Showing 48001 words to 51000 words out of 196754 words
Chapter 17 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
dai ka ji me Daddy zai ce kafin ka fara murnar.”
“Ai Daddy namu ne in sha Allah da ya gan ni zai gane ni kadai na dace dake duk duniya.”
Haka suka karasa hirarrakinsu cikin nishadi da jin dadi, duk wata damuwa da ya dawo da ita wannan
albishir da tayi masa sai da ya sa shi farin ciki domin ya dade yana so ayi maganar aurensu tunda yanzu ya
fi shekara da fara aiki kuma yana ganin lokaci yayi. Bai taba yin wata budurwa ba sai a kan Khairiyya, bai
dade da fara aiki ba suka hadu a nan Abujan. Mahaifinta babban ma’aikaci ne suna zaune a unguwar
Maitama. A jami’ar Bayero ta Kano take karatunta don ko lokacin da suka hadu tana level 3, a yanzu kuma
ta riga ta fara bautar kasa a nan Abujan shi yasa mahaifinta ya yi mata maganar auren.
Duk da bai so komawa Kano da wuri ba amma yanzu wannan maganar ta Khairiyya ta sa yana tunanin zai
koma nan da sati biyu domin yayiwa Abba da Mommy maganar Khairiyya, don in banda Ahmad babu
wanda ma ya san yana da budurwa. Sai da ya kwana biyu a Abuja sannan yayiwa Ahmad waya ya ce masa
zai turo a karbi motar
“Me za ka yi ita kuma? Ka bari na koma da ita mana.”
Yace
“Ba komai akwai amfanin da zan yi da ita.”
“Kai! Amma wallahi da ka bari na koma da ita wallahi da dole a dinga kai Mommy unguwa a cikinta in ba
haka ba sai dai kowa ya tafi gidan ubanshi wallahi.”
“Kar ka damu ba komai in Sha Allah. Upper week zan je gidan in Sha Allah zan maka waya sai mu huce tare
don a mota za mu je.”
Haka sukayi sallama Ahmad ya na ta zumbura baki saboda shi ya shirya tsiya. Amma haka ya hakura ya
bayar da motar ba tare da Baban ya gaya masa abinda zai yi da ita ba. Itama Mommy ta shiga damuwa
kwarai da gaske gani take kamar fushi suka yi suka bar gidan, musamman da taga an haura sati Ahmad bai
zo weekend ba. Ba wai tana tsoron suyi fushi ne ba amma dai ba ta so a samu matsalar da za ta shiga
tsakaninsu da mahaifinsu, ko ba komai shi ya haifesu kuma idan suka sami matsala zai taba ci gaban da
suke samu a rayuwa saboda bin iyaye bin Allah ne.
Bayan ta idar da sallar isha’I ta zuba abincinta ta zauna taci, da yake ba itace da girki ba bata bukatar jiran
Abba. Sai bayan ta gama cin abincin ya shigo ya duba su da gidan suka dan taba hira sannan ya fice ya
koma wajen Saudah ya zauna a falo ya kunna tasahar BBC. Ta duba agogo wayarta karfe 9:30pm, ta shiga
nemo lambar Ahmad ta kirashi sai ta jiyo hayaniyar Bala maigadi yana bode gate. Yanda ta jiyo shewarsa
ta tabbatar shi da Ahmad ne daga baya kuma ta gane harda Baba ma. Sai da suka tambayi Bala maigadi
inda Abban yake ya tabbatar musu yana wajen Saudah, sun ji dadi domin dama sun so su sameshi a
gabanta. Nan da nan kuwa suka bawa Malam Bala jakunkunansu ya shigar dasu gida suka huce wajen
Abba.
Yana zaune a falon yayinda Saudah take zaune a kusa dashi tana karatu. Bayan ya amsa sallamarsu ya
gyara zamansa da fara’arsa ya tare su, suka samu guri kusa da kafarshi a kan kafet suka zauna. Suka gaishe
da Abban sannan suka gaisheta. Ya dube su da fara sannan ya dubi Baba yace
“Yau girma ne ya tashi ka biya ka taho da kanin naka? Ina motar kuma ban ji shigowarta ba.”
“Abba ai na siyar da ita, in ya so in na tashi aure sai na sayi wata.”
Sai da jikinshi yayi sanyi sannan ya amsa cike da nadama
“Me ya sa baka gaya min ba, ai da ka dawo da ita sai ka barta a nan in ya so in za ka hau sai ka dauka. Ban
ji dadi ba.”
