Showing 24001 words to 27000 words out of 196754 words

Chapter 9 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15413

mamaki za ta yi magana ya tareta
“Na kira Anti Baraka dazu na ce mata gobe zan je Jigawan, kin ga tunda Baban Ummi babbane shi a NNPC
in Sha Allah zai samo min aiki, Lagos kuma na kaiwa Baba Aliko. Ina ji a jiki na in Sha Allah daya daga cikinsu
zai samar min aikin nan.”

Ta ce

“Lallai kam mai uwa a gindin murhu ai ba zai ci tuwonshi gaya ba.”

Ya sa dariya

“Abun sa’a ne Mommy, ki dai yi addu’a.”

“Toh Babana, Allah ya sa a dace. Bari inyi magana da Abbanku sai mu shirya duka mu tafi Jigawan, na dade
ban ga Baraka ba.”

Baraka yar wan mahaifinta ce, tare aka rikesu saboda su su Baraka ita da yan uwanta su hudu mahaifinsu
mutuwa yayi tun suna yara, bai shekara biyu da rasuwa ba mahaifiyarsu ta samu miji ta sake aure don
haka ta barsu a wajen mahaifiyarta. Da yake mahaifiyar tata ta tsufa gashi babu wani mai kula haka suke
rayuwarsu barkatai, babu kulawa. Wataran da Abban su Rabi ya je ganinsu bai ji dadin yanda ya same su
ba don haka da zai taho ya taso su a gaba ya taho da su. Sai da ya tara su Rabi da mahaifiyarsu yayi musu
bayani da nasiha sosai, yace

“Ku taimake ni mu hadu mu kula da yaran danuwana Ina fatan nima ko bayan raina ba za ku wulakanta
ba.”

Shi ke nan rayuwarsu ta dawo gidan su Rabin su kayi zamansu lafiya, dama Baraka sa’ar Rabin ce ga shi ita
kadai ce mace don haka suka zama kamar tagwaye. Aure ne kawai ya raba su. Rabin aka fara aurarwa sai
da ta shekara 2 a daki aka aurar da Baraka, kafin nan kuwa Baraka tana level 2 a Jami’a. Shi yasa yanzu
lecturer ce ita a kwalejin ilimi dake dutse yayinda maigidanta yake aiki a NNPC Abuja. Iyayenshi da ‘yan
uwanshi duk suna Jigawa shi ya sa ya ajiye iyalansa a nan, sai dai kawai Barakan tana yawan zuwa Abujan.
Yaranta biyu, Ummi da Fa’iza kuma duk an musu aure suna gidajensu.

__

Sako ta tura masa ta Whatsapp ta sanar da shi gobe za su je Jigawa ita da yara. Sakon bai yi kama da
izininshi take nema ba don ta riga ta yanke shawara ko ya hanata sai ta je, shima kuma bai yi tunanin
hanawa ba. Yana so ya dawo ya sameta da walwalarta don haka ya ce Allah ya kiyaye hanya, ya sanar da
ita idan suna bukatar kudi su gayawa Madu ya basu. Karfe shida na safe suka shirya gaba dayansu sai
Jigawa. Ranar asabarce don haka tana gida. Dadin da ta ji da ta ga Yar uwarta ba zai misaltu ba. Nan da
nan aka yi musu maraba suka ci abinci suka huta. Sai kuma Rabi da Baraka suka kule a daki bayan ta hada
yara da Musa direbanta ya kaisu yawo cikin gari su dan yi siyayya.

Suna ta hirarrakinsu har suka kawo kan amarya, Baraka tace

“Ya amarya kuwa? Kin san tun lokacin da ta haihu na zo muku barka rabo na da gidanku fa.”

Sai da ta tabe baki sannan ta amsa

“Hmmmn! Muna nan dai kamar yanda kika sanmu. Amarya kama bani da matsala da ita amma shi uban
gayyar gaba daya ma maganar nan da nake miki ya gama fice min daga rai. Nuna min yake yi kawai
amaryarsa ta fi ni mahimmanci, har yara sun gane sun fara jin haushinsa.”
Ta rike haba

“Amma gaskiya Usman ya bani mamaki, duk wannan uwar soyayyar a nan ta tsaya? Lallai duniya.”

Rabi ta ce

“Da kenan lokacin yana ganin da mamora a jiki na, ko da yake ba zan ce haka ba tunda wataran ma in
kwana ya zo kaina sai ya zama kamar wani mayunwacin zaki, abinda nake tunanin zan samu saukinshi
karuwa ma yayi.”

