Showing 15001 words to 18000 words out of 196754 words
Chapter 6 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
tunanin sune wanda aka ce
a barbadawa Rabi, dayan kuma a turara a gidan da asuba. Sai guda biyu a ‘yar roba irin ta yoghurt, ya
tabbatar bakin shine wanda aka ce a zuba masa a miyar kuka.
“Yanzu ke baki ji kunya ba? Islamiyyar da kika yi ta zama ta banza ke nan kin koma shirka da bin yan tsubbu.
Wallahi ba’a gida na ba, za ki cuce ni ki cutar da iyalina.
Ke da ‘yanuwanki kuka kashe min yaro kika zo kika ce Rabi ce, ashe ku ne, ga tsafi kuma ga sharri.”
Tuni jikinta ya kama rawa.
“Wallahi ba tsafi bane, ni fa bana ma amfani da su, wallahi ba ruwana, don Allah kayi hakuri, ga su nan ma
duk ka sa a kona.”
Ta fada tana tura masa kayan, tana ta faman rusa kuka. Ya mike ya kwashi kayan ya kama hanya zai fita
sai kuma ya dawo ya tsaya a kanta
“Da Ummu da Kaka kada su sake zuwar min gida.”
“Toh, toh wallahi ba za su sake zuwa ba.”
Ta amsa tana rawar jiki. Ya juya ya fice.Ta dora hannu a ka ta kara fashewa da kuka. Toh wa ya gaya masa,
in dai ba megadi ne yayi musu labe ba, dama ta dade tana zarginsa me kama da mufukai. Ta rasa wanda
za ta kirawo ta gaya masa, wayar ma tsoronta take kada tayi magana wani ya na jinta.
Haka dai ta dauki waya ta kirawo babarta. Ta labarta mata abinda ya faru suka jajantawa juna, suka kara
tsinewa Bala maigadi domin shi suke zarge da labe. Haka ta kwana ranar tsakanin bacci da ido biyu, tana
yi tana istigfaari.
……..
Shi kuwa Abban Khalifa yana fita daga wajenta da kanshi ya tsaya a famfon tsakar gida ya zubar da na
ruwan tsaf ya tabbatar sun bi ruwa, na garin kuma ya zuba a aljihunsa don da su zai fita ya watsar a hanya.
Shi kanshi sai da ya ji kunyar kanshi saboda ya manta rabon da ya shiga wajenta ya ce mata sai da safe
idan dai ba a can zai kwana ba. Zuciyarshi tana gaya masa kada ya je sai da safe sa yi magana amma
kafarshi tana janshi.Tun kafin ya tura kofar ya jiyo ta ita da yara suna ta kyalkyala dariya, ya tura kofar ya
shiga da sallama.Yaran suka yi masa sannu da zuwa suka fara mikewa suna shigewa daki.
Kafin su gama ta yi masa sannu da zuwa, bata saurari amsarsa ba tayi sauri ta shige nata dakin. Madu ne
ya mike ya dauki kofin shayin da yake gabansa zai huce ya ce
“Madu shayi ka sha ne?”
“Eh Abba, Mommy ce ta sha ta rage sai na shanye.”
Ya amsa yana sosa keya.
“Duba kichin din idan da shayin Nima ka hado min.” ya fada yana kara yin gyatsa don kazar da yaci ta cika
masa ciki.
Ya huce ya hado shayin ya kawo masa ya ajiye ya dan zauna tunda auta ma yana nan. Suka dan taba hira
da Abban nasu sannan sukayi masa sai da safe suka shige daki. Ya zauna a nan shi kadai yana Shan shayi,
TV tana ta surutu yana kallonta amma bai san me ake yi ba. Tunani kawai yake yi; lallai Rabi ta yi fushi don
ya ga yanzu ko son ganinshi bata yi duk da ba yau ya kula da hakan ba amma yau dai abun ya dame shi,
yaran ma sai ya ga duk sun chanza.
Bai tashi ba sai wajen 10:30pm. Ya dubi kasan kofar dakinta ya hango duhu don haka ya zata bandaki ta
shiga. Ya tashi ya karasa a hankali ya tura kofar dakin nata ya shiga. A kashe fitilar take amma saboda
hasken farin wata da yake shigowa ta taga dakin ya dan yi haske.
