Showing 195001 words to 196754 words out of 196754 words

Chapter 66 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15370

ya bugo wa Abba waya ya sanar da shi ya
gama yi musu order din kayan gado daga Turkey ana jiran Abban ya fadi ranar da za a doro kayan, kawai
sai ji tayi yana cewa

‘Bari naga ko za mu sami visa zuwa jibi sai mu wuce Turkey din ni da Mommy idan naje sai a doro kayan.’

Sukayi sallama suka ajiye waya.

Ba karamin bacin rai Saudah ta shaka ba lokacin da yace mata zasu wuce Turkey, da kyar ta hadiye
malolon da yake makogoronta tace

‘Allah ya kiyaye hanya, to daga can kuma sai ina za ku wuce.’

Yayi dariya yace

‘Sai Nigeria in sha Allah.’

Sukayi sallama suka ajiye waya, ta ja tsaki ta gyara zama. Sai kace masu honeymoon sai ana jiran ku
dawo sai ya wani ce sun wuce wannan kasa shi ko kunya ma baya ji. Gashi duk ta riga ta cinye kudin da
ya bari a durowa a kan bukatunta na son zuciya, kuma tana jin Madu bai isa ta tambayeshi ba. Da yake
ma yaran gaba daya basa shiga harkarta, ko yaran aka zo kaiwa makaranta sai dai Salim ya shiga mota
yayi ta danna mata horn har su fito. Don haka jin kanta take kamar a prison tunda Abban da yake kulata
baya nan.

Sai da suka kwana bakwai a Turkey sannan suka dawo Nigeria, da yake ta san da dawowarsu ta shirya
masa abinci da duk wani abu da yake bukata. Suna sauka a gidan ya wuce dakin Mommy, duk kayansa
can aka ajiye masa da na Mommy gaba daya. Yana dakinsa Mommy ta sameshi tace

‘Sannu da hanya Abba.’

‘Sannunmu.’

‘Kaga yanzu idan ka tafi wajen Umman Nawwara na baku sati daya ka huta a can tunda kaga mun dade.’

Ya kalleta yana dariya

‘To ai fa shikenan mun dawo Nigeria Rabi ta daina so na yanzu zata fara korata.’

Tayi dariya tace

‘Duk cikin so ne, ka ga ita da yara duk sunyi kewarka babu komai kayi min godiya kawai ka wuce.’
‘Idan ban gode ba zaki fasa kenan?’

‘Sai dai na kara maka sati daya watakil isarkane sati daya bai yi ba.’

‘To ban karba ba, sati dayan dai na karba.’

Ta fice ta barshi yana mamaki, lokacin da suka je Dubai da Saudah ranar da suka dawo ya fara rabon
kwana ta kan Mommy sai da tayi mita, wai ai a wajenta ya kamata ya zauna su huta tare.




Duk da ya gaya mata ba zai saya mata waya ba amma bata taba sa rai ba zai saya din ba, sai da taga ya
gama bata tsarabarta; Abaya guda uku, set din sarka da dankunne fashion masu kyau da agogo sannan
da takalma guda uku ga turaruka da kayan bacci duka ya hada mata su a wata travelling bag mai kyau ya
bata, ga yara ma an siyo musu kaya kowa kala uku da takalmi sannan Mommy ta siyo musu kayan wasa
da chocolates. Ta ji dadi saboda kayan daga gani duk masu tsada ne sai dai kawai ta so ace wayar ya
bata. Ta ga computer a kayansa sabuwa dal ta zata kanshi ya siyowa don haka tana ta tsara yanda zatayi
ya bar mata kawai sai taga ya bawa Auta.

Sai da sukayi sati biyu da dawowa sanna furniture din Abba suka zo, akwai wani karamin gado da Madun
ya hado da shi wanda shi irin na turawa ne bashi da girma sosai, mudubi shi ma haka sanna da dan tebur
na karatu wanda har an riga an biya kudin.

