Showing 168001 words to 171000 words out of 196754 words
Chapter 57 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
Sai da ta saka Madu a gaba ta ja masa kunne ta sanar da shi bata ma so kowa yaji zancen nan don
so take kawai Saudah din ta ji sammaci.
EPISODE 36
Lokacin da lawyer din Mommy ya shigar da kara ya kama saura kwana takwas babbar sallah, don haka
bayan an yi komai aka sanar da shi ba za a zauna sha’riarsu ba sai bayan sallah ranar da za a koma hutun
sallah ya dawo ya ji bayani. Ba tare da bata lokaci ba ya kirawo Mommy ya sanar da ita, kuma ya gaya
mata tayi amfani da lokacin ta kara samo musu hujjoji saboda da an zauna a kotu a yanke musu hukunci
da wuri. Suna gama waya ta rufe kanta ta shiga gidan Maman Farida. A falo suka zauna bayan sun gama
gaisawa mommy tace
‘Na fa shigar da karar Saudah.’
Ta dubeta tana murmushi da alamar mamaki a fuskarta
‘Allah kawata? Ai na zata ma Abban Khalifan ne da kanshi zai dau mataki a kanta ba sai kin kai ta kotu
ba.’
‘A’a, na ce ya barshi kawai saboda ko ba komai uwar ‘yayansa ce kin ga abun zai zama kamar ya goyi
bayana an yi mata cin mutunci. Ya barni kawai zan koya mata hankali, bata san girman kazafi irin
wannan a shari’a ba shi yasa ta mayar da shi ba komai ba.’
‘Wannan kuwa za tayi hankali? Kuma itace me abun da za a iya nunawa da tsiya ma, nifa gaskiya ko
ciwon da Madu yayi kafin ki dawo ma ita nake zargi.’
Ta dan zaro ido da mamaki tace
‘Wane ciwo kenan?’
‘Au baki sani ba?’
Nan ta zauna ta bata labarin yanda Madu yayi ta hauka da tsakar dare, ta kara da
‘Amma kin san maza shi Baban Farida yace wai ba aljanu bane, amma wallahi su ne.’
Ta kama haba tana jijjiga kai
‘Ai kuwa lallai biri yayi kama da mutum, basu gaya min ba kin san su. Abubuwan da suka faru a gidan sai
a hankali suke fitowa daya bayan daya suna bani labari.’
‘Gaskiya wannan yarinyar fitnar ta tana da yawa.’
‘Zan yi maganinta, don ba ni na aurota ba balle ta dora min hawan jini. Yanzun ma zuwa nayi nace miki
lawyer na ya ce muyi kokari mu kara samo hunjoji.’
Tayi ‘yar dariya
‘Ai wannan mai sauki ne, bari kiga na wanke kaina gobe Hajaraye za ta zo min kitso sai na kunna
recording a wayata sannan zan tabo ta da zancen za ki ji bayani dalla-dalla kawai sai ki tura masa.’
‘Ai kuwa da kin taimaka sosai.’
Suka gama hirarrakinsu suka yi sallama Mommy ta koma gida. Haka ta wuni tana mamakin ashe har
Madu aka so a sabauta mata bata sani ba, ko da yake bata yi mamaki ba da basu gaya mata ba don ba
haka ta koya musu ba. Ta san dai idan aka zauna hira a hankali za su gaya mata.
‘Haka kawai muna zaman mu lafiya mutum ya je ya dauko mana kara da kiyashi ana neman a sabauta
min yara.’
Ta fada a fili yayin da take rataye hijabin da ta cire.
……….
Sallah saura kwana biyar aka kawo dinkunansu na sallah wanda kamar yanda suka saba Abban ya bawa
telansu ya dinka. Kasuwa ya fara kaiwa don haka tun daga can Abban ya karbi na Saudah da yaranta, ya
sa aka kawo musu takalma harda karamin mayafi na Nawwara ya hada. Ya bawa Lalo yace ya kai mata,
ya hada da kudi naira dubu goma a envelope ya bashi yana fadin
‘Kace mata wannan na yara ne ko za su bukaci wani abu.’
Ragowar kayan kuma na Mommy ne sai Auta da Khalifa sai na Zulaiha don haka Madu ya karba ya sa a
mota. Su manyan yaran bana kowa shadda da yadi Abban ya basu yace su kai dinki da kansu.
