Showing 123001 words to 126000 words out of 196754 words
Chapter 42 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
komai ya ‘dan debe min
kewa.”
“Ga abubuwan sayarwa nan da yawa, kayan sawa, kayan kichin, kayan yara, zannuwan gado da
sauransu. Sai kawai ki hada kina sayar da wani abun kuma ki koyi wata sana’ar.”
Ta dan yi jim tace
“Toh me zan koya Baraka? Ni dai bana son dinki.”
“Toh girki fa, kin ga yanzu snacks yawanci duk siya ake.”
“Kai gaskiya na girku haka, ba zan yi wani abincin sayarwa ba. Kin ga ina son harkar kamshi, da zan samu
a koya min turaren wuta sai na dinga yi kuma na hada na saro turarukan kanti da irin su burner haka na
dinga sayarwa duka.”
“Kwarai kuwa idea ce mai kyau sosai, don kinga yanzu kwarai mata sun ganewa turare.”
“Saura masu sayen kuma.”
Ta bugi kafadarta tace
“Kada ki damu wannan duk koya ake yi kuma duk ga mu nan da ni da yaranki su Ummi da Yaya Shafa da
nata ‘yan matan duk tare za mu yi ta sayarwa ana hada miki kudin har ki kafu, in ta kama ma sai mu
bude shago.”
Tayi murmushin jin dadi tace
“Kar ki zugani na shiga duniyar mafarki.”
“Au toh zauna ki yi ta kallo kya ji ana yi.”
Suka dan yi jim sannan Barakan tace
“Gobe in sha Allah zan sa a samo wadda zata koya miki turare irin na ‘yan Maiduguri masu kyau, jibi zan
tafi Abuja nayi sati kafin na dawo ma san kun gama.”
“Au jibi za ki tafi, zakara ya ja kaza kenan.”
Tayi dariya tace
“Toh ya za ayi. Amma a nan zan bar Zahra fa, duk abinda ake bukata akwai kuma akwai waya in akwai
wani abu. Ga Yalwa nan duk abinda kike so a dafa ki gaya mata kawai.”
“An gama Hajiya Baraka.”
Ta daki kafadarta tace
“Ke da ba Hajiyar ba.”
Suka kwanta suka yi baccinsu.
Kwanan Baraka biyu da tafiya Abuja matar da suka yi za ta koyawa Rabi turare ta zo. Duk wani abunda
ake bukata na aiki da shi ta zo sai, don haka nan da nan a kwana biyu ta koyawa Rabi hadin turare kala-
kala na wuta da humra. Duk wani bayani da take bukata an yi mata ta sami littafi a wajen Zahra duk ta
rubuta. Da yake ita tazo da kayan aikinta sai da aka gama ta dibar musu kadan a ‘yan robobi ta tafi da
saura, ta ce su ajiye turarukan na wani lokaci kafin suyi amfani da su. Sannan kuma ta yi mata bayanin
inda za ta samu duk wani kayan turare da take bukata a kasuwar kurmi ta Kano. Tayi musu sallama ta
tafi.
Ita kuwa Baraka kafin ta dawo daga Abuja sai da ta nemi masu bayar da sarin kaya a Lagos inda za ta
sarowa Rabi zannuwan gado su kuma turaruka aka hada ta da wani Alhaji dan kasuwar kurmi aka ce idan
ta zo Kano ta nemeshi za su sami duk wani turare da suke so. Bata dai yiborder din kayan ba amma ta yi
magana da su ta ji farashinsu da sauran bayanai sai ta dawo sun karkare magana da Rabi sai a yi order.
Sai da ta kwan bakwai sannan ta dawo Jigawa. A nan ta nunawa Rabi hotunan da aka turo mata na
turaruka da zannuwan gado, tana ta dubawa tana murmushi. Barakan tace
“Don ma yanzu babu wanda yake da lambarki ai da tun yanzu za mu fara dorawa a status.”
“Babu damuwa, ai kwanan nan zan koma Kanon sai mu ga yanda za ayi.”
Suka yi jim sannan Rabin tace
“Yanzu Baraka kayan nan fa suna da tsada sosai ina ta saka ki kashe kudi, ki bari kawai idan na koma
Kanon sai Ahmad da Baba Karami su bani ko dubu dari biyu ce sai ayi order din. Allah abun da yawa.”
