Showing 21001 words to 24000 words out of 196754 words

Chapter 8 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15402

ruwa ba suka kawo. Har aka gama cin abincin nan suna ta yi
masa cari; mace har biyu amma a rasa wadda za ta yi girki. Da yake abincin yayi dadi sai surutun nasu bai
yi tsaho ba, matsalar daya dai farfesun kazar ya yi yaji kuma naman bai yi laushi ba. Yana shiga gidan ya
gaya mata lallai gobe ta shirya don itace da girki za ta yi masa abincin shan ruwa, ko sauraronta bai yi ba
balle ta kawo wani korafi.

Da yaje wajen Rabi ma sai da ya kara latsa ta don ya san idan ya biyewa Saudah sai ranshi ya baci a kan
abincin. Ya kawo mata shawarar toh ita Saudah din za ta yafe kwananta ta hadawa Rabi kwanan da girki.

“Don Allah kayi hakuri ka bar zancen nan, kwana biyun yanzu su kadai nake samu na yi ibadah a nutse
saboda bani da aiki, kowa kawai yayi aikinsa.”

Haka ya sake ficewa ba tare da yace komai ba.Haka ya kwana yana jin haushin su duk su biyun. Inda Allah
ya taimaki Saudah ranar lecture daya ce da ita 12pm to 2pm, don haka kafin 2:30pm ta dawo gidan. Nan
da nan ta goye Nawwara suka kama aiki ita da Jamila mai aikinta.

Duk yanda ta so ta gama da wuri sai da ta kai 6pm a tsaye. Kosai da kunu ta hada, sannan ta dafa shinkafa
da miya ga farfesun kifi da kunun aya. Ta harhada nan da nan aka kai masa kasuwa.

Haka aka kare azumin nan Saudah tana cikin yanayi na damuwa saboda wahala ga azumi, kallonshi kawai
take yi saboda ta ga yanzu kamar da gayya yake mata abubuwa saboda mugunta.

Duk da waccan sallar ta roke shi kada ya sake yi musu kaya kala daya amma bana ma haka yayi musu,
kowa atamfa biyu da leshi amma kala daya sak. Ta so tayi magana da ya kawo amma da ta kula fitina ya
ke nema sai kawai ta ce

“Mun gode, Allah ya kara arziki da rufin asiri.”

Leshin ta bayar aka dinka mata, atamfofin kuma ta ajiye su da nufin leshin za ta sa ranar sallah da yake ba
ta fita ko Ina.

Sai da Saudah ta gode Allah da ya kasance ranar sallah girkin Rabi ne, ko ba komai itama ta samu na bawa
baki. Tuwon shinkafa da masa Rabi ta yi musu ga kuma zobo da kunun Aya sannan ga cake. An Kai abinci
majalisa yanda yake so kuma an kai gidan yan uwansa. Tana saukewa ta sami babban flask ta cikawa
Saudah da abinci, ga roba ta kunun aya sannan ta hada da rigar yara mai kyau da dankunne da ribbon ta
sa a leda ta bawa auta ta ce ya kaiwa Anti, kayan kuma ya ce ayiwa Nawwara kwalliyar sallah.

A falo ya sami Abbansu don haka a gabanshi ya bayar, tana karba ta nuna masa ta cewa Auta ya ce
Nawwara ta gode. Sai da yazo har wajen Rabin ya yi mata godiya, don bai taba tunanin za ta iya wannan
kyautar ba; abinda ya kasa fahimta ba wai bata son iyalinsa bane, ita dai bata so a takura mata da hidimar
da ba tata ba.

Haka Suka ci gaba da hidimominsu har Sallah ta huce.

…………..

Ranar Asabar ce don haka ba zai fita da wuri ba, tunda ya gama cin abincin safe ya koma dakinsa ya turo
kofa. Sai da ta gama gyara gidan sannan ta bi shi dakin. A zaune yake a kan kafet ya mike kafa, waya ce
sabuwa dal samfurin iphone 11 ya kunna yana ta dube dube a kai, gefe kuma ga tsohuwar wayarsa kirar
Samsung a ajiye. Da murmushinta ta karasa ta zauna a gabansa.

