Showing 141001 words to 144000 words out of 196754 words
Chapter 48 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
da ido tunda ko ta tambaye shi ko akwai abinda yake damunsa sai yace mata babu komai.
Haka har ranar Lahadi, tun kafin karfe tara Lalo yazo don haka yana gama shiryawa ya fito suka kama
hanya bayan ya sanar da su Madu su hadu a kasuwa. Sai da suka dauki hanya tukuna yana yiwa Lalo
kwatancen gidan Munzali don yana son ya fara ganinsa kafin ya wuce Jigawan. Bayan an yi masa iso suka
zauna a falo shi da Munzalin, ya dube shi yayi gyaran murya yace
“Dama zuwa nayi na baka hakuri kai ma game da abinda ya faru, in sha Allahu haka baza ta sake faruwa
ba.”
“Toh ai shikenan babu wani abu, nima sai daga baya Shafa take gaya min Rabin tana Jigawa wajen
Baraka sai ka sameta idan kun daidaita ma ji.”
Ya jijjiga kai
“Ai wato ita din ina ga fushi tayi don ka ga tunda ta dawo fa har yanzu bamu hadu ba. Duk yanda zan yi
na ganta ta ki tsayawa tunda har Dutsen naje sai da na tsaya a bakin kofar gidan nayi mata waya take
sanar dani wai suna Abuja.”
“Ikon Allah, kwarai sun je Abuja amma ina ga bata san za ka ba ai da sun gaya maka ko kuma ta jira ka.”
“Hakane ban sanar da ita ba. Yanzu dai don Allah ko kiranta ne kayi ka taya ni bata hakuri ina ga idan ka
sa baku sai ta fi hakura tunda na san Baraka dai sai dai ta tayata rigima kawai. Kuskure ne ya riga ya faru
kuma in sha Allahu ba zai sake faruwa ba.”
“Toh in aha Allahu zan yi mata magana sai a kiyaye a dinga hakuri, mata sai hakuri duk inda ka hada
sama da daya toh akwai bukatar ka ninka hakurinka.”
“Hakane, yanzu ma zan wuce Jigawan don Allah ko waya kayi mata don tayi hakuri mu dawo tare.”
“Jigawa kuma? Ai suna Kaduna.”
“Rabin tana Kaduna?”
“Eh, ita da Barakan suna gidan Mubarak. Ka san ranar alhamis matarshi ta haihu, an samu mace. Su
kuma daga Abuja sai kawai suka wuce Kadunan tun rana Juma’ah suna can sai ranar litinin kamar
Mubarak din yace min zaa su koma gidan Barakan.”
Ya gyara zama yace
“Ikon Allah.”
Gaba daya lissafin kanshi ya kare wannan sabani daga Allah ne ko kuwa dai haka Rabi ta tsara? Jiya da
daddare ma ya kirawota, yanda ta saba haka take amsa shi da kyar don haka hirar batayi tsawo ba balle
ya samu ya gaya mata zai zo. Don shi a wannan lokacin ma ya zata tana Jigawan, ashe tana Kaduna. Sai
da kyar sannan ya nemo nutsuwarshi yayi sallama da Munzali a kan alkawarin zai yiwa Rabin magana.
Ya fito ya sami Lalo a mota yace su koma gida. Gaba daya damuwar da yake ciki ta nunku sau babu iyaka,
wai me Rabi take nufi ne? Ya San dai karshenta so take ta kure shi ya sake ta kuma wannan ba zai yiwu
ba, ko me zata yi sai dai tayi amma ba zai saketa ba. Suna isa gida ya sallami Lalo ya shiga gidan, kai tsaye
ya shige daki ya kwanta. Bai san me yake damunsa ba ba ya son ganin kowa baya so a dameshi shi yasa
ba za shi kasuwa ba, haka ya kwata yana tunanin in sha Allahu ba zai gaji ba ranar Talata zai kuma
komawa Jigawan watakila ma kafin nan Munzali ya bata baki sa fi saurin daidaitawa.
