Showing 177001 words to 180000 words out of 196754 words

Chapter 60 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15387

kai ta share kwalla, bata da amsar da zata bashi don haka tayi shiru kawai kanta a kasa.

‘Shi ya saka dama nace miki bana son masu aiki saboda irin wannan kwasan zancen, kuma idan baki gaya
mata ba toh a ina zata ji dole a bakinki taji ko kuma a bakin wani wanda kika gayawa.’

‘To don Allah kayi hakuri ka ji. Ni yanzu ma bana jin zan sake daukar wata mai aiki nan kusa itama
Balaraba bazata sake shigowa gidan nan ba in sha Allahu.’

Tunda yake da ita bata taba yi masa wani laifi ta bashi hakuri kamar haka ba, ko da zata bashi hakurin sai
dai tana yi tana murgude baki da harare-harare. Yanda ta zauna yau a nutse tana bashi hakuri ya
tabbatar masa da lallai tayi nadama, nan take ta bashi tausayi. Babu mamaki zaman gidan nasu bai yi
mata dadi ba don shi gani yayi kamar ma tayi baki ta rame. Ta katse masa taunani tace

‘Don Allah ka rakani wajen Mommy na bata hakuri ta janye karar, wallahi ni duk abinda ma take so zan yi
mata in dai zata hakura.’

Sosai ta bashi tausayi, ya dubeta yace

‘Kinga irin abinda nake jiye miki ko?’

Ta sake sunkuyar da kai tana share kwalla. Ya mike tsaye yana fadin
‘Tashi muje.”

Ta mike ta dauki hijabinta da yake ajiye a kan kujera ta saka, ta kama kasan hijabin ta goge fuskarta da
shi ta don gyara fuskar ta bishi a baya suka fice.

Ahmad ne shi kadai a falon ya a kallon ball Abban ya bude kofa ya shigo tana biye da shi. Yayiwa Abban
sannu da zuwa bayan ya amsa sallamarsa, yace

‘Mommynka ta kwanta ne?’

‘Ban sani ba Abba ta dai shiga ciki.’

‘To bari na duba.’

Ta karasa ta zauna yayinda Abban ya nufi dakin Mommy shi kuma Ahmad ya wuce dakinsu. Tana nan
zaune suka fito Mommy tana biye da shi tana sanye da hijabi

‘Umman Nawwara sai da Abba ya taso ki ko?’

Ta dubi Abban tace

‘Ai da ka barta ka gaya mata rabon kwanan a can.’

Suka zauna shi da Mommy din kowa a kujera da ban. Kafin suce wani abu Saudah tace

‘A’a nice ma na taso shi, Allah ya sa baki kwanta ba ke dai.’

‘A’a idona biyu, ina yaran? Duk sun yi bacci?’

‘Um.’

Suka danyi shiru ita Mommy a tunaninta tarasu yayi don yayin musu rabon kwana kamar yanda yayi
lokacin da ta dawo. Saudah ce ta katse musu shirun

‘Dama cewa nayi ya rako ki na sake baki hakuri, na san dazu baki hakura ba.’

Ta sake marairaicewa sannan ta cigaba

‘Don Allah kiyi hakuri ki janye wannan karar Mommy, wallahi ban fadawa kowa wannan maganar ba ban
san yanda akayi Balaraba ta je ta fada ba. Don Allah ki janye wallahi bazan sake ba.’

Ta tabe baki ta kalli Abban wanda yake ta wani faman yage baki, takaici ya kamata. Wato shi nan zuwa
ma yayi da shi da matarsa su saka ta ta janye kara. Ta tabe baki tana kau da kai tace

‘Ai na gaya miki maganar tana hannun lawyer dina watakila bayan mun dawo daga kotun sai a duba
yiwuwar janyewa.’

Ta dago ta dubeta a razane yayinda shi kuma Abban ya tsuke fuska, yace

‘Ah, ai shi magana kawai za kiyi masa ki bashi umarni ya janye karar.’

Ta bishi da kallon takaici, ta rasa ma me yake damun mutumin nan yana abu kamar wani yaro. Da ba shi
yace zai mata hayar lawyer ba amma yanzu ya zo yana cewa ta janye.