Sai da ta harareta sannan ta bata amsa
“Kin san Allah za muyi fada dake, wai shikenan ba zan baki abu ba sai kice yayi yawa? Gaskiya bana so.”
Ta kama lebenta alamun tayi shiru ta bita da kallo tana mata murmushi kawai sai ta matso ta
rungumeta. Suka dan dauki lokaci a haka sannan suka saki juna, Barakan tace
“Ki kawo list din kayan turaren da Hajja ta baki next zuwa na Kano na siyo tunda ta ce yana bukatar a
bashi lokaci ya tsumu kafin a fara sayarwa in ya so in kika hada sai mu rufe shi har sai al’amura sun yi
daidai kafin nan ya tsumu.”
“Haka za a ayi.”
Baraka ta dauki wayarta tacewa Rabi
“Bari kiga hoton yarana na wankan Sallah na samo a status din Yaya Shafa.”
Ta budo hoton ta mikawa Rabi, ta karba tana dubawa tana murmushi tace
“Wannan ma ai a falon Yaya Shafan ne ina jin yawon sallah suka je mata.”
Ta bi hoton da kallo na dan lokaci a hankali murmushin dake fuskarta ya gushe ta dago ta dubi Baraka
wadda take ta binta da kallo tana karanta fuskarta tace
“Kalli auta yanda yayi zuru-zuru.”
“Toh ba dole ba, ‘dan marayan Allah tunanin kin mutu ko kina raye ma kadai ya ishe shi.”
Ta sake mayar da kallonta kan hoton idanuwanta suka fara cikowa da hawaye. Baraka tace
“Kalli Ahmad mana da Baba, suma duk sai wuya siriri da ido kulukulu. Ai duk suna cikin damuwa.”
Ta mikawa Baraka wayar ta share kwalla tace
“Wallahi da sai na yi kwana sittin nayi niyyar komawa Kanon, amman kuma sai naji kamar ko zuwa
karshen satin nan ma zan iya komawa. Kawai dai in naje ba zan kwana ba, yanda muka je tare toh haka
za mu dawo ai sun san inda nake. In ba haka ba in na zauna gidan Ya shafa ba zan sami yanda nake so ba,
shi ko Ya Munzali ko zama gidanshi ma ba zan gwada ba.”
Ta kama hannunta tace
“Babu wata damuwa tare za mu je mu dawo tare in sha Allah, in muka dawo sai muyi tunanin abun yi
tunda kin ga har yanzu da igiyar auren Usman a kanki.”
“Hakane, duk za a yi ta ta kare in sha Allahu. Bana son wannan auren nashi tunda yanzu ya riga yayi
masoyiya toh ya barni ni ma na fuskanci abinda yayi min saura na rayuwarta.”
Baraka ta sake rungumeta, nan da nan kuma hawayen da take rikewa ya kwace. Suka dago a tare sannan
Baraka ta ga hawaye a fuskarta ta sa hannu tana share mata. Tace
“Don Allah ki daina kuka Bibi, komai zai yi daidai in Sha Allah.”
Ko daya bata son ta ga Rabi ta shiga damuwa. Wannan yanayin da suka shiga ya tuna mata farkon
lokacin da aka kai su gidan su Rabi aka ce innarsu za ta koma Dukku tayi aure a can. Su yayyenta da yake
maza ne su biyu tuni suka sake suke harkarsu ita kuwa kullum sai tayi ta kuka. Haka Rabin take saka ta a
gaba tana kuka tana share mata hawaye.
‘Ki daina kuka Baraka ki ji dadi, ke yanzu innarki biyu da Ummanmu da kuma Inna kin ga kin ma fi ni
morewa.”
Cikin shesshekar kuka tace
“Ai yanzu Inna ta daina son mu ni da su Yaya da tayi aure za ta haifi wasu yaran ta manta da mu.”
Rabi ta rufe mata baki da hannunta tace
“Wa ya gaya miki, ai kullum tana sonku, ai ta ma fi sonku fa. Kanne fa za ta haifar muku kuma ta san
Baffanmu yana sonku kamar yanda Baffanku yake son ku shi yasa ma kika ga ta barku a nan.”