Ta kyalkyale da dariya ta doki kafadar Rabin sannan ta ce

“Ai ke ce sister me ba kya wasa da gyara.”

“Toh ai dole nayi gyara ko don na ji dadin jikina ma ba don wani ba.”

Suka yi jim sannan Rabin ta ce

“Ni yanzu abinda yake damu na rashin abun yi, ina son nima na fara wani dan business ko don ma daina
zaman jiranshi da bukatu na, kuma na sami abinda zai dinga debe min kewa.”

“Gaskiya ne, Toh yanzu zai barki kuwa? Ko da yake ya sauko tunda ya bar amarya tana boko.”

“Yanzu kam ai ba shawararsa zan nema ba, abun da yayi min dadi a rai shi zanyi. Da can da na hakura na
bi umarnin nasa me ya haifar min, ba gani nan ba ina karbar takaici.”

Baraka ta dafa ta ta ce

“Haka ne, toh gaskiya ya kamata mu zauna mu shirya business din da zaki yi. Wallahi shi ya sa na so ace
kwana za ki yi, amma zanzo Kanon in sha Allah. Kawai ki tanadi abinda za kiyi ko ni kadai ma sai na tara
miki jari sister me.”

Haka dai suka yi ta hirarrakinsu. Kafin su tafi sai da ta kira maigidan ta gaya masa ga takardun yaronta
suna neman aiki. Ya ce ta tambaye shi yana son aikin custom ko ya fi son na office kamar FIRS ko ministry,
shi kuwa Baba cewa yayi duk wanda ya samu yana so.

Ta ce

“Yauwa nawan muna godiya ni da yaro na, Allah ya kara arziki.”

Ta ajiye waya.

Sai bayan la’asar sannan suka kamo hanya, kowa zuciyarshi wasai musamman Rabi. Ta ji dadin yanda suka
tattauna da Yar uwarta, ko babu komai ka samu wanda za ka gayawa abinda ke damunka cikin aminci ma
rahama ne. Gashi kuma ta tabbatar yanda Baraka tayi mata alkawarin jari toh tabbas za ta bata kuma ba
kadan ba, don ko yanzun ma bata gazawa da hidimarta.

…….

Kwanan su hudu suka dawo daga Dubai. Da safe suka dawo don haka kafin yamma Saudah ta sa an kawo
mata Nawwara.
Dakinsa na wajen Rabi nan ya sa aka sauke masa kayansa, ita Kuma ya nuna akwati daya ya ce da auta ya
ja ya kaiwa Saudah nata ne.

Sun sha tsaraba kam. An siyowa Ahmad da Madu computer kowa, shi kuma Salim an siyo masa waya
Samsung mai kyau. Auta da Khalifa kuma TV game aka siyo musu da kuma kayan sawa kala uku uku. Baba
karami kuma aka siyo masa agogon hannu mai kyau da turare.

Yanda ya saba idan yayi tafiya ranar da zai dawo toh Rabi tana yi masa snack din da yafi so ko samosa ko
cake da kuma zobo, don haka yau din ma ya zata haka zai tarar. Ita kuwa babu abinda ta yi. Da ya dawo
ya sauka a wajenta ma mamaki ta yi, ta zata can zai sauka wajen amaryarshi haka dai ta tashi ta kai masa
ruwan sha. Ya sha ruwan kadan ya dube ta ya ce

“Ina zobon?”

Tace

“Ai baka ce a yi ba, ni na ma zata a wajen amarya za ka sauka in kun kwan biyun sai ka dawo nan don ni
ko abincin ranar ma ban daura ba sai yanzu ne Salim ya dora Mana danwake.”

Yaceda

“Toh a nan zan fara kwana biyun sai a zubo min danwaken nima idan an sauke.”

So take tace masa ya koma ya fara rabon kwanan daga wajen Saudah amma dai ta daure ta ce

“Toh.”

Ta tashi ta dauki kayan ruwanta za ta fita ya ce

“Toh ai ban gama shan ruwan ba.”

Ta mayar ta ajiye, ta sake zama. Sai wani binta yake da kallo yana kokarin su hada ido, tace

“Wai meye kake ta faman hararata ne?”

“Ai dole in harare ki don naga ke kamar baki ji dadin ganina ba ma.”

