Showing 18001 words to 21000 words out of 196754 words

Chapter 7 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15415

zancen ba har kawo yanzu da yara suke gaya mata ana
shirin saka Saudah (amarya) a jami’a. Duk yanda ta so kada tayi kuka amma idanunta sun ki bata hadin
kai, sai da ta shiga daki ta share hawaye. A zuciyarta tace

‘wato da yake ni jaka ya auro ya kulle ni a gida bani da aiki sai hidimarsa da ta yaransa, amma yanzu da
yake ya auro matar so gashi nan dan da na haifa aka saka yayi mata shirin shiga jami’a. Ai shike nan.’

Ta daga hannu ta ce

‘Allah kai ka dora min wanna kaddarar Allah ka kara min hakuri da juriya.’
Ta goge hawayenta ta koma ta ci gaba da hidimarta.

……..

Gobe ba ita ce da girki ba don haka idan ya ci abincin safe toh Saudah ce za ta yi masa abincin rana wanda
zai tafi da shi kasuwa. Ya cinye tuwonshi sannan ya cika kofi da zobo yana kurba yana mata hira tana amsa
shi cikin nishadi.

“Yauwa, da Allah gobe ki dafa min abincin rana in tafi da shi kasuwa.”

Ta kalleshi da mamaki

“Saudan lafiya take? Ko ka manta gobe itace da aiki?”

“Uhm! Ban manta ba. Za ta fita ne da sassafe wajen 6:30, shi ya sa ba za ta sami lokaci ba.”

Ta dan gyara zama kafin ta bashi amsa

“Allah sarki ai za ta iya yi ma ko kafin asuba ne in ka tashi sai ka tafi da shi.”

Sai da ya bata rai sannan ya bata amsa

“Yanzu ba za kiyi ba kenan?”

Kafin ta bashi amsa ya ci gaba

“Jarrabawa za ta yi itama shi yasa ta roke ni Allah a kan ba zata iya yi ba, don ma kwana biyun nan idan na
ci abincin kasuwar bata min ciki yake yi ne da ba za ki ji ba.”

“Jarrabawa kuma? Dama tana makaranta ne?”

“Yara basu gaya miki ba, ai JAMB za ta yi gobe in Allah ya kai mu.”

Ta kalle shi ta kawar da kai

“Allah sarki, Allah ya bada sa’a.”

Daga nan aka yi masa waya ya tashi ya koma daki yana amsawa.

Da gari ya waye aka taso Ahmad ya zo ya kai Saudah jarrabawa cewa yayi shima yana da test da karfe 8 in
ya fita zai makara tunda center dinta da nisa.

“Ina Madu? Je ka taso shi ya zo ya kaita.”

“Abba ai bashi da lafiya da zazzabi ya kwana, ko masallaci ma bai je ba da asuba.”

Ahmad ya bashi amsa.

Ya wuce ya nufi dakin don ya gani da idonsa. Ai kuwa a cikin bargo ya tarar da shi, har rawar dari yake yi.
Ya yi masa sannu, sannan ya bawa Ahmad umarnin da zarar ya dawo daga makaranta ya kaishi asibiti. A
karshe dai da kanshi ya dauki mota ya tafi kai ta. Yana fita sai ga Madu ya fito ya fada kicin. Katon bredi ya
dauko ya hado shayi mai kauri cikin babban kofi ya fito zai shige daki, har ya kusa kofar ta ce

“Zo nan don ubanka.”
Ya juyo yana zazzare Ido

“Mommy don girman Allah kada ki ce komai, abinci kawai zan ci na koma na kwanta don Allah ki yi hakuri.”

“Dama lafiyarka kalau kenan ake kiranka danuwanka na cewa baka da lafiya, ashe bakinku daya.”

Ta fada tana harararsa.

“Shayin nan kawai zan sha na kwanta Mommy, lafiyarma ba isa ta tayi ba don Allah kada ki ce komai.”

Sai da ta kare masa harara sannan da yake ita ma bata cikin yanayi na jin dadi ta ce dashi

“Allah ya shirye ku.”

“Yauwa Mommy, Amin ya Allah. Bari in je in sha shayin kafin su dawo.”

Ya wuce yana sauri ya rufo kofa.

