Showing 66001 words to 69000 words out of 196754 words

Chapter 23 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15359

bashi din kuma ba zan bawa nata yaran ba tunda ba ita ta tara min dukiyar ba. Ka gaya mata haka in
ta sake kiranka, ko da yake zan je ma na gaya mata.”

Shima Fatihu ya mike tsaye ya rike shi yana Fadin

“Ba haka za ka yi ba mutumina, ai a hankali ake bi. Ko dan wani abu ka samu ka bata itama ta samu
natsuwa.”

“Babu damuwa zan duba, bari nayi sauri na tafi gida in ba so kake na sha ruwa a hanya ba.”

“Hakane, da yake mu a nan za mu sha ruwa.”

Sukayi sallama ya rakoshi bakin mota suka tafi. Tunda ya shiga motar Madu ya kula ranshi ya baci, har
suka je gida bai ce komai ba. Wajen Saudah ya kamata ya sha ruwa amma sai ya shige wajen Rabi. Yana
shiga ya huce dakinshi. Yanda ya saba nan kichin din zai zo ya sameta ko kuma daga inda yake ya kwala
mata kira don haka da ta ji bai yi ko daya ba sai ta wanke hannunta ta fito ta sameshi a dakin.

“Sannu da zuwa.”

“Yauwa.”

Bata gamsu ba don haka tace

“Ya kasuwa?”

Yace

“Alhamdulillah.”

Ta kula ranshi a bace yake kuma shi in ranshi ya baci ya fi so a barshi kawai ba wai a dame shi da tambaya
ba. Don haka sai ta mike tace

“Bari naje na karasa mana abincin kar mu makara.”

“Me kike dafawa ne?”

“Kosai ne da dankali sai farfesun kifi da taliya da miya.”
“Ki dama min kunu na, a nan zan Sha ruwa.”

Kafin ta amsa ya shige bandakin ya barta a nan tsaye, yanda ta ga yanayinshi kuma ta tabbatar akwai
matsala don haka ta fice ta cigaba da aiki. Nan da nan ta dama kunun, ta dan silala nama ta sa amiyar da
za aci taliyar tunda da ita da yara ne kawai ta yi babu nama. Kafin ayi kiran magariba ta ajiye ruwan sanyi
da kuma yankakkiyar kankana da ayaba da lemo, ya sha ruwa suka tafi masallaci shi da yara.

Tana jin dawowarsa kuma tana hangoshi ta taga ya shige wajen Mommy, amma bata kawo komai ba, ta
yi zaton wani abun yaje kaiwa ko ya dauko. Har aka dawo daga masallaci bai shigo ba ga abinci ta gama ta
shirya komai a tebur, shi kawai take jira kuma ya ki shigowa. Da ta ji motsin shigowarsa ya huce can sai ta
dauki waya ta fara kiransa, haka wayar ta karachi ringing dinta ba tare da ya dauka ba domin a daki ya sa
wayar chaji ya zauna a falo cin abinci. Da ta ga shiru ya ki daga wayar sai ta turo Nawwara tace tacewa
Abbansu ya zo. Tana shigowa da yake kujerar Mommy tana kallon kofar shigowa sai tace

“Salamu alaikum Mommy.”

“Wa alaikum salam ta amsa da murmushi.”

Ta matso kusa dashi tace

“Abba Umma ta ce kazo.”

Ya ce

“Toh ina zuwa Nauwara.”

Ta huce kan kafet inda ta hango Khalifa da su Salim suna cin abinci tace

“Ya lifa zan sha shayi.”

Ya nuna mata auta da yake kan tebur wanda da bata kula dashi ba yace

“Kinga naku shayin can a gurin Auta.”

Da gudu ta karasa da murnarta

“Auta shayi.”

Ya bata rai yace

“Sai kin ce Yaya.”

Ta Bude bakinta ta rufe da hannunta kamar wadda tayi ba daidai ba tace

“Yaya, Yaya, Yayana ko? Ka yi hakuri?”

Yace

“Eh.”

Ya dauki abincinshi ya koma kan kafet ya sa ta a gaba suna ci tare. Abba ya dubi Mommy yana dariya yace

“Mutuminki fa an samu wadda za a disfula.”

Itama dariyar tayi tace
“Toh, girma mai dadi.”

“Abba me kace?” Inji auta wanda ya tsargu da dariyar da suke yi.

