Showing 57001 words to 60000 words out of 196754 words

Chapter 20 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15406

kake korafin nan na ce kaje asibiti ka ki.”

Bai sake ce mata komai ba ya gama cin abinshi ya fice, da yake baya jin zai iya tukin Madu ya sa ya kai shi
kasuwar. An ‘dan zauna an fara harkoki wajen sha daya na safe ya mike zai tashi daga kujerar da yake
zaune kawai sai gani aka yi yana yin baya zai fadi. Nan da nan aka tare shi kafin ya kai ‘kasa, aka samu guri
aka zaunar dashi ya jingina. Yacewa Madu su tafi gida, ya dan ji kwari don haka da kanshi ya shiga motar
suka kama hanya. Kawai sai gani yayi Madu ya dauki hanyar asibiti, ya dube shi yace

“Ina kuma zamu.”

“Abba ai gara mu fara tsayawa kaga likita kafin mu je gidan.”

Shiru kawai yayi don bashi da kwarin da zai iya musu a wannan lokacin. Asibitin kudin da suka saba zuwa
nan ya nufa da shi, su kayi sa’a kuwa suna isa likitan yana zuwa don haka nan da nan aka shigar da Abba.
Bayan likita yayi masa tambayoyi ya amsa ya kirawo ma’aikaciyar lab ta shigo. Takardu yayi rubutu a kai
ya mika mata ta dauki jinin Abba da fitsari da likita ya bashi roba yayi ta fice. Bayan wani lokaci ta dawo ta
mikawa likita takardun ta fice. Tashi likita yayi ya fito ya kirawo Madu suka koma cikin office din, bayan ya
zauna ya dubi Abba yace

“Alhaji sakamakon nan ya nuna diabetes ne da kai, yana early stage. Duk da dai akwai sauran gwaje gwaje
da zamu yi kafin mu tabbatar amma yanzu gado za a baku saboda blood sugar dinka yayi high ana bukatar
ayi monitoring dinshi for a while ka dawo dai dai kafin ku tafi gida.”

Abba ya daga kanshi da kyar ya dubi likitan yace

“Likita ban taba wannan ciwon ba fa.”

“Alhaji ai komai yana da farko, babu mamaki in ka duba akwai masu ciwon a iyaye da kakanninku.”

Ya sunkuyar da kai yace

“Hakane shi ya kashe mahaifina.”

Likita yace

“Allah ya ji kanshi. Kada ka damu Alhaji ai ciwo ne wanda abinci ne yake saukar dashi, in dai aka yi sa’a
madam ta jajirce wajen abincinka toh baka da matsala sosai.”

Waya yayi ya kirawo ma’aikatan jinya suka kama Abba aka kai shi daki. Nan da nan Madu yayi wa Mommy
waya ya sanar da ita, da cewa likita yace a kawo masa abinci amma na alkama ko wake. Da kanta ta shiga
wajen Saudah ta gaya mata tace ta fito Salim ya janyo motar Abban ya kai su ita in ta gama abinci sai ta
taho. Saudah tace

“Ai na gama abinci ma sai kawai mu tafi dashi.”

Tace

“Da yake ance diabetes ne da shi lokitan yace a hada mai abincin wake ko alkama.”

“Ok, ai kuwa shinkafa na dafa.”

A wajen Zulaiha ta bar yaran suka tafi ita da Salim, Auta da Khalifa. Sai da Mommy ta tuka masa tuwon
alkama da miyar kuka sannan ta kirawo Madu ya zo ya dauketa. Tana zuwa ya Farka, likita yace a bashi
abinci ya ci don haka ta zuba masa tuwo ya ci ya koshi. Kafin ya gama cin abinci yaran duk sun fice daga
dakin sai Mommy da Saudah kawai. Itama Mommy yana gama cin abincin sai ta fito ta dawo reception ta
zauna don ta basu waje shi da Saudah. Tana nan zaune likitan ya zo ya huce ya nufi dakin don haka ta bishi
a baya bai ma san tana biye ba. Ya kwankwasa kofar ya ‘dan yi jinkiri sannan ya tura kofar ya shiga a daidai
lokacin da Mommy ma ta karaso suka shiga tare. Yana shiga bayan ya yiwa Abban sannu da jiki ya dubi
Saudah yace

“Abban naki ya ci abinci ko?”