Daga nan ta fahimci cewa dabara suka hada shi da Ahmad don kar su kai matar babansu jarrabawa. Da
wani abun ne tabbas sai ta yi musu fada, amma yanzu kam bata da lokacin kowa ma su karata. Sai wajen
8:30 ya dawo gidan. Nan da nan yayi wanka ya karya, ya gama shirin fita. A dakin ta ya same ta a zaune a
gefen gadon tana nunke kayanta da aka wanke jiya.

“Ina abincin ranar?” Ya tambaye ta yana daga tsaye.

“Ai bata kawo nan ba ko a can ta ajiye maka?” ta fada cikin halin ko in kula.

“Jiya ai na ce miki ki dafa min abincin rana ko?”

“Ai ban ce maka zan dafa ba, tunda ba girki na bane.”

Ta bashi amsa.

“Yanzu ba za kiyi mata uziri tayi jarrabawa ba, idan kin yi abincin ai ba ita kika yi wa ba ko?”

“Tunda ita ce me kan karatu sai ta tafi jarrabawa ni kuma me kan kwando sai na zauna nayi mata girki ko?
Idan dai kai ne Allah ya kai mu jibi zan girka maka duk abinda kake so.”

Ya yi shiru yana mata kallon takaici, sai kuma ya juya a fusace ya banko mata kofar ya fice. Ta so a ce ya ci
gaba da jan zancen da duk abinda yake ranta sai ta amayar, amma ya fice ya barta. Ta ja tsaki kawai ta ci
gaba da abinda take yi. Duk yanda ta so a yi rigima wannan karon bai yiwu ba, domin fushin ma da ta zata
zai yi da ita bai yi ba sai faman binta yake yi a hankali. Don haka ita ma ta share ta hakura, amma tabbas
ta yi alkawari tana nan tana jiran ranar da za ta gaya masa irin cutarwar da yayi mata.

Ya aurota da kiruciyarta, duk wani buri da take da shi a rayuwarta ya rushe shi, tana ji tana gani haka ta
sadaukar da rayuwarta wajen yi masa duk abinda yake so, kula da gidansa, kuma rainon yayansa da kuma
biyan duk wata bukata tasa; amma daga karshe ya auro sa’ar ‘danta na uku sannan kuma duk wani abu
da take da buri a rayuwa ya dauka ya bawa wannan yarinyar. Harma wani so yake yi ta taya shi su so
matarsa.

Tabbas ta yadda da kaddara, kuma ta yarda hakan da Allah ya kaddara mata akwai tarin alkhairi a ciki;
amma tana nan tana jiran ranar da za ta karanta masa irin karatun da ya dade yana rubuta mata.
…………

Da yake makarantar da zata yi WAEC a nan kusa da gida ne a kas Saudah ta dinga tafiya. Haka ta karasa
jarrabawar da yaron ciki. Cikin ya zo mata da saukin laulayin, amma duk da haka daga lokacin da ya gane
tana da ciki ya ce karatu sai dai ta bari idan ta haihu. Ta yi kuka kamar ranta zai fita, duk wata dabara tata
ta kare.

……….

Tunda gari ya waye ya sanar da su cewa Aliko zai zo da amaryarsa, don haka a shirya taryarsu. Ita Rabi
dama ta san shi, Dan wajen Baffa Hassan ne. A Lagos yake aiki don haka shi yasa ba a ganishi sosai. Shi da
Uwargida Fatima da yaransu duk suna can Lagos din. Kafin a auri Saudah ne ya kara aure, ita kuma amaryar
da ya aura lecturer ce a jami’ar Bayero ta Kano don haka ya samar mata gida a Kano har zuwa lokacin da
zai samar mata aiki a Lagos din.

Sun shaku sosai da Abban Khalifa don tare suka taso, tare suka yi secondary da jami’a, sai da Aliko ya tafi
bautar kasa Lagos shi kuma Abban Khalifa ya tsaya a Jigawa sannan suka rabu. Har yanzu kuma suna tare
sosai domin ko a harkar kasuwancinsa ma Aliko yana taimakonsa kasancewarshi babban ma’aikacin banki.