Ranar lahadi Mommy ta shirya ita da Auta da Zahra Ahmad ya tafi kaisu Jigawa, sai a lokacin Madu ya
gayawa Abba Mommy ya sayowa wannan gadon. Ya ji dadi kuma yayi mamaki, ya sa masa albarka. Wasu
lokutan yana kishin yanda Madu yake son Mommy yake son burgeta kuma in ya tashi sai ya burge kowa
ma. Nan da nan aka kawo kaya aka fara aiki, har wallpaper ya sa aka saka mata a bango daya, ya canza
labulayen da carpet ya sa mata furniture din da teburin karatu wanda aka dora ‘yar fitila a kai, Khalifa ya
sake jera mata kayanta a wardrobe kamar yanda take so sannan ya kunna turare. Nan da nan waje ya
dauki kamshi. Sai wajen biyar na yamma suka dawo lokacin Khalifa ne kawai a gidan, tana shiga falon
tace

‘Khalifa ka san turaren da ka kunna idan na sayarwa ne sai ka saya ka biyani ki don ba zan yarda ba.’

Yayi dariya yace

‘Yes Mommy, zan biya na sayawa mamana.’

Tana bude kofar dakin ta tsaya a bakin kofar tana mamaki, ta ma rasa me zata ce. Ita gaba daya Abba ta
kawo duk da ta san ba irin wadannan gadajen yake sayarwa ba amma dai shi ta kawo don taga kwana
biyu abun kirki yake ji. Khalifa ne ya karaso kusa da ita ya ja hannunta ya karasa da ita ciki yana ta washe
baki yace

‘Hajiya Mommy Alhaji Muhammadu Usman Usaini ne ya gyara miki daki ni kuma na gyara miki
wardrobe.’
Tace

‘Madu?’

Auta yace

‘Shi mana.’

Sosai taji dadi kuma tayi mamaki, haka ta dinga saka musu albarka gaba daya.

……………

A ranar Saudah ta tareshi da mita bayan ya gama cin abinci

‘Ni sai gobe za a kawo nawa kayan gadon.’

Ya kalleta

‘Gado kuma?’

‘Eh, ai naga an canzawa Mommy gado.’

Cikin halin ko in kula yace

‘Ohh! Ai ba ni na canza mata ba Madu ne ya saya mata.’

Ta bata rai tana so tayi magana amma ya da taga ya bata rai ta san duk abinda zata fada zai iya gaya
mata mai ciwo don taga yanzu baya shayin gaya mata magana ko yaya.

‘Ai shikenan, ina kallo sai dai ayi ta bata abu ana cewa yara ne. Nima Allah ya raya min nawa yaran.’

Yace

‘Amin.’

Ta mike ta bar wajen kafin ya gaya mata bakar magana.

…………….

Haka rayuwa ta cigaba a gidan Usman, ba wai Saudah ta daina fitna bane amma dai tayi sauki sosai,
yawancin lokuta ma sai dai tsaya a kan Abban. Shi kuwa yanzu idan yaga zata daga masa hankali sai
kawai yayi mata yaji, ba zai kaiwa Mommy kwananta ba sai dai kawai ya siyo abincin sa a waje kuma ya
kulle dakinsa. Har sai ta gaji da kanta ta nemi shiri sai su shirya, haka kowa ya hakura da ita saboda
hausawa sun ce hali zanen dutse.

Duk Sallah zai yi musu kaya kala uku ita da Mommy, sannan Baba da Ahmad za su yiwa Mommy kaya
masu tsada kowa daya yayinda su kuma Madu da Salim za su siyo mata takalmi da jaka masu kyau da
tsada ga mayafi irin wanda ake yayi. Haka shima Abban za su yi masa dinki. Sai da Mommy tayi da gaske
da su sannan suke hadawa da Baffa Karami shima suyi masa kayan Sallah. Duk Sallah da fushi Saudah
take yinta saboda ita gani take kamar kawai wayo ake mata a bawa Mommy kaya da suka fi nata, gashi
Abban yana kara bata haushi idan yaran suka yi masa dinki, ya dinga rawar kai kenan yana yabon yaran
har sai ya bata haushi. Haka ma da babbar sallah bayan an gama raba naman za a yanka ragon Madu a
shige dashi wajen Mommy tana ji tana gani. Kusan duk wani abu da take burin mallaka tana zaune sai
dai ta ganshi a wajen Rabi, in ba ayi haka ba to sai dai Abba ya sai biyu ya basu kowa daya.