“A’ah, sabuwar waya ka siyo min ne?”

Shi ma da fara a ya kalleta yana mata dariya

“Ke yanzu me za kiyi da iphone, ki dai ce min kina rikon wannan.”

Ya nuna tsohuwar.

“Allah sarki ni, toh ai kwance in dai na maigida ne a bani ina so.”

Ta tuna wayarta ta farko kaninta ne Mubarak ya siya mata da ya gaji da yi mata waya ta wayar mijinta, shi
Abban Khalifa a wancan lokacin kiri-kiri ya ki siya mata waya, sai ya ce wai me za ta yi da waya. Don haka
Mubarak ya saya mata Motorola irin mai murfin nan. Ba ita ta canza waya ba sai da tashi ta tsufa ya bata
kwancen ta, ita ce har yanzu a hannunta ga shi za a kuma bata wani kwancen.

“Toh shi kenan idan na gama zan bar miki ita. Kin san wadannan manyan wayoyin suna da features da
yawa idan baka san me za ka yi da ita ba ta zama aikin banza.”

Ta ce

“Haka ne. Na hada abincin tafiya kasuwa yana nan a kan table.”

Ta fita ta barshi yana ta hada wayarsa.

Sai da aka kwana biyu sannan ya bata tsohuwar wayar tasa, a kan mudubin dakin ya ajiye wayar da ta
shiga ya ce mata gata nan ta dauka.

“Toh Yallabai, na gode Allah ya kara arziki.”

Ya amsa da “Amin.”

Kullum ta shiga dakin da niyyar ta dauki wayar sai ta manta, in ta gama hidimarta sai ta fita bata dauki
wayar ba.

Zaune suke ita da yara a falon bayan isha suna hira ta duba wayarta ta ga chaji yayi kasa. Ta ce

“Salim dauko min chajar tsohuwar wayar Abba a dakinshi, tana nan a kan mudubin.”

Ya tashi ya tafi. Da ya kawo ya karbi wayar ya sa mata chaji, sai ya dawo kusa da ita ya zauna.

“Mommy.”
Ya kira sunanta a hankali kamar wadda zai tsara.

“Mommy don Allah ki ce Abba ya bar min tsohuwar wayar kin ga nine bani da babbar waya.”

Kafin ta bashi amsa Ahmad ya katse shi

“Mommy sai dai a bani in ya so sai na bashi tawa, ni nama riga na tambayi Abban.”

Salim ya ce

“Haba malam kwance ma za ka bani, haba mana.”

Kafin wani yayi magana ta katse su

“Toh duk ku bar hargowa ya riga ya bani. Shikenan ko?

Madu da bai ce musu komai ba ya katse su a yanayi na mamaki

“Mommy ya baki? Amma lallai mutumin nan ya raina ki wallahi.”

Ta bata rai itama tana masa kallon mamaki ta ce

“Uban naka ne mutumin nan, toh idan bai raina ni ba kai zai raina?”

Ya zumbura baki sannan ya ce

“Mommy iphone 11 fa ya siya musu shi da amaryarsa, ina zaune a kasuwa a kai cinikin aka kawo masa.’

Duk suka yi shiru har ita.

Su suna kishin ya za a yi ya bawa mahaifiyarsu kwance ya siyawa amaryarsa iphone 11, ita kuma tana
mamakin irin rainin da yayi mata, wato shi yasa ya ce wai in baka san me zaka yi da waya ba, wato itace
bata san abinda za ta yi da babbar waya ba.

Tashi kawai ta yi ta barsu a nan ta shige dakinta.

Bata taba tsammanin rainin da yayi mata ya kai haka ba, wato ita duk tsahon zamansu bata kai ya siya
mata sabuwar waya ba sai yanzu ya auro matar da ta kai matsayin a siya mata sabuwar waya.

