Showing 159001 words to 162000 words out of 196754 words

Chapter 54 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15358

kwaso yaran suka koma gidan.




Shi kuwa Abba bayan ya gama shiryawa sai da ya zauna ya ci abincin safe a nan da yake shayi da burodi
ne kawai kuma ta riga ta zuba ruwan zafi a flask, yana gamawa ya fito ya fada wajen Mommy. Shi Salim
ya riga ya tafi makaranta don haka yana shiga Madu ya fito wajen mota don ya jirashi. A daki ya sameta
ya sakata a gaba da hira har sai da ta dubi agogo tace kada fa ka makara, ya mike yana dariya

“Bari na tafi tunda kin kore ni.”

Itama dariyar tayi

“Saboda kada cefane na ya sami matsala ne.”

“Toh ai shikenan, sai na dawo.”

Tayi masa a dawo lafiya ya fice tana yi masa dariya.

………….

Sai bayan magriba suka dawo daga kasuwa kamar yanda suka saba, wajen Saudah ya fara shiga. Da yake
tana son taji mai zai ce a kan sace wayarta da ta ce masa anyi tana nan a falon tana jiransa. Bayan tayi
masa sannu da zuwa ya amsa ya karasa ya zauna kusa da ita

“Yanzu shikenan ba’a ga wayar taki ba.”

“Hm, wallahi kuwa. Tun lokacin ma dana gane bata jakar da muka kira layukan duk an kashe su.”

“I, toh dama ai cirewa suke su zubar sun yiwa mutum asara.”
“Allah ya sauwake, gobe sai ayi miki swapping layin wayar kuma sai ki dauki tsohuwar taki tana nan a
cikin kwalin iphone din in aka samu kudi sai a siyo miki wata.”

Ta kalleshi da mamaki don bata zata zai ce haka ba, da ta san haka zai ce da tuni ta dauke tsohuwar
wayar ta kawar. Yanzu daga iphone yake so ta koma waya nai torchlight. Ta riga ta san yana da kudi
tunda ai ga kaya nan ana ta sayarwa, sai dai kawai yace bai gama yi mata wulakanci ba.

“Ba fa ta rike chaji wannan.”

“Haka za kiyi maleji kafin a sami kudi. Itama iphone din ai za a iya sawa a kamo barawon na san ana
tracking ai.”

Kafin tace wani abu ya zaro waya ya dannawa Madu kira tana nan zaune tana takaici suka ji sallamarsa,
Abban yace

“Shigo Muhammadu.”

Yana shiga kafin ya zauna Abban yace

“Iphone din Antinka aka sace, ai za a iya tracking ko?”

“Eh, akwai lambar da ake kwafa a jikin kwalin in dai kwalin yana nan za a iya tracking a gane inda take.”

Ya mike daga inda yake yana fadin

“Kwalin yana nan mana, bari na dauko maka shi.”

Ya shiga dakinsa, jimawa kadan ya fito ya mika masa kwalin yana cewa

“Gashi nan in dai an sami wanda zai iya kawai a nemo wanda ya dauka, ko ba’a samu wayar ba dai a
kama barawon.”

Madu ya karbi kwalin ya fice. Tana nan zaune ta kasa magana saboda takaici ya wuceta ya koma dakin.
Yanzu idan aka kama Kamilu me za tace masa da shi da iyayensa? Ta bashi wayar ya sayar mata sannan
ta zo ta sa an kamashi a matsayin barawo. Bata taba tsammanin zai ce ayi tracking wayar ba da tuni ta
kawar da kwalin amma gashi tana zaune ya bayar wai a kama masa barawon waya. Gaba daya tunaninta
ya kare ji take kamar tayi bindiga saboda takaici. Ya fito dubeta yace

“Ina zuwa.”

Ya sa kai ya fice. Wajen Mommy ya nufa, a falo ya sameta da yara kamar yanda ya saba kafin su samu
matsala. Ba karamin dadin ganinsu yayi kamar haka ba sai yanzu ya san cewa wannan ganin nasu da
yake haka ita da yaran suna nishadi yana kara masa walwala. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya karasa
ya zauna a kusa da ita yana fadin

“Bari nima na zauna a yi hirar dani.”