“Ni bance komai ba Auta, hirarmu kawai mukeyi da Mommy.”

Nan ‘yar aike ta zauna ta ci ta koshi kafin su dawo daga masallaci bacci ya kwashe ta don haka Mommy ta
sa Zulaiha ta kaita wajen Umman. Da taga an kawo Nawwara tana bacci takaici ya kara kamata, wa ma ya
sani ko ta fadi aiken ko bata fada ba. Da ya dawo daga masallaci wajen Mommyn dai ya sake komawa,
tana zaune a kan dadduma a dakinshi ta idar da Sallah dama kuma shi take jira. Ya dauki wayarshi zai fice
ya dubeta yace

“A nan zanyi sahur, ki tanadar min abinci.”

Ta dube shi tace

“Don Allah ka zauna muyi magana.”

Ya zauna a gefen gadon yana kallonta

“Yaufa ba ni ce da girki ba.”

Kafin ta karasa ya tare ta

“Na sani, ko ba za ki yi min abincin bane.”

Cikin taushin murya tace

“Wa ce ni? Ai dole nayi maka, ammafa ka ga yara suna kallonka kuma sun san inda ya kamata ka ci abinci
amma ka zo nan. Kada fa su dauka haka akeyi bamu san ko cikinsu akwai mai rabon zama da mace fiye da
daya ba.”

Ya dan sauka daga fushin yace

“Hakane, na fahimta amma dai a nan din zan yi sahur.”

Tace

“Toh.”

Ya fice ya barta a nan tana zaune tana mamaki, ita ba itace da girki ba amma sai a zo ayi kicin kicin ace sai
ta girka. Yana fita ya huce wajen Saudah, a falo ya sameta da goyon Baffa tana karatu. A fusace ta amsa
sallamarsa, ya dube ta a banzace ya ce

“Me zan yi miki kika tura Nawwara ta kira ni?”

“Wannan wacce irin tamabay ce? Baka ma san nice nake da girki ba ga abinci nan na hada amma sai ka zo
ka barni da shi.”

“Mtseww, ai sai ki kirawo Fatihun ki gaya masa ya zo yayi min fada.”

Sai a lokacin ta fahimci inda ya dosa ta tabe baki tace

“Au daga ya gaya maka gaskiya.”
“Ke yanzu saboda lalacewa kima rasa wanda za ki kai karata wajensa sai Fatihu, wato a gidana bani da sirri
saboda kin san abokina ko?”

“Ai na ga ba a sirri kayi abinda kai ba, da ka so sirrantawa da adalci za ka yi.”

“Toh bazan yi adalcin ba, ki koma ki gayawa alkali Fatihu ya tursasa ni nayi ko kuma ya kwatar miki abinda
kike so.”

Ya juya zai fice. Har ya kai bakin kofa sai kuma ya rike labulen ya juyo yace

“Da yake shi ma Fatihun yana da kudi in kina so sai na sawwake miki ki je ki aureshi ina ga shi zai fi yi miki
adalci.”

Kafin tace wani abu ya fice ya barta. Tana ji tana gani ya daina kulata, ga shirin jarabawa ga azumi gaba
daya sai ta shiga damuwa. Sha daya ga watan azumi za su fara jarabawa da kyar take samun ta dan yi
karatun ba tare da ta san ya zauna ko bai zauna ba. Tana son ta bashi hakuri su shirya amma ita bata ga
laifin da tayi ba, don haka ta sa masa ido taga gudun ruwansa. Abinda ta sani dai shine ba zata bar maganar
gidan nan ba har sai itama ya bawa yaranta.
EPISODE 16



Tunda Muntari ya bar gidan ya kasa fidda Zulaiha a ransa, yana son yayi magana amma yana tunanin in
dai Alhaji ne ya haifeta zai yi wuya a bashi ita. Don haka washegari ya sami Madu a kasuwa

“Dan Alhaji wajenka na zo fa.”

Yaran Abba na kasuwa Dan Alhaji suke kiran Madu. Ya mike ya bawa Muntari hannu yana fadin

“Ta samu kenan, bari in taso saboda yan sa ido.”

Ya nuna sauran yaran da suke zaune a shagon. Suka kyalkyale da dariya wani a cikinsu yace

“Zuwa yamma in ta yi wari ma ji.”