Sai da ta share kwalla saboda takaici.
EPISODE 6



Ranar haka ta wuni zuciyarta babu dadi. Ba Samsung din da ya bar mata ba hatta wayar da take amfani da
ita ma ta fita daga ranta, don haka nan ta bar masa wayarsa a inda ya ajiye ta. Da tana da kudi tabbas da
ta sayawa kanta waya, yau kam ta ga ranar sana’a. Akwai lokacin da itama ta so ta fara sana’a bayan da ta
tabbatar ba zai barta karatu ba, amma a wannan lokacin sai ya nuna mata shi baya son mutane suyi ta yi
masa shige da fice a gida. Ta na tunanin sayar da pure water ne daman don haka da ya nuna mata baya
son mutane a gidanshi sai ta hakura. Ta yi zancen za ta fara alawar madara nan ma ya nuna mata shi baya
so, saboda kada a dinga debe masa madarar shayi a siyar. Daga haka ta hakura, dama itama ba wai tana
son sana’a bane don bata son harkar mutane da yawa; ta fi son aiki. A rashin aikin ne za tayi sana’a kuma
da ya Hana sai ta hakura.

Gaba daya ma wayar ta fita daga ranta. Ta yi tunanin tayi masa magana kuma sai ta fasa, domin in tayi
maganar ma kanta za ta batawa rai ko kuma ya dauka ta sa Madu ya dinga gaya mata abubuwan da yakeyi
a kasuwa. Don haka ta rabu da shi. Da kanshi ya gaji da ganin wayar tana zaune a dakin ya dubeta ya ce

“Kin bar waya sai kura take yi, ko ba kya so ne?”

Ta kalle shi ta kawar da kai ta bashi amsa tana nuna wayarta

“Da yake wannan ma tana komai shi yasa na ji kyuyar canzawa, inaga sai dai ko ka bawa Saudah ita ce ‘yar
zamani.”

Gaba daya ya hangame baki wai shi an yi zancen rabin ransa

“Itama da wayarta ba za a bata ba, sai dai na dauke wayata don masu son ta da yawa.”

Ta ce

“To lallai kam sai a basu.”

Ya dauke wayar ya ja durowa ya ajiyeta. Ta yi mamaki da bai ce komai ba, wato shi har yanzu yana zaton
bata san ya canzawa amarya waya ba, lallai ya raina ta. Haka dai ta bar maganar domin bata son ma hirar
ta tsawaita.

Haka ta hakura ta bar zancen ya huce.

…….

Kwanci tashi har Nawwara ta shekara 2, yayinda Saudah ta shiga level 2 a matakin karatu. Duk yanda aka
kai ga so a hana ta shiga wajen Rabi ta ki hanuwa, da kanta take zuwa ita kuma Rabi dama mace ce mai
son yara sai ta biye mata su yi ta gwaranci. Tun uwarta na biyota ta dauke ta har ta gaji ta daina. Ta saba
da auta sosai, in ta fito tsakar gidan ta ji shiru sai ta fara kira: Atta, wai auta.

Kawo yanzu idan banda Baffa Hassan da ‘yayansa babu wanda Rabi take jin dadin shi a dangin miji sai
kaninsa Atiku, wanda shi kuma a Kaduna yake da zama. Har tsoron zuwa bikinsu take yi, domin da an hadu
sai su ware ta su koma su tare a gindin amarya suna ta rawar kai. Tunda Baffa Hassan ya kirawo Sa’a yayi
mata fada kuma ya bata umarni kada ta sake zuwa gidan wan nata idan ba wani abun akeyi ba take jin
haushin ta, bata san me ta gayawa sauran dangin ba suka hade mata kai haka. Ta san cewa suna jin haushin
ta saboda suna ganin bata yi musu kyauta, amma abinda suka kasa ganewa bata da abun bayarwar ne. Ita
ba aiki ba, ita ba sana’a ba, shi kuma baya bata bata kudi haka kawai tunda komai yana siya, daidai da pad
duk wata yana siyowa ya kawo mata. Wani lokacin haka take daukar kayan da ya siyo mata ta basu amma
ba sa godewa. Itama amaryar ba wai wani abu take basu ba, suna yi ne dan dai kawai su kuntatawa Rabi.