Ta bude baki tana mishi kallon mamaki da haushi yayinda dariya ta dan kubcewa Mommy da kyar ta hadiye
dariyar tata, kafin su ce wani abu Abban da yake kula da abinda yake faruwa yayi sauri yace

“Eh na ci doctor na koshi.”

“Toh Alhamdulillah, yanzu za ka ji dama in sha Allah. Amma ka yi hakuri sai da safe zan sallameka saboda
dare.”

Ya juya ya dubi Mommy yace

“Madam ki bashi hakuri fa, gara ku kwana a nan saboda kar wani abu ya taso cikin dare.”

Tace

“Hakane Doctor ai in sha Allah za mu kwana.”

“Yauwa.”

Ya matsa ya duba drip din dake hannun Abban sannan ya gwada bugun zuciyarshi, ya danyi rubutu a
takardun da ke file din hannunshi sanna ya yiwa Abban sai da safe ya juya yace wa Mommy

“Hajiya muje sai na hadaki da dietician saboda su yi miki bayani don yanzu dole ki canza masa abinci.”

Ya juya ya fice. Mommy ta dubi Saudah tace

“Ai sai ki zo mu je don mu jiyo tare.”

Ta bata rai tace

“Ki je kawai na ji daga baya.”

Ai kuwa kafin ta rufe bakinta Mommy ta fice ta rufo kofa. Ya dubi Saudah yace

“Ai gara kije ki ji ko.”

Tace

“Na ji daga baya, kana ji don raini yana wani cewa wai Abba na.”

Tayi kwafa ta kauda Kai. Shi kuwa da yake ba zai iya musu da ita ba kwanciya ya gyara ya dauko wayarsa
yana dubawa. Sai wajen goma na dare

Sannan ma’aikaciyar jinya ta shigo tace musu su fito zai yi bacci. Mommy ta matsa kusa da gadon tace

“Abba za mu tafi, wa za a bar maka.”

Ya dube ta yace

“Ke mana.”
Tace

“Toh.”

Ta fice don ta sallami yaran ta barshi da Saudah suyi sallama. Kafin wani lokaci ta dawo Saudah ta fice suka
tafi. Gari na wayewa aka sallame shi suka koma gida. Daga wannan lokacin suka canza tukunya. Ita Rabi
dagewa tayi ta koyi abinci kala-kala wanda suka dace da mai diabetes da yake dama tun a asibiti sun bata
bayanai masu mahimmanci. Dole ta raba tukunya, tayi abincinsu ita da yara shima tayi masa nasa. Duk
yanda za ta kawata masa abincin nan ta koya a wajen Hajiya Salma kawarta, da yake ita Babanta yana da
diabetes kuma mijinta ma haka. Bai fi sati ba a gida suka koma asibiti likita ya duba ya tabbatar masa
komai yayi normal sai dai za a ci gaba da kula da abinci kuma da shan magani.
EPISODE 14



Sauyin abincin da Abba ya samu ya yi matukar hargitsa musu lissafi, shi kanshi ma saida ya nemi shiga
damuwa domin babu abinda yake so kamar shinkafa kuma yana shan suga sosai domin ko Rabin ma
takance sugan da yake zubawa a shayi kofi daya zai ishi mutum biyu su sha shayi me zaki. Don haka kullum
yana mita yana ci, idan kuma ya ga an dafa abinda yake so a gidan sai yayi mita. Duk tunaninsu ya kare
musamman Saudah wadda karatu da rainon yara duk sun dabaibayeta ko tunanin ma bata iyawa sosai.
Sai da aka yi wajen sati biyu da sallamosu sannan Mommy ta tuna lokacin da likita ya hadata da dietician
bayan ta gama bata bayani tace mata tana da group na wahtsapp wanda take koyar da girke girke
wadanda suka dace da masu diabetes. Nan da nan ta nemo lambar matar ta kirawo ta, ta sanar da ita
naira dubu biyu ake biya a shiga don haka ta turawa Baba karami account number din matar ya tura mata
kudin. Shigarta wannan group din ta ga abubuwa da yawa, wasu daga cikin girke girken ma masu sauki
don haka Abban yana shigowa ta gaya masa ta bashi lambar matar tace masa ya sa Saudah ta shiga. Tana
gani ta wayarta lokacin da aka saka Saudah a group din, kafin minti talatin kuma ta fice. Haka suka cigaba
da fafutukar kula da lafiyar Abba, ko wacce tana iya bakin kokarinta.