EPISODE 31
Sosai Rabi taji dadin tafiyar nan daga Abujan har Kadunan. Tunda tayiwa Baba karami waya tace masa
tana Abuja bai huta ba, yana tasowa daga aiki zai taho ya sameta a gidan Baraka suyi ta hira. Ranar
Talata yana zuwa bayan magriba ya dauke ta suka fice, wajen cin abinci ya kaita ta zabi duk abinda take
so. Ya so ta zauna su ci a wajen amma ta ce masa sai dai idan shi zai ci sai su zauna ta jirashi ya cinye ita
sai ta je gida. Don haka sai suka hada da youghurt da ice cream aka saka musu a ledodi. Sai da suka je
gida suka zauna shi da ita da Baraka da Zahra suna ci ana hira. Sai da dare yayi sannan yayi musu sallama
ya koma nashi makwancin.
Ranar Laraba ma haka ya dawo bayan isha’I ya dauki Mommy yace zai kaita shopping, ta kirawo Zahra
suka shirya suka fice. Tace masa taji ance akwai Sahad a Abuja, yace hakane tace nan take son zuwa.
Abubuwa kadan ta dan tsinto a Sahad din da suka hada da turaruka da kuma man shafawa, haka ya
takurawa Zahra sai ta dauki wani abu don haka ta dauki janbaki da mascara. Suna fitowa har sun kama
hanyar gida ta dube shi tace
“Baba babu bookshop ne a nan kusa?”
Yace
“Akwai sosai.”
“Toh ina son na dan siya littafi don na dade ban yi karatu ba.”
Take ya juya kan mota suka nemi bookshop suka shige. Sai da ya duba agogo yaga sha daya ta kusa ya
gaya mata sannan ta hakura suka fito. Ta siyo littafai na hausa harda na turanci wadanda yawanci na
labari ne da kuma na addini, ita ma Zahra ta samo diary me kyau da biro. Sai da aka zo biya aka yi musu
total mommy ta dauko jaka za ta biya Baba ya hanata, babu yanda bata yi da shi ba saboda akwai dubu
arba’in da Mubarak ya bata kuma da su a jakarta ta fito amma shi da Baraka sun hanata kashewa, haka
ta hakura ta zuge jakar ya dauko kayan suka fito.
Ranar alhamis Mubarak ya gaya musu matarsa Maijidda ta haihu, don haka suka shirya za su fasa tafiya a
jirgi su tafi a mota ranar alhamis sai su kwana biyu a Kaduna don suyi barka. Nan da nan kuwa ta sanar
da Baban Ummi wanda yace dama shima yana so ya tafi Jigawan ranar alhamis madadin Juma’ah da
suka tsara. Suna cikin mota Mommy da Baraka a baya yayinda Zahra take gaba Mommy ta dubi Baraka
tace
“Wallahi na ji dadin zuwa Kadunan nan, ba za ki gane yanda nake ji ba.”
“Allah, kar dai ki ce min baki taba zuwa ba?”
“Kin manta tare muka zo wa Maijiddan gaisuwa lokacin da Babanta ya rasu, shikenan zuwana guda daya.
Ban taba zuwa mata barka ba sai dai ta waya, sai dai in sun je Kano naje masaukinsu nayi mata barka,
wataran ma don abun kunya sai dai kawai na ganta a gidana kafin ni naje barkan.”
“Lallai kam dole ki ji dadi.”
“Ba za ki gane ba, ina kaunar Mubarak amma kinga yaranshi ko sabawa bamuyi da su sosai ba saboda
nisa kuma ko wani abu ya faru ni ba ganina suke a gidansu ba. Kin san gaisuwar ma da kyar fa ya barni na
zo, cewa yayi wai ke da Yaya Shafa ku wakilce ne.”
Ta tafa hannu ta rike haba tace
“Dan duniya.”
“Wallahi sai da na nuna masa dole sai na je sannan ya yarda.”
“Shi dai baya so kije ko ina abunku.”
Suka yi dariya gaba daya.
Sai ranar Asabar da daddare suna hira da Mubarak yake sanar dasu Lahadi da safe zai taho Kano don
akwai kwangilar da ya samu zai zo ya sayi wasu kaya a Kano. Mommy tace
“Toh ai sai mu tafi tare, in ya so idan ba dadewa zaka yi a kasuwar ba sai mu tsaya gidan Yaya Munzali
ayi maganar gidan nan a san inda aka tsaya.”
“Kwarai kuwa haka za a yi, sai ku shirya ana idar da sallar asuba mu kama hanya kunsan ni goben zan
dawo. In ya so zan yi mishi waya in an jima don ya san da zuwan mu.”