………………
A zaune suke a falo Abban ya kunna tashar BBC yana kallo ita kuma Mommy tana zaune a gefensa tana
taya shi hira. Ya tashi daga kashingide ya dubeta yace
‘Sallah fa ta zo, me kuka shirya mana.’
Tayi ‘yar dariya
‘Me ka shirya mana dai ai kaine da shiri. Saura kayan sallanka sune ban gani ba.’
‘Ina jin sai jibe yace zai kawo min nawa kayan.’
Yayi gyaran murya
‘Mun sayi sa fa saboda layya da raguna uku, sannan kuma Ahmad ma da Baba kowa ya sayi rago.’
Da fara’arta tace
‘Toh ma Sha Allahu, Allah ya karbi ladan gaba daya. Kace bana za mu sha aikin suya!’
‘Kwarai kuwa, Allah ya saka muku da alkhairi kuma.’
‘Amin.’
Suka dan yi shiru, jimawa kadan yace
‘Ya za ku yi da su Nawwara ne wajen rabon naman?’
‘Ai kai zan tambaya, yanda kace ai haka za ayi.’
Ya gyara zama yana kallon fuskarta
‘Idan aka soya sai a dibar musu?’
‘A’a, ragonsu dai za a kai musu in ya so sai ka tura a je can a yanka musu. Ko kuma a yanka a nan idan
aka fede sai a dauka a kai musu can Ummansu ta soya musu.’
‘Hakan ma babu laifi, Allah ya nuna mana ranar.’
……………
Ranar jajiberin ne don haka duk gidan kowa yayi azumin Arfa, gaba dayansu suna zaune a falon ana shan
ruwa har Baba karami ma da yake ya zo hutun Sallah. Suna cin abinci Mommy tana yi tana tashi saboda
mai tayata aikin sallah Rakiya tana bayan gidan inda suka riga suka dora miyar sallah. Suna gama cin
abinci Abba ya taso ya dawo kan kafet inda dama nan Khalifa da Auta suke zaune suna cin nasu abincin.
Abban yana zama Madu ma ya mike daga kan table din ya dawo kusa da Abban ya yi gyaran murya yace
‘Abba an sami wanda wayar nan take hannunsa fa.’
Ya gyara zama ya dubeshi yace
‘Allah Muhammadu? Ka gayawa DPO din?’’
‘Eh ai ya bayarda officer ma mun je har yamma muna can.’
A nan Mommy ta dawo daga waje da taje duba miya ta zauna a kan kujera. Abban ya cigaba
‘Toh kun karbo wayar ko?’
Ya Shafa kai yana dan murmushi
‘Abba ai akwai matsala ne wallahi.’
‘A’a! Wace irin matsala kuma?’
Ya sake shafa kai yana kallon Abban yace
‘A hannun wani mutum muka sameta Abba, amma sai yace saya yayi a wajen wani yaro mai sayar da
wayoyin don haka sai officer ya saka shi a gaba muka je har shagon yaron. Wallahi Abba yaron nan dai
dan makotan su Umman Nawwara ne kuma ya ce ita da kanta ta kirawo shi ta sayar masa da wayar, don
har cewa yayi ma na zo muje gidan a tambayeta.’
Ba Abban kadai ba gaba dayansu da suke wajen mamakin sukeyi. Yace
‘Ikon Allah, ita ta sayar da wayar? Toh don me za ta sayar da wayarta kuma tace min sacewa aka yi?
Tana fa kallo na baka kwalin nace ayi tracking wayar.’
‘Wallahi Abba haka dai yace kuma zancenshi yayi kama da gaskiya don shi ya so ma muje gidan mu ji
daga gareta.’
Suka yi shiru kowa da abinda yake tunani. Jimawa kadan Mommy ta danyi murmushi tace
‘Babu mamaki wata bukatarce ta taso mata shi yasa ta sayar.’
Ya dubeta da mamaki
‘Bukata? Toh wacce bukata ce da ba za ta iya gaya min ba?’
‘Kai dai baka sani ba, wannan dai ba zancen da zaku daga bane. Ku bar yaron mutane yayi tafiyarsa,
tunda dai tace maka an sace to an sace kawai.’
Yayi ‘yar dariya
‘To yanzu ke kareta kikeyi ko me?’