Yayi murmushi yace
“Babu komai Abba in Sha Allah kwanan nan zan sake siyan wata.”
“Ban ji dadi ba wallahi, Allah ya nuna mana lokacin. Ta Kadunan ka biya kuka taho tare?”
Suka yi dariya sannan Baba yace
“A’a Abba a hanya muka hadu da yake da wuri muka shigo sai muka huce Jigawa mu ka gaida Anti Baraka,
idan za mu huce kuma sai na tsaya na gaida Baffa Atiku da Baba Mubarak.”
Yace
“Toh da kyau, Ma Sha Allah. Allah ya bar zumunci. Ya Anti Barakan da iyalanta?”
“Lafiya kalau suke Abba suna gaishe ku.”
“Toh muna amsawa.”
Suka dan yi shiru. Baba karami ne ya zaro takardu daga aljihunsa ya mikawa Abban yana cewa
“Abba na biyawa Mommy Umra.”
Take murmushin jin dadi ya bayyana a fuskarsa yayinda ita kuma Sauda dake gefe ta ‘bata rai
“Kai ma sha Allah, Alhamdulillah na ji dadi wallahi. Ka fanshe ni kenan don nayi mata alkawari kuma da
yake tare nake son mu tafi hidimomi sun hana ni tafiyar. Ma sha Allah.”
Ahmad yace
“Ka bari kawai Abba ni zan biya maka.”
Ya kara gyara zama ya kyalkyale da dariyar jin dadi yace
“Allah Amadu na kace na bar ma wata fafutukar tara kudi biya min za ka yi. Toh Allah ya nufa, Allah ya
baku arziki mai albarka ya baku iyalai na gari.”
Suka amsa da Amin suka karbi takardun suka yi masa sallama suka huce. Suna shiga wajen Mommy suka
sameta da ‘yan uwansu suna hira, a nan suka zauna ana ta maraba. Baba ne yayi gyaran murya ya mika
mata takardun yace
“Mommy umra na biya miki.”
Ta karba da baki bude tana mamaki tace
“Allah Baba na.”
Kawai sai ji tayi hawaye suna bin idonta saboda farin ciki. Ta rike hannunshi ta kalleshi tace
“Na ji dadi Babana, na gode. Allah ya yi maka albarka.”
Duka suka amsa da Amin
“Kai da za ka fara biyawa kanka aikin hajji sai ka fara dani Baba?”
“Ba komai Mommy in sha Allahu badi da ni za a yi aikin hajjin.”
Tace
“Amin ya Allah, Allah ya nuna mana.”
Khalifa ya ce
“Mommy zan baki sautu ki siyowa Auta shashashan Madina.”
Suka yi ta dariya Auta yana bata rai.
Bayan sun fito daga wajen Abba kuwa sai ya dubi Saudah yace
“Baki ji abun arziki bane baki ce komai ba, yaran nan sai son barka wallahi.”
Tace
“Na ji. Allah ya kai ‘yan baya.”
Yace
“Amin”
Tace
“Ni sai yaushe za a bani tawa kujerar Hajin?”
“Haji ai kiran Allah ne ki dai cigaba da addu’a Allah ya kira ki.”
Yanayin yanda ya bata amsa ya nuna mata ba zai dauki rigimarta ba don haka sai kawai ta tashi ta shige
dakinta. Ko bi ta kanta bai yi ba ya kashingida ya ci gaba da kallonsa. Ya riga yayiwa kanshi alkawarin ba
zai sake yi mata alkawarin wani abu ba domin tunda tana amarya yayi mata alkawarin saitin gold shine
har yanzu da bai samu ya siya ba duk inda taga gold sai ta yi masa gori, shi kuma ya rabu da ita ne yaga
iyakar gorin nata. Sai wajen 10:30pm sannan ya tashi ya fito ya nufi wajen Rabi.
A daki ya sameta a kan dadduma ta idar da shafa’I da witri, bayan ta amsa sallamarshi ya zauna a gefen
gadon yana fuskantar ta yace
“Sabuwar Hajiya.”
Ta kyalkyale da dariya.
“Yarona ya fanshe ni ko? Yanzu lallabaki kawai zan fara yi ki tafi da ni ko jaka na rike miki.”
Ta harare shi tace
“Babu wanda ya fanshe ka sai dai ka fanshi kanka in ba haka ina nan ina
Jira.”