Ta tabe baki tace
‘Gaskiya ba zan janye ba, ai ba a nan tayi min kazafin ba da zata biyo ni nan cikin dare ce nayi hakuri.
Mutum ya yaga maka zani a kasuwa ya biyoka daki zai daura maka ai an zo da rainin hankali. Duk tsawon
lokacin da aka dauka bayan ta yada abinda ta yada me takeyi bata zo tace nayi hakurin ba sai yanzu
bayan na shigar da karar, ni ai na zata ma tana da wasu hunjoji kwarara da ta tanada.’

‘Wallahi babu wata hujja, don Allah dai kiyi hakuri na san nayi miki laifi amma in sha Allahu ba zan sake
ba.’

Ta kawar da kanta ba tare da tace konai ba, Abba yace

‘Kiyi hakuri mana, komai ya wuce ai in sha Allahu bszata sake ba.’

Ta dan yi murmushi da gefen baki tace

‘A wajen ku ne ya wuce ni a wajena bai wuce ba, muna nan da ku ta haihu babu rai tace ni na kashe
yaron a lokacin ba mutan unguwarnan kadai ha har kai ma sai da ka zarge ni. Har yau har kwanan gobe
bata taba cewa nayi hakuri ba a kan wannan kazafin kisan da tayi min kai ne kace komai ya wuce. Haka
na bawa kaina hakuri na bari komai ya wuce, da yake ban dauki wani mataki ba shine yanzu ta zagayo
tayi min kazafin Zina kuma kake ce min wai komai ya wuce. Yanzu ma na bari ya wuce? Hmn!’

Saudah ta bude baki zata yi magana Abban ya riga ta

‘To ai daman duk wanda aka ce yayi hakuri an san an cutar dashi, ki daure dai ki janye tunda kinga yanzu
ai ta gane kurenta. Shi dan Adam haka yana canja hali ai kuma idan mutum yayi nadama ai sai ayi masa
uzuri ko.’

Ta tabe baki tace

‘Uhm! Abinda ya hana tayi min uzuri lokacin da take yada zancen shi yasa nima bazan yi mata uziri yanzu
ba. Tun kafin a haifeta kake aurena amma ban taba tafiya yawon bariki ba saida aka haifeta ka aureta
sannan nafara. Idan na janye karar yanzu ka ga ai wadanda suke yada zancen suna can suna ta cigaba da
yadawa, amma idan muka je kotu na tabbatar za su sami labari watakila ma a gabansu za ayi. Ka ga daga
nan sai su dauko sabon labari su soke wancan da suka yada. Watakila dai idan an yi zaman farko ko
kuma idan muka shiga kotun sai ayi sulhun a gaban alkali.’

Gaba dayansu binta sukeyi da kallo cike da mamaki, musamman Abba da yake ganin kamar shi take jin
haushin don a maganganunta gaba daya da shi take kuma shi take kallo.Yanda take maganganun nan
yanzu baya so ya sake bata hakuri don ya fara tsoron abinda zata gaya masa. Abinda zuciyarsa take son
ya fada da ban amma bakinsa yaki bashi hadin kai don haka ya jijjiga kai yace

‘To Allah dai ya huci zuciyarki don ina ganin janye karar dai shine maslaha. Amma zuwa da safe ma
karasa maganar.’

Bata da niyyar magana don haka ya mike ya dubi Saudah

‘Muje.’