Haka dai ta dinga lallashinta har sai da ta gamsar da ita lallai Inna tana sonta. Don wani lokaci tana jin da
ba don wannan zaman da suka yi da Rabi ba da yanzu ta taso bata da alaka da mahaifiyarta don a lokaci
da gaske haushinta take ji. Tana ji a ranta ita kawai ta hakura bata da uwa. Sannan kuma Umman su Rabi
ma ta zauna da su tsakani da Allah bata taba nuna mata banbanci tsakaninta da su ba. Auren Rabi aka
fara yi sai da ta shekara biyu a daki aka yi na Baraka amma a wannan lokacin Umma bata nuna mata
wani banbanci ba sai ma shakuwa da suka kara yi. Idan ma Rabi ta je gidan duk abinda ta nema sai ace ta
tambayi Baraka in tayi mita sai Umma tace
“Ai yanzu Baraka ce kawai ‘ya ta, ke matar Usamanu ce yayarki kuma matar Aminu.”
Ita kuwa Baraka tayi tayi mata dariya tana cewa
“Umma ta yaye ki.”
Ko da ta sami admission kuma a kwalejin ilimi ta FCE haka Baffan su Rabi ya tsaya mata da kanshi ya
dinga rakata har cikin makaranta registration kafin ta saba. Don haka take ji Rabi har cikin zuciyarta.
Rabin ce ta katse mata tunani tana goge fuskarta tana fadin
“In sha Allah komai zai yi daidai Baraka.”
Suka yiwa juna murmushi. Barakan ta sake kama hannunta tace
“Kinga nima gobe zan je kanon akwai wata abokiyar aikin mu da mahaifiyarta ta rasu zan je mata
gaisuwa. Sun je daga office lokacin ina Abuja toh bana son lokaci ya ja ban je ba. Idan naje da nayi
gaisuwar zan je har gidan na dubo miki auta.”
Ta yi murmushi Baraka tana mata dariya tana fadin
“Mommy Mommyn autanta.”
Da safe kafin ta tafi Kanon sai da Mommy ta yi mata list na sunan chocolates din da Auta yake so tace ta
saya masa, ta karba tana murmushi tace
“In ce masa in ji ki?”
Ta harareta tana fadin
“Ki dai bashi kawai kin yi masa tsaraba, next week in sha Allah nima din zan je sai su gan ni gaba daya.”
Ta karba ta kama hanya.
Sai da yamma likis ta shigo gidan daga Kano don haka basu samu zama da Rabi ba har sai bayan sallar
magriba. A daki suke a zaune a kan kujera ta rasa wanne labarin za ta fara bata; yanda ta baro yaran a
cikin damuwa har suka saka ta kuka ko kuwa na albishir din da ta jiyo mata a wajen Mubarak da yake
shiri ya siya mata gida da gadonta. Kafin ta gama yanke shawara Rabin tace
“Ya kika baro min yaran naki?”
Bata da zabi dole ta fara bata amsar wanna tambayar, tace
“Lafiya kalau suke duka, na sami Khalifa, Salima da Auta, Madu yana kasuwa shi kuma Ahmad waya
muka yi da shi da ina hanya yana office.”
Ta bita da kallo alamar tana jiran karin bayani, don haka ta cigaba
“Kawai dai suna cikin damuwa, haka muka zauna mukayi ta kuka a falo ni da su babu mai bawa wani
hakuri, Auta kam ma har na taho yana kuka na dai bashi tsarabarki. Shine da ina hanya na kirawo Ahmad
nace in ya koma ya kara basu hakuri na saka su kuka. Shi ma kuma kina jin muryarshi kin san yana cikin
damuwar.”
Suka hada ido ta matse kwalla
“Tunda yau Monday Allah ya kai mu Asabar sai mu je don bana son zuwa ni kadai ba lallai su barni na
dawo ba musamman Yaya Shafa cewa za tayi sai dai na zauna a gidanta. Gara muje da ke ki kwatkwall
Suka yi dariya duka su biyun tace
“Allah ya kai mu ai kuwa kafa ta kafarki dama na dade ban yiwa Yaya Shafa tsiwa ba.”
Suka sake sa dariya.
