Showing 93001 words to 96000 words out of 196754 words

Chapter 32 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15399

komai
kkuma na san wajenshi suka tafi, sun barni da yara babu wanda yace min wani abu.”

“Lallai wadannan yaran naki yan raini ne? Ke da mijinki Amma ba za su miki bayani ba, su sun zama
matar shi kenan.”

“Toh wa ya sani ne Umma.”
“Toh kin ga, rabu da su, shirya ki tafi asibitin ai kin san inda yake ganin likita ko?”

“Na sani Umma, toh amma haka zan kwashi yara na goya wannan na ja sauran har asibiti bayan suna
yawo a mota.”

“Umm haka ne kuma, toh kawo min yaran sai ki tafi asibitin ke kadai.”

Suka yi sallama nan da nan ta hau shirya yara. Sai da ta gama shirin ta tsaf tana sakawa yara kaya mai
mata wanke wanke ta zo don haka tace mata ta tafi sai gobe don ba ta san lokacin da zata dawo ba. Ta
riga ta yanke shawarar in a asibiti zai kwana tog ita a gidansu zata kwana jibi ta dawo.

Can a asibiti kuma wajen karfe tara likita ya shigo ya sake yiwa Abba gwaje gwaje ya dubi Baba da yake
tsaye a gefenshi yace

“Alhaji ya dage yanzu zai tafi gida, ka ga BP dai ya dawo normal amma blood sugar yana daukan time, sai
an kula da diet dinshi sosai.”

“Babu damuwa doctor in Sha Allah za a kula.”

“Gashi ya dage sai yayi azumi don haka sai a kula da abincin nan sosai da shan magani.

Ya rubuta musu sallama suka kamo hanya.

Tana tsaye a bakin titi tana jiran tasi da yara ta hango motocinsu sun dawo, da yake Abban baya gefen
da take ma bai kula da ita ba sai dai su sun ganta itama kuma ta ga Abban ta ja tsaki a fili tace

“Gayyar tsiya.”

Sai kuma ta tuna kamar fa Abban ta hango a gaban mota, don haka sai kawai ta tsallako da yaran suka
dawo cikin gidan. Tana shiga Abban har ya riga ya bude falonta ya shiga yana mamakin inda take, a
tsakiyar falon ta same shi kafin ya amsa sallamarta yace

“Daga ina kuke haka?”

“Hmn, yanzu muka fita mu biku asibitin sai kuma kafin mu sami mota naga kun dawo.”

“Eh, ai na samu lafiya don kin ga ina ma azumi.”

“Uhm, Allah ya kara lafiya.”

Yace

“Amin.”

Ya shige daki ya barta a nan sai da ta share kwalla saboda takaici, wai itace matar ko kuwa wadannan
yaran nashi marasa mutunci. Shima kuma ga shi ko wani kulawa bai yi da ita ba ya shige daki. Daga mishi
kafa kawai za tayi ya warke amma wallahi zai ji daga gareta don wannan wulakanci ya isheta. Haka ta
daure zuciyarta ta shiga hidima da shi har ya gama wanka ya kwanta. Ta kara bawa kanta hakuri bayan
la’asar ta shiga kicin tayi masa Alala da miyar hanta ta soya masa kwai. Sai da aka sha ruwa ya zauna a
kan table ta hada masa shayi kenan sai ga Khalifa ya shigo da kwano ya huce table din yace

“Abba gashi, Ya Salim ne ya dafa maka.”
Da fara’arsa ya amsa

“Kai ai kuwa na gode, Allah yayi muku albarka.”

Ya amsa da Amin sannan ya juya ya fice, ya sa hannu ta bude kwanukan. Funkaso ne yayi kyau sosai ga
kuma miyar alaiyahu irin wadda yake so, ya ture kwanon alalan dake gabansa ya janyo na funkason, ya
dauki miyar hantar ya juye a kan miyar alaiyahu ya fara ci. Kafin ta sake yin magana sai ga Khalifa ya
dawo da kunun tamba a flask yace

“Abba ga kunun tamba.”

A ranta tace shegun yaran nan har sun iya dama kunun da ita in dai ta dama baya dadi, haka yace mata
ta zo ta zuba mishi kunun ya ture kofin shayi ya hau cin abinci yana mata surutu.