Don haka suka kwana da shirin su na tafiya Kano ranar Lahadi da safe.
Amarya Halima ce da girki don haka itace a falon tana zaune kusa dashi suna hira wayarshi tayi waka, ta
tashi ta zaro wayar daga chaji ta mika masa. Yana karba ya amsa ya saka a kunnenshi, bayan ya amsa
sallamarsa yace
“Mubarak dama yanzu nake shirin kiranka, ya masu jego?”
“Lafiyarsu kalau Alhamdulillah, ya mutanen gidan.”
“Lafiya kalau.”
“Ina su Rabin.”
“Suna nan, kiranka ma nayi magaya maka gobe za mu taho tare dasu zamu fara zuwa wajenka tukuna ni
sai na barsu a nan na wuce zan je kasuwa ne.”
“Toh yayi daidai, dama nima neman da nake maka ce maka zanyi ka ce musu su tsaya a Kano ina son
ganin Rabi toh tunda ma za ku zo goben shikenan.”
Sukayi sallama suka ajiye wayar, ta tashi ta karbi wayar ta mayar ta sa masa a chaji. Tana zama ta
dubeshi tace
“Rabi ta ki ta zo mana ko da ziyara ta tafi wajen Baraka ta ‘buya.”
Ya jingina da kujerar ya fuskanceta sannan ya bata amsa
“Ko nima maganar da zan yi mata kenan, yanzu fa suna Kaduna. Ta biyewa Baraka sai yawo suke yi ba
tare da ta nemi izinin mijinta ba.”
Tayi dariya tare da tafa hannuwa
“Wai wane mijin, wanda yace ta fice masa gida? Shine za ta tambaya idan za ta fita. Kai ma dai wallahi,
toh ai ko ni kace na fice maka daga gida wallahi sai inda mai na ya kare.”
Ya kalleta da mamaki
“Eh tunda an tabo mutuniyarki ai kya ce haka. Matar aure ce ita har yanzu don haka kinga duk inda za ta
je tana bukatar ta nemi izinin majinta.”
“Toh wane izini kuma, ba shi ya bata blank ticket ba ka ga kuwa kawai sai ta cike destination ta dau jaka
a dawo lafiya. Ai wannan kalma ta fice min daga gida tana nufin duk inda ba gidansa bane taje.”
Ya kalleta ya kara bata rai, ya mayar da kallonsa kan talabijin din dake falon sannan yace
“Hmn, Allah ya sa ma ba ke kike zugata ba don wannan zancen banzan da kikeyi ban yarda dake byac
Ta gintse dariya don ta kula ya fara hasala, tace
“Ni tunda ta dawo ma kobwaya bamuyi da ita ba, Yaya Shafa dai ta turo min sabuwar lambarta amma
Allah bai sa na kirawo ta ba, watakila dai zuwa jimawa mayi wayar ko gaisawa ne muyi.”
Ya juyo ya galla mata harara ya jijjiga kai sannan ya sake mayar da dubansa ga talabijin din. Ta gintse
dariyarta ta tashi ta fice daga falon tana masa dariya ta san ana jimawa za su shirya. Ya bi bayanta da
kallo yana mamaki, wai ko su mata bakinsu daya ne. Mutumin da yayi kuskure kuma shima ya ji haushin
wulakancin da aka yiwa ‘yar uwarsa amma mutumin nan ya nuna yayi nadama toh a hakura mana.
Menene kimar mace idan ba aure ba, bayan shekaru sama da talatin a gidan miji kuma yanzu me ya
ragewa mace idan ba tayi hakuri a karasa ba, rabuwa yanzu kam ai sai dole.
Da yake sun taho da wuri kafin karfe tara da rabi suna Kano, sai da suka biya suka taho da Shafa sannan
suka isa gidan Yaya Munzali. Suna isa Halima ta riga ta shirya musu abincin safe, don haka nan suka
zauna tare da shi suka karya. Sai da suka gama aka kwashe kwanukan sannan Mubarak yayi gyaran
murya yace
“Yaya dama akan maganar gidanmu ne, muna so a sayar da shi a bawa kowa rabonsa.”
Baraka ta mike ta bi bayan Halima da wasu kwanukan saboda wannan ba zancen da zata sa musu baki
bane.