Ta dubi Mommy ta kara marairaicewa

‘Ki yi hakuri don Allah, sai da safe.’
Suka fice suka barta an ba tare da tace musu komai ba. Suna ficewa tayi tsaki ta mike ta leka dakin su
Ahmad tace masa yazo ya rufe musu kofa. Ta wuce dakinta ta turo kofar ta yada hijabinta akan dadduma
ta zauna a gefen gado, ta saka fuskarta a cikin tafukan hannunta ta runtse idonta. Nan da nan hawaye
tsuka fara bin idonta. Yanzu shi Abba ko kunya bai ji ba ya zo yana wani cewa ta janye kara, shikenan sai
a dinga ci mata mutunci ana zagayowa ace tayi hakuri. Wannan zancen da Saudah ta yada ya janyo
mutane da yawa sun rage mu’amala da ita, saboda wasu zancen ya koma kunnen mazansu har sunce su
daina kulata. Bata so ta gaya masa maganganu masu zafi haka ba amma abubuwa ne suka taru suka cika
mata zuciya, bata da lokacin yi da Saudah saboda ba sa’ar yinta bace, shine dai-dai da ita don haka dole
ta gaya masa abinda yake mata wanda bata so. Bata son magiya, ta tsani a dinga yi mata magiya ana
hadata da Allah a kan abimda Bai fobkarfinta ba wannan shine dilim da yasa ake yawan cutarta saboda
da ance tayi hakuri don Allah take hakura. Tabbas Saudah din ta bata tausayi kuma taga kamar da gaske
tayi nadama, sai dai ita kuma yanzu bata jin zata saurari kowa a kan wannan zancen. Sai da ta gaji da
zama ta share fuskarta ta juya zata kwanta sai kuma ta canza shawara. Bandaki ta shiga tayo alwala ta
dawo ta tayar da sallah duk da tayi shafa’I da witri. Raka’a biyu tayi sannan ta daga hannu tana rokon
Allah ya zaba musu abinda ya fi alkhairi garesu baki daya.

………..

Su Saudah suna shiga falon Abba ya rufe kofar yana juyowa ya ganta a zaune a kan kujera tana ta faman
goge hawayen da ta kasa tsayar dashi. Takaici ya kamashi, waccan ta gaya masa abinda take so ita kuma
wannan ta saka shi a gaba da kuka. Ya dawo inda take ya zauna kafin yayi magana tace

‘Don Allah ka sake bata hakuri ta janye, bulala fa za ayi min idan aka yanke hukunci. Ka ga yau Asabar
kuma ranar Talata aka ce muzo kotun, don Allah ka sa ta janye.’

Ya jijjiga kai cikin damuwa. Tabbas a da ya so a hora Saudah amma ai zuwa yanzu tayi nadama, ya
kamata ace Rabin ta hakura haka. Ya fara tunanin wanda zai sa yayi mata magana, tabbas ya san da
Baffa yana da rai da da yayi mata magana za ta hakura. Yanzu kam sai dai ko Baraka zai nema sai dai bai
san ko Barakar zata bashi hadin kai ba. Ya gaji da jin shesshekar kukantaya dubeta gaba daya ta bashi
tausayi yace

‘Ki bari in sha Allahu kafin talatar za a san abin yi, ba za ayi shari’ar ba in sha Allahu a nan za kuyi sulhu.’

Ta share hawayenta ta gyara zama, ta jingine kanta a bayan kujerar. Ko da aka ce ta dawo su bawa
Mommy hakuri bata zata Mommyn zata ki hakuraba saboda yanda take ganinta mai saukin kai. Sai daga
baya ta tabbatar kotun musulunci aka kai karar gashi kuma Baban Najwa ya tabbatar mata bulala za ayi
mata a gaban mutane. Ya za ayi ace a zaneta za ayi? Da wane idon zata sake fita idan aka yi mata bulala
a idon mutane. Ta sake share hawaye ta mike yayinda Shima Abban ya tashi ya shige daki. Sai daga baya
bayan ta gama saka yara a fitsari sannan ta shiryo ta bishi dakin.
EPISODE 38



Yanda Abba da Saudah suka kwana da damuwa haka itama Mommy ta kwana da damuwa. Ta san Abban
yana sonta kuma ta yarda yana son ya kare mutuncinta amma don me zai zo yace ta janye kara bayan
wannan kazafin da akayi mata? Don me zai ce ta janye? Tana ji tana gani ana nunata a unguwa, gaskiya
bazata iya janyewa ba ko sulhu za ayi sai dai ayi shi a kotu mutane su shaida alkali ma ya shaida. Babu
wanda ta gayawa wannan zancen a ‘yanuwanta sai Yaya Shafa, goyon bayan da Yaya Shafan ta nuna
mata shi ya hana ta gayawa sauran, tana tunanin ba ma sai ta daga musu hankali ba musamman Yaya
Munzali wanda yana Saudiya ma don ya je hajj. Yaranta kuwa duk suma suna bayanta saboda suma suna
kullace da wancan karon da aka yi mata kazafin tsafi, don Khalifa da Auta fada aka dinga yi dasu a
islamiyya a kan wannan zancen. Ta gyara kwanciyarta share hawayen da ta kasa hanashi fitowa. Ita ba
ita ta kara aure ba amma tunda yarinyar nan ta tare take janyo mata matsala, gaskiya ba zata janye ba
gara kawai ayita ta kare.