Sai da ya gama cin abincin sannan tace

“Abba toh idan bani da wani amfani in tafi gida mana.”

Ya dube ta da mamaki

“Ya za kice ba ki da amfani, saboda me?”

“Toh kai da ‘yayanka kun ware ni, tun jiya baka da lafiya ba wanda ya gaya min sai ganinsu nayi goman
dare suna rufe gate, sai da na tambaya aka gaya min gashi kai ma ka kashe wayarka baka meme ni ba.
Gashi an sallameka babu wanda ya gaya min har na fita na kama hanya sai ga ka, abincin ma da na girka
maka basu barka ka ci ba suka kawo wani. Toh ka ga ai bani da wani amfani, daidai da magani fa ina kallo
ana yin kira Baba ya zo ya baka maganin ko kallona bai yi ba. Ai sai na tafi gida kawai na huta na daina yi
muku shisshigi.”

“Wa yace miki kina shisshigi ke da mijinki.”

“Toh me nake yi in ba shisshigi ba?”

“Kada ki zama mai yin kishi da yara mana? Ke da za kiyi farin ciki yara suna kula da ni, ai taya ki suke yi
fa. Da su Nawwara ne haka za ki ce?”

Ranta ya kara matukar baci wato itace ma take kishi da yara, ta sunkuyar da kanta don maganar da take
so ta fada masa ta yi tsauri da yawa kuma bata so suyi fada yanzu. Suka dan yi shiru sannan yace

“Ai ba wani abun damuwa bane, ki gode Allah kina da masu taya ki ma.”

Take ta mike tsaye don ta ga kamar so yake ya zage ta tace

“Bari na dubo Baffa yana bacci a daki.”

Tana shiga dakin ta sa hannu ta share kwallar da take idonta. Lallai tana da aiki, wannan abun da yaran
nan suke mata ai karuwanci ne gaba daya sun hanata kula da mijinta, lallai akwai aiki. Dole ta kirawo
Umma su sake lissafi.

………,……….
Bayan ya rufe musu kofa yana tsaye a dining table shi kadai a falon yana kallon bango yana tunani har
hawaye suka fara bin idonsa. Har Ahmad ya fito daga dakin yazo kusa da shi bai sani ba sai ji yayi ya dafa
kafadarsa

“Za a ganta fa Baba in sha Allahu.”

Ya juyo ya fuskanci kaninsa ba tare da ya tare hawayen ba yace

“Toh ina ta shiga Ahmad? Sai yaushe za a ganta? Kwakwalwata ta kasa hutawa Ahmad. Inna lillahi wa
Inna ilaihi rajiun.”

Rike hannunshi Ahmad din yayi suka zauna yace

“Ka goge fuskarka kada Auta ya leko ya ganka bai yi bacci ba fa, za a ganta in Sha Allah.”

Shima Ahmad din ya share kwalla suka yi shiru suna rike da hannun juna.
EPISODE 22



A haka Baba ya daure ya koma Abuja zuciyarshi cike da damuwa da tunanin inda Mommy ta shiga. A
Abujan ma bai huta ba, yana dai can ne kawai amma zuciyarshi tana Kano. Halin rashin lafiyar da ya bar
Abban ma ya kara masa damuwa, ko ba komai ubansu ne idan ya mutu yanzu sun yi biyu babu, ba uwa
ba uba. Don haka kullum da safe sai ya yiwa Abban waya ya tuna masa ya sha maganinsa, haka kuma sai
ya kirawo Madu ya tuna masa ya shirya su fita kasuwa sannan da yamma yayiwa Salim waya ya gaya
masa abinda zai dafawa Abban; don kafin ya tafi sai da ya siyo komai na bukata suka gyara suka ajiye a
kicin. Tun wajen la’asar ya isa Abujan don haka magariba na yi ya shirya ya tafi wajen Khairiyya ko zai
samu mai kwantar masa da hankali.

Falon da ta saba tarbar shi nan ta sa aka bude masa, bayan ya zauna yana duba waya ta shigo tana rike
da faranti wanda ta dora ruwa roba daya da kuma lemon five alive. Ta ajiye ruwan da lemon a table din
da yake gabansa sannan ta zauna a kujerar kusa da wadda yake. A nutse suka gaisa ta tambaye shi
mutanen gidan

“Ya labarin Mommy kuwa?”