Ya hangota a kwanche ta na bacci, ya dan yi jim sannan ya fito ya rufe mata kofar a hankali. Ya leka dakin
su Baba karami ya kirawo shi don ya rufe musu kofa, shi kuma ya koma bangaren amarya don kwananta
ne.
Ko da ya shiga babu kowa a falon don haka ya rufe kofa ya hau saman ya shige dakinsa ya kwanta. Ko
ganinta baya son yi yau don shi tsoronta ma yake yi, haka suka kwana kowa shi kadai a dakinsa.
……………..
Washegarin ranar ya kama Rabi ke da girki, ta riga ta saba ba ya cin abincinta wajen wata uku kenan; ko
ta dafa ma yanda ta ajiye haka take kwashe kayanta. Don haka ta dafa shinkafa da wake da rana, ta bawa
Madu N300 ta ce in ya tashi daga makaranta ya siyo gurasa a hanya da daddare sai ta dumama musu
ragowar miyar taushe su ci. Tun kafin ta gama fadin sakon Khalifa ya ce
“Mommy don Allah bandashe za muyi, ni zan daka mana kuli kulin da Baba Yalwa ta bamu in na dawo
daga makaranta.”
Ta ce
“Toh shikenan na ma huta da dumamen.”
Suka huce Baba karami ya tafi kaisu makaranta, don tun da ya gama jami’a shi yake kaisu makaranta.
Yanzu ma da yake bautar kasa a Abuja in dai ya zo hutu shi yake kaisu makaranta sai su dawo da kansu.
Bayan la’asar sai ga Baba karami da kaji guda biyu a leda ya ce
“Mommy kinga na siyo mana kaji gasawa za muyi sai mu hada da gurasar mu yi dinner.”
Yana ta wani yage baki.
“Toh mun gode Babana, Allah yayi maka albarka. Shi kwadayayye dama a haka kudinsa yake karewa, haka
dai za mu cinye alawee din yau mu ci kaza gobe mu ci kwai.”
Ta karasa tana dariya.
“Aah Mommy ai ana saving.”
Ya huce ya kai kicin.
Wajen 5:30 na yamma duka su shidan suka shige kicin din. Tana daki ta jiyo hayaniyarsu ta zo same su a
kichin din. Ta bisu da kallo kowa Sai aiki yake.
Ta ce
“Yanzu kaza da gurasar aka yiwa wannan taron dangin haka? Lallai yau za mu ci dadi.”
“Mommy ai don muyi sauri ne.”
Inji Baba Karami.
Ta dubi auta ya tsuguna a kasa yana yanka albasa idonsa sai hawaye yake yi, ta ce
“Kuma shine a rasa aikin da za’a bawa auta na sai yankan albasa ko.”
Ta karasa ta karbe wukar hannunsa
“Tashi auta bar musu albasarsu, daga a saka ka daka sai a sa ka yanka albasa? Taso mu je mu yi kallo in
sun gama ka yi tabin gishiri.”
Nan da nan kuwa ya mike:
“Mommy toh albasar fa.” Inji Khalifa wanda shi auta yake bi don ya san shi zai yankata.
“Wani ya yanka.”
Shi kuma auta ya faki Ido ya yiwa Khalifa gwalo suka fice daga kitchen din.
Da suka dawo daga sallar isha’I suka hada abincin, aka yanyanka kazar da aka riga aka gasa a tray, wani
tray din kuma aka yanyanka bandashen gurasar a kai. Ga kabeji, tumatir da albasa da cucumber an hadasu
a wani kwanon, sanna ga zobo cikin babban jug. Kowa ya zauna sai Baba karami ya fito daga kitchen da
wani karamin jug din.
Ta ce
“Nan kuma ruwa ka debo mana?
“A’a Mommy zobo na ne a ciki.”
“Ai kuwa baka isa ba don ciyayya za muyi, duk tare za mu shanye.”
Kafin su gama wannan takaddamar su fara cin abincin suka ji shigowar motar babansu, don haka suka
tashi don yi masa sannu da zuwa. Ta matsa gefe tana jiransu su shigo. Duk da ta san nan zai kwana amma
yanzu tunda yana jin haushin ta sai wajen 12 na dare yake shigowa yayi bacci a dakin nashi da asuba ya
fice, don haka bata sa ran shigowarshi ba har sai da ta ji shi da yaran sun shigo gaba daya. Ya kalli tsakiyar
falon inda aka here abincin ya tsaya a kanta bayan ya amsa sannu da zuwanta.