Sai bayan magriba suka iso, da yake wajen Rabi ne a bakin kofa nan suka sauka. Sukayi ta raha da
barkwancinsu aka kawo musu abin tabawa. Yana wajen amarya don haka yayi masa waya ya zo ya raka su
wajen amarya. Suna shiga aka yi kiran isha’I don haka ya bar Karimatu a wajen Saudah suka tafi masallaci
da Abban Khalifa. Wannan ya ba su dama suka yi hira sosai har suka saba, duk da dai Karimatu ta girmewa
Saudah sosai. Bayan.sun dawo daga masallaci a bakin gate suka tsaya suna ta hirar yaushe gamo, dariyarsu
kawai kake jiyowa. Har suka gangaro kan zance amare, a nan ne yake gaya masa ai Karimatu lecturer ce
wani aikin ma yake nemar mata a Lagos din.

“Da yake ita bara ta gama makarantar ta dai yi JAMB amma kuma yanzu ciki ne da ita don haka da kyar za
ta samu wannan karatun.”

Sai da Aliko ya harare shi sannan ya bashi amsa

“Haba mutumina wai me yasa kake haka ne? Haka za kayi ta tara mata a gida babu ilimi? Sai wata fita ta
tashi kuma ka rasa wadda za ta raka ka taro?”

Nan dai ya saka shi a gaba yana nuna masa mahimmancin ilimin mace da bashi dalilan da za su sa ya bar
Saudah ta yi karatu. Haka suka gama hirarrakinsu Aliko ya dau matarsa suka tafi.

Maganganun Aliko sun yi masa tasiri don haka JAMB tana fitowa ba tare da wata doguwar magiya ba ya
amince.

Tare aka samo musu admission da Salim, sai dai shi course din shi Agricultural sxience ya samu ita kuma
ta sami applied biology, don haka yana new site tana old site. Suna daf da fara registration jami’oi suka
shiga yajin aiki. Sai da aka yi wata shida ana yajin don haka kafin su fara karatu Saudah ta haifi yarta
Rukayya, wadda ake wa lakabi da Nawwara.

Sai da yayi kamar ya hana saboda ko arba’in ba suyi ba aka fara registration, gashi duk yanda yake tunanin
zai sa Madu yayi mata registration abun ya ci tura, kullum uzurinshi da ban, wata ran har hakura yake da
kudin makaranta ya tafi haka saboda kar Abba ya ce yayi mata wani abu. Don haka dole ya hakura ya barta
ta goya Nawwara suke zuwa registration din a kan cewa idan an fara lecture tare za su dinga tafiya da mai
mata aiki tana rike mata ita. Nan da nan karatu ya kankama; haka za ta shirya ta dauki Nawwara da mai
aikin ta su tafi makaranta.

Tunda aka fara lissafin watan azumi take fargabar aikin azumi, ga karatu gashi kuma ana zabga rana.
Babban abinda yake damunta shine girkin abincin buda baki, domin shi Abban Khalifa abinci ake masa
sosai kamar na mutum goma a zuba a kuloli a kai musu majalisa, can suke shan ruwa. Ko wancan azumin
ma da bata haifi kowa ba ta sha matukar wahala, ga shi kullum ya dawo sai ya yi mitar wani abu da bai yi
daidai ba a girkin. Ga shi yanzu semester ta zo tsakiya karatu yayi zafi.

Ta same shi ta lallabashi a kan ita dai ya taimaka ya lallaba Rabi ta dinga yi masa abincin kaiwa majalisa in
ya so ita ta yi na sahur. Shi ma ya so hakan don kullum sai abokan cin abincin sun yi masa shakiyanci. Sai
ka ji ana gyaran murya ana

“Aci da Bismillah girkin sabon hannu ne.”

Idan kuma Rabi ce ta girka sai ka ji ana

“A luma hannu kawai, girki in na tsohon hannu ne ko a duhu ma ci ake komai daidai sai dai kawai mutum
ya tokare da bango saboda tsaro.”

Haka za suyi ta shakiyanci suna dariya. Don haka shi cikin rawar jiki ya amince zai cewa Rabi an bar mata
girkin azumi.