Bai zata zancen da za suyi masa kenan ba don ya zata sun kyale masa gidan. Idan banda Shafa da duk
karshen shekara sai ta tambaye shi kudinta Mubarak da Rabi duk ya kwana biyu bai basu ba Kuma basu
nema ba. Idan yace bari ya ranta ya biya su daga baya yaji sun yi shiru shikenan. Babu yanda zai yi da su
don sun wuce ayi musu wayo kuma ko babu komai shima yana so ya basu hakkinsu ya huta. Ya gyara
zama yayi gyaran murya yace
“Uhm, hakan ma shawarace mai kyau, tunda daman kwana biyu da kyar ake yago kudin hayan.”
“Yauwa nima shi na gani, idan aka siyar sai a nemi alkali ya raba kowa a bashi rabonsa, rabon Umma
kuma sai a sake rabawa tunda ka ga da ranta Baffan ya rasu itama sai an fitar da nata.”
Shafa tace
“Hakane, Allah ya ji kansu.”
“Amin.”
“Toh akwai dai ‘yan haya a ciki kuma duka shagunan jikin gidan ma da ‘yan hayan, don haka ka sa lokaci
ka dawo muje wajen wanda yake kula da gidan sai a saka shi a kasuwa a bawa mutanen notice.”
“Toh hakan yayi, zuwa wani satin in sha Allahu zan zo, ko kuma ma kuje da Yaya Shafa kawai yanda aka
yi ma ji.”
Shafa ta dube shi tace
“Hakan yayi, Juma’ah mai zuwa babu aiki sai muje.”
“Toh Allah ya nuna mana.”
Suka karasa hirarrakinsu daga baya Mubarak ya barsu a nan ya fice shi da Yaya Shafa. Nan Munzali ya
bar Halima da su Rabi ya shiga ciki don ya shiryo ya fita. Sai da ya shirya ya koma falon nashi ya kirawo
Halima yace ta turo masa Rabi.
A zaune ta sameshi a kan kujerar zaman mutum uku don haka ta zauna a kujerar zaman mutum daya
Dake kusa da ita.
“Rabi.”
Ta dubeshi
“Na’am Yaya.”
“Sai yaushe za ki koma?”
“Yanzu za mu tafi ai Yaya.”
“Ba gidan Baraka nake nufi ba, yaushe za ki koma naki gidan.”
“Toh ai sai yanda ta yiwu.”
“Yaya za kice haka? Usman din har nan yazo ranar Talata da shirinsa na wucewa Jigawa wajenki sai ni na
gaya masa kuna Kaduna. Ya kamata ai ki hakura ki koma ko ni ma baki ga yanda yake ta bani hakuri ba.”
“Ni kam ai bamu hadu dashi ba.”
“Ina za ku hadu baki tsaya ba? Kina ta yawo da aure a kanki ba tare da izinin mijinki ba?”
“Toh ai Yaya shi yace na fice masa daga gida, ka ga kenan duk inda naje idan ba gidansa bane ai banyi
laifi ba.”
“Kinyi laifi mana, kina yawo babu izinin mijinki.”
Ta kalleshi yayinda mamakinta ya karu
“Toh Yaya shi ya koreni ba tare da ya gaya min inda zan je ba, kuma sai na zauna a cikin kunci ina jiran
abinda zai ce? Ai duk wani abu da zai fada ya gama fada Yaya, sai da ya kafa shaidu a gaban yaransa da
matarsa sannan yace na fitar masa daga gida. Ko baya so na ai yayi min kara saboda yaran da yake so
idan dai so ba karya bane.”
Ya jijjiga kai
“Kowa ya san bai yi miki adalci ba amma ki yi hakuri. Kin dade da sanin zaman aure babu komai a cikinsa
sai hakuri don haka ni ma ina baki hakuri ki koma dakinki, shima idan kin tsaya kin saurareshi zai baki
hakuri da kansa. Damuwar da ya shiga lokacin da na ce masa kina Kaduna na san ba zai sake yi miki irin
wannan ba, don haka ki dubi Allah kiyi hakuri.”
Ta dauke kai tace
“Toh Yaya.”
A ranta kuma tace ai dai toh bata karya wuya.
“Don Allah kuma kada ki sake fita ko ina ba tare da saninsa ba.”
“Babu ma inda zan sake zuwa sai dai idan wani abun ne ya taso.”