Tayi ‘yar dariya
‘A’a saboda me zan kareta? Kawai dai na ga ba wani abu bane don da kunyi shawara da ni ma ba za ku
fara wani tracking waya ba.’
Yayi murmushi ya kau da kai
‘Ai shi kenan Allah ya kyauta.’
Madu yace
‘Abba wanda ya sayi wayar ya ce idan za a mayar masa da kudinsa zai bayar da wayar, dubu chasa’in da
yara ya siya.’
Cikin halin ko in kula yace
‘A’a ai ka ji abinda Mommynka tace, shike nan. Idan lokaci yayi na ji bayanin daga bakin ita me wayar.
Kawai ka sallami yaran DPO da kuma wanda yayi tracking din.’
‘Ya fi dai.’
Mommy ta fada lokacin da ta mike ta nufi bayan gida dubo abincinta.
Da ba dan wannan maganar ta Mommy ba tabbas ya so ya nuna mata iyakarta, har wace bukata ce da
ita da za ta dauki wayar ta sayar. Amma kuma yanzu dai abun ya zo ya fara bashi dariya ma, yarinya
kamar wata ‘yar wasan kwaikwayo da ta gama wannan fitnar sai wannan. Ko da yake ma ya san tunda an
yi haka shi yaron da ta sayarwa wayar zai je ya bata labari. Shi bai ma san zaman da takeyi a gidansu ba,
shi dai ya san ba shi yace ta tafi ba don haka ba zai ce ta dawo ba. Duk yanda zuciyarshi take raya masa
ya saketa kuma yayi wa kansa alkawarin ba zai saketan ba saboda darasin da ya dauka lokacin da ya kori
Rabi, don haka idan dai ba ita da iyayenta suka nemi ya saketa ba shi dai ba zai saketan ba yana dai jira
yaga gudun ruwanta da ita da walliyanta.
………..
‘Salamu alaikum.’
Tun daga bakin kofa yake rafka sallama, duk da ya jiyo Umma tana amsashi amma kafin ta gama amsawa
ya karasa tsakar gidan. Ummance ita da Saudahh suna zaune a akan tabarma tare da su Nawwara
yayinda Yaya Ummu take zaune daga kofar kichin tana yanka salad.
‘Umma ina wuni.’
Ya rage tsawo ya gaida Umma, kafin ta gama amsawa ya zauna a kan farar kujerar robar da take ajiye
daga gefe. Ya dubi Saudah yace
‘Haba Anti Saude, sai ki bamu waya mu sayar da ita kuma ki sa mijinki ya turo mana ‘yan sanda.’
Gabanta ya fadi
‘Ban gane ba!’
‘Wallahi haka kawai dazu sai ga su harda dan sanda sun yi tracking sun taso wanda ya siya a gaba har
shagonmu wai sace wayar aka yi ya siya.’
Ta bude bakinta ta sa tafin hannunta ta rufe alamar mamaki, yanda ta ga an kwana biyu ba a yi zancen
wayar ba ta zata an kasa tracking din ashe za a yi.
‘Toh kai me kace da su?’
Ya yarfe hannuwa cikin yanayi na ko-in-kula
‘Gaya musu nayi kawai ni saya nayi a wajenki, da harma za mu zo da su akwai wani da aka zo da shi
Muhammadu yace ba sai mun zo ba. Shine suka sallamemu suka tafi.’
Ta sunkuyar da kai na dan lokaci, Umma ta tashi ta wuce cikin daki. Yaya Ummu ta bata rai sosai tace
‘To ai shikenan tunda sun barku kun tafi, Allah ya sauwake.’
Ya mike tsaye yana bin su da kallo daya-bayan-daya ya nufi hanyar fita yana fadin
‘Amma dai gaskiya kun so ku kwafsa za ku sa mutane a matsala a aikin banza.’
Bayan ya fice ta dubi Saudah wadda takaici ya hana magana tace
‘Gaskiya mutumin nan dan wulakanci ne an ce maka na sace waya meye na wani tracking!’
‘Hm, in bai yi haka ba ai bai nuna min iyaka ta ba.’
‘Allah ya sauwake.’
……..