“A’ah! Walima kuke yi ne ke da yaran?”
“Aah abinci dare ne fa za mu ci.”
Ta bashi amsa.
“Lallai na zo a daidai bari in wanko hannuna.”
Ya huce ya shige dakin.
Yaran suka zauna suka fara cin abincinsu tare da ita. Sun san ba fitowa zai yi ba don ta saba irin wannan
cin abincin da yara shi kuma in dai ya gani sai yayi mita: sai ki sa kattai a gaba kuna cin abincin a kwano
daya, harda wanna gotai gotai da shi (wai Baba karami), don haka da ya fito ita da yaran duk sun yi mamaki.
Nan ya zauna cikinsu ya janyo karamin jug ya cika kofi da zobo ya shanye. Yana dire kofin Ahmad ya
kyalkyale da dariya yana kallon Baba karami, duk kuma sai suka kyalkyale da dariya. Ya bisu da kallo.
Auta ya ce cikin dariya
“Abba zobon jug din da ka sha na Yaya Baba ne kuma sai da yayi mana warning a kan baza mu sha ba shi
kadai za sha shine ka sha Ya Ahmad yake masa dariya.”
Shima dariyar yayi ya dubi Baba da ke ta muzurai. Tare da shi suka cinye gurasar nan da kaji tas. Shi da
yara suna ta hirarsu, kafin a gama ta tsame hannunta ta ce ta koshi, ta wanko hannu ta dauki kofin zobonta
ta shige daki.
Wajen 11 na dare ya je ya yiwa amarya sallama ya dawo. Har yanzu dai bata fito ba, don haka ya tura kofar
dakin nata ya shige. Kamshin da ya dade bai ji ba shine ya daki hancinsa har sai da yayi murmushi. Kamshin
turaren wuta ne wanda da shi takeyi a dakinsa, amma tunda ya hanata ta daina yi a falo da dakin nasa, sai
dai kawai ta yi a dakinta. Baccinta take yi sai da ya kunna fitila yayi gyaran murya sannan ta tashi, ta tashi
zaune ta ce masa
“Sannu da zuwa.” Tana mamaki.
“Yauwa. Har kin yi bacci ko?”
Ya zauna a bakin gadonta.
“Eh, akwai wani abun ne?”
“Aah. Magana nake so muyi.”
Ta bishi da kallo kawai yayinda shi ma ya tsare ta da ido har sai da ta sunkuyar da kanta.
“Rabi kenan.”
Ya fada yana murmushi.
“Toh ai sai a daina fushin da ni haka ko?”
Ta kawar da kanta gefe sannan ta amsa
“Aah ai ni ba wani fushi da nake yi, kai ne dai kake fushinka. Toh ni me aka yi min ma da zan yi wani fushi?”
“An yi miki sharri mana…”
Kafin ya karasa ta katse shi
“Ba’a yi min komai ba ni, aniyar kowa ta bishi ni ma tawa ta bini.”
Sai da yayi murmushi sannan ya bata amsa don ya san sai ya yi tsinin baki kafin ta huce.
“An yi miki sharri Rabi kuma ni da kaina na gane.”
Ta bishi da kallo yayinda ya gyara zama ya bata labarin abinda ya faru. Ya rufe da
“Ita din ma na dauki duk wani mataki da ya dace a kanta kuma komai ya huce. Allah ya kare mu.”
A ranta ta ce ka ji wadda ake karban uzirinta, wato komai ya huce tunda tsiya ta zo kan matarsa, lallai
mutumin nan.
A fili Kuma tace masa
“Amin.”
Ta kauda kai.
“Yauwa. Toh ki taso mu je daki sai mu karasa maganar a chan.”
Ya fada yana ta bin fuskarta da kallo.
“Toh zan taho yanzu.”
Ta amsa shi kuma ya mike ya tafi dakin. Sai da ta ji rufe kofar dakin nashi sannan ta ja wani dogon tsaki
mai zafi ta jefar da abin rufar ta gyara zama.