Ya ja Muntari suka dan yi nesa da shagon don ya zata wata harkar ce ta kasuwancinsu.

“Wata kanwarka na gani Zulaiha.”

“Ooh, Zulai ba. Ai ‘yar kanwar Abba ce.”

Da murmushinsa ya amsa

“Allah sarki, toh mutumina don Allah ya za ayi ne? Ina so na ‘dan abun nan.”

Madu ya dube shi yace

“Allah ko? Toh ai wannan ba zai zama matsala, ka ga Abba kawai.”

Ya harareshi yace

“Ka ji ka mutumina, ai kai za ka yi masa magana ka ‘dan tsaro min shi.”

“Kada kaji komai an gama.”

Sukayi sallama ya koma shago yana murna yana tunanin garama Muntarin ya aureta ko ta daina yaudarar
kanta. Sai da suka kama hanyar gida sannan yayiwa Abban maganar Muntari da Zulaiha, bayan Abban ya
gama sauraronsa yace

“Ka san yana da mata ko, ina jin ma fa ko shekara biyar bai yi ba da auren fari.”

“Eh, Abba ai karawa zai yi.”

“Toh ai shikenan, zan nemi Baffanta muyi magana in ya amince sai ka gaya masa yazo indai suka daidaita
ai sai ayi auren.”

Sai da aka sha ruwa sannan Abban ya kirawo mahaifin Zulaihan. Da murnarshi ya amince tunda ya ji zancen
daga bakin Abba ya ajiye zancen Habu. Auta aka tura ya kirawo ta, bayan tayiwa Abban Barka da Shan
ruwa ya dube ta yace

“Kin gane Muntari wanda ya zo kafin azumi kika kawo masa ruwa ko?”

Tace
“Eh.”

“Yauwa, yana maganar neman aurenki don na ma gayawa Baffanki, zai zo in sha Allah in kun daidaita
shikenan. Tashi ki je.”

Ta tashi jiki babu kwari ta koma dakin. Tabbas ta tunashi amma ko kallonsa ma bata yi da kyau ba, abunda
ta tuna kawai baki kirin ne sannan kuma kamar a babur ya zo yana ta wani sunkuyo a kafar Abban kamar
wani maroki. Kai anya kuwa! Bata taba tunanin za ta auri wanda bashi da mota ba. Yanzu shikenan tana
kallo Ahmad zai yi aure ya barta da wannan bakin mutumin. Tana shiga dakin ta dauki waya ta kirawo
Umma, bata dauka ba don haka ta ajiye wayar in an jima sai ta sake gwadawa.

Ranar da aka kai azumi uku Muntari yazo zance bayan sallar isha’i. Duk da bata san me za ta ce masa ba
sai da ta dan goge fuskarta, tana fitowa ta ci karo da Ahmad a falo tana shan shayi. Kamar yanda ya saba
haka yayi mata, ko kallon inda take bai yi ba haka ta huce. Saida ta tsaya a bakin kofa ta share kwalla
saboda takaici, ba zata iya daina son Ahmad ba amma ta hakura domin bataga alamar nasara ba.

Dayake zance zai taho yayi kwalliyarsa tsaf dashi yana zaune a kan Babur dinshi kusa da dakin Malam Bala.
Tunda ta zo ta tsaya yake ta faman yashe baki kamar wanda aka yi wa wani albishir. Da yake azumi ne ba
dadewa yayi ba kuma duk wasu bayanai yayi mata. Ya sanar da ita cewa yana da mata daya da yara biyu,
bai taba tunanin kara aure ba amma kuma da ya ganta sai ya ga bai kamata ya bari ta huce shi ba. Ya gaya
mata kuma shi karamin dan kasuwa ne yana karbar kaya a wajen manyan ‘yan kasuwa irinsu Abba in ya
sayar sai ya basu kudinsu ya sake karabar wasu.

Sai bayan sun gama hirar sannan ta tuna bata sanar da Ummanta maganarshi ba, don haka tana shiga gida
ta dauki waya ta kirawo ta, bayan ta gama yi mata bayani tace

“Kika ce ya gayawa babanku?”

“Eh, haka yace min kuma Baffan namu yace ya amince babu damuwa.”

Sai da tayi kwafa sannan tace

“Wato Yaya don kar yaranshi su aure ki shine ya samo miki wani karamin fan kasuwa ko? Kuma madadin
ya fara gaya min shine ya zagaye ya gayawa u ubanki ko?”