Ya yi yar dariya ya gyara zama yace
“Wallahi hidimomi ne suka yi min yawa. Kin san idan business yana garawa ana ta samun ayyuka ba zan
tafi na bar yara ba shi yasa kika ga kwana biyu na kasa motsawa, amma in sha Allah kwanan nan ko bamu
je Umra ba za mu je Dubai in Sha Allah.”
“Toh Allah ya nufa.”
“Amin. Yaushe ne yace tafiyar taku?”
“Sati mai zuwa yace min.”
“Ma Sha Allah, Allah ya nuna mana.”
Yayi mata sallama ya fice ya koma inda zai kwana.
Duk yanda Saudah ta so ta ce wani abu a kan tafiyar nan bai bata dama ba, gashi kuma tana shirin fara
jarrabawa bata son ta ja rigima ta kasa samun natsuwar yin karatun don haka ta bari komai ya huce.
Sai da su Baba karami suka shirya za su koma sannan ya yiwa Abba maganar Khairiyya, da yake ita Mommy
ya riga ya gaya mata ta waya tun kafin ya zo. Bayan Abban ya nuna farin cikinsa sai yace da Baban idan
sun isa Kaduna ya gayawa Baffa Atiku in ya so za suyi waya. Don haka Kaduna suka tsaya bayan ya yiwa
Baffa Atikun bayani, ya tambayesu iyayenta da garinsu duk ya gaya masa sannan ya huce Abuja.
Saura kwana biyu su tashi Baraka ta iso Kanon, ta riga ta saba sauka a hotel tunda iyayensu suka rasu
musamman da yake suna yawan zuwa da maigidanta don haka yanzun ma a hotel ta sauka. Bayan ta huta
kuma ta fice sai gidan Rabi. Nan suka zauna suka yi ta hirar yaushe gamo, har suka zo kan labarin tafiya
Umra. Baraka tace
“Ai wallahi Baba Allah yayi masa albarka, ko ni ma ina alfahari da shi don kuwa ya haifu sai dai muce shima
Allah ya bashi iyalai na gari.”
Mommy tace
“Amin. Gaskiyar ki ni ya bani mamaki, kuma na ji dadi.”
Baraka ta gyara zama ta riko hannun Mommy tace
“Toh bari in kara miki wani albishir din.”
Murmushinta ya fadada, ta sa hannuwanta biyun ta rufe bakinta ta zaro ido tana kallonta. Baraka ta kara
gyara zama sannan tace
“Tare za mu Umrar nan.”
Sai da suka yi kara sannan suka rungume juna, bayan sun saki juna kuma da suka tuna ashe sun girma da
irin wannan ihun sai suka hada ido suka tuntsire da dariya. Mommy tace
“Wai don Allah da gaske.”
Tace
“Allah kuwa. Ai wancan satin da su Baban suka zo dama muna shirin tafiya Umra daga nan mu huce Dubai
da ni da Baban su Ummi toh kuma sai wata tafiyar aiki ta taso musu, next week za su huce UK shi kanshi
bai san lokacin da zasu dawo ba. Sai yace na tafi ko kuma shi ya bawa Ummi ko Nana tashi kujerar, su
kuma daga mai ciki sai mai goyo, nima ina Shirin fasawa su Baba suka zo don haka kawai nace tare za mu
tafi.”
Sai da suka tafa sannan Mommy tace
“Amma na ji dadi ba kadan ba, ko ba komai ke ‘yar gari ce na huta da tambaya.”
Tace
“Toh tsaya ki ji mana daya albishir din.”
Ta bude baki tana mamaki tace
“Au wai da saura?”
Baraka ta dafa cinyarta tace
“Daga can Dubai za mu huce, Baban su Ummi ya bar min ticket dinshi na bawa yara ni kuma ke na bawa.”
Tana rufe baki za ta yi magana sai kwalla, kawai sai ta fada jikin Baraka suka rungume juna. Nan suka zauna
suka yi ta hirarsu har dare yayi sanna suka yi sallama Baraka ta koma masaukinta. Da yake a wajenta zai
kwana sai da ta bari ya ci abinci ya huta sanna ta yi masa albirshi ta nuna masa takardun tafiya Dubai. Cike
da mamaki da jin dadi yace
“Toh ai da sai ki ce mata aah saboda kinyi alkawarin da ni za ki je Dubai.”
Ta harare shi tana murmushi, kafin tayi magana yace
“Baraka bata kyauta min ba ta dai kusa ta kyauta.”