Taki kuma ta gane ta kawar da kanta daga kan Rabin don haka take yawan zama cikin damuwa. Gashi ta
gama karatu result ya fito har tayi bautar kasa a makarantar ‘yan mata dake kusa dasu. Sai dai kiri-kiri
Abba ya hanata aiki, ya gaya mata shi ba zai juri fita kullum ba. In tana so sai dai ta tara alawee dinta tayi
jari ta sami wani abunda zata dinga sayarwa, ta zata zata iya canza masa ra’ayi don haka ta cinye alawee
din kuma yaki barinta aikin sannan ya hanata jari, in tayi magana sai yace:

‘Itama Rabin ba ni na bata jari ba da kanta ta nema, har yanzu babu ko dari na a kasuwancinta. Kema
idan kika samu ki fara ba zan hana ba.’

Haka dai rayuwa ta cigaba.

----------

ZULAIHA



Da yake lokacin da tana bautar kasa tana samun dan kudin alawee da gwamnati take basu to abubuwa
sun zo mata da sauki. Domin ko Baffan nata ma baya wani damunta da aure saboda yanzu tana bada
kudin cefane a gidan har shima ta bashi na kashewa. Itama Sa’a hankalinta a kwance. Bayan ta gama
bautar kasa ne matsaloli suka yi kunnowa, don a lokacin babu kudi kuma bata samu aiki ba don haka nan
baban nata ya tasa su a gaba Ita da Sa’a, ga mutan garin suna cewa ta zama uwar mata ko saurayi babu.
Mahaifinta ya bawa limamin garin ita sadaka amma kafin bikin ya hadu da hatsari ya gamu da shanyewar
barin jiki don haka aka hakura da auren. A haka sai da ta shekara uku a gida Fathiyya da Zahra har sun
haihu sannan katsam ta samu aiki a nan FCE Bichi, aka dauketa a non-academic staff. Bata shekara da
fara aiki ba ta hadu da mijin aure a makarantar. Lecturer ne shi yana da mata biyu, ita Zulaihan zai yi ta
uku da ita ya ajiyeta a nan Bichin. Nan da nan kuwa akayi biki irin wanda suke so don ya sakar musu kudi,
amarya ta tare a gidanta nan Bichi yayinda sauran matan nasa suke cikin Kano.




Rabi ce a zaune a kan teburin karatun da yake dakinta tana shigar da cinikin da akayi na zannuwan gado
da turare a wannan watan. Tsakanin zannuwan gado, turaruka da kuma burner ta sayarda kaya na wajen
naira dubu dari uku a watan, don yanzu kaya har Abuja take aikawa da su Fathiyya da kuma Ummi ‘yar
gidan Baraka suna siyar mata. Ta ajiye biron ta kalli total din tana yiwa Allah godiya, bata son kishiya
amma zuwa yanzu zata iya cewa kishiya ta zamar mata alkhairi kuma mabudin ido.

Da basu sami wannan matsalar har Abban ya koreta ba ta san da yanzu tana nana bata da komai nata sai
fada da kishiya, amma yanzu ga kasuwancinta kuma ga gidan hayarta duk shekara ana karbar mata dubu
dari uku. Gashi tana zuwa islamiyya tana cigaba da karo ilimi. Kazafin da Saudah tayi mata na yawon
bariki kuma sai ya sa aka kara saninta a unguwar saboda yanda aka dinga nuna ta, da abun ya wuce
kuma sai ya zama mutane da yawa a unguwar sun zama customera dinta musamman na turare da
humra. Su kansu yaran sai yanzu ta gane yanda suke sonta suke tattalin farin cikinta, kuma shima Abban
sai dai kawai tace Alhamdulillah domin tun bayan wannan rigimar abubuwa suka yi musu sauki. Tana
kallonsa idan matarsa ta birkice masa zai yi ta kuncinsa shi kadai, don wani lokacin ma bata ko
tambayarsa damuwarsa.



KARSHE
GODIYA



Alhamdulillah, In godiya ga Allah da ya bani ikon rubuta wannan littafin har karshe.



Godiya ga FIKRA WRITERS ASSOCIATION, Allah ya kara basira.

Masoyan labarin Rabi da masu sharhi Ina godiya, sharhinku ya kara min ilimi fiye da yanda kuke
tunani. Na gode Allah ya bar zumunci.



Domin Karin bayani 07037834667.

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login