“A cuci mutum sannan a zo a ce masa komai ya huce, wai mu je mu karasa magana.”
Ta fada a fili. Ta kara jan tsaki ta sauko daga kan godon ta kashe fitilar ta da ya bari a kunne ta koma ta
kwanta ta gyara rufarta.
“Ku je can ku ci kanku ku sha bakin ruwa, ‘dan rainin hankali, haka kawai an katse min bacci na.”
Nan da nan kuma sai hawaye suka fara wanke mata fuska, tun tana gogewa har ta barshi kawai yana zuba
haka. Ita kanta ta rasa kukan me take yi? Murna takeyi da ya gane gaskiya ko kuwa takaici takeyi na yanda
ya mayar da ita kamar wata abar wasan shi, in yana so ayi aure idan kuma baya so sai yayi watsi da ita
lokacin da ya ga dama sannan ya dawo kanta.
A haka har bacci ya dauke ta.
EPISODE 5
Duk yanda yake tunanin abun zai zo da sauki ba haka ya kasance ba. Ita amarya yanzu fushi yake da ita
baya ko cin abincinta, ita kuma Rabi bai ma san me take nufi da shi ba. Shi dai ba zai ce bata kulashi ba
domin za tayi abincin tayi komai amma fa babu fuska, toh yaushe ma ta zauna kusa da shi balle wani zance
ya shiga tsakani. Komai tana yi, girki, gyaran dakinshi da sauransu, amma gaisuwa ce kawai take hadata
da shi. Ko ya kulata ma gajeriyar amsa take bashi, eh, Aah, toh; shikenan. A haka har suka kwashe sati
biyu, sai da ya fara bata tausayi; saboda ba mutum ne shi mai jurar shariya ba. Duk ya shiga damuwa yayi
ta wasu kame-kamen dalilin da zai sa ya shiga dakinta ko ya ja ta da hira. Ga shi daman kuma fushi yake
da amarya, don haka duk yayi zuru-zuru. A hankali komai ya dawo daidai, itama amarya ta samu da kyar
ta samo kanshi ya hakura.
Babu yanda bai yi da Rabi ta dinga saka masa turaren wuta a dakinsa ba amma ta ki, sai dai kawai ta saka
a dakinta. Ga shi ya saba da kamshi kuma saboda ita din ma’abociyar kamshi ce tun farkon aurensu. Ko
tayi kamar za ta sa in ta tuna da yanda a gaban Baba karami ya hantare ta a kan turaren wuta sai ta fasa
ta kai dakinta. Da ya dame ta da mita dakinshi ba kamshi, har bandaki yana neman fara karni sai ta siyo
freshner ta ajiye a dakin take fesa masa. Tun yana korafi har ya gaji ya sawa sarautar Allah Ido.
Haka ma zobo, sam ta daina ba shi sai dai ita da yara su shanye, idan yayi magana sai ta ce zobon ne bashi
da yawa. Sai da ya gaji ya siyo zobo, flavour da kuma abarba ya bata da hannunsa sannan ta dafa masa
zobo. Maganar Baffa kawai yake tunawa
“Mata suna da yafiya amma basu da mantuwa”
Lallai yau ya gani domin ya san tabbas abubuwan da yayiwa Rabi ne ta rike a ranta ya sa take ta share shi,
don haka shi ma yake binta a hankali.
………………
Ko da Saudah (amarya) ta ga komai ya dawo daidai kuma ga shi an kusa fara jarrabawar JAMB sai ta sake
yi masa tuni, kamar ba zai yarda ba amma daga baya sai ya hakura. Madu shine idan ya taso daga
makaranta da wuri yake zuwa kasuwa wajen Abban, don shi yana son kasuwanci ba kamar Baba Karami
da shi ko daya ba ya son harkar kasuwa ba, shi kanshi Abban cewa yake yi
“Wannan cikakken ‘dan Rabi ne, ko nawa za’a bashi in dai sai an yi hayaniya toh baya so.”
Shima Ahmad duk da yana son kasuwanci amma baya son irin na Abbansu don haka shima baya zuwa
kasuwar.