Tayi dariya ta mike ta dauko jug da kofi a dining table ta zuba masa kunun aya ta ajiye masa a kan table
sannan ta koma ta zauna. A hankali yaran suka tashi suka fice daga wajen. Bayan sun dan taba hira
kadan yace

“Kanwar ki ta shigo kuwa?”
“Wai Umman Nawwara? A’a bata shigo ba ni din ma kuma ina ta aiki ban samu na shiga ba ko don nace
mata na dawo.”

“Babu komai bari a kirawo min ita don nayi magana daku gaba daya.”

Ya daga murya ya kirawo Auta ya aikashi ya kirawo ta. Sai da ta dauki sama da minti talatin kafin ta fito
ta zo kiran, tana zaune a falon tana tunanin wane dalili ne ya sa zai kirawota can. Da taga dai lissafin nata
ba zai kare ba ta tashi yaran suna biye da ita suka nufi falon. Da sallama ta shiga bayan Mommy ta amsa
sallamarta ta wuce ta zauna a kan kujera mai zaman mutum daya, sai yanzu ne ta samu ta karewa falon
kallo ta gane abubuwan da aka saka.

Baffa Karami ne ya karasa wajen Mommy din ya tsaya a gabanta yana

“Mommy, Mommy.”

Ta daukeshi tana dariya tace

“Baffa, muga hannunka. Ma Sha Allah hannu yayi kyau Allah ya kara lafiya.”

Su Nawwara ma suka shigo da gudunsu ita da Ummi da kuma Hanan. Suma wajen Mommy din suka
wuce suna mata hira. Tsaf ta samu ta kare mata kallo, lallai sai dai idan barikinta ta tafi kam. Matar da
miji ya kora ina taga ta walwala amma ita tayi wani haske tayi kyau sosai sai sheki kawai takeyi, lallai da
akwi ayar tambaya. Mommyn ce ta katse mata tunani

“Umman Nawwara ya gida? Ya yaran gaba daya.”

“Lafiya Alhamdulillah.”

Ta bata amsa tana kokarin saita fuskarta.

“Toh ma sha Allah.”

Yayi gyaran murya sannan yace

“Yauwa dama kiranki nayi ku gaisa kuma kamar yanda mukeyi da haka zamu raba aikin, kwana bubbiyu.
Saboda haka sai Mommy ta fara daga yau ko?”

Ya karasa zancen yana kallon Mommy, tace

“Babu laifi.”

Ya kalli Saudah yana jiran yaji me zata ce, ta dauke kanta tace

“Uhm, yayi.”

“Yauwa.”

Suka dan yi shiru ta mike tace

“Shikenan ai ko?”

“Eh.”

“Allah ya bamu alkhairi.”
Ta tattara kan yaranta suka fice.

Shi kuma Abba ya tashi ya koma kan dining table din cin abinci. Tuwon alkama tayi da miyar gyada irin
wadda yake so, don haka ya zauna ya ci ya koshi, yana ci suna hira.

………….

Tana shiga falon ta zauna a zuba tagumi a kan kujera, gaba daya ma yanzu ta rasa haushin me zata ji;
kayan da aka zubawa Mommy a falon ko kuwa wannan rainin hankalin da yake yi mata. Sai wani yage
baki yake a gaban wata matarsa, lallai da akwai sauran rigima don wallahi ba zata yarda ya kwaso cuta
ya saka mata ba. Dole a sake lissafi.

Sai da ta lallaba Baffa da Hanan suka kwanta sannan ta fara laluben wayarta, nan da nan ta tuna yanzu
bata da waya don ba ayi swapping din sim card ba tsohon kuma jefarwa tayi don ma kar ya gani. Ta kalli
Nawwara da Ummi taga kamar suma sun yi bacci a hankali kamar mai rada tace

“Nawwara.”

Ta bude idonta kamar wadda dama labe take yi

“Taso mu je.”

Ta sauko da ita daga kan gadon ta ja hannunta suka fice daga falon, sai da ta rakota bakin kofa sannan ta
tsuguna tace

“Je ki wajen Mommy kice Abba ya zo.”

Nan da nan kuwa ta zura da gudu da yake akwai fitulu a tsakar gidan babu wani duhu. Bayan ta fadi
sakon ta zuro da gudu ta dawo, taja hannunta ta shige daki ta kwantar da ita ta fito falon ta zauna tana
jiransa. Bata dade da zama ba ya shigo, bayan ta amsa sallamarsa ya karaso ya zauna

“Ashe ba kuyi bacci ba, akwai wani abu ne Nawwara tace na zo?”