Da yake an riga an kawo mata kayan sallanta da yara damuwarta ta dan ragu don har ta fara tunanin tayi
masa waya sai dai kuma zancen wayar nan da Kamilu ya zo yayi mata ya sa tana tsoron kiranshi. Har ana
I gobe sallah babu alamar zai kawo mata ko da rago be, to me yake nufi? Ita da yaranta ba zai basu nama
ba kenan ko me? Gaba daya ma zuwa yanzu zaman gidan nasu ya fara isarta. Bata taba zaton zai kai
yanzu bai biyo ta ba, ita a yanda ta zata kafin ta kwana biyu ma ya biyo ta. Amma gashi yau ta kusan sati
biyu bai ko yi waya ba balle ya zo. Ta ji dadi kwarai da Lalo ya kawo mata dubu goman nan don akwai
abubuwan da take bukatar ta saya wa yaran kamar kayan shayi da dan biskit, ga kuma kitso da kunshin
Sallah. Sai dai tana shiga da kudin gidan bayan ta nunawa Umma kudin Umman ta zari naira dubu ita
kuma Yaya Ummu tace sai an bata naira dari biyar, ta bata naira dubu ta samo canji kaka ta ji ana lissafi
itama ta karbe naira dari biyar din don haka ya zama saura naira dubu takwas. A ciki ta samu ta sayi
simcard ta saka a tsohuwar wayarta da ta taho da ita don shi yayi mata rijistar wancan sim din kuma har
ta taho bai yi mata swapping din ba. Ta bude jakarta ta ajiye ‘yan canjin. Tun daga ranar kuma sai ya
zama duk abinda za a saya a gidan sai Umma tace
‘Saude ki dan bamu kudi a siyo mana abu kaza.’
Omo, sabulu, maggi, gishiri, salak har kudi ta biya aka yiwa kaka wanki. Dan kudin kitson ma da take
boyewa duk a haka suka tafi don haka sai ana I gobe sallah sannan ta samu da kanta tayiwa Nawwara,
Ummi da Hanan kitson sallah ta karbi lalle a wajen Kaka ta lallaba musu. Har kwanciya bacci babu sakon
Abba babu wayarshi, gaba daya ta saka rai zai aiko musu da rago ita da yara amma gashi shiru. Ta juya ta
gyara kwanciyarta a kan gadon Umma wanda ya zama wajen kwanansu ita da yaran tun da suka dawo
gidan, ita me ma aka yi mata ne tayi wannan yaji? Ta kasa tuna abu guda daya takamaimai da ya sa ta
baro gidanta, ta san da yanzu ta gama shirya abinda za ta girka gobe ga kuma kayan suya an kawo. Ga
shi Ummansu ba layya zata yi ba, daman Abban ne yake bayar da cinyar sa da naira dubu goma a kawo
sai kuma mijin Yaya Maryam duk da ba ganin mutuncinsa suke a gidan ba shima yana aiko mata da dubu
goma wanda shima an kawo jiya da safe. Ta kasa gane dalilin da yasa ko waya Abba bai yiwo ba, ai dai ko
Umma ya kirawo yayi mata bayani amma yayi kunnen uwar shegu da ita. Haka ta tashi ranar sallah
idanuwanta a kumbure saboda yanda bacci bai isheta ba. Tun da wuri Ummansu ta gama tuwonta harda
cincin Yaya Ummu tayi, tana gamawa tayi wanka sannan ta shirya su Nawwara tayi musu kwalliya da
kayansu da Abban ya yi musu. Sai can wajen sha biyu na rana Lalo yayi sallama a gidan shi da Salim Abba
ya aikosu. Gudan rago suka kawo wanda an riga an fede shi sannan ga kayan ciki a baho da kuma naman
sa shima da yawa a buhu, bayan sun gama ajiye kayan Lalo ya zaro envelope ya mikawa Saudan da take
tsaye tana kallonsu yace
‘Ya ce a baki wannan.’
Ta karba tayi musu godiya suka fice.
Suna ficewa ta wuce Umma da su Kaka da ke tsakar gidan ta shige daki ta sami loko ta bude envelope
din, kudine a ciki naira dubu goma sha biyar. Nan da nan ta zare dubu goma ta tura a kasan akwatinta ta
mayar da biyar cikin envelope din. Kafin ta fito su Kaka har sun fara shirin gyaran nama, tana fitowa ta
mikawa Umma kudin tace
‘Dubu biyar ya bayar, gata nan a siyo mai da maggi da itace a soya naman.’