Da yake Abba ba mutum ne mai son wake ba ko wata ba ayi ba ya gaji da cin waken. Yau ma waken ta
dafa masa a matsayin abincin dare, sai da ya zauna ya bude flask din ya ga faten wake. Ya juya ya kalleta
inda take zaune da ‘yan biyu tana basu abinci

“Bana son waken nan wallahi.”

Ta dube shi tace

“Me kace?”

“Waken nan ya isheni, ko dambun alkama ba za kiyi ba ko dashishi?”

“Ka san ni ba wani iya abincin gargajiyar nan nayi ba wallahi, amma zan bincika na ji.”

Ya riga ya saba jin wannan amsar don haka ya debi waken kadan ya zuba a faranti ya janyo burodinshi na
alkama ya hada ya ci yana mita.

Washe gari Mommy za ta karbi girki don haka itace za ta yi masa abincin rana wanda zai tafi da shi kasuwa,
gudun ‘kurna ta dafa masa wanda ya sha nama sannan ta hada mishi salad ta sami ‘yar mitsitsiyar roba ta
zuba salad dressing din a ciki yanda in ya tashi ci zai zuba ta hada masa a kwando. Da ya dawo da daddare
kuma tuwon alkama tayi da miyar kubewa danya, don haka ya zauna ya ci ya koshi. Bayan ya gama cin
abinshi ya zauna kallon labarai, yana yi suna hira. Ya dubeta yace

“Ban san yanda za ayi da abincinta ba a gidan nan.”

Ta dube shi da mamaki tace

“Kamar yaya? Gashi ana dafawa kana cinyewa.”

“Kina dafawa ina cinyewa dai.”

Tayi dariya ttace
“Duk daya.”

“Kin san kanwarki bata iya wadannan abincin na masu diabetes ba, da yake babu varieties da yawa sai an
hada da dabara yake dadi.”

“Ka yi hakuri ka bata lokaci, za ta koya. Ka san sai kana yi mata uziri saboda yara, goyon ‘daya ma yana da
wahala fa balle biyu.”

Ya gyara zama

“Hakane, amma bata ma da niyyar koya fa.”

“Ka dai bata lokacin ka gani, na san za ta gyara.”

Ya jijjiga kai yayi shiru na dan lokaci sannan ya ‘kara dubanta yace

“Toh mai zai hana ki dinga dafa min abincin kawai? Tunda ke in kika dafa yana yin dadi.”

Tayi dariya sannan tace

“Amma dai rigimarka tana da yawa wallahi, ka san kuwa yanda mu mata muke alfahari mu girka abinci
mijinmu ya ci ya ji dadi? Ya za ayi ka ce ta daina yi maka girki ta ji dadi.”

“Toh ai girkin ne ba ‘kiwa ba biyan bukata.”

Tayi yar dariya tace

“Haka za ka hakura, a hankali na gaya maka za ka ga ta gyara da kanta.”

“Hmmmn!”

Ya mayar da hankalinshi ga kallon TV.

Bai sake tayar da zancen ba sai ranar da Mommy za ta fita daga girki. Bayan ya shigo daga masallaci sallar
asuba ya same ta a kan dadduma, ta yi masa sannu da zuwa ta mike don ta je ta shirya abincin safe. Har
ta kama hanya ya dakatar da ita

“Mommy.”

Ta juyo ta tsaya ta na sauraronsa.

“Ki dafa min abincin rana zan tafi da shi kasuwa.”

Yanda ya tsuke fuska yana jira tace wani abu ya yi fada ya sa ba tayi musu ba tace

“Toh.”

Ta juya ta fice.

Sandwich tayi masa da burodinshi na alkama don karin kumallo sannan ta yi masa dashishi da miyar
alaiyahu ta sa masa a kwando. Yana cikin cin abincin ita kuma tana zaune a kusa dashi tana cin nata
sandwich din na farin burodi ya dubeta yace

“Ke da kanwarki ko kara bakwa yi min, kin sa ni a gaba kina cin farin burodi ba za ki ci na alkama ba.”
Ta kyalkyale da dariya tace

“Ina ka taba ganin a bawa mara lafiya allura an ce nurse dinshi tayiwa kanta rabi.”

