Showing 147001 words to 150000 words out of 196754 words

Chapter 50 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15404

sonta kuma za ka rike min ita
amana don bana son ku zo ku aurar min yara kuma ku kasa rike min su.”

“In sha Allahu mommy ba za a samu matsala ba.”

“Toh Allah ya sanya albarka a ciki, bari ta dawo sai muyi maganar.”

Ta ji matukar dadi da wannan aure guda biyu da ake shirin kullawa, fargabarta daya kada a sami
matsalar da zata taba musu zumuncinsu. Duk da ba ta shakkar yaran gaba dayansu amma ta san ‘dan
Adam yana canzawa a kowanne lokaci. Duk da haka ta ji dadi kuma zata yi ta addu’a daga nan har
karshen rayuwarta a kan Allah ya hade mata kansu ya bar musu zumuncinsu. Bata sa rai Ahmad zai yi
aure yanzu ba amma ta ji dadi sosai tunda dukansu suna aiki kuma suna samu daidai gwargwado,
zamansu haka zai iya zama fitna musamman Baba karami da yake Abuja.

Suna nan zaune aka kirawo Sallah don haka Ahmad dasu Madu suka fice masallacin kofar gida don suyi
sallah yayinda ita kuma Mommy ta haye sama don yin tata sallar. Bayan an idar da sallah Ahmad ne ya
fara shigowa ya wuce kan dining table ya zauna inda suka tashi suka bar chess din da suke wasa dashi.
Suna shigowa su kuma suka zauna suka kunna TV, Madu ya kai sport’s channel don shi mayen kwallon
kafa ne, suna kallo suna hira. Suna nan zaune Zahra ta sauko ta shigo falon da sallama bayan sun amsa
sallamarta ta dubi su Madu tace

“Ashe kune kuka zo, ina wuni.”

Suka amsa a tare

“Lafiya kalau.”

Ta wuce ta nufi kicin tana fadin

“Inna tana kicin ne.”

Salim yace

“Inna daya ta fita, daya Innar kuma tana sama.”

Suka danyi dariya gaba daya har itama ta tayasu. Ta karaso wajen dinga table ta dubi Ahmad tace

“Ina wuni.”

Duk da yaji shigowarta amma sai yanzu ya dago ya kalleta da murmushi ya amsa gaisuwarta. Ta kama
hanya kamar za ta wuce kichin din yace

“Ki samo min ruwa na sha.”

Ta juyo tace

“Mai sanyi ko mara sanyi?”

“Mai sanyi.

Jimawa kadan ta fito da robar ruwa da kofin tangaran a tray, ta ajiye a kan dining table kusa da chess din
da yake wasa dashi tace

“Ga shi.”

Ya dubeta yana murmushi yace

“Na gode.”

Idonta yana kan game din da yakeyi kafin ta juya yace

“Kin iya chess ne.”

Tayi yar dariya tace

“Ai in dai mutum yana zaune da Inna dole ya iya wannan game din.”

“Toh ki zauna muyi.”

Ya ja mata kujerar kusa da shi ta zauna, suna game din suna hirarsu babu wanda yake jin abinda suke
fada da yake ma inda suka zauna sun bawa su Madu da Salim baya ta gefe. Can jimawa Salim ya dago
daga kallon tv ya kallesu yayi murmushi. Ya sa kafa ya tabo Madu, ya nuna masa su da baki. Suka kunshe
dariyarsu a bakunansu, Madu ya dubi Salim yace

“Ikon Allah, an zo daidai wajen kenan.”

Salim yayi Yar dariya yace

“Ai kwarai kuwa.”

Suka ci gaba da kallonsu.

A nan mommy ta sauko ta samesu sai da shige kicin sannan Zahra ta tashi ta bi bayanta. Nan da nan aka
zubawa kowa abincin rana, kafin su fara ci Baraka ta dawo da su Khalifa suka zauna gaba daya suna cin
abincin. Daga baya Mommy take gayawa Baraka sakon Ahmad suka hadu suka yo ta murna. Baraka tace

“Tsoro na daya sai dai aje gidansu da hakuri.”

Mommy tace

“Na me fa?”

“Toh da ita da shi duka basa son jama’a kuma gasu da mugun shiru da miskilanci.”

Tai dariya

“Yaran da za su haifa ai za su saka su surutu ko ba sa so.”