Fuskarshi ta nuna damuwa ya kawar da kai sannan ya bata amsa

“Wallahi har yanzu shiru, babu wanda ya san inda take.”

“Subhanallah, ka san na zata za ka ce min an ganta, amma in sha Allahu za a ganta muna nan muna
rokon Allah.”

“Haka muke fata in sha Allah.”

Suka dan taba hira sannan yayi mata sallama ya koma gida. Haka yayi ta bin wayarshi yana duba inda ya
dora cigiyar Mommy a Facebook ko zai samu wanda ya ganta amma shiru.

Sai can baya goma na dare yana shirin kwanciya bacci sai kiranta ya shigo, yana dagawa yace

“Khairy.”

Sai da tayi murmushi sannan ta amsa

“Mijin Khairy.”

Yayi dariyar jin dadi

“Ka san wani abu, yanzu Abba yace na gaya maka yana so a zo maganar aurenmu saboda yana so ayi
bikin kafin Babbar sallah don za suyi tafiya da Mommy kuma za su jima basu dawo ba.”

Ya danyi shiru sannan yace

“Na ji dadi sosai my Khairy, matsalar dai yanzu kinga ba ma cikin yanayin da zanyiwa Abba wannan
maganar don ba shi ma da lafiya fa, ga Mommy ba a ma san inda take ba.

“Eh ai nima na gayawa Daddy, na dai gaya maka ne don ka sani. In sha Allahu kuma za a ga mommy kafin
karamar sallah.”
“Haka muke fata.”

“Toh cheer up habibi, ka daina yawan damuwa in sha Allah everything will be just fine.”

Yayi murmushi ya kara kashingidewa, suka dan taba hira kafin suyi sallama kowa ya kwanta.




Duk yanda ta so su Salim su daina yiwa Abba abinci sun ki su daina, gashi yaron ya iya girki sosai. Ta yi
korafi a wajen Abba har ta gaji sai dai kawai yace ya kamata ta dinga farin ciki yara suna tayata kula da
shi, don haka ta hakura ta zura wa sarautar Allah ido. Gashi ta karbe mukullin store din don ko hanyar
basa yi amma kullum sai sun dafa abinci mai rai da lafiya. Ta saka Abba a gaba a kan lallai in ta basu
abinci bayarwa suke don haka ita za ta daina, don haka tana zaune a falon ya kirawo Madu ya shigo har
falo ya zauna a gaban Abban yace

“Gani Abba.”

“Kai antinku ta ce kuna girka abincin buda baki, wai in kun karbi na wajenta bayarwa kuke yi.”

“A’a Abba, kai kadai Salim yake wa abinci kuma Ya Baba ne yace ya dinga yi kullum, wanda muka karba a
nan mu shi muke ci ba ma bayarwa.”

Abba ya kalleta ba tare da yace komai ba alamar kin ji abinda yace ko, ta dauke kai tana zumbura baki.
Kafin tace wani abu Madu yace

“Sai dai in ka ce sai mu dinga dafawa.”

Yayi sauri ya daga masa hannu

“A’ah, za ku ci gaba da karba, babu matsala.”

Ya sallami Madu ya tashi ya fice, ya mayar da hankalinshi ya dubi Saudah yace

“Kin gani ko? Ya za ki ce ba sa ci, sai dai in baza ki dafa musu abincin ba. Dole fa ki yi hakuri da yaran nan
don kin san dai da uwarsu tana nan ba za su nemi komai a wajenki ba, ki cigaba da taya mu addu’a Allah
ya sa a ganta.”

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro ta sunkuyar da kai tace

“Ai shike nan.”

Wato yanzu tana ji tana gani zancensu shine gaskiya kenan itace makaryaciya, kenan haka za ta cigaba
da girka musu abinci suna bayarwa. Tashi tayi ta bar masa wajen saboda yanda ta gane idan ta cigaba da
zama lallai za ta iya gaya masa abubuwan da suke ranta.