Suka dan yi shiru sannan tace

“Toh ke ya kika ganshi?”

“Umma babu laifi, Babur ne dai dashi Kuma yana da mata da yara biyu kuma dai gaskiya ya fi Habu don
ko babu komai a nan zamu zauna ba a nan Bichi ba.”

“Lallai Yaya, ai shikenan. Za mu yi magana da Baffan naku don ko maganar bai yi min ba shima.”

Suna ajiye waya Sa’a ta kirawo Baffa Atiku domin shine wanda take tsarawa zance ya tayata ko da a ita ke
da gaskiya ba, bayan sun gama gaisawa tace

“Kaji wulakancin da Yaya yayi min ko? Wato saboda kada yaranshi su auri Zulaiha shine ya samo mata
wani karamin dan kasuwa mai mata ya hadata da shi.”
“Ya zaki ce wulakanci, mun yi magana da Yayan jiya ai. Na san Muntarin fa, tun kafin yayi aure Yayan ya
hada ni da shi muna business sosai. Da yana da matsala ko nima bazan bari ayi ba kuma na san Yayan ma
ba zai yarda ba. Sai dai kuma idan kin yi mata miji a nan Bichi? Ko da yake Yayan ya ce min sunyi magana
da Baffanta.”

Ta numfasa sannan tace

“Ai shike nan.”

“Yauwa, in dai sun daidaita bashi da wata matsala.”

Suka yi sallama suka ajiye waya. Shima Baffan su Zulaihan da yake ta san ba zai saurara mata ba babu wani
abu da tace masa, shi murna yake ta yi ma da aka yi haka don ya cewa Abban ya bashi wuka da nama ko
babu komai yana tunanin za a rage masa hidima ta biki da kayan daki.




Har girki ya zagayo kan Saudah bata ga alamun zai daina gaba da ita ba, tsakaninshi da ita kawai ya ajiye
mata kudin makaranta a kan durowar idan ya fita kuma ya aiko da chefane. Yau ma da yake kwananta ne
a wajen ya kwana amma ko da aka tashi sahur ficewa yayi wajen Mommy. Da yake yana samu yana koshi
babu abinda ya dameshi harkokinsa kawai yake. Bayan ya gama shiryawa zai fita ya fito falon tana zaune
tana karatu; da yake basu fara jarrabawar ba baza ta fita ba; ya nufi kofa zai huce. Ta yi sauri ta mike tace

“Za ka sha ruwa a nan ko ba za ka sha ba don kar ka sa na wahala.”

“Bazan Sha ba.” Ya bata amsa ba tare da ya dube ta ba.

Kafin ta ce wani abu ya fice ya barta tana ta huci kamar mai shirin fashewa. Yana fita ya shiga wajen
Mommy, jimawa kadan Kuma ya fito ya fice. Har ta koma ta cigaba da karatunta ta kasa jurewa don haka
ta fito ta shiga wajen Mommy. Tana daga labulen ta sameta a bakin kofa tana shirin rufe kofar don tayi
bacci.

“A’ah, Umman Nawwara ce.”

“Eh nice.”

Mommy ta juya tana fadin

“Karaso daga ciki mana.”

Ta tsaya a inda take tana yatsina fuska tace

“Nan ma ya isa. Zuwa nayi dama naji wai ke da mijinki me kuka mayar da ni ne? Tunda aka fara azumin
nan fa nan yake cin abinci, kin hana shi cin abincina, wanna ai zalunci ne kuma wallahi Allah yana kallonku.”

Mamaki ya cika Mommy saboda basu taba tsayawa sun yi wata doguwar magana ba balle irin wannan, ita
duk lokutan da ya daina kulata ya koma wajen Saudan jira kwai take yi har ya dawo da kanshi Amma ita
ta kasa hakuri. Tayi murmushi sannan tace
“Mijin naki dai za kiyiwa wannan tambayar don ba ni nake aurenki ba, idan kika hanshi ina jin ba zai zo ya
ci ba ni kuma bani da matsala idan mutum bai zo inda nake ba ban fiya damuwa da shi ba.”

“Allah dai yana kallon kowa.” Ta fada tana ta wani murguda baki.

Dariya abun ya bawa Mommy don haka sai da ta dara sannan tace

“Tun kafin a haifeki na san da haka.”