“Yanzu kuma zan kara miki wani albishir din.”
Ta kalleta da murmushi tace
“Ina sauraronki, gara ki sanyaya min zuciya ko na samu nayi bacci.”
“Mubarak ya ce zai yiwa Yaya Munzali magana a sayar da gidan Umma a bashi kasonshi da naki ya hada
ya siya miki gida a Kanon, kuma Yaya Shafan ma ta ce a hada da nata.”
Idanunwanta suka ciko da hawaye ta sa tafukan hannunta ta rufe bakinta, ta sauke hannuwan tace
“Allah! Amma gaskiya Mubarak ya dade bai sani farinciki kamar wannan ba.”
“Toh kin ji dai don ya ce shi ya manta ma rabon da ya karbi nashi kason a kudin hayar gidan.”
“Hmmn, ni ma ai na manta rabon da ya bani nawan. Kinga da dubu dari da ashirin yake bani a shekara
da yake har kudin shagunan jikin gidan yake karba, ya koma yana bani dubu hamsin daga baya kuma ma
ya daina bani ko sisi don ni din ma yanzu kam na manta rabon da ya bani.”
Ta kalleta da mamaki tace
“Toh ke da sai kawai kika yi shiru?”
“Toh me zan ce masa, da yake bana cikin wata damuwa in na karba ma a durowa nake zubawa nayi ta
zara da kadan kadan har su kare. Don haka da ya daina bayarwa ma ban nema ba don na kula baya so
ayi maganar gidan.”
“Toh ai kuwa yanzu za a yi ta dole, ko ba komai ku raba shi da cin haram kafin yaranshi su taso su ce
gidan ma na babansu ne shi kadai.”
“Haka ne kam. Kinga ko ba komai nima na sami wajen zama na kaina a daina yi min gorin gida. Yanzu sai
na nemi saki da hujja tunda dama zullumin wajen da zan zauna yana daya daga cikin abubuwan da suka
sa nake tsoron ma ayi maganar.”
“Ai kuwa ko ni zan tsaya lallai a baki kason ki, yanzu kam ko su Baba ai sai su hada su saya miki gida a
daina baki tsugul-tsugul.”
“Haka ne Kam.”
Bata taba tambayar Yaya kudinta ba duk da ta san gidan yana nan ana karbar kudin, ta yi zaton ita kadai
yake hanawa da yake ya ga ita mace ce ashe Mubarak din ma baya bashi. Lallai Yaya, ko me ya aike shi
wannan son zuciyar oho? Ko ya dauka su basu da bukata ne? Gashi kuma shima kanshi tun kafin ma a
fara karbar kudin hayan za a saka shi a lissafin masu kudi don babban ma’aikacin gwamnatin jiha ne
sannan kuma yana da gidan gona nashi na kanshi wanda yake cike da dabbobi da kaji masu nama da
kwai kullum cikin sayarwa ake. Da ace baya samu ne sai suce ko bukata ce ta sa baya basu, amma abun
yayi kama da son zuciya kwarai.
Ta nisa tace
“Haka za a yi ko ni din ma yanzu ba zan sake yadda a cuce ni ba.”
EPISODE 28
Tun daga ranar da Abba ya gaya mata Zulaiha ta kai gulmarta Bichi gaba daya ta canza, ta daina sakina
jiki da Zulaihan kwata kwata kuma ko waya za ta yi in dai bata son a ji abinda za ta fada toh sai ta kule a
daki sannan. Ita kuwa Zulaiha abun bai dameta sosai ba saboda dama yawancin lokuta a haka suke; wani
lokacin Saudan tayi ta walwala suna harka yanda ya kamata wani lokacin kuma tayi ta kunci. Don haka
yanzu ma da taga sauyi ta zata kuncin nata ne ya tashi.
Yau ranar Laraba ce a al’ada karfe takwas Zulaiha take fita ta tafi makaranta amma har Saudah ta gama
shirya yara Abba ya tafi kai su 7:30am bata fito ba, sai can bayan ya dawo ta fito take sanar da Saudah
yau baza ta makaranta ba an kansile musu lecture din safe ta yamman kuma ba za taje ba don haka tana
gida. Ta ji dadi kwarai don haka ita ma a take ta kirawo kawayenta ta sanar da su ba za ta zo ba suyi
mata attendance. Tunda ta san gulmar da Zulaiha ta kai Bichi take jiran wannan ranar, ranar da babu
kowa a gidan daga ita sai Zulaihan don a ranar ne za ta koya mata hankali saboda in bata yi wasa ba sai
ta gurje mata baki. Jimawa kadan Abba ya gama shirinsa suka fice shi da Madu.