Ta karba tana tabe baki
‘Dubu biyar kama? Duk wannan uban naman me dubu biyar zata yi? Sai dai kawai ayi maleji.’
‘Haka ya bayar.’
‘Ai shikenen, bayan sallar ma ai dole a nemo shi ya zo a san matsayin auren naku don a samu ki koma.’
Kaka tace
‘Gaskiya Kam, shima kuma ai bai kyauta ba da girmanka matarka tayi yaji amma ka kasa bin sawunta.’
Ta bawa Umma kudin ta juya daki don ta gama yanke shawarar ko basu neme shi ba itama za ta neme
shi. Da an sallace za su koma makaranta kuma ba dadewa za su fara final exam duk da ita tana da spill
over. Idan ta zauna a nan kudin mota ma ya isa ya sata kuka, gashi kuma in tana can sai ta fi samun
natsuwar yin karatun.
Nan da nan Umma ta nemi dan aike aka fara shirin suya. A haka Saudah ta shiga hidindimun Sallah ranta
babu dadi saboda hankalinta ya koma dakinta, gashi kullum yara suna tambayarta ina Abbansu? Yaushe
za su koma gida.
…………
Duk shekara kaka ta saba ranar washegarin sallah sai ta je gidan sarkin Kano tayi ziyarar abokan arzikinta
kuma ta tsaya ta yi kallon sarki; takan ce idan baka yiwa sarki gaisuwar sallah ba to ba kai sallar ba.
Bayan rasuwar kakan su Saudah a nan cikin gidan sarkin tayi aure kafin daga baya shima mijin ya rasu ta
koma gidan su Saudah wajen ‘yarta. Sun yi zama na aminci kwarai da mutanen don haka duk washegarin
sallah sai ta je musu yawo. Yau ma haka ta shirya tayi kwalliyar sallarta sannan tayi sallama da mutan
gidan ta nufi gidan sarki. Bata saba dawowa da wuri ba don haka babu wanda ya nemeta, can gefin
magriba aka kirawo Umma a waya aka sanar mata Kaka ta gamu da tsautsayi; doki ya taka mata kafa har
an kai ta asibitin Murtala emergency. Nan da nan Umman ta shirya ta sallami su Ummu da Saudah ta tafi
asibitin. Yatsun kafarta ne guda biyu suka karye sannan kuma da ta fadi ta buge a ka, binciken likitocin
kuma ya nuna jininta ya hau don haka bayan Umma ta je aka gama gwaje-gwaje sannan aka kwantar da
ita. Yayan Umman ma ya zo da shi da ‘yayansa don haka shi ya biya duk wasu kudade da ake bukata. Sai
da aka basu daki sannan Umma ta kirawo Yaya Ummu tace ta dubowa Kaka kaya a dakinta ta hado da
abinci da sauran kayan bukata ta kawo musu. Har ta mike za ta hada kayan Saudah tace
‘Kin san me Ya Ummu, bari kawai na kai musu kayan ki zauna da yaran.’
Ta koma ta zauna
‘Kin taimaka wallahi don ba karamin gajiya nayi ba don ni na soya kusan duka aman nan.’
Sai da ta gama shiryawa sannan ta shiga dakin kaka don ta dauko mata kaya. Katifa ce a dakin wadda
take lullube da zanin gadon mai fulawoyi, daga gafe kuma akwai tebur wanda aka fi sani da center table
an tura shi jikin bango da ‘yan tarkacenta a kai. A jere ta teburin kuma akwai tsohuwar sif me kofa biyu
wadda a ciki ne duka kayan kaka na sawa suke.
Ta karasa gaban sif din ta bude, ta zaro wasu kaya da suke daga sama. Har ta juya zata fita sai kuma ta
kalli kayan taga sun tsufa da waya don haka ta yanke shawarar ta dauko na can kasan sif din masu dan
kyau. Ta juya ta mayar da kayan ta daga su gaba daya, a hankalin ta janyo wata shudiyar atamfa sabuwa
‘wannan ta dan fi kyan gani’
Ta fada a ranta tare da mayar da sif din ta rufe. Ta daga kayan za ta ta gyara musu ninki sai ta ji wani abu
ya
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good