Ranar da aka kai azumin farko daman Rabi ce da girki, don haka nan da nan ita da yara suka gama komai.
Ta riga ta saba tun safe take wasu aiyukan da shirya kayan abincin, shi kuma wanke wanke azumi akwai
Salamatu; dattijuwa ce gidanta na nan cikin unguwa;ita take zuwa duka azumi tana mata wanke wanke
har sai an sallace. In ta zo da azahar sai ta yi wanke wanke ta tayata aiki in an kusa kira a zuba mata nata
ta tafi gida. Funkaso suka yi da farfesun kaza, sai fried rice da fish sauce ga Kuma ruwan shayi da kunun
gyada kowanne a flask da ban. Madu ya dauka suka kai kasuwa shi da Khalifa.

Sai wajen goma saura ya shigo gidan, wajen Rabin ya fara shiga tunda in ya fito wajen amarya zai kwana.
A dakinta ya same ta tana zaune a kan dadduma tana karatun kur’ani, da ruwan sanyi a jug da kofi a
gefenta.

Sai da ya fara zuba ruwan a kofi bayan ya amsa sannu da zuwanta, ya dago kai ya dube ta

“Ashe ruwa ne, ai da naga kofin yana gumi na zata zobo ne.”

Tayi dariya

“Ruwa ne kawai.”

Ya shanye ruwan ya gyara zama

“Ya gidan?”

“Lafiya Alhamdulillah.”

“Toh Madalla.”

Ya danyi jim sannan ya ce
“Yauwa! Da Allah abincin Shan ruwan nan ki dinga yi mana kawai, kin ga yarinyar nan ba sa dawowa
makaranta da wuri kuma dama abincin baya yin yanda nake so wallahi, gara dai ke din ki dinga yi.”

Ta kyalkyale da dariya harda kyakyatawa. Ita kanta ba dariya ta so yi ba kuma bata san me yasa ta dariyar
ba, watakil dai yanda yake maganar ne.Kafin ta gama dariyar mamaki ya bayyana a fuskarsa da takaici. Ya
Bude baki zai yi magana ta tare shi.

Sai da ta hade ranta kamar ba itace ta ke dariya yanzu ba

“Don Allah wai me ka mayar dani?”

Ta saba idan suka hada ido ita take fara kawar da nata idon musamman a irin wannan lokutan amman
yanzu sai shi ya gaji ya kawar da idonsa.

“Kamar yayaa me na mayar dake?”

Ta gyara zama ta ajiye kur’anin da ke hannunta

“Bari na yi maka fashin baki. Da yake ni ce jakar gida, ni a rayuwarta ba ni da wani abu da na iya, sai na
zauna a gida na rike mata auren ita kuma tana yawon barbada SI yasa za ka ce na yi girki ita ta je yawon
karatu ko?”

Ya kalleta da mamaki da alamar abun ya masa ciwo sanna ya bata amsa da tambaya

“Saudan ce take yawon barbada?”

Ta sake kallon idonshi kafin ta bashi amsa

“Eh mana. Ai duk matar da fita yawon karatu da aiki madadin ta zauna zaman aure da tarbiyyar yaranta
yawon barbada take yi.”

Ya gyara zama zai katse ta ta tare numfashinsa

“Ko ba haka ka fada ba lokacin da ni nake son yin karatun ka hanani? Da yake a lokacin ka san me kake ba
kamar mijin Yaya Shafa ba. Ko da yake ai ni ba so na kake ka auro ni ba dama me aiki ka samo, kan nawa
ba zai dau karatu ba sai hidimarka da ta yaranka.”

“Yanzu Rabi saboda na ce kiyi min abincin buda baki kike gaya min wannan maganganun?”

Ta gatsine baki sannan ta amsa

“Aah, toh ai ba karya na yi ba. Ni dama aka yiwa alkawarin idan an yi amarya zan huta, ko kuma hutun ma
bai dace dani ba kamar yanda karatu bai dace da ni ba.?”

Mamaki ya cika shi har ya kasa magana. Ita kuma ta kawar da kai ta kyaleshi. Sai da ya kosa da zaman
sannan ya ce

“Yanzu don tana karatu shi ya sa kike bakin ciki a kai? Kowa ai da kaddararsa, hana ki karatun da na yi ma
ai ya kamata ki gane ba da son rai na ba, lokacin ne ya chanza. Idan kaddararki ce babu karatu a ciki ba za
kiyi hakuri ki dauka ba?”