Dariya tayi sannan ta bashi amsa

“Haka dai kace, amma ka san ba haka bane.”

“Toh ai shikenan.”

Ya janyo karamin akwatin da shigo da shi ya bude ya ce mata zo ki gani. Ta taso ta matso kusa da shi ta
zauna a gefen akwatin. Ya zaro wani dan akwati irin wanda ake saka zobo ko agogo ya bude ya mika mata,
agogo ne mai kyau ruwan silver da zobe sai sheki suke yace

“Na san ki da son zobe, saboda zoben na siyo miki wannan Allah ya sa dai zoben yayi miki daidayac

Ya zaro zoben ya mika mata, ta zura a yatsanta na tsakiya. Daidai zoben ya zauna, tace

“Na gode, Allah ya kara arziki.”
Ya zaro kwalin waya iphone 11 ya mika mata yace

“ga wayarki kuma”

Yana ta wani murmushi, ta karba ta ce

“Na gode.”

Ta ajiye wayar a gefenta. Ya tura mata akwatin ya ce

“Duk kayan ki ne a ciki.”

Ta kara yin godiya shi kuma yana daddaga mata kayan. Material ne kala uku masu kyau sai doguwar riga
guda daya, da takalmin da jaka masu kyau da turare body spray samfurin Victoria’s secret guda 2 sai rigar
bacci guda daya. Ta sake yin godiya.

Yace

“Kinji kiran Sallah can bari na je masallaci, na samu mu gaisa da makota.”

Ya tashi ya nufi bandaki ya barta a zaune. Kafin ya kai ga shiga bandakin ya dan tsaya ya ce

“Ba iri daya na siyo miki da kanwarki ba don kar ki je ki ki sakawa, ke kadai na siyowa.”

Ya shige bandakin ba tare da ya saurari amsarta ba. Abun ma sai ya bata dariya; wato yana sane da cewa
idan yayi musu kaya iri daya bata dinkawa. Ta yi dariya kawai ta tashi ta nufi kichin don ta dubo Salim da
danwakensa. Kafin ya dawo daga masallaci ta koma dakin ta dauke akwatin ta mayar dakinta, amma inda
ta ajiye kwalin wayar a nan ta barshi.

Bayan ya dawo daga masallaci a falon ya zauna don ta riga ta raba abincin. Tare suka zauna shi da ita da
kuma Salim, Auta da Khalifa. Suna cikin cin abincin suka jiyo Yar murya daga bakin kofa

“Atta, Atta.”

Auta ya amsa

“Nauwa.”

Nan da nan ya tashi daga inda yake cin abincin ya daukota daga bakin kofa. Alawa ce a bannunta take
tsotsa, ta fara gwaranci tana kokarin sa masa alawar a baki. Abban ya kalle su sanna ya dawo ya kalli Rabi
yace

“Wai Auta ne Atta.”

Ya kyalkyale da dariya.

Tace

“Haka suke yi ita tace masa Atta shi kuma ya ce mata Nawwa, gashi nan ya sa ta da an ce ya sunanki sai ta
ce Wawwa.”

A gaban kwanonshi Auta ya ajiyeta, ya dauko danwake zai sa mata a baki cikin sauri Mommy tace

“Ka sa yaji fa zai mata zafi, ga wani a flask ka zo ka dibar mata ka sa mata maggi da kwai.”
Haka suka zauna suka gama cin abincinsu a nan har bacci ya dauke Nawwara, Mommy ta sa Auta ya kai ta
wajen babarta.

Sai da ya gama cin abincin sanna ya shiga dakin. Bai kula da wayar ba don haka saura kadan ya takata. Ya
kalli wajen yayi murmushi tare da jijjiga kai. Wato bata hakura ba kenan, don ya zata tunda yanzu sabuwa
ce za ta dauka da murna. Sai yanzu ma ya gane ainahin dalilin da ya sa ta ki dauka waccan wayar ma. Wato
ba fushin ya bata kwancen takeyi ba, fushin ya fara canzawa Saudah take. Ya jijjiga kai kawai. Nan ya huce
ya ci gaba da hidimarsa a dakin ba tare da ya dauki wayar ba shi ma.