“Ai sai ka zabi daya, an kyauta ko ba’a kyauta ba.”
Yayi dariya sannan ya bata amsa
“Ba zan zaba ba saboda wannan tafiya tace tayi min shigar sauri, amma babu laifi. Zan kirata in sha Allah
nayi mata godiya, Allah ya bar zumunci.”
Tace
“Amin.”
Haka suka kwana suna farin ciki yara ma sunata murna. Auta ne yake tambayarta
“Mommy ni a wajen wa za ki barni?”
Ta kyalkyale da dariya tace
“A gidan ubanka mana.”
Khalifa da Salim suka sa shi a gaba suna yi masa dariya wai shi har yanzu baby ne.
Washe gari da safe suna zaune a falo suna cin abinci aka yiwa Abba waya ya tashi ya fita. Bai dade da fita
ba aka bude gate aka shigo da mota kirar Honda Accord 2017 baka kirin da ita sai sheki take yi, ya nuna
gareji aka ajiye masa ita sannan ya karbi mukullin ya sallami bakon shi kuma ya koma ciki. Yana shigowa
Auta yace
“Abba mota ka siya?”
Yace
“Eh. Ka ga tunda Mommy za ta tafi Saudi ta barmu mun sami ta zaga gari ko?”
Yace
“Haka ne Abba, yau ita za ka kaini makaranta ma ko?”
“A’ah sarkin zumudi, toh ba tamu bace ta ajiya ce.”
Khalifa ya kyalkyale da dariya yana yiwa Auta gwalo. Ita kuwa Mommy da yake a gabanta aka yi wannan
hirar bata ma yi maganar motar ba. Kafin su gama cin abincinsu ya fito ya shiga wajen Saudah domin ya
sallameta ya fita. Yana shiga ya sameta a falo tana karatu yaran kuma suna daki su da Zulaiha. Bayan ta
amsa sallamarshi tace
“Na ga an shigo da dalleliyar mota ko tawan ce ta zo.”
Ya kyalkyale da dariya yace
“Toh ko kece mai idon cin naira wannan ba taki bace, tawa ce na saya ko zan sami wata ‘yar budurwa
candy bana na tsarata na yo amarya.”
Nan da nan ta daina fara’ar ta zumbura baki tace
“Kai yanzu sai ka kara aure.”
Ya ja da baya ya baza Babbar rigarshi yace
“Toh ke ya kika gani, ai yanzu babu abinda yayi min saura sai amarya kawai.”
Ta ‘dan yi dariyar yake ta raba ta gefenshi za ta huce yayinda ya ce mata
“Bari in yi sauri ‘yan makaranta suna hucewa ko Allah zai sa a dace.”
Kafin tace wani abu ya fice ya barta tana kwafa. Sai da ya sauke su a makarantar ya huce ya zauna sannan
ya zaro waya ya kira Mommy , bayan ta amsa sallamarshi tace
“Me ka manta ne?”
Yace
“Ke na manta.”
Tayi dariya tace
“Toh ai gani ko tahowa zan yi.”
Shima dariyar yayi sannan yace
“Mantawa nayi na baki kudin shopping in kun je Dubai, gashi ma ke baki da account ko ta account din
Barakan zan tura miki.”
Tace
“A’ah harda wani kudin shopping, Madallah na gode, Allah ya kara arziki. Bari na kirawo Barakan naji.”
“Toh Babu laifi, ina sauraronki.”
Bayan sun yi sallama ta kira Barakan suka gama magana sannan ta tura masa account number din da ta
turo mata. Minti kadan Barakan ta kirawo ta, tana dauka tace
“Kin san kuwa nawai ya turo?”
Tace
“A’ah”
“Dubu dari biyu da hamsin fa, gaskiya ya burge mu. Ga kudin da ke hannunmu gashi jiya ban gaya miki ba
da ina jira sai mun hadu Ahmad ma dubu ashirin ya turo min wai na baki ki kara.”
“Kai ma sha Allah, ina ga mutuminki kunya dai yaji yayi wannan kyautar, kin san tun tuni yayi min alkawarin
Dubai din amma ya koma yayi shiru. Lallai bari na kirashi na yi godiya kafin ya dawo na kara.”
Suka yi sallama suna titsira dariya.