Sai da aka kusa Kiran magriba sannan suka kama hanya suka koma Kano.
EPISODE 32



Tana shiga gidan Umma bayan sun gaisa ta bar yaran a wajen Yaya Ummu ta shige daki ta kwanta, sai
daf da azahar sannan ta farka. Tayi juyi tare da mika a ranta tana fadin ‘haba ai na huta, ace mutum
bashi da hutu sai dai yayi ta yawo yana gyangyadi.’ Tana turo kofar dakin za ta fito ta juyo muryar Kaka
tana wasa da su Nawwara, sai da gabanta ya fadi saboda ta san dole sai kaka ta tuna mata maganar
kudin nan. A hankali ta fito ta zauna ta gaisa da kaka sannan ta wuce bandaki ta yiwo alwala. Sai da ta yi
sallah ta gama cin abinci sannan kaka ta sameta a falon Umman tare da Yaya Ummu da kuma Umman

“Na ji ki shiru Saude, kudin malamin nan fa don wallahi kin san idan ba’a bashi ba sai ya taba mu ni da
ke. Domin kayan nan da kinyi amfani da su daidai toh da yanzu wani zancen muke ba wannan Umma

Ta juya kai cikin damuwa tace

“Kaka wallahi kudin ne sun ki samuwa, na rasa dabarar da zan yi masa.”

“Toh gaskiya dai ki san yanda za kiyi don kinga na sa an ranci dubu hamsin na bashi kuma itama wadda
aka ranta a wajenta har ta fara tambaya.”

“Toh ni dai don Allah ku dan kara daga min kafa don dubu goma ce kawai da ni. In aka kwana biyu naga
na kasa hadawa sai na bayar da wayata a sayar a biyashi daga baya na nemi wata wayar.”

Yaya Ummu ta dubeta tana rike haba tace

“Iphone din za ki sayar?”

“Toh ya zanyi Yaya Ummu, ni dama shi yasa ban so wannan aikin ba wallahi.”

Kaka ta galla mata harara tace

“Au haka ma za kice, ana miki yaki kina wasa. Ba ke kika je kikayi wasa ba.”

Umma ta katse su saboda an fara daukar zafi

“I, haka za ki daure ki biya tunda dai an baki kuma da bakinki kika fadi yanda aka samu akasi. Nima ga
dubu goma sha biyar a wajena ki kawo goman a hada ashirin da biyar in ya so sauran ki san yanda za kiyi
ki lallaboshi ya baki.”

Ta tabe baki ta share kwalla

“Na gaya miki fa Umma yanzu ba zai saurareni ba, matarsa ta dawo sai faman zuwa wajenta yake can
Jigawa. Shirye shiryen dawowa sukeyi yanzu idan ba maganarsa kayi masa ba babu abinda zai saurkwall

Kaka tace

“Ikon Allah, wannan fitinanniyar matar ta dawo kenan. Toh da da aka ce ta bata ina ta tafi?”

“Shi dai yace wai gidan kanwarta ta tafi, su dai suka sani.”

Yaya Ummu ta murgude baki tace

“Ta dai tafi barikinta kawai, a toh mu za ayiwa basaja.”
“Allah ya sauwake dai.”

Umma ta fada tana sauya taguminta. Suka yi shiru na dan lokaci, kaka ce ta katse musu shirun tace

“Toh gaskiya dai kiyi kokari nan da sati biyu kudin nan su fito.”

Haka suka karasa hirarrakinsu suna jajanta mata dawowar Mommy sannan kuma suna gaya mata
dabarun da zata yi amfani da su wajen samun kudi a hannun Abban.

Ita ta rasa wanna mugun abu, aiki bai yi ba amma ace sai ta biya kudin. Ta yi matukar nadamar yadda da
wannan aikin na kaka don ita a yanzu ma gani takeyi kamar kaka ce za ta ci wannan kudin, ko dai ba a
biya wannan kudin kayan ba toh tana tunanin kudin aikin nan bai kai dubu dari ba kakace kawai take son
tayi cuwa cuwarta. Ta riga ta hango babu dabarar da zata yi masa ta sa ya bata kudi, shi din yana da
kyauta amma sai lokacin da yaga dama. Idan dai kika ce ya baki kudi komai kankantarsu sai kin gaya
masa abinda za kiyi da su, idan ya gamsu ko nawane zai baki amma idan bai gamsu ba toh fa ba zai baki
ba. Ita kuma a halin yanzu bata san me zata fada ta gamsar dashi ya bata kudi har kusan dubu dari ba.
Don haka ta san ta kusa rabuwa da iphone dinta ne kawai, sai dai kawai in ta bayar an sayar tace masa
sacewa aka yi.