Ya kalleta ya jijjiga kai don ya san wannan amsar tana nufin idan wani abu ya taso za ta fita kenan. Suka
yi shiru na dan lokaci sannan yace
“Toh don Allah ki kira shi ki sanar da shi kin koma Jigawan idan kun isa.”
Ta bata rai ta dauke kanta tace
“Ni bazan kirashi ba in dai ya kirawo ni zan gaya masa.”
Yanayin fuskarta ya nuna masa tabbas tana nufin abinda ta fada don haka yayi shiru. Bayan wani lokaci
ya mike yace
“Ni bari naje na fita.”
“Toh Yaya a dawo lafiya.”
“Allah yasa, kuma ina dada baki hakuri ko albarkar yaranki ai ya ci ko.”
Ya sa jai ya fice. Basu jima ba suka fita ita da Baraka, sai da suka tsaya a kasuwar kurmi suka sayi kayan
turare sannan suka kama hanyar Dutse.
Tun ranar Lahadi da daddare Yaya Munzalin ya kirawo shi ya sanar da shi Rabi ta koma Dutse, don haka
ranar litinin da safe ya kirawota a waya bayan ta tabbatar masa tana nan ya kama shiri. Sai da ya gama
shiryawa tsaf sannan ya fito falon ya zauna cin abincin safe, bayan ya gama ya sami Saudah a kicin yace
“Yau ba za ki makarantar bane?”
“Eh, ka san mun shiga level 4 lectures din babu yawa don ma ina da carry overs ne. Project ne yafi shigar
damu makarantar.”
“Ok, toh ni fita. Za mu tafi Dutse sai na dawo zan tsaya a kasuwar.”
Ta kalleshi da alamar tambaya kafin tayi magana yace
“Kin san Rabi tana can.”
Ta fasa fadan maganar da zata fada tace
“Allah sarki, Allah ya kiyaye hanya.”
“Amin.”
Ya fice ta bi bayansa da kallo, sai da ya gama wucewa taja tsaki. Gaba daya haushi yake bata sai ya dinga
maganar wata tsohuwar matarsa kamar wanda zai je zance wajen budurwa. Kalli yanda yayi wata
kwalliya sannan yana yashe baki yana gaya mata Dutse zai je, wato yanzu su ko kunya basa ji kenan haka
zai dinga tafiya har Jigawa zance. Gaskiya ba zata jura ba, in dai ya cigaba da wannan gantalin dole ta
dau mataki.
Cikin walwala da nishadi suka yi tafiyar yana ta yiwa Lalo Hira. Suna zuwa aka yi masa iso ya shigo ya
zauna a falon kasa, mai aikin Baraka ta kawo masa ruwa da lemo ta ajiye ta fice. Ta koma falon cikin
gidan ta sami Baraka da Rabi tace
“Hajiya an kai masa ruwan.”
Ta wuce kicin. Baraka ta dubi Rabi tace ke fa yake jira. Ta tabe baki tace
“Toh ai sai ki tashi muje.”
Tayi dariya tace
“Ni a suwa? Ki dai je daga baya na zo mu gaisa.”
Ba tare da ta ce komai ba ta mike ta nufi falon. Tunda ya jiyo motsi ya zubawa kofar ido, duk da wani
barin na zuciyarshi yana gaya masa Baraka ce ta taho. A hankali ta bude kofar ta shiga da sallama, sai da
yaji kamar an tsayar da bugun zuciyarshi kafin da kyar ya samo nutsuwarshi ya amsa mata sallamar. Ta
zauna a kujerar zaman mutum daya wadda itace tafi kusa da kofar da ta shigo. Fuskarta kawai yake kallo,
tayi haske kuma ta yi kyau, ji yake kamar ya fi shekara bai ganta ba. Fuskar tata bata dauke da wata
damuwa ko fushi, shi gani ma yayi kamar murmushi take don haka shima ya fara murmushi. Tasowa yayi
daga inda yake zaune ya dawo kujerar da take kusa da ita, ya zauna ya dan zamo gaba yanda zai dinga
ganin fuskarta sosai. Yana zama suka hada ido sannan ya tabbatar tabbas murmushin take yi wanda
shima bai san sanda ya mayar mata da murmushinta ba
“Rabi kenan.”
Ta dan dauke kanta saboda kallon da yake mata yana kokarin dole sai sun hada ido ya fara isarta.
“Uhm, ina kwana.?
“Lafiya
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good