Tun kafin Abba ya fita ta je kichin ta hada shayi ta dauki burodi ta koma daki. Tana gama cin abinci sai
tayi zamanta tana chatting, sai wajen goma da kwata sannan ta fito rike da kofin shayin don ta kai kichin.
Babu kowa a falon sai Saudah ita kadai, Baffa da Hanan duka suna bacci. Sai da ta je ta ajiyo kofin a
kichin ta fito za ta koma dakin ta dubeta tana yatsina fuska tace
“Zo nan Zulaiha.”
Ta ji abun wani banbarakwai, ta saba kiranta tace ta zo amma ba da isa da gadara irin haka ba. Duk da
haka dai sai ta daure ta karaso inda Saudan take daga tsaye itama tana ta wasu murgude murgude tace
“Ga ni.”
Sai da ta kare mata kallo daga dama har kasa sannan ta bata amsa
“Zauna, magana za muyi.”
Ta zauna ta mayar da hankalinta ga Saudan tana jiran ta ji me za ta ce. Ta sake kare mata kallo sannan ta
bude baki da kyar tana magana kamar wata sarauniyar da aka batawa rai tace
“Wane zancen nawa kika kwasa kika kai Bichi?”
Ta kalleta da mamaki
“Zance juma, uhmmn to wane zancen ne wannan da na kwasa ba tare da na sani ba?”
Ta tsananta harar da takeyi mata kafin ta bata amsa
“Wane munafikin ne ya je yace maganin karfin maza ma zubawa Abba a abinci yayi ta amai.”
Sai yanzu sannan Zulaihan ta gane inda zancen ya dosa, ta kalli Saudan suka hada ido kallon raini da
wulakancin da take mata ya sa tayi murmushin keta ta fadi abinda ba shi tayi niyya ba
“Au toh ai ke zan tamabaya kin yi ko bakiyi ba, idan ba kiyi ba shine za ki ce an yi miki munafurci. Ko ba a
gun maman Surayya kika siya ba kika tashi za ki kashe musu uba sannan….”
Taga dai cin fuskar na Zulaiha ya fara isarta ta daga mata hannu tare da katse ta tana fadin
“Ke dakata, ni za kiyiwa munafurci kuma nayi miki magana ki zauna za kiyi min bura uba. Dama ni na san
wanna karatun naki kawai uwarki ce ta turo ki ki sawa mutane ido toh…”
Ta mike tsaye sannan ta tari numfashin Saudan wadda itama tayi saurin mikewa tace
“A’ah fa, kada ki kuskura ki zagar min uwa. Ke dai da uwarki ta turo ki ki tara muku kudi baki sami yanda
kike so ba shine……”
Marin da Saudah ta kwada mata shine ya katse mata zance, kafin tayi wani tunani itama ta daga hannu
ta mareta. Nan da nan suka kama kokawa kowacce tana hayaniya iya karfinta.
“Ke kin isa ki mare ni don ubanki!”
Saudah ta fada cikin karaji
“Sai dai ubanki don uba bai fi uba ba.”
Suka cigaba da kokawa kowacce tana kokarin ta kai ‘yar uwarta kasa, suna yi kuma kowacce tana fadar
maganganu son ranta.
Mal Bala maigadi yana zaune a tsakar gidan yake jiyo hayaniya, ya dan dawo daga tsakiyar gidan ko zai
fuskanci abinda yake faruwa. Da yake labulayen tagar falon a dage suke sai ya hango abinda yake
faruwa, duk da ba zai iya tantance su waye suke fadan ba amma ya san mutum biyu ne a cikin gidan
Zulaiha da Saudah. Yana nan tsaye yana shawarar abin yi Salim ya fito daga falonsu da shirinsa zai tafi
makaranta; da yake sai 11am yake da lecture nan suka fice
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good