Sai bayan la’asar da bata ga ya fito tafiya masallaci ba sannan ta bishi dakin ta gani ko lafiya, domin in dai
yana gidan toh baya Sallah a gida sai a masallaci. Tana shiga dakin ta same shi zaune a kan gado yana
muttsike Ido alamun yanzu ya tashi daga bacci. Bayan ya amsa sallamarta tace

“Bacci ne ya dauke ka ashe, shi yasa ban ji ka tafi masallaci sallar la’asar ba.”

Yace

“Wallahi kuwa sai yanzu na Farka.”

Ta juya za ta fito ya ce

“Rabi.”

Ta juyo tare da amsawa. Ya nuna wayar da ta bari a kasa yace

“Kin bar wayar taki a nan, ko ba kya so ne?.”

Ta dubi wayar Dake ajiye a kasa ta kai hannu ta dauka tana fadin

“Lah! Mantawa nayi fa.”

Ta karasa ta ajiye wayar a kan durowar gefen gadon tace

“Na dauka in na zauna.”

Ta fice daga dakin kafin ya kara cewa komai. Sai da wayar nan ta fi sati yana mita sannan ta dauke ta daga
dakinsa. Yayi zaton zai gani a hannunta amma bai gani ba har ya hakura. Ya so yayi magana amma sai ya
yi shiru saboda baya son wannan halin na Rabi. Shima ya san tana da saukin kai amma bai taba sanin haka
take da zuciya ba sai yanzu.Waje ta nema a dakinta ta boye wayar, ba ta jin za ta iya amfani da wannan
wayar saboda sai da ya raina mata hankali sannan ya bata ita.

Kafin karshen satin Anti Baraka ta bugo waya ta ce Baba karami ya sami aiki a hukumar Federal Inland
Revenue Service dake Abuja, don haka ranar litinin ya shirya ya tafi Abujan. Ta basu adireshin inda zai sami
Abban su Ummi ya karbi offer din shi. Ranar kwana sukayi suna murna, shi kanshi Abban nasu ya ji dadi
mara misali. Sai da ya Kira Abban Ummi din a waya yayi masa godiya, itama Barakan ya kirata.

Baba karami yana ta Shirin tafiya Abuja suka sami labarin Baffa Hassan ba lafiya, don haka Abba ya ce Rabi
su shirya ita da Saudah Baba karami ya kai tare da shi don su dubo Baffa Hassan. Hakan kuwa aka yi, da
safe suka shirya don sai sun je sun dawo sannan Abban zai huce kasuwa.

Da suka shiga gidan a tsakar gida suka samu Baffa Hassan yana zaune yana shan shayi Baba Yalwa kuma
tana gefensa tana yi masa hira. Nan da nan ta tashi ta yi musu maraba. Suka zauna nan kan tabarma suna
yiwa Baffa sannu, yayinda Mama Yalwa ta shiga kichin ta kawo musu ruwa. Kafin ta kawo Abban ya yiwa
Baffa albishir din aikin da Baba ya samu a Abuja. Ta ajiye ruwan ta dubi Baba karami tace

“Mai gida ba chefane in sammaka ruwan?.”

Kafin ya ce wani abu Baffa ya bata amsa

“Toh ki sha kuriminki chefanenki ya kusa ya fara zuwa daga Abuja.”

Ta ce

“Tace kai ma Sha Allahu shiryawa kawai zan yi mu tafi Abujan na dinga karba daga chan ba sai an kawo
nan ba.”

Nan Baffa ya bata labarin samun aikin Baba

“Kai ma Sha Allah, Allah ya sa albarka megidana.”

Daidai nan ta karso cikin gidan da sallamarta. Ko ba ace ba sun san Sa’a ce domin muryarta bata buya.
Tare take da karamin yaronta da take goyo Mahmud. Nan ta sake shi ya kama wasa da Nawwara.

Bayan ta gaida Baffa ta juya wajen su Rabi ta gaishe su ba yabo babu fallasa, ta dubi Baba karami tace

“Baba ya Abuja? Ko harda Kai a wadanda suka gama bautar kasar wannan wata.”

Kafin ya bata amsa Baba Yalwa ta bata

“Ya gama, yanzu aiki ya samu a can Abujan ma kusa da shugaban kasa shi yasa kika jiyo karadinbat

Nan da nan ta washe baki

“Ah lallai son barka, Allah ya sanya albarka.”

Suka amsa da Amin.Jimawa kadan suka yi sallama da mutanen gidan suka tafi.



…….