Washe gari da azahar jirginsu ya tashi sai Saudiya inda za su yi sati uku su huce Dubai su yi sati daya. Duk
da Mommy ta taba zuwa Saudiya ita da Abban amma wannan tafiyar da ban take, dadin da take ji ba zai
misaltu ba. Sannan kuma ga Baraka a gefenta, godewa Allah kawai take musamman da ta san za ta je
dakin Allah ta yi ibada a nutse, duk wasu bukatunta ta roka tayi azumi tayi sallah.
Kwanan su Mommy biyu da tafiya Zulaiha ta gama jarrabawa, nan da nan kuwa ta shirya ta tafi gida. Hutun
nasu da ‘dan tsaho don haka sati biyu ta tafi da shirin yi. Ko da wasa bata bari sun zauna su biyu da
Ummanta ba, har ta so ta gane gudunta Zulaihan take yi. Bayan kwana biyu da zuwanta gidan tana kwance
a dakinsu ita da kannenta duk sun yi bacci ita kuma tana chatting a waya Umman ta ritsa ta, bata ji
tahowarta saboda hankalinta yana kan waya sai kawai ji tayi tace
“Yauwa Zulaiha zo nan ina jiranki a falo.”
Babu yanda zata yi don ta riga ta juyo sun yi ido biyu da Umman balle tace bacci take yi don haka ta taso
ta fito, ta nemi guri kusa da Umman ta zauna tana ta wani sunkuyar da kai. Cikin zumudi Umman tace
“Ya maganarmu ne na naji shiru, kin yi amfani da kayan nan kuwa?”
Ta kalli Umman ta kara sunkuyar da kanta, idonta ya ciko da kwalla sannan tace
“Uhm Umma gaskiya zubewa sukayi.”
Ta dora hannu a ka tace
“Subhanallah yanzu duka kwallin da turaren kika zubar don wulakanci Zulaiha, kin san kuwa nawa na biya
na samo kayan na. Shi ke nan kin min sawarwara do kula ke ba son auren nan kike yi ba.”
Cikin sauri tace
“Ba haka bane Umma, wallahi na yi amfani da su amma a lokacin bamu hadu da Baban ba sai Ahmad muka
hadu dashi, da na koma dakin kuma garin na kwashe su daga kan mudubi suka fado kwalbar turaren ma
fashewa tayi kwallin kuma ya watse a kasa.”
Binta kawai take yi da kallon takaici, sai da ta nisa sannan ta nuna ta da yatsa tace
“Idan kika kuma yi min zancen Ahmad in na rufe ki da duka sai kin kasa tashi, yau na ga ikon Allah. Ana
son a samo miki hutu garin shegiyar rawar kan tsiya kina son ki watsa min tsakuwa a ido.”
Ta share kwallar da take makale a idonta tace
“Toh Umma yanzu ya za a yi?”
A fusace tana nuna ta tace
“Ubanki za a yi, kin ji ko? Nace ubanki za a yi. Tashi ki bace min da gani kafin takaici ya sa na rufe ki da
duka.”
Nan da nan kuwa ta tsahi da sauri ta fada dakin ta bar Sa’a a zaune tana tunanin mafita. Bata ga wani miji
da ya dace da Zulaiha ba bayan Baba, ko babu komai tana son tayi amfani da wannan damar ta samu
kasonta a dukiyar yayanta da take zargin Rabi ta hanata samu. Sannan kuma idan ta sami yanda take so
toh ba Yayan nata ba hatta ‘yayan Rabin ma so take su dawo hannunta. Idan ta samu suka aurawa babban
Zulaiha toh ta nan za su sami lagon su gaba daya, haka ta kwana tana tunanin mafita domin ji take a ranta
wannan auren babu fashi. Matsalar dai guda ‘daya ce bata da kudi kuma ba ta da hanyar samun su yanzu.
Haka ta kwana tana ta juyi, bacci yana fizgarta tana farkawa firgigit saboda tsabar lissafi, sai can wajen
asuba sannan dabara ta fado mata.
Gari yana wayewa ta gayawa babansu Zulaiha za ta je Kaduna wajen kaninta Atiku, ba tare da wani musu
ba ya barta domin tun tuni ya daina hanata fita saboda ko ya hanatan ma sai ta je. Ta dai san ba zai bata
kudin mota ba don haka tun da sassafe ta tafi wajen Sala dillaliya ta aro dubu biyu tunda ta san in ta je sai
ya bata kudin mota harda na kashewa. Bayan ta gama shirya ta yiwa Zulaiha sallama ta gama yi mata
bayanin hidimar gidan domin kwana za
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good