi a wajen
ne. Ta dai jiyo kakacin Bala kuma idan dai wannan ne duk wanda ya san shi ya san in dai yana son kudi
haka yake musu yayi ta kakaci har sai sun masa kyautar kudi.

Tana shiga dakin ta fada kan gado ta zauna ta kafa tagumi. Madun ma kamar fari yayi yayi kiba kadan,
sannan gashi harda Salim suka fita. Kenan yanzu shima Salim din an kai shi kasuwar su biyu za su hadu
sai yanda suka yi ko kuma sai yanda uwarsu ta basu umarni.

‘Allah ya sa ma kar a ganta har abada.’

Ta fada a fili ta kara jan tsaki. Wannan Balan ma ta tsane shi amma ta rasa dabarar da zata yiwa Abba ya
sallame shi, kullum kamar su yake yiwa aiki. Maganganun da ya dinga yiwa Madu kirari da su ma yau sai
ta ji kamar da ita yake, kamar ya san abinda tayi ne yana tura mata haushi har wani kara daga murya
yakeyi. Haka ta wuni zuciyarta babu dadi.

Can wajen bayan azahar kawarta Maman Surayya ta kawo mata ziyara. Da yake Zulaiha tana zaune a falo
da yaran sai kawai suka shige daki. Bayan ta kawo mata ruwa da abinci suka turo kofa suka shiga hirar
yaushe gamo, har suka zo kan hirar da suka yi a waya kwana biyu da suka wuce. Maman Surayya ta dubi
Saudah tace

“Kawata ga kayan fa a jaka na taho

Miki da su, kin san mata sai da gyara musamman ku masu hamshakan kishiyoyi.”

“Mtseww! Toh mijin nata me yake iyawa, duk abinda na siya na sha sai dai kawai na dami kaina ni
kadai.”

Maman Surayya tayi dariya ta sa hannunta a jaka ta zaro wani gari ta mika mata tace

“Ai na ce zan baki wani kayan aikin ki saya masa, toh gashi nan. Sai kin gama miya sai ki barbada masa in
sha Allahu ranar sai kin gaji da aiki.”

Ta karba ta tabe baki

“Mtseww, kuma ba zai bata min miyar ba?”
“Bashi da wani dandanon kawata sa a bakinki ki ji. Shi

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login