Haka dai har bayan sallar magriba sannan ya zo daukarsu ya mayar dasu gida.




Ranar juma’ar da daddare shima Baba karami ya iso da yake jirgi ya biyo. Ranar Asabar da safe da Abban
ya shigo ya same su a falon Mommy bayan sun gaisheshi ya zauna a falon, bai dade da zama ba Baba
karami ya fito daga tsohon dakin Zulaiha wanda suka gyara suka mayar nasu. Bayan ya gaisa da Abban
yace

“Kaddai koroka sukayi daga dakin na ganka daga nan?”

“A’ah Abba ai gyara dakin mukayi sai muka koma ni da Ahmad da Salim.”

Ya fada yana shafa kai.

“Toh Babu laifi, amma Baba kai da muke shirin korarka mu aurar da kai kuma me ye kake gyara wajen
zama.”

Madu yace

“Daga musu kafa nayi kawai Abba, ni suka gyarawa.”

Sukayi dariya gaba daya. A kusa da Abban ya zauna sukayi shiru na dan lokacin. Sai a lokacin ya sami
dama ya gayawa Abba yanda suka kare da Khairiyya, bayan Abban ya jajanta masa kuma ya kawo masa
maganar Fathiyya. Da fara’arsa yace

“Ma sha Allahu, ai bana jin Abban Fathiyya wannan Kam nine uban amarya ai sai ka fara lallabanyac

Yayi dariya ya sunkuyar da kai.

“Toh kaninka fa? Ka ga da ya shirya ai sai mu hada mu sha biki gaba daya.”
“Eh Abba shi din ma Zahra yake so ‘yar wajen Anti Baraka don shima yace in za a bashi ita sai a hada
din.”

Murmushin Abba ya karu

“Na san dai yaran Baraka duka sun yi aure toh amma zan yiwa Abban Ummi waya naji.”

“Eh ai ‘yar ‘dan uwanta ce da take riko.”

“Allah sarki, za muyi magana in sha Allah. Idan babanku Aliko ya zo ko shi ko Atiku sai muyi magana su
je.”

“Toh mun gode Abba Allah ya kara lafiya.”

“Amin ya Allah.”

Suka karasa hirarrakinsu daga baya Abban ya shirya suka wuce kasuwa da Madu da Salim.




Ya gama tsara yanda zai je Dutse wajen Rabi ranar litinin don har ya sanar da ita. Ranar Lahadi da
yamma sai aka bugo masa waya cewa kayansa da yayi order za su sauka a Lagos ranar litinin din da safe,
don haka dole ya soke tafiya Dutse ya sa aka yi masa booking din jirgi shi da Salim za su tafi Lagos. Kayan
daki ne su gado, kujeru da carpets, bai taba yin order din irin wadannan kayan ba sai yanzu; shi
electronics yake kawowa na manyan kamfanoni daga Japan, China da Germany; don haka da kansa yake
so yaje ana sauke kayan ayi clearance a doro a mota sannan ya dawo. Kafin wani lokaci Madu ya bugo
masa waya ya sanar da shi cewa yayi musu booking jirgin 7:30am. Tashi yayi daga falon ya fito ya koma
dakinsa da yake wajen Rabi, sai da ya zauna a kan kujerar da yake dakin yayi wani dan gyaran murya
sannan ya danna mata kira. Tana dauka bayan ya amsa sallamarta yace

“Ya mutanen gidan?”

“Lafiya kalau.”

“Rabi.”

Kawo yanzu tana jin da suna yana karewa da tuni sunanta ya kare saboda yanda idan suna waye duk
zancen da zai yi sai ya ambaci sunan. Tayi murmushin da har sai da ya jiyo sautin murmushin sannan ta
amsa

“Na’am.”

Ya marairaice murya

“Kinga yanzu ba zan sami zuwa Dutsen ba gobe, za mu tafi Lagos ni da Salim sai Talata ko Laraba za mu
dawo kinga ba lallai na sami zuwa ba watakil sai Juma’ah ko asabar.”

“Toh Allah ya nuna mana.”

“Amma dai idan na zo karshen satin za mu taho ko.”
Ta dan yi murmushi

“Kada ma ka damu zan dawo da kaina fa.”

“Toh yaushe za ki dawo Rabi, kullum cewa kawai kike yi za ki dawo amma babu rana.”

“Hmn, in sha Allah zan dawo.”

Ya danyi shiru, jim kadan yace

“An siya gidan ne?”

“Sai zuwa karshen satