Showing 99001 words to 102000 words out of 196754 words
Chapter 34 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
EPISODE 23
A falon nata ta tarar da Zulaiha tana kallon TV bayan tayi mata sannu da zuwa tace
“Bayan azahar na iso shine Abba yace na kwaso kayana na dawo nan tunda Mommy bata nan, yace min
gidan Umma kuka tafi ya su Umman?”
“Lafiya kalau, ya jikin Umman taki?”
“Da sauki sosai, har ma ta koma harkokinta.”
Ta barta a nan da yaran ta shige daki. Duk da ta so ace ta gama aiki da abinda Kaka ta bata kafin Zulaihan
ta dawo amma ta ji dadin dawowartata, ko babau komai yanzu ta sami me rike mata yara ta dan huta.
Washe garin sallah ma haka aka cigaba da hidimon bikin sallah, gaba dayan su Baba karami suka je suka
suka yiwa Yaya Shafa barka da sallah daga nan suka huce gidan Baba Munzali kamar yanda suka saba
duk shekara. Bayan sallar isha’I nan falon Mommy suka zauna gaba dayansu har Abba suka yi hira,
sunata alhinin bacewar Mommy a nan wajensu Abba ya tura Khalifa ya karbo masa abinci wajen Saudah
ya zauna ya ci. Sai wajen Sha daya na dare sannan Abba yayi musu sallama ya huce wajen Saudah don ya
kwanta.
Katifu ne guda uku a dakin nasu, da safe sai su dora su daya kan daya idan an zo baccin dare sai a sauke
su kwanta mutum biyu a katifa daya. Madu tare da Auta suke kwana a katifa don haka yau ma haka suka
yi. Karfe biyun dare da ‘yan mintuna Madu yana kwance a rigingine yayinda auta yake kwance rub da ciki
Madun ya farka. Firgigit ya farka da karfi garin yunkurin mikewa ya doki bayan auta wanda shima ya
tashi a firgice, bai ko saurareshi ba ya nufo kofa ya fizgi kofar da karfi ya budeta. Bude kofar ya farkar da
su gaba daya har Baba karami wanda yake kwance a falo
“Kai Madu menene haka?”
Baba karami da ya riga ya mike tsaye ya tambaya, su kuma su Ahmad gaba dayansu sun biyo shi da
gudu. Kofar fita ya nufa ya kama fincikarta iya karfinsa, da yaga dai baza ta finciku ba sai ya fara
bangazarta. Baba karami ne ya karasa kusa dashi ya dafa shi yace
“Madu wai ina zaka ne acikin daren nan?”
A firgice ya juyo yana ta zare ido ya doke hannun Baba karami yana fadin
“Tafiya za muyi ni kadai suke jira ba ka ji suna kirana?”
Ya zabura a guje yayi kicin sai gashi da tabarya ya nufo kofar zai maka mata, kafin ya kai ga kofar Ahmad
ya sa mishi kafa ya fadi yaceda sauran
“Ku tayani mu rike shi mana, baya hayyacinsa fa.”
Duka suka rufa suka danneshi a kwance Baba ya ce da auta
“Tashi kayiwa Abba waya.”
Ya tashi ya dauki wayar Baban ya kirawo Abban wanda nan da nan ya taso ya taho. Yana zuwa auta ya
bude masa kofa, ko da Madu ya kyalla ya ga an bude kofa motsi daya yayi ya watsar dasu ya nufi kofar,
sai dai kafin ya kai Auta ya kuma tade shi ya zube suka sake danneshi aka rufe kofar. Kawai sai Ahmad ya
kama karanta ayatul kursiyyu yana tofawa Madun a kansa, da yake a fili yake karatun suma duk sai suka
fara. Nan da nan jikinshi ya fara saki ya fara wani irin nishi. Suka cigaba da karatun yayinda Abba ya dauki
waya ya kirawo makocinsu mijin Maman Farida; da yake shi babban ma’aikacin jinya ne wato nurse. Tare
suka shigo falon da Malam Bala ya dan tattaba Madu yana yi masa sannu yace
“Alhaji yana shaye-shaye ne?”
“Babu abinda yake sha wallahi, ko maganin asibiti ma sai anyi da gaske yake sha fa.”
Ya kara kallonshi a nutse yace
“Wannan dai matsalar kwakwalwa ce, idan ka amice sai na kirawo mota a kai shi dawanau can ne gari na
wayewa za mu je yaga babban likitan kwakwalwa don yanzu duk asibitin da za muje ma babu abinda za
su iya yi masa.”
Kan Abba ya kara kullewa ya kalleshi yace
“Alhaji Sule daman mutum zai iya samun matsalar kwakwalwa haka kawai? Tunda ka ga lafiyarshi kalau
fa.”
“Komai ma zai iya faruwa Alhaji.”
Da yake sun danyi shiru da karatun ya faki ido ya kara yunkurawa zai fita Baban Farida yayi sauri ya rike
shi suka sake danne shi yace su cigaba da karatun don ya ga kamar yana nutsar dashi. Haka suka danne
shi suna karatu kowa yana kwalla, Baban Farida yayi waya aka turo musu ambulance daga asibitin
dawanau. Sai da aka yi da gaske sannan aka iya saka shi a motar yana ta fizge fizge da ihu, suna kokarin
rufe motar khalifa yayi wuf ya shige ya cigaba da yi masa karatu. Baba karami ya juya da gudu ya dauko
motarsa , Abba ya shiga suka bisu a baya. Nan aka bar su Ahmad a tsakar gida suna share kwalla, Malam
Bala me gadi ya karaso kusa da Ahmad yace
“Allah ya bashi lafiya.”
“Amin Bala.”
“Wannan ba ciwon asibiti bane Dan Alhaji, wallahi sihiri ne ko kuma shafar shaidanun aljanu sune suke
kiranshi don ma makarancin kur’ani ne kuma kuma kuna ta ayatulkursiyyu da tuni sun tafi dashi.”
Ahmad ya kalleshi a gajiye, ya cigaba
“Ba za suyi tasiri ba in Sha Allah, ko nima gobe in naje gida zan samo masa taimako.”
Haka suka koma suka karasa daren a falo, Ahmad da Salim suna karatun kur’ani, shikuma Auta yana
kuka.
Kamar yadda ta saba tana tsaye tana kallonsu ta taga da yake akwai fitulu a tsakar gidan tar take gani.
Ana ficewa da motar tayi shewa ta fada a fili
“Daya kenan, kadan kuka gani in sha Allahu ba zai dawo ba.”
Maganganun da Bala ya fadawa Ahmad da su ya kwana a ransa kuma shima ya yarda da haka, toh idan
ba aljanu ba menene? Haka kawai mutum ya farka wai shi ake jira tafiya zai yi, ga wani karfi da Madun
yayi wanda ya fi na mutum. Basu iya samu sun je masallaci ba a nan suka yi sallar asuba, suna sallamewa
Ahmad ya dubi Salim yace
“Ku zauna kada ku fita, zan je na gayawa Baffa ka san shine malami.”
Ya fito ya sami Bala yace masa ya fita don haka kar ya fita sai wani ya dawo a cikinsu saboda yanda yaga
su Auta sun kasa nutsuwa. Karfe shida yana kofar gidan Baffa, a hankali ya kwankwasa kofar. Baffan ne
da kansa ya taho yana magana
“Kamar bugu nake ji.”
Daga waje ya amsa
“Nine Baffa.”
Cikin yanayi na mamaki Baffan ya amsa
“Ikon Allah, kamar Ahmadu kamar Tijjani.”
“Ahmad ne Baffa.”
Ya bude karamar kofar yana fitowa farfajiyar gidan ya hangoshi ya kama kokarin bude gate din yana
fadin
“Ahmadu lafiya kuwa?”
Ya karasa budewa ya kamo hannun Ahmad suka shigo ciki suka zauna a falo. Suna zama Ahmad yace
“Madu ne bashi da lafiya Baffa.”
“Subhanallahi, me ya sami Muhammadun?”
Nan yayi wa Baffa bayanin yanda abun ya faru, bayan ya gama yace
“Toh Baffa maigadinmu yace sai dai ko shafar aljannu ce sai nima naga kamar haka ne, amma shi Baban
Farida yace matsalar kwakwalwa ce.”
Baffa yayi gyaran murya yace
“Nima din kamar hakan na fuskanta tabbas akwai shaidanu a cikin lamarin, Muhammadun lafiyayyen
yaro yaushe kwakwalwarshi ta sami matsala kuma a cikin dare.”
Ya dan yi shiru kamar yana nazari, ya dago yacewa Ahmad
“Ka ga wayata can a socket, miko min ita.”
Ya tashi ya mika masa wayar, nan da nan ya danna kira tana shiga kuwa aka dauka yace
“Malam alfarma nake nema, yarona ne bashi da lafiya ko za muje ka duba min shi ko da akwai taimakon
da za ka iya yi masa.”
Bayan ya jiye waya ya cewa Ahmad
“Tashi mu je.”
Ya tashi Baba Yalwa da take bacci yayi sallama da ita suka fice. A hanya suka tsaya suka dauki Malam
wanda Baffa yayiwa waya suka wuce.
Kafin su isa asibitin Baban Farida ya kirawo shugaban ma’aikatan asibitin don haka suna isa aka yi musu
duk abinda ya kamata. Ma’aikata ne majiya karfi su uku suka kamo Madu suka shiga dashi wani daki su
Abba suna biye, sai yunkurin fizgewa yake yi yana cewa
“Kuna ji suna kira na ku sake ni mu tafi mana.”
Babu komai a dakin sai turke guda biyu na karfe ga ankwa da kuma manyan kwadi, duk yanda
ma’aikatan nan suka kai ga kokari sukankasa daure Madu, aka yita kokawa da shi. Sai da Khalifa ya shiga
dakin ya fara karanta masa suratul bakara sai jikinshi ya fara mutuwa yana numfashi dakyar yana fesar
da wata iska mai zafi. Nan da nan ma’aikatan suka jashi suka daure hannuwansa da kafafuwansa sukayi
masa allura take bacci ya kwashe shi a nan a ‘kasa aka daure shi da sarkoki. Khalifa yana karatu bakinsa
yana rawa har yayi shiru ya sa kuka, yanzu Yaya Madu ne a haka kamar wani mahaukaci. Nan ma’aikatan
suka janyoshi suka fito suka mayar da kofar suka kulle. Abba da Baban Nafisa suka zauna da ma’katan
jinyar suka yi musu bayani
“An yi masa allura yanzu zai yu bacci na awa shida, kafin ya farka in sha Allahu likita ya zo sai ya duba
shi.”
Suka fito daga office din suka samu guri suka zauna, Abba ya dubi Baba yace
“Baba ka mayar da Alhaji Sule gida sai ka dawo da safe.”
“A’ah ai muna nan Alhaji gara mu jira likita yazo idan ya duba shi sai mu tafi gaba daya.”
Don haka nan suka zauna gaba daya babu wanda yake cewa komai sai Baban Farida da yake ta faman
danna waya. Ko awa biyu ba ayi ba aka jiyo ihun Madu yana ta faman bangazar kofar, gaba dayan su
suka dawo bakin kofar suka tsaya. Baban Farida ne yake tambayar ma’aikatan ko za su sake yi masa
allurar
“Yallabai ai za ta yi masa yawa, dole sai awa shidan nan ta cika.
Abba yace
“Toh yanzu haka za ku barshi yana ta faman bangazar kofar?”
“Ba zai iya bude kofar nan ba don haka ina ganin nan da wani lokaci zai gaji idan ya fadi sai a shiga a
sake daureshi don yanzu ma ina ga ana budewa fa zai gudu.”
Suka tsaya a nan suka yi jugum jugum, Khalifa ya matsa jikin kofar ya fara karatu. A haka su Baffa suka
samesu ya dubi Abba yace
“Muhammadun ne a dakin nan yake wannan ihun haka?”
Kafin a bashi amsa ya fara share kwalla yana fadin
“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.”
Malam ya matsa jikin kofar ya kara kunnenashi kamar mai sauraro ya dubi Khalifa yace
“In kana yin karatun yana kuka.”
Baba ya matso yace
“Sai dai jikinshi ya saki haka ya kasa motsi sai yayi ta haki yana fitar da iska mai zafi, in kuma aka daina a
hankali sai ya cigaba da kokarin gudu wai shi kadai ake jira tafiya za su yi.”
Ya dubi Baffa yace
“A bude shi.”
“Gudu zai yi ai, da ya ga babu kofa gabanshi hanya kawai yake bi da kyar fa ake rike shi.”
Abba ya fadawa Malam, kafin yayi magana Baban Farida yace
“Ba dadewa ma za ka ga likita ya zo sai a budeshi.”
Malam yace
“Ku bude shi, zan rike shi ba zai iya gudu ba.”
Suka bishi da kallon mamaki, Baffa ya kalli Abba. Nan da nan ya cewa ma’aikatan
“Ku bude mana shi babu komai.”
Aka fara kokarin bude kofa daya ma’aikacin yana
“To gaskiya Alhaji in ya gudu baza mu bishi ba sai dai ku ku bishi.”
Malam ya matso daf da kofar, ana budewa kuwa ya bangazo kofar ta karasa budewa zai sheka da gudu
Malam yayi wuf ya rike hannunshi na hagu yace
“Babu inda za ka.”
Ya juyo a fusace suka hada ido da Malam, nan da nan ya tsaya chak. Jikinshi ya fara karkarwa yana hada
wani gumi kamar wanda aka yayyafawa ruwa. Malam ya matso kusa da kunnenshi ya fara karatu kamar
rada don babu wanda yaji me yake karantawa, ya gama ya busa masa a kunne. Ya daga kanshi sama ya
kwalla wata kara sannan ya fara zazzare ido. Malam yace
“Babu inda za ka azzalumin Allah sai na kai kararka wajen Allah ka zo kana zaluntar bawansa.”
Malam ya dubi Baffa yace
“Muje gida Malam.”
Baffa ya dubi Abba yace
“To ai sai mu tafi ko?”
Malam ya ja hannun Madu suka huce gaba yana biye da shi yana ta wasu muzurai. Su Abba suka biyo
bayansu. Malam da Baffa suka sa Madu a tsakiya a bayan mota, Abba ya shiga gaba, shi kuma Baba sai
ya dauki Baban Farida da Khalifa suka nufi gida. Suna ajiye Baban Farida suka huce gidan Baffa suma.
Ana shiga unguwar su Baffa ya nunawa Ahmad hanya har gidan Mallam, ya rike Madu suka shiga ciki ya
taso yaronshi guda daya. Suka zaunar da shi a jikin bango aka mike masa kafafu, Malam ya zauna a
wajen kafarsa yayinda yaron Malam ya tsaya a kansa da wani ruwa a kofi yana yayyafa masa a ka Malam
kuma yana ta karatu. Numfashi kawai Madu yakeyi yana fesar da wata iska mai zafi, in ya tafi zai fadi sai
Malam ya daka masa tsawa yace
“Zauna.”
Sai ya zauna daidai, sai da aka dauki tsahon lokaci a haka sannan da kyar kamar wanda aka shake yace
“Ka bari zan fita, zan fita ka rike ni, kana ta konani ka hana ni tafiya har sun tafi sun barni. Ka barni na
tafi.”
Malam yace
“Ba za ka fita ba sai ka gaya mini me kazo yi.”
“Toh ka daina konani, ya daina diga min wuta a ka.”
Yaron Malam ya daina yayyafa ruwan Madu yayi ajiyar zuciya, ya ja dogon numfashi sannan yace
“Tashi za muyi aka ce mu tafi dashi mu yada shi a kan dutse, shine tun da nazo kuke konani kuma kun
hana ni tafiya.”
Yayi shiru yana numfarfashi, Malam yace
“Me yayi muku za ku tafi dashi.”
“Bai yi mana komai ba, mu bamu sanshi bama saka mu aka yi.”
“Saboda zalunci ko?”
“Ku barni na tafi.”
Malam yace
“In ka tafi za ka dawo?”
“Ba zan dawo ba, ba zan kuma dawowa ba, ba zan dawo ba.”
Yaron Malam ya kara yayyafa masa ruwa, yayi karaji yace
“Ba zan dawo ba.”
Malam yace
“Toh wa ya turo ka?”
“Bamu santa ba, sarki ya santa, shi ya turo mu, yace mu tafi dashi mu barshi a kan dutse, sun gudu sun
barni, ku barni na tafi.”
Malam ya ci gaba da karatu yaron Malam yana yayyafa ruwa, mintuna kadan Malam ya saki manyan
yatsun kafar Madu da yake rike dasu yace
“Fita. In ka sake dawowa sai gawarka.”
Jimawa kadan Madu ya fara atishawa, yaron Malam ya matsa daga kanshi yana Hamdala shi kuma ya
bingire ya fadi a nan.
Khalifa da Baba Karami suka shigo ya radawa Ahmad
“Yaya?”
“Gashi nan dai ina ga suma yayi.”
Malam ya gyara tabarma ya shimfida dadduma a kai, ya sa filo ya dubi yaron Malam yace
“A gyara masa kwanciyarsa.”
Su Baba suka taya shi suka kama Madu suka kwantar dashi a kan shimfidar, sannan Malam ya dubi
Khalifa yace
“Izu nawa ka haddace abokina.”
Yayi murmushi yace
“Sittin.”
“Ma sha Allah, barakallahu fi ka. Zo ka zauna nan kusa da yayanka kayi ta tilawa amma murya kasa kasa,
bacci yake yi.”
Khalifa ya zauna ya fara, Ahmad ma ya zauna a kusa da shi. Malam ya mike ya ja hannun Baffa suka fice
Abba da Baba suka bi bayansu. Sai da suka zauna a falon Malam ya dubi Baffa yace
“Aljani ne ya shige shi, kuma ga dukkan alamu tafiya suka so suyi dashi saboda zalunci. Amma
Alhamdulillah ya fita, ba zai sake dawowa ba, ko ya dawo ma ba zai iya shigarsa ba.”