Ta bata rai, ba da son ranta zata yi wannan maganar ba amma shine kawai abunda zai kwatar mata
‘yanci, tana tuna wahalar da Yaya Ummu ta sha wajen zaryar asibiti. Ga matsaloli kala kala haka kawai
itama a kwaso a kwasa mata.

“Eh, yanzu suka kwanta.”

“Toh gani.”

Ta sake shan kunu tana ta faman kaubda kai kamar wadda aka yiwa dole

“Mun yi magana a tsaitsaye ban samu lokaci mun zauna ba. Ni fa ban gane wannan dawowar to
Mommyn su Khalifa ba gaskiya.”

Mamaki ya bayyana a kan fuskarsa yace

“Ban gane baki gane ba, ai dai kin san ba sakinta nayi ba ko? Da yake ma a gabanki komai ya faryac

“Eh nima din ban ce ka sake ta ba, amma ya za ayi mace taje yawonta kusan wata biyu babu wanda ya
san inda taje ta dawo ace an cigaba da raba mana kwana, ba tare da wani bincike ba.”
Mamaki ya karu a fuskarsa

“Ban gane fa me kike so ki ce ba ki yi min dalla-dalla.”

Ta kalleshi ta dauke kai tace

“Babu wanda ya san inda taje, ko kai ma baka sani ba sai da taga dama ta dawo suka hada baki da
kanwarta tace tana gidan. Yanzu idan yawon barikinta taje kenan haka za ta zo ta raba mana duk wasu
cututtukan da ta kwaso ka zo ka shafa min, ai sai taje asibiti ayi mata gwaji a ga sakamakon kafin a raba
kwanan.”

Kawo yanzu bai san mamaki take bashi ko haushi take bashi ba, wadannan maganganun da takeyi ji yake
kamar zaginsa take yi. Ya dago ya kalleta da idanuwansa wadanda kawo yanzu sun riga sun yi ja zur, sai
da yayi murmushin takaici sannan yace

“Um, wato yanzu kina nufin da ta tafi yawon karuwanci ta tafi take tana zina da wasu mazan sannan
yanzu ta dawo min gida.”

Ta gyara zama

“Toh tunda ba a san inda mutum yaje ba ai komai ma zai iya faruwa.”

“Hakane.”

Ya sunkuyar da kai suka dan yi shiru. Ta dan fara samun nutsuwa a ranta don zuwa yanzu tana jin ko
bata saka shi ya kuma korar Rabin ba to tabbas ta saka masa wasiwasi a rai. Ya dago ya dubeta yana
murmushin takaici

“Ban san a ina kika samo wannan zancen ba kuma ban san ma me yasa kike yinsa ba, abu daya na sani
Rabi tawa ce ni kadai. Kamar yanda na aureta ba tare da wani ya taba taba ta ba toh yanzu ma ina da
yakinin idan na jefe ta tsakiyar maza ba zata yarda wani ya kusanceta ba idan ba ni ba. Yanda aka raba
kwanan nan kuma haka za a cigaba da yi sai dai ke din kina da zabi na ki kare kanki ta duk hanyar da ta yi
miki dadi. Amma ni na Rabi ne duk cutar da ta kwaso ko a ina ne nima ina so idan ta bani zan karba. Ina
fatan kinsan girman kazafin zina, kuma ina fatan kin san baki isa ki bata min suna ba don yanzu da ni za
kiyi ba da Rabi ba.”

Kafin tace wani abu ya tashi ya fice ba tare da ya rufo mata kofar ba. Bin bayansa tayi da kallo, wato ita
dai bazata taba yi masa gwaninta ba kenan. Yanzu daga tana kokarin kare su daga fitnar da ka iya tasowa
shine yake gaya mata wadannan maganganun. Da ya san shi din na Rabin ne ya je ya aurota, toh wallahi
ita baza ta yarda a cuce ta ba idan dai ba zai kai matarsa asibiti ayi mata gwajin HIV da sauran gwaje
gwaje ba toh ita kam ba zai ra’be ta ba.

…………….