Haka ta kwana da tunani kala-kala, abunda ta sani shine gaskiya bazata iya janyewa ba ko babu komai
idan aka je kotun shine zai sa alkali da shari’a su wanketa.

…….

Tun da asuba da ta tashi bata koma saboda tanada sauran ayyuka na gyaran gidan da bata gama ba.
Tana yi tana tunani, Allah yasa dai a janye karar nan tunda dai Abban yayi mata alkawarin za a janye.
Babban abinda yake bata takaici shine yanda zancen ya fita, ita ba ita ta yada zancen nan ba amma kowa
ya ki fahimtarta. Ta tsinewa Balaraba sau babu iyaka saboda ta san wannan sharrintane, ba da ita ake
zance ba amma tana nadewa. Lokacin da suke wayar da Yaya Umma tana cikin damuwa sosai shi ya sa
gaba daya ta ma manta da wata Balaraba. Ita dai tana sa’ar haduwa da ‘yan gulma, Zulaiha ta gama nata
yanzu kuma ga na Balaraba. Sai da ta gama tsaf ta shirya abincin safe, bayan ta gama ajiye abincin a kan
table ta dubi agogon bango taga karfe 7:45am; lokacin yayi gudu sai dai ta gode Allah yara basu tashi ba.
Ta koma kicin ta dauko wayarta ta dawo ta zauna a falon ta kirawo Yaya Maryam wadda ta sanar da ita
suma gasu sun kama hanyar Bauchi. Ta bata labarin duk abinda ya faru inda ita kuma ta kara jaddada
mata ta cigaba da lallabawa. Tana ajiye wayar Abba ya fito daga dakinsa, bayan ta gaishe shi ya karasa
inda take ya zauna. Ya dubeta yace

‘Kin sa wa wayar layi ne ko kin samu kin yi swapping din?’

Ta sunkuyar da kai sannan ta bashi amsa

‘A’a wani ne na saya, wancan ai kai ne zaka iya yi min swapping din.’

‘Hakane fa, to bari na fita yau ko a barshi tunda kin sami wani.’

‘A’a gara dai ayi don kaga ko file dina na makaranta ma shine a kai. Gara dai a dawo da shi.’

‘To za a dawo da shi in sha Allahu.’

Gabanta sai faduwa yakeyi kada ya taso da maganar iphone dinta, sai wasu ‘yan soshe-soshe takeyi. Ya
mike ya nufi kofa yana fadin

‘Bari na shiga cikin gidan idan na dawo sai na ci abincin.’
Tayi ajiyar zuciya bayan ya fice, ta mike ta shige daki.

Yanda take ta sunne kai tana soshe-soshe ya bashi dariya don bayan ya fita sai da yayi murmushi. Ya san
ta zata zai yi mata maganar wayarta ne amma ba zai yi ba, zai jira har sai ita da kanta ta kawo kanta da
zancen. Ya dai yi alkawarin shi da kudinsa ba zai sake saya mata waya ba ko me zata yi sai dai idan ita ta
saya ko wani ya saya mata, tunda gashi nan ya bata iphone a lokacin da take da tsada amma taje ta
sayar dubu chasa’in.

…………

Yaranne su kadai a falon Mommy suke hidimarsu suna cin abinci, yana shiga bayan sun amsa sallamarsa
suka gaishe shi. Ya karasa ya zauna yana fadin

‘Ina Mommy? Ko bata tashi ba.’

Khalifa ya bashi amsa

‘Ta tashi yanzu ma ta koma daki.’

Ya tashi daga inda ya zauna ya wuce dakin nata. Tana zaune a kan dadduma ta jere kwalaben turaren
wuta da humra a gabanta tana zuba wadanda aka saya a leda. Bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya
zauna a gefen gado yace

‘A’a, bari na zauna na kwashi kamshi, ya naga ana ta karkasawa a leda?’

Ta dan yi murmushi a takaice

‘Saya akayi zan bayar a kai wa masu shi.’

‘Alhamdulillah, Allah ya karawa kasuwa albarka Hajiya Rabi.’