“Haka ma za ki ce ko?”

“Toh na yi shiru, gobe na taya ka.”

Ya dubi kwandon abincin shi daka ajiye a gefe yace

“Me kika zuba min ne?”

Tace

“Dashishi da miyar alaiyahu.”

“Yauwa, da Allah kiyi min abincin dare mana.”

Ta kalleshi da mamaki tace

“A’ah, Saudan lafiya take?”

“Na fa gaya miki babu abinda take dafa min sai wake, ki yi min tuwo mana da miyar agushi.”

Tace

“To ai na ga likita ya ce blood sugar din naka ya dawo normal, za ta iya hada maka da shinkafa ko taliya
kadan in ya so in na karbi aiki sai kaci wanda kake so.”

“Hmmn. Kin san fa ciwon nan shi ya kashe Baffana, wallahi kana yin wasa da abinci za ka ji jiki.”

“Ai kuma ka ga ana kula, in Sha Allah duk muna addua babu abinda zai same ka, Allah ya ji kan Baffa.”

“Amin. Za ki yi min tuwon ko ba za ki yi ba.”

Ta dubeshi ya yi wani kicin-kicin ta kauda kai tace

“In dai kayi alkawari ba za ka sake saka ni girki ranar da ba girkina ba toh zan yi.”

“Mtseww. Toh na yi alkawarin.”

“Toh in Sha Allah zan yi.”

Ya dauki kwandon sa ya juya ya fice bayan ya amsa a dawo lafiya da ta yi masa. Da yake ya riga ya gayawa
Saudah a wajen Mommy zai ci tuwo ko dora tukunya ma bata yi ba, shinkafar da ta dafa da rana ita suka
kara ci da daddare ita da yaran. Bayan ya dawo wajen Mommy ya fara shiga ya duba su, da zai fito Salim
yana zaune a falo ya dube shi yace

“In an jima ka karbo abinci a wajen Mommy ka kawo min falon antinka.”

“Toh Abba.” Salim ya bashi amsa.

Bayan kamar minti goma Mommy ta hada abincin ta dora a tray ta bawa Salim, yana shiga ya mikawa
Saudah abincin yana fadin
“Gashi Abba ne ya ce a kawo masa.”

Ta nuna masa dining table ya ajiye sannan ya juya ya fice. Jimawa kadan Abban ya fito daga daki sanye da
jallabiyarsa ta zaman gida, kafin yayi magana ya hango flask din Mommy a table don haka ya nufi table kai
tsaye. Bayan ya zauna ya juyo ya umarceta da ta kawo masa faranti da cokali. Bayan ta kawo ya bude flask
din tuwon ya mulmulu sosai ga miyar agushi sai kamshi take, nan da nan ya cika kwano ya kwaso katuwar
loma. Da kyar ya hadiye wannan lomar saboda azabar yaji, kafin ta huce ya jike da gumi idanuwanshi duk
sun fito. Ya juyo ya kalli Saudah ya ga kamar ma bata kula da abinda yake yi ba hankalinta yana kan Hanan
da Baffa Karami. Bashi da ulcer amma baya son yaji ko kadan, don haka abincin gidan ba sa yin mai yaji.
Wannan rashin son yajin shi yasa baya cin abincin sayarwa. Yayi matukar mamaki yanda za a ce Rabi ta
zuba masa wannan uban yajin a abinci kamar yau ta fara yi masa girki. Nan da nan ya mike zai fice kafin
ya kai bakin kofa Saudah tace

“Ka gama cin abincin na kwashe kwanukan?”

Ba tare da ya juyo ba ya bata amsa

“A’ah, ina zuwa.”

Yana fita ta kyalkyale da dariya harda kwalla tace

“Sai na koya muku hankali kai da ita. Likita ya ce kaci shinkafa da taliya amma ka tsaya fitnar tsiya kai in
baka wahalar da mutum ba ba ka jin dadi.”