Sai da ya yi kokawa sannan ya hada nutsuwarsa, yayi sa’a da ya shiga falon babu kowa don haka ya
karasa kan dining table ya cika kofi da ruwa ya shanye. Har ya ajiye kofin malolon da ya tokare masa
makogoro bai fada ba, ya daga murya ya kirawo Ahmad ya bashi umarni ya rufe kofa. Ya shige dakinsa,
yayi zaton tana ciki amma sai ya tarar babu kowa. Ya fada bandaki yayi alwala don yayi shafa’I da witri.
Yana nan yana sallar ta shigo, ta wuce ta zauna a kan gadon ta mike kafafunta ta lullubesu. Yana idar da
sallah ya dauki alkur’ani ya fara tilawa saboda ya dan kara samun natsuwa. Daren nan na yau so yayi ya
more sosai amma wadannan kalaman na Saudah sun hargitsa masa lissafi. Yanda ya san zai mutu haka
ya san Rabi tasa ce shi kadai juma babu inda taje, amma zargin nata kawai da Saudah take yi ya haifar
masa da damuwa. Bai taba nadamar auren Saudah ba sai yanzu, da ba dan abinda ya faru da Rabin ba da
tabbas Saudah ba za ta kwanar masa a gida ba. Sai dai da yake shi mutum ne mai daukar darasin rayuwa
yanda bai ji dadin abubuwan da suka biyo bayan korar da yayiwa Rabi ba baya jin zai sake korar wata
mace sai dai idan itace ta nema. Idan kuwa ta nemi ya sake ta toh tabbas ya gama aurenta. Kawo yanzu
ma gaba daya ta fice masa daga rai, toh wai me ma ya kaishi ya aurota? Wannan ai shine me rabon ahan
duka. Kawai dai tazo ta tarwatsa masa gida, ko babu komai ya san kawo yanzu kimarsa ta ragu a wajen
Rabi da yaran da ta haifa masa. Wannan wace irin musiba ce?

Yanda ya so ya huta da daren sai da yayi saboda ko babu komai akwai bukata, sai dai ita kanta Rabin ta
fahimci walwalarsa ta ragu. Bayan ya dawo daga masallaci ma sai da ta tambayeshi ko wani abu yana
damunsa domin ita dai duk lokacin da ta farka za ta tarar da shi idonsa biyu. Da ya nuna mata babu
komai taga ya kama harkarsa da yara itama sai ta rabu da shi. Ahmad ne da ‘yan makaranta suke fara
karya kumallo saboda sune suke fita wajen bakwai da rabi, suna zaune suna shan shayi ya fito daga
dakin. Bayan ya amsa gaisuwarsu ya dubi Ahmad yace

“Ahmadu hakuri fa zakayi ka karbi CR-V ka dinga tafiya da ‘yan makaranta tunda in sun tashi su suke
dawowa.”

Ya sunkuyar da kai, shi dai bai damu da fita da motar ba saboda kamar yanda ya fada idan yaje banki
ajiyeta kawai zai yi sai an tashi ya dauko ya dawo, ya fi so ya dinga tafiya a ta haya yana dawowa a ta
haya. Weekend dai idan zai fita yana daukan motar amma baya son zuwa da ita aiki. Duk da baya so
haka dai ya amsa

“Toh Abba.”

“Yauwa.”

Ya dubi Auta yace

“Ka je ka kirawo kannenka ku tafi gaba daya.”

Ya amsa sannan Abban ya koma dakin. Haka suka gama shiryawa Ahmad ya hada har su Nawwaran ya
tafi da su. Tun tuni Abban yake son ayi hakan amma rigingimun da suke ta faruwa a gidan da kuma
kasancewar shi baya son bacin ran yaransa ya sa bai yi maganar ba. Don wani lokacin ita kanta Rabin
tana fadan da ba dan ita ta jajirce ba toh da ba zai bari ta yiwa yaran tarbiyya ba saboda yanda baya son
ya gansu a damuwa.

Sai wajen takwas da rabi sannan ya fito, tana kichin bata ji fitowarsa ba. Ta daga murya daga kicin din
tana magana da Salim da yake kan dining table

“Salim dauko kudi a kan mudubina ka siyo kwai guda shida, kayi sauri don Allah kafin Abba ya fito na
soya masa.”

Ya karaso kicin din ya tsaya daga bakin kofa yayinda Salim din ya shige dakinta.

“Babu kwai ne a store ba ranar Juma’ah aka kawo ba?”