Saura kwana hudu sallah suna zaune a kasuwa Abba ya kirawo Madu ya bashi kudi ya je kasuwa ya yiwo
musu cefane; kayan miya, kifi, kaza, nama ga vegetables haka aka siyo komai da yawa sosai, sugar, zobo,
aya, agushi duka haka. Sannan ya yi waya daga kasuwar aka kai buhunan shinkafa aka lode a store.
Bayan Madu ya gama wannan sayayyar ya nufi gida. Yana shiga gidan ya kirawo Bala suka sauke kayan a
tsakar gida ya dubeshi yana nuna tagar Saudah yace
“Gata nan a taga ka gaya mata ta zo ta kwashe ta kai store.”

Ya juya ya shige falo, Bala yaje ya buga mata kofa tazo ta bude store din haka ya dinga kwasan kayan
tana nuna masa inda zai saka yana kaiwa, aikin da da duk su Salim ne suke yi. Madu yana shiga ya zauna
suna hira da su Khalifa, jimawa kadan Abba ya kirawo shi yana dagawa yace

“Abba yanzu na gama sauke kayan tahowa zan yi.”

“A’a kar ka taho ma, munje wata janaiza da su Alhaji Musa za su sauke ni yanzu na gaji gara na dan huta,
sai dai ka koma kasuwar in an tashi ka taho.”

“Toh Abba a dawo lafiya, nima yanzu zan tafi.”

Suna ajiye waya kuwa ya tashi ya koma kasuwar.




Tsaf aka kwashe kayan nan Saudah tana tsaye tana nuna inda za a ajiye mata a store da yake ba wani
abincin kirki take dafawa ba kuma akwai abinci ma dayawa a ciki, haka dai aka jibga kayan wasu kan
wasu. Bayan ta shiga daki ta zauna tana tunani. Tana son ta debarwa Ummanta kaji da nama ko ta sami
na miyar Sallah, duk da ta san kamar yanda ya saba duk shekara Abban zai bayar da kudi dubu goma
yace ta bawa su Umma suyi cefanen sallah sannan kuma ya basu turamen zani. Toh amma tunda naman
yana nan a jibge idan ma ta diba ba ganewa zai yi ba sannan kuma ita Umman sai tayi wata hidimar da
kudin, gashi ma tace za a samo mata taimako ta san za a bukaci kudi duk da sai ta ma san yanda tayi ta
nemi kari a wajen Abban. Har ta yanke shawarar gobe za ta dibarwa Umman sai kuma taga gara ta diba
yau kafin Abban ya dawo yaga yawan kayan, don haka ta bugawa Umman waya tace

“Umma ki turo yaronki ya zo ya karbar miki sako.”

“Toh yanzu zai taho. Me na samu ne?”

“Nama ne daman Umma naga an siyo shi da yawa shine nace bari na debar muku na miyar Sallah.”

“Lallai gidan ya fara samuwa, yanzu baki da ‘yar sa ido ko?”

Tayi murmushi tace

“Uhm, ba laifi Umma amma da sauran aiki. Kin san da itace take tsayawa a sauke kayan ita da yaranta
yanzu kuma kin ga komai yana hannuna.”

“Da kyau, sai ma an gama aiki sannan gidan zai kara samuwa.”

Suka yi sallama Umma ta turo almajirinta wanda daman ya san gidan don ya saba zuwa kawo wa Saudah
sakon Umman. Da yake Malam Bala ya san yaron yana zuwa ya bude masa gate ya shige.

A falo ya same ta tana jiranshi, tun kafin ya zo ta riga ta ware kaji guda hudu da kuma nama ta hada a
leda, ta auna suga kwano daya da fulawa kwano daya. Da suga da fulawa sai ta hadasu ta saka a babbar
bakar leda ta daure ta dora masa a ka, shi kuma naman da kazar sai ta saka masa a buhun semovita ya
dauka a hannunsa, ttac
“Don Allah Sadi kar ka tsaya kayi sauri ka kai mata.”

Ya amsa ya fito, yana gama rufe kofar Abba ya bude gate din ya shigo, yana sako kafarshi cikin gidan shi
kuma Sadi ya zo saukowa daga kan barandar Saudah sai kafar shi turgude ya tafi taga-taga kamar zai
fadi. Kafin ya kai kasa ledar kanshi ta fado kasa da karfi ta fashe, sugan da fulawar suka zube a kan
interlock yayinda ya sa hannunshi ya dafe kasa don kada fuskarshi ta baugi kasa. Abba da yake karasowa
yayi masa tsawa

“Kai kula mana kar kaje ka ji ciwo.”