Yana shiga ya tarar da ita da yara suna cin tuwon shinkafa da irin wannan miyar da yaci mai yaji. Bayan
sun amsa sallamarshi ya dube ta yace

“Ke kuwa yau wane irin yaji kika saka a miyar, ko dai don kar na ci abincin ne kika zuga yaji?”

Ta dubeshi ta dubi kwanon da yake gabanta tace

“Yaji kuma? Ka ga fa miyar muna cin abinci da ita ko alamar yaji babu.”

Ya dubeta cike da mamaki, ya sa hannu ya dauki cokalinta ya kwashi miyar gabanta ya zuba a bakinshi,
bayan ya hadiye yace

“A’ah, toh ni miyar da Salim ya kawo min yaji har tsakar ka don loma dayan da na saka a baki na da kyar
na hadiye ta.”

Tace

“Ikon Allah, toh kuma wallahi itace dai wannan. A tukunya daya nayi miyar sai nayi Mana tuwon shinkafa
ni da yara da yake bana son na alkama.”

Ya ja kujerar dining table ya zauna kusa da ita yana fadin

“Sai ki zuba min wani tuwon naci tunda miyar in ta fita daga nan yaji take yi.”

Ta kyalkyale da dariya tace

“Ai kuma tuwon alkamar shike nan na kwashe maka.”
Ya tashi Auta ya turo shi ya dauko masa abincin da aka kai can. Bayan an kawo Mommy ta dandana miyar,
yajin da ta ji yayi matukar bata mamaki. Nan dai ta zuba masa wata miyar yaci tuwon, bayan ya gama suka
dan taba hira sannan yayi musu sallama ya koma wajen Saudah. Yana shiga tace

“Ai har zan rufe kofa da naji shiru na zata a can za ka kwana.”

Kallo ya bita da shi, kafin ta gane me yasa yake kallonta haka yace

“Me yasa kika zuba min yaji a miya?”

Yanayin fuskarta ya tabbatar masa da cewa ita din ce ta zuba yajin, nan da nan ta bata rai tace

“Ka ci abinci na ne da za kace na zuba maka yaji a miya?”

“Abincin da aka kawo kafin na fito kin zuba yaji, kuma kin san bana son yaji ko?”

Tayi kicin kicin ta zumburo baki

“Inda aka yi maka abinci nan aka zubo maka yaji amma ka zo kana so ka lika min.”

Ya jijjiga kai yana mamakin karfin hali irin nata. Ya dube ta tana ta wani kau da kai don kar su hada ido

“Kin zata kowa ma bashi da hankali kamar ki ko?”

“Lallai ma …..”

Kafin ta karasa ya tare numfashinta yana fadin

“Sai da na gaya miki abinda za ki dafa min na baki zabi ki dafa ko naje a dafa min amma saboda mugun
hali ke baki dafa min ba wata ta dafa kin hana min ci. Wallahi idan kika kara yi min irin wannan sai kin gane
kurenki.”

Ya juya ya huce dakinshi ya barta nan a tsaye jiki babu kwari. Ta yi mamaki kwarai da ya gane don ta
tabbatar babu wanda ya ga lokacin da ta zuba yajin. Ta yi tunanin idan ya je can ba zai sami wani abincin
ba don haka a zatonta a can zai je yayi ta fada sai kuma abun ba haka bane. Abu daya ne ya tsaye mata a
rai wai bata da hankali, tunda suke bai taba yi mata irin wanna zagin ba. Haka ta kwana ranta a bace duk
da ta san itace da laifi amma a ganinta wannan ba abune da za a ce bata da hankali a kai ba. Da yake ta
san ta yi laifi da safe bayan ta dafa masa shayin da zai sha da burodin shi na alkama ta soya kwai sai ta
daure ta yi masa alala da miyar alaiyahu don shi baya cin alala da yaji, duk da tana ji tana gani sai da ta
makara saboda ta tsaya yin alalan ga shi sai ta tsaya gidan da take kai rainon ‘yan biyu.

Dole tasa Abba ya nemi restaurant din da suke yin abincin masu diabetes saboda in dai Saudah ce da girki
toh ba lallai ya samu yanda yake so ba, takan ce hidima ta yi mata yawa gashi abincin da yake so suna da
daukar lokaci. Shi kuma bai yarda da wannan uzurin ba sai dai yace

“Sannu agogo sarkin aiki.”

Ita kuma

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login