Ta muskuta ta bashi amsa
“Matarka bata kai yawan da zan yi bakin ciki da ita ba balle kuma wani mutum. Na dauki kaddarata saura
ita ta dauki kaddararta ta yi maka abinci ko kuma kai ka daukar mata kaddarar tata.”

Suka dan yi jim kowa da abinda yake ransa, ita ce ta karya shirun

“Ni fa tunda ka kara aure na gaya maka baka da matsala da ni ko mata hudu za ka aura, amma kar ka dora
min hidimar kowa. Kai da kanka ka yi min alkawarin hutu kuma yanzu sai a hanani hutawa?”

Bai bata amsa ba ya tashi ya fice. Duk da ta yi wa kanta alkawarin ta daina kuka a kan takaicinsa amma
yau sai da ta yi kuka. Abubuwa da yawa suka yi ta dawo mata.

Shi ma haka ya kwana yana juyi; tabbas ya san Rabi tana kaunar karatu kuma sai yanzu ya ke nadama. A
wancan lokacin bai ga amfanin karatun ba amma yanzu tabbas duniya ta canza, kuma ko ba komai ai gashi
nan yaranta suna karatun, wannan ma ai ya isa ta gode Allah, amma tana wasu maganganu.

Haka yayi ta juyi har asuba.

Tun lokacin sahur din ya gaya mata Rabi ba za tayi girki ba don haka kawai ta dawo ta yi. Sai da ta
shagwaggwabe tayi kalar tausayi sannan ta bashi amsa:

“Haba Habibi, wallahi ba zan iya ba. Ka san fa laraba ce, busy day din mu. Tun 8 har 4pm muna lecture, ga
shi ma 3pm to 4pm test za mu yi. Don Allah ni dai a yafe min.”

Haushi ma ta bashi da take wannan zancen, a fusace ya bata amsa.

“Ni fa shi yasa bana son wannan karatun gaskiya, toh yanzu ni zan tsaya na dafa abincin ko ya kike so na
yi? Ko kuwa da mutunci na da mata har biyu amma ban isa ayi min abincin Shan ruwa a gida ba?”

“Toh don Allah ni dai ka yi hakuri. Ana order din abincin fa, abinda kake so kawai za ka fada za su girka su
bayar a kawo maka a kan lokaci.”

Bai amsa mata ba ya tashi ya barta a zaune. Sai da ta ji rufewar kofar dakin shi sannan ta murgude baki
ta ce:

“Wallahi ba zan yi ba, kamar wata jaka. Mutum ba zai ci abinci shi kadai a gida ba sai ya kai kwararo ya
tara kattai.”

Sai da ta shirya za ta tafi makaranta sannan ta same shi a dakin

“Zan tafi. Uhm!ba kai maganar abincin ba, in ana son na order din fa da wuri ake fada musu.”

Sai da ya ja tsaki sannan ya bata amsa

“Toh ki yi mu gani, ki fada musu inda za su kawo ki basu lambar Madu. Abincin mutum goma za su yi, sai
ki turo min account number dinsu na saka musu kudin.”

Ta amsa tana murna ta juya ta fice. Ba ta san wata me order din abincin ba don haka Instagram kawai ta
duba ta samo lambar. Sai da suka gama bayani suka daddale ciniki a kan naira dubu hamsin, tace musu za
su ga an turo da karin dubu biyar za ta tura account number su tura mata; sai da suka amince sannan ta
tura masa bill din.
“Abincin mutum goman ne dubu hamsin harda biyar saboda a daji ake samo kudin? Yanzu kenan haka zan
yi rabin azumi ina siyan abincin dubu sittin da biyar? Toh wallahi ba zai yiwu ba.”

Katse shi tayi yana cikin magana

“Toh don Allah kayi hakuri, yau din dai tunda na riga nayi musu magana ka taimaka ka tura in ya so sai na
dinga yi daga yau din.”

Tsaki kawai ya ja ya ajiye mata wayar. Jimawa kadan ya turo mata rasit ta Whatsapp ta tura musu, nan da
nan kuwa suka turo mata dubu biyar dinta.Har wajen 6pm basu kawo abincin ba don haka ya sake yi mata
waya yana ta fada.

Sai wajen 6:30pm bai fi saura minti 15 a Sha

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login