Ko da Sa’an ta haihu ma da suka je suna ita Rabin bata zauna ba. Tun da aka gaya musu sunan ya ce zai
kaisu idan zai tafi kasuwa in ya dawo sai ya dauko su ta ce masa ita sai dai ta biyo shi ya dawo da ita gida
ba za ta zauna ba, ba tare da musu ba ya amince domin shi ma yana jin haushin yanda Sa’an take yi mata.

Ya riga su fitowa ya tayar da mota, Rabi ce ta fara fitowa daga wajenta tana rufe kofa itama Saudah ta fito
ta saki Nawwara wadda ta nufo wajen Rabi da gudu. Nana da nana ta kulle kofarta ta kama sauri kamar
za ta fadi; sairin da takeyi don tana so ta shiga gaban mota. Duk saurin nan Rabin sai da ta riga ta Isa wajen
motar dauke da Nawwara, ta kama kofar baya ta bude ta shiga ta dora Nawwara a kan cinyarta ta rufe
kofa.

Ya juyo ya kalleta

“Nan kuma wa kika barwa?”

Ta ce

“Umman Nawwara mana.”

Kafin ya ce wani abu ta karaso ta ja kofa ta zauna a gaban motar suka tafi.

Ta tuna ranar da ya fara fita da su tare, lokacin Saudah tana amarya.

Baffa Hassan za su je gaisarwa sai kuma wata kanwar mahaifiyarshi da ke nan cikin gari. Rabin ce ta fara
fitowa don haka ta shiga gaban mota ta zauna. Saudah kuma sai da ta gama yaukinta sannan ta fito,
madadin ta shigo motar sai ta tsaya ta bangarensa tana masa magana a kunne. Duk da a yanayi na rada
take maganar amma sai da Rabin ta ji me take cewa

“Habibi ai nice da kwana ni ya kamata na zauna a gaban mota.”

Dariya yayi ya juyo ya kalli Rabin ya ce

“Kin ji me kanwar ki ta ce, ita ce da gaban mota tunda ita ce da kwana.”

Ta yi murmushi ta ce

“Haka ne kam, ni ma sabo da yi ne ya sa na fada gaban mota.”

Ta fito ta koma baya.

Tun daga wannan ranar ta yiwa kanta alkawarin ba za ta sake shiga motarsa tare da amaryarsa ba, in don
ta ita ne zai fi mata sauki ta hau motar haya. Kuma tun daga lokacin bata sake hada fita da ita ba, duk
yanda aka yi sai ta zame. In biki ne dama ita ta fi son zuwa da yamma, yayinda ita Saudah yanzu ita ake
yayi don haka sabgarsu da wuri take zuwa. Yau din ma ta bisu ne saboda bata son zuwa gidan Sa’a ita
kadai gara ya kaita ya dawo da ita. Don haka duk da ita ce da kwana ta yi zamanta a bayan mota bata ma
san saurin me Saudan take ba. Suna shiga kuwa ta yi musu barka ta yi sallama ta fito ya dawo da ita.

……….
A harkarshi ta kasuwanci kayan wuta yake sarowa daga China da Japan yana kawosu Nigeria, saura shekara
guda ya auri Saudah ya fara zuwa Dubai yana shigo da kayan sawa. Tun wannan lokacin Rabin take masa
nacin tana son zuwa Dubai, don Allah ya je da ita. Bai taba zuwa da ita ba amma kullum yana mata alkawari

“In Sha Allah wata rana za mu je dake. Kin san idan tafiyar kasuwanci ce babu lokaci, ajiye ki kawai zan yi
a hotel na shiga gari. Ki bari in Sha Allah wataran za mu je dake ki ga gari ki yialkawar

“Allah ya nuna mana.” Kullum shi ne amsar ta.

A zaune suke a dakinshi suna hirarsu. Ya dube ta yace

“Kin dai kusa zuwa Dubai in Sha Allah.”

Jin dadin da tayi sai da ya bayyana a fuskarta domin daman Madu ya ce mata Abban zai tafi Dubai a cikin
sati mai zuwa.

“Kai ma sha Allah. Ka ce na fara shirya kaya na.”

Ya kyalkyale da dariya ya ce

“Toh Hajiya zumudi. Kya bari dai lokacin yayi.”

“Toh ai ni ban ki ba ma a ce gobe ne.”