Ya fada yana janta da hira. Ta amsa itama tana murmushi, suka yi shiru na dan lokaci. Ya kula dai bata
cikin yanayin walwala duk da ya san dalili Kuma ya san tana jin haushinsa, yayi gyaran murya

‘Rabi.’

‘Umm.’

Ta amsa ba tare da takalleshi ba.

Yayi shiru bai ce komai ba ita kuma ta cigaba da aikin da takeyi, yaga dai tabbas bazata kulashiba don
haka ya sake kiran sunanta

‘Rabi.’

Ta saki ledar hannunta bayan ta saka kwalabar turaren a ciki ta dago ta dubeshi

‘Na’am.’

Ya kalleta suka hada ido kamar wanda yake nazarin fuskarta sannan yace

‘Don Allah kiyi hakuri ki fahimceni, ba wai ina goyon bayan Saudah bane saboda tabbas na san ta cutar
dake wanda a cikin haka nima din ta cutar dani. Idan kuka je kotun nan kinga ai abin ba zai yi dadi ba,
kuma ace yanzu ina nan matsala tsakanin matana sai anje kotu? Ina ga ai tunda ba rai aka kashe ba zai fi
kyautuwa kuyi sulhu a nan duk da idan kince sai an je kotun fa ba wai zan hana bane. Wannan cutarwar
da tayi miki na san babban abune kuma nima ya taba mutuncina Allah ne kawai zai bi miki hakkinki shi
yasa ma nake hadaki da Allah kiyi hakuri tunda kinga ita din ma yanzu ta gane kurenta.’

Tayi murmushi ta kalleshi suka sake hada ido, ta kawar da nata idon ta kalli gefe

‘Kayi hakuri ka fahimceni, ba wai naki jin maganarka bane amma idan munyi sulhu a gida ya za ayi
wadanda ta gayawa zancen su sani su daina yadawa? Har yanzu fa maganar ake a unguwa don ko jiya a
islamiyya saida wata tayi min maganar. Ni kaina ban zata abun ya kai girman haka amma ka san yanzu
wasu zancen da suke shine wai kanjamau ne dani shi yasa kishiyata ta bar min gidan kada na shafa mata,
ina fita ana nunani ana nuna yarana.’

‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, subhanallah kice nima din kallon da ake min kenan? Wai me yasa ne
mutane suke son su dauki maganar da ba alkhairi ba suyi ta yadawa.’

Ta tabe baki ta kauda kai

‘Gaya musu akayi ai ko? Ita magana lokacin da take cikinka ne kake rike da linzaminta amma da zarar ka
saketa ta fito to mutanene za su ja linzaminta su kaita inda suka ga dama a yanayin da suka so.’

Bashi da abinda zaibiya sake fada don haka yayi shiru, itama din tayi shiru kowa da abinda yake tunani.
Jimawa kadan yace

‘Rabi.’

Ta ture ledodin da zuwa yanzu ta gama zuba kayan a ciki ta kukkule, ta dago ta kalleshi ba tare da ta
amsa ba

‘Duk da haka babu abinda zan iya yi miki sai dai na kara baki hakuri kuma duk da haka inaso zuwa gobe
ki sake duba yiwuwar janye wannan karar a samu ayi sulhu a gida. In sha Allahu wannan maganar idan
muka barta za a gaji a daina yinta tunda ni dai ina nan tare dake da izinin Allah.’

‘Uhm!’

Jimawa kadan ya mike tsaye yana fadin

‘Bari na je na shirya na fita kada cefanenki ya sami matsala ko?’

Tayi dariya

‘Gara kam ka bada himma, a dawo lafiya Allah ya bada sa’a.’

Bai dade da fita ba Madu ya buga mata kofa, tace ya shigo. Yana shigowa ya zauna nan kusa ita yace

‘Hajiya Mommy me turare, bari in dauko rigata ki goge hannu yau in shiga kasuwa ina basu kamshi.’

Tayi dariya

‘Ka kaisu in kaya ne.’

Suka dan yi shiru jim kadan yace

‘Mommy Abba cewa yayi ki janye kara ko?’
Ta kalleshi da mamaki don a iya saninta ba ayi wannan zancen a gabansaba, ta san dukansu da kanta ta
gaya musu halin da ake ciki don Madu ma shine yake biyan lawyer duk wani charges kamar yanda Abba
ya umarta; jiya kawai suka

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login