“Um, ai bani da mukullin store din yara sunce ka karba.”
Ya dan jijjiga kai

“Haka ne, kanwarki ce ta batar da nata sai aka bata wanna. Ai naga kayan abinci a nan din ba suna
karbar mukullin su debo ba? Kai Salim je ka karbo mana.”

“Abba ba ma karba, Ya Ahmad ne da Ya Baba suke siyo kayan abincin.”

Mamaki ya bayyana a fuskarsa

“Ba za ta baku mukullin ba ko me?”

“Mu bamu ma tambaya ba Abba.”

Ya wuce yana fadin mu je a bude ka debo kawan, Salim din ya bishi a baya. Wato yanzu duk abincin da
yaran nan suke ci har ma suke ciyar dashi su suke siya bai sani ba, kawai ya cika store da kayan abinci ta
kulle ta ajiye mukullin sai dai ta diba ta kai gidansu nasa yaran suna ciyar da kansu. Lallai yarinyar nan ta
dade tana cutarsa.

Suka karasa ya shiga falon yayinda Salim ya tsaya a bakin kofa. A falon ya sameta tana kwance a kan
doguwar kujera, bayan ta amsa sallamarsa yana daga tsaye yace

“Ina mukullin store?”

“Bari na duba.”

Ta tashi ta shiga kicin. Har ta dauko mukullin tace ba zan ma bayar ba haka kawai za a zo ana min
muzurai saboda za a karbi mukullin store. Da kyar ma yake mata magana saboda yana jin haushinta a
kan ta fadi gaskiya. Ta fito tace

“Ban gan shi ba bari na dubo dakin.”

Ta nufi kofar dakin kafin ta karasa yace

“Barshi ma.”

Ya juya ya fice kafin tace wani abu, tana jinsa ya kirawo Bala yace ya buge kwadon kofar store ya gayawa
Salim din a sayo kwado a canza. Nan da nan kuwa Bala ya sa dutse ya balle kwadon Salim ya shiga ya
debo kwan.

…………..

Kwanakin nan biyu haka yayi su a wajen Rabi ba tare da ya bi ta kan Saudah ba, musamman da ya samu
Ahmad zai kai masa su Nawwara makaranta. Sai dai kawai da safe ya shiga dakinsa ya ajiye mata kudin
makarantar ta kamar yanda ya saba.

Yau da kwana ya zagayo kanta tana ta saka rai ya shigo amma har ya tafi kasuwa bai shiga wajen ba,
daga baya itama ta fice ta tafi makaranta. Yanda ta saba haka ta dawo tare da ‘yan makaranta, nan da
nan ta gama abincin dare ta jere ta shige daki. Don ita yanzu gani take yi itace za ta yi fushi ba shi ba.
Kafin ya dawo sai da ya tsaya ya siyo abinci a restaurant sannan, don haka yana dawowa ya wuce daki
sai da ya cinye abincin ya fito da ledodin sannan ya shirya ya zauna a falo yana kallon labarai. Jimawa
kadan ta fito daga dakin ta wuce kicin, ta fito daga kicin din ta zo ta tsaya ta bayan kujera tace
“Sannu da zuwa.”

Ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa

“Yauwa.”

“Baka ci baincin ba.”

“Na koshi.”

Ta kara shakar haushi don haka ta juya ta koma daki ta rufo kofa.

Haka suka dinga yi har kwananta ya kare ya sake komawa wajen Rabi. Sai da aka kwashi wajen sati biyu
suna haka, shi kwata kwata ya daina shiga harkarta ita kuma tana ganin ita aka yiwa laifi an yi mata
wulakanci kuma ba a sa Mommy tayi gwaje gwaje ba. Yana sane da ita yayi mata haka, jira yake sai da
kanta ta gane munin abinda tayi in ya so in ta bashi hakuri sai su shirya.

Yau ma kamar kullum ya shirya ya fito daga dakin ba tare da ya ci abincin safe ba ya nufi kofa zai fice. Ta
karaso ta sha gabansa tace

“Baka ci abincin ba.”

“Na koshi.”

Yana kokarin ficewa tace

“Wai me ka mai da ni a gidan ne, daga na fadi gaskiya shi kenan sai ka mayar da ni wata sakaratac

Ya kalleta ya dauke kai zai wuce, ta sha gabansa tace

“Kafin ka fita sai ka gaya min matsayi na a gidan nan, na gaji da yin girki ina kwashewa ka daina kula ni
kamar wata shara. Haba mana.”

Ya

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login