Ta bashi amsa.

Ya gayra murya ya ci gaba

“Sati mai zuwa za mu tafi da kanwarki, in ya so ke next month in sha Allah sai mu je dake.”

Shiru ta yi tana kallonshi da alamar tambaya don haka ya sake gyaran murya ya ci gaba

“Da yake ita next month din zai kama suna jarrabawa, shi yasa sai mu tafi da ita yanzu sai mu je da ke next
month. Kwana uku ma kawai za mu yi , da yake kayan da zan sayo duk na gama order din su zuwa kawai
zan yi na gani sai a dorosu a jirgi.”

Shirun dai ta sake yi

“Wata kila next month din ma ki ga mun samu kamar kwana biyar ko sati a can.”

Sai da ta numfasa sannan ta bashi amsa

“Allah sarki ai duk daya ne, Allah ya nuna mana.”

Ta tashi za ta fice ya riko hannunta ya dawo da ita ta zauna.

“Ni tsiyata da ke fushi Rabi…”

Ta katse shi

“Fushin me zanyi, zuwa kawai zan je na yi shirin bacci ne.”

“Banda wanda kika riga kika yi, ai na ce kema za mu je da ke fa.”

Ta ce
“Uhmm. Ni ba fushi nayi ba, amma dai idan da layi ake bi a je da na riga ta kama layi, ko ba haka ba ma ai
ni ce babba. Ina nan ko Abuja baka taba zuwa da ni ba kuma yanzu ka ce za ka tafi da amarya Dubai ai dole
rai na ya sosu.”

“Toh na ji ranki ya sosu, ki yi hakuri in sha Allah next month za mu je. Kinga ita na gaya miki uzirinta kuma
na riga na gaya mata da ita za mu fara zuwa. Ki yi hakuri kin ji.”

Da kyar ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro ta bashi amsa

“Ba komai Allah ya nuna mana.”

Haka ta kwana a kusa da shi ba tare da tayi bacci ba saboda takaici, shi kuma ya kwana yana minsharinsa.

…….

Tunda ta san da ita za a Dubai take ta rawar kai. Ta so a ce ta barwa Rabi Nawwara, saboda tana ganin duk
inda za ta barta baza ta nutsu ba kamar a nan don ko gidansu bata son kai ta. Ummansu ba cikakkiyar
lafiya gareta ba gashi ba kowa sai Yaya Ummu, ita kuwa ta san ba za ta zauna ta kular mata da yarinya ba.
Shi da kanshi ya ce ba za a barta wajen Rabi ba don ya san ba za ta karba ba kuma baya son rigimar da
Rabi yanzu don ya san tabbas bata ji dadin wannan tafiyar ba. Amma shi kanshi ya shirya in Sha Allah next
month in ya tafi da ita har Umra za su je suyi. Ko ba komai ya wanke kansa a wajen Rabin.

………

Washegarin ranar da suka tafi Dubai Baba karami ya dawo daga Abuja, an gama bautar kasa. Dawowarashi
ya dan wanke mata wani takaicin da take ciki, suka zauna ita da yaran suna ta hirarsu. Sai da ta same shi
shi kadai sannan ta ce

“Baba na an gama bautar kasar lafiya ko?”

Ya ce

“Lafiya kalau Mommy, saura neman aiki. Kiyi ta yi min addu’a don yanzu aiki a garin nan sai kana da hanya.
Kin ga shi Faruk Mahmud da yake babanshi Babba ne a Abujan har ya samu tun kafin ma mu gama.”

Ta ce

“Kai Baba.”

Ya ce

“Wallahi Mommy. Dama a ministry of finance babanshi ya sama mishi yayi service din kuma kafin mu
gama sun bashi offer.”

“Kai ma in Sha Allah za ka samu Babana. Bari Abban naku ya dawo shi ma ba zai rasa wanda ya sani ba.”

Ya ce

“Mommy ai ba zan iya jiranshi ya dawo ba, kin ga takarduna can na yi photocopy na rubuta komai, gobe
in Sha Allah sai Jigawa daga nan kuma na huce Lagos.”

Ta kalleshi da

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login