Tun kafin wannan semester din tayi nisa ta fara laulayin, ga Kuma rainon Nawwara. Haka dai take
lallabawa tana zuwa makarantar. Ta gaya masa ya tambayi Rabi ta dinga bar masa Nawwara da mai
rainonta taje ta dawo amma Sam Rabi ta ki yarda. Shi kuma baya son ya ja zancen ta fara yi masa mitar
yanda ya tauyeta ta hanyar hanata karatu; domin ya san duk abubuwan da take fada gaskiya ne. Don haka
bai wani ja zancen ba ya bari, ya ce mata kawai ta dinga tafiya da ita idan kuma ba haka ba toh ta hakura
da karatun. Dole ta daure suka ci gaba da tafiya haka don ta kula dama yake nema ya hanata karatun. Sai
dagag baya tayi dabara, sai ta Kai Nawwara gidansu Jamilar ta zauna a can tare da Jamilan. Nan ma kyar
ya amince saboda shi baya son a dinga kai masa yaro makota. Ranar da suka gama jarrabawa ranar ta
haihu, ta haifi ‘yarta mace. A ranar Abba ya rada mata suna Fatima; sunan mahaifiyarshi. Duk wanda aka
gaya haihuwa tare da sunan ake fada, sai ya ce
“An sami Innanmu.”

Nan da nan ‘yanuwanshi suka dauka da murna, kowa sai son barka don sun ji dadin sunan. Tun haihuwar
Nawwara suka sa rai amma sai aka saka mata Rukayya, 4mahaifiyar Saudah, sai da kuwa suka yi mita.

Tun ana gobe suna dangi suka fara cika gidan, wasu a wajen Rabi yayinda mafi yawansu suke wajen
Saudah. Ranar suna kuwa kafin azahar gidan ya kuma cika. Can da yamma bayan mutane sun fara watsewa
ta jiyo murayar Sa’a a falonta tana hira da mutane. Mamaki ya cika ta, don haka ta taso ta fito daga dakin
don ta ga me yake faruwa domin ta san ko kofar wajenta Sa’an bata kalla idan ta zo gidan. Ta zo hucewa
ta ga Inna Hajara; wadda goggonsu Abban ce; yana zaune a kan kafet ta mike kafa. Ta tsuguna a gabanta
tace

“Sannu da hutawa Inna.”

“Yauwa diyata, ya hidima?”

Kafin ta amsa Sa’a ta chafe

“Yauwa dama ke nake jira.”

Ta taso daga inda take ta dawo kusa da Innan sannan ta cigaba

“Inna kin san Mommy bata kulani, kuma bayan Baffa ya ce mu yi hakuri komai ya huce.”

Sai da Inna ta dafa hannun Rabi sannan ta ce

“Ai kuwa ya kamata ku dinga hakuri da juna diyata, rayuwar nan bata da tabbas kada ku rusa zumunci kin
ji ko.”

Ta ce

“Ni bata yi min komai ba ma Inna, komai ya huce wallahi. Allah ya yafe mana gaba daya.”

Nan suka zauna Inna tana ta yi musu nasiha ana mayar da zance. Sai da aka gama taron kowa ya tafi har
Sa’a sannan Rabi ta sami natsuwa. A yanda ta san Sa’an ta san tabbas wata fitinar take son tayarwa ta yi
wannan boring kunyar a cikin mutane saboda ta kafa hujja, amma gashi sun tafi bata ji komai ya faru ba.
Tun tana saka ido taga ta inda fitina zata bullo har ta gaji ta watsar.

…….

Sammako ta yiwo don haka karfe takwas na safe a kofar gidan ta yi mata. Sai da ta tambayi Bala maigadi
inda Alhajin yake sannan ta karasa ta huce cikin gidan. A zaune yake a dining table yana shan shayi yayinda
Rabi take zaune a kujerar da take kallon tasa tana shafa masa butter a buredi yana ci suna hira. Sai da
gabanta ya fadi da ta jiyo muryar Sa’a dama Kuma ta san lallai wanna sulhun da sa’an ta nema akwai
sauran bayani.
EPISODE 7



Ta karaso ciki tare da sallama, Rabin ta amsa. Ya dubeta ya ce

“Lafiya dai ko Sa’a na ganki da sassafe.”

Tace

“Lafiya kalau Yaya.”

Bayan sun gama gaggaisawa ya nuna mata kujerar da ke gefenshi ya ce

“Bismillah, zo ki zauna ki

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login