Don haka Madu Abban ya ritsa a kasuwa yayiwa Saudah rijistar jarrabawar JAMB din, tunda shi yayiwa
kaninsa Salim satin da ya wuce. WAEC da NECO ma haka aka yi mata rijista a makarantar yan mata dake
nan kusa da su don ta gyara result dinta. Duk abubuwan da ke faruwa Rabin tana sane da su; tunda duk
da Madu ake yi; ta dai yiwa kanta alkawarin ba za ta yi masa magana ba har sai lokacin da shi da kansa ya
kawo mata zancen sannan za ta juye masa cikinta.
……
Tana da shekara 19 aka aura mata shi, a lokacin shekararta 1 da gama secondary school. Tana matukar
son ta cigaba do karatu, ba don komai ba sai domin ta zama malamar home economics, burin ta kenan
guda daya.
Har an fara kokarin samar mata gurbin karatu a kwalejin ilimi sai ya fito da maganar aurenta, a daidai
lokacin kuma ana shirin auren yayarta Shafa. Su hudu ne a wajen mahaifinsu dukansu kuma uwarsu daya;
domin amaryar babansu bata taba haihuwa ba har Allah ya karbi rayuwarsa. Don haka nan da nan aka
hada bikinta da na Shafa akayi aka kai kowacce dakinta. Shi mijin Shafa dan boko ne domin kannensa mata
ma duk jami’a suke, don haka ya samarwa matarsa gurbin karatu a School of Nursing, shi ya sa tana nan
tana aikinta a asibitin Murtala a halin yanzu. Ita kuwa Rabi duk wata dabara da take jin cewa za ta yi amfani
da ita don ya yarda ya barta ta yi ko da diploma ne ta yi amma sam ya ki
“Me za kiyi da wani karatu, in kin tafi yawon karatu da aiki wa zai miki tarbiyyar yaran.”
“Duk abinda kike so ni Allah ya dorawa kuma zan yi miki gwargwado, in dai ba rainawa kikai ba toh me za
ki yi da kudi da kike wani son karatu ko aiki.”
“Duk matar kirki tana gida tana zaman aure amma ke kina so a barki kiyi ta gariri a titi, toh ba zan dau
wannan ba.”
“Saboda kina kallon yayarki tana yawo ne da sunan karatu shi yasa kike min wannan fitnar toh ni ba
shashasha bane irin mijinta, na san me nake yi.”
Irin maganganun da yake gaya mata kenan duk lokacin da ta tayar da maganar karatu. Sau da dama ta
kwana tana kuka saboda bakin cikin yanda ya hanata karatu, a haka har ta gaji ta hakura. Islamiyya kawai
ya yarda ta shiga a nan unguwar, ita ma da kyar saboda ya ce kawai haduwa mata suke suyi ta gulma a aji.
Shekararta uku da fara zuwa islamiyya hedimasta ya ce idan tana so ta nemo izinin mijinta za su dauke ta
koyarwa a bangaren yara da yamma; saboda yanda take fitowa gaban aji ta yiwa yan ajinsu tilawa idan
babu malami. Ranar da murnarta ta isa gida, ko kafin ya dawo ma ta riga ta gayawa Shafa a waya.
Wannan maganar da ta gaya masa kuwa sai da yayi sanadin cire ta daga islamiyyar sannan kuma ya kaita
kara wajen mahaifinta. Tunda aka yi mata aure Abbanta sau daya ya taba zuwa gidan, shine bayan an kaita
da sati sai kuma wannan lokacin.Ya sa ta a gaba ya dinga yi mata nasiha
“Ban san ki da son duniya ba Rabi’a, ki rabu da yayarki tunda mijinta ba irin naki bane. Baki rasa komai ba
toh ki yi hakuri kiyi zamanki lafiya, aure babbar ibada ce kuma biyayya wa miji ita ce ginshikin wannan
ibadar. Ki yi hakuri kiyi zamanki kinji, Allah yayi miki albarka, ya raya miki yaranki bisa tarbiyya.”
Haka ya tafi ya barta tana faman share hawaye, gashi dama lokacin tana dauke da cikin Ahmad wanda ita
kanta bata san da shi ba. Sai da tayi da gaske da rokon Allah sannan ta cire wannan damuwar daga ranta,
kuma tun daga wannan ranar bata kara yi masa
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good