Baffa ya jijjiga kai, kafin yayi magana Abba yace
“Toh Malam ai bai fadi wanda ya turoshi ba, da ya fada mun ji.”
“Alhaji ai shaidanu makaryata ne, yanzu sai ya fada muku wanda ba shi bane saboda ya tafi ya barku da
wata fitnar kuyi tayi a dangi.”
Baffa yace
“Haka ne, tunda dai an samu an rabu ai shike nan sai mu godewa Allah.”
Malam yace
“Yaran ma ma Sha Allahu da karatunsu shi yasa abun ya zo da sauki.”
Suna nan suna mayar da zance Khalifa ya shigo yace musu ya tashi. Suka tashi gaba daya suka shiga
dakin suka sameshi a zaune yana tambayar Ahmad abinda suke yi a nan yana bashi amsa. Suna shiga ya
gaishe da Baffa, ya zauna a kusa dashi yace
“Sannu Maduwa, ka tashi.”
Malam yace
“Me yake damunka yanzu?”
“Babu komai, jikina ne kawai yake ciwo sai ciwon kai kadan.”
Malam ya dubi Baffa yace
“Toh Alhamdulillah, za ku iya tafiya gida amma a bar mana shi a wajenka domin zai yi sati yana shan
magani da addu’oi.”
“Wannan ba matsala bane yana nan Malam.”
Sukayi sallama da Malam suka fito, suka huce gidan Baffa. A falo suka zauna Baba Yalwa ta zauna ana ta
mayar da zance, Madu ya dubeta yace
“Baba nifa yunwa nake ji”
Tace
“Toh maigidana ai sai na zubo maka tuwon Baffa ka cinye in ya so shi sai a bashi gayan burodi.”
Suka kyalkyale da dariya Malam yace
“Sai dai ki bawa maigidan naki gayan burodin kuwa ku bani tuwona na cinye.
Abba ya mike yayi sallama da Baffa shi da su khalifa za su tafi, har sun kusa fita Baffan ya dawo dasu yyac
“Yauwa do Allah kada ku gayawa kowa yana nan, ku barsu a kan yana asibiti kawai tunda ba a san waye
yayi masa haka ba. Idan Malam ya gama da shi sai ya dawo. Suma sauran yaran kowa yazo a bashi dafa’I,
kwanan nan dama aka yiwa su Tijjani.”
Sukayi sallama da Baffa suka fice.
Gari yana wayewa Saudah ta kirawo Ummanta, bayan sun gaisa tace ta bata Kaka. Suna gaisawa tace
“Kaka na ga aikin malaminki fa, kin san cikin dare aka fita da mutuminki.”
Kaka tayi dariya
“Ai nace miki aikinshi zafi zafi ne.”
Nan ta bawa kaka labarin iya abinda ta gani sukayi ta murna. Tace
“Har yanzu ma basu dawo ba ni ban san ina suka tafi ba na dai ji ambulance ina jin asibiti suka tafi.”
“Ko ma ina suka je bazai zauna ba don Malam yace arna zai hadashi da su su fitar da shi daga garin yaje
ya cigaba da rayuwa a wani yankin na duniya.”
“Yauwa kaka.”
“Toh kinga, da zafi-zafi a kan bugi karfe, yanzu kin san da yunwa zai dawo don haka sai ki tsala girki ki
zuba wancan in ba haka can zai balbalce a wajen neman magani. Amma in kika janye hankalinsa gaba
daya kinga basu ma da mai neman musu maganin.”
“Haka ne kaka, daman na gama abincin zubawa kawai zanyi.”
“Yauwa, toh kada fa ki ci abincin.”
Tace
“Ai bazan ci ba kaka.”
Sukayi sallama suka ajiye waya. Da yake ta riga ta yiwa Abba tuwon alkama miyar kuka sai kawai ta dauki
garin maganin take ta barbada ta juya, ta mayar da kwano ta rufe tana jiranshi.
Basu dawo gidan ba sai wajen karfe tara da rabi, tana jin tsayuwar mota ta fito daga dakinta ta shige
dakinshi saboda Zulaiha da yaran suna falo. Yana shigowa sukayi masa sannu da zuwa Zulaiha tace
“Ya mai jiki?”
“Da sauki Alhamdulillah.”
“Allah ya bashi lafiya.”
Ya amsa ya huce dakinshi. Bayan tayi masa sannu da zuwa tace
“Ya mai jikin?”
“Alhamdulillah, yana can asibitin.”
“Wai me ya same shi ne?”
Yana jijjiga kai ya bata amsa
“Toh gashi nan dai kamar me shafar aljannu,
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good