Ta rasa abinda zata ce ya batawa Mommy rai don haka ta ja tsaki

“Mtseww!” Ta juya ta fice zuciyarta na kara tafarfasa saboda yanda Mommy take mata dariya kamar
wadda take hauka.

Mommy ta rufo kofa tana mamaki, wato yanzu abun har ya kai ta fara zuwa tana mata rashin kunya haka.
Lallai wataran za ta rufe kofa ta zane mata jikinta don ta kula bata da tarbiyya haka ta huce dakinta ta
kwanta tana ta dariya domin ita abun gaba daya dariya ya bata, ta dai yi wa kanta alkawarin indai ta kuma
takowa cikin falonta tayi mata rashin kunya tabbas sai ta zaneta don idan ‘yarta ce tayi irin wannan
zanetan zata yi.




Ranar sha daya ga watan azumi Saudah zata fara jarrabawa kuma a ranar Zulaiha ta gama. Har kawo
wannan lokaci Abba Bai daina gaba da ita ba, tana kallo zai huce ya tafi wajen Mommy ya ci abinci ranar
kwananta. Bacci kawai yake zuwa yayi a dakinta kuma in ya zo baccin ma rufe kofarsa yake yi. Tana cikin
damuwa amma saboda jarrabawa sai ta kawar da kanta tana ta karatunta kawai, musamman da yake in
suka fara jarrabawar kullum sai sunyi a jere har guda biyar sannan su huta kwana hudu sai su koma su
sake yin guda biyu a jere sun gama, lokacin kuwa zai kama Sallah saura yan kwanaki. Ita Zulaiha tun karfe
goma ta gama jarrabawar ta don haka lokacin da ta dawo Saudah bata tafi ba. Tana ajiye jakarta a daki ta
fito ta nufi wajen Saudah domin ta yi mata sallama, da yake ta dade bata je gida ba yanzu duk ta matsu
taje tunda dai an bar maganar Habu. Tana shiga ta same ta a shirye tana shirin fitowa bayan ta amsa
sallamarta tace

“Yauwa, dama ke zan je nema. Ki dan zauna min da su Baffa naje na dawo 11:30am to 1:30pm ce dani.”

“Lah sallama fa nazo yi miki Bichi zan tafi, Amma bari na Jira in kika dawo sai na tafi dama Muntari yace
na jirashi ya zo.”

“Yauwa, ai ko kin taimaka min.”

Nan ta barsu ta fice tana ta sauri don ta kusan makara. Bata dade da fita ba Muntarin ya zo, waya kawai
yayi mata ta riko ‘yan biyu ta fito. Bayan sun gaisa envelope ya mika mata yana fadin

“Ga wannan saboda tsaraba tunda kin ce baki da account.”

Tana dariya ta karba tace

“Na gode.”
Suka dan taba hira sannan suka yi sallama. Saudah tana dawowa ta bata yaranta ta kama hanya sai Bichi.
Tana isa gidan Sa’a ta fara tamabaya a kan Muntari, burin ta kawai ta ji an ce yana da kudi. Tunda dai
Zulaihan ta mika mata N5000 tace bata yayi tayi kudin mota sai ta sassauto, tace

“Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi wannan abu ba dai haka na so ba.”

“Uhmmn. Umma shima fa bashi da wani laifi.”

“In ma yana da laifi ya na iya, tunda ubanki ya riga ya gama gayawa dangi an yi miki miji. Shima yayan har
yanzu bi ko neme ni yayi min maganar ba da shi kawai yake zancen. Sun hadu sun mayar da ni mahaukaciya
ai sai dai na sawa sarautar Allah ido, Allah ya kyauta.”

Suka yi shiru na dan lokaci, can kuma ta ce

“Tsoro na kawai yana da mata, zaman kishin nan ba shi da dadi ko daya. Amma babu komai.”




Tunda Zulaiha ta tafi sai ya kasance idan Saudah za ta tafi jarrabawa sai dai ta fita da Yan biyu ta kai su
gidan da ta saba kaisu. Inda abun ya zo mata da sauki yawancin jarrabawarta da safe ne, tana dawowa za
ta dauko su, su Nawwara kuma dama sai 4pm suke tashi tunda azumi ya fara. Don haka sai ta dawo sannan
sai ta koma ta dauko su ko kuma ta lallaba Auta ko Khalifa su dauko mata

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login