Daidai nan Khalifa da Salim suka fito don yi masa sannu da zuwa da suka ga abinda yake faruwa sai suka
tsaya suna kallo. Sadi ya mike tsaye yana kallon sugan da fulawar a kasa yana shafa kai, Abban ya dube
shi yace

“Ina za ka haka?”

“Sako na karba daman.”

Ya kalli farin abun da yake kasa yace

“Wannan ai suga ne, wa ka kawowa suga haka?”

“Ba kawowa nayi ba Saude ce ta bayar a kaiwa Innarta.”

“Allah ya sauwake.”

Ya juya ya kwalawa Malam Bala kira yace

“A zo a gyara wajen nan kar a janyo mana sha zumamu.”

Har ya daga kafa zai huce sai ya kula da buhun hannun Sadi yace

“Meye kuma wannan a cikin buhun?”

Ya shafa kai yace

“Eye”

Abba ya karasa ya kama hannun buhun ya bude ya leka ya hango kaji masu kankara a sama, sai da yaga
wannan kajin sannan hankalinshi ya kawo masa abinda yake faruwa. Wato abicinshi Saudah take kwasa
tana kaiwa gidansu kenan? Lallai ta tabbata butulu, domin duk da gidan nasu ba matalauta bane amma
kullum cikin yiwa ummanta kyautar kudi yake. Gashi da sallah ka’ida sai ya bata dubu goma, duk lokacin
da yaje gaisheta kuma ko yaje ajiye Saudan sai ya bata kudi yace ta bawa Umma. Abincin ma kuma bai
fasa kai musu ba, ga su lemo da ruwan roba. Haka ya kewaye Sadi ya shige bayan ya amsa sannu da
zuwan da su Khalifa suke masa.

Babu kowa a falon domin tana hango abinda yake faruwa ta taga, tana ta addu’a kada Abban ya ga
abinda Sadi yake dauke da shi kawai sai ta hango shi yayi bari. Ta kama zarya a falon don bata son Abba
ya san ta bayar da wadannan kayan amma gashi sun bare a gabanshi, ta dafe kai ta shige daki da ta
hango Abban ya nufo falon. Yana shigowa sai yara a falon, nan da nan suka taso suna yi masa oyoyo. Ya
sallamesu ya kwala mata kira yana jiyota ta amsa daga daki don haka sai ya huce nashi dakin ya san za ta
biyo shi. Sai da ta gama bitar abinda za ta ce masa sanan ta fito jiki babu kwari ta tura kofar ta shige da
sallama.

“Wancan yaron wa ya bashi kayan abinci haka wai ya kaiwa innarki?”

Yanda ta diririce ya tabbatar masa bata da gaskiya, sai da ta karasa gefen gadon ta zauna sannan tace

“Uhm, daman saya mata nayi saboda hidimar sallah shine nace ta turoshi ya karba.”

Duk yanda ya so su hada ido ta ki tsayawa, yace

“Yanzu ke a ina kika sami kudin sayen wannan kayan harda kaji wajen guda hudu?”

Ta sunkuyar da kai tace

“Uhm uhm…”

“Ban san tun yaushe kika fara kwasar min abinci kina kaiwa gidanku ba amma ko ban gaya miki ba na san
kin san sata ce abinda kika yi. Duk da na san ba a rasa yanda za ayi a gidan naku ba amma kullum cikin
yiwa Umman aike nake. Buhun shinkafa na bata da azumin nan da kudi dubu biyar, ko last week da na
kai ku da safe sai da na baki dubu biyu ki bata kuma kin san da sallah ma sai na bata amma shine daga
kawo kayan har kin yi waya kin fara rabarwa.”

Da kyar ta samo muryarta cikin rawar murya tace

“Wallahi ban taba dibar maka komai ba wannan ne kawai, kuma shima kuskure ne.”

Ya kalleta ya dauke kai

“Ba zan iya ganewa ba ai, amma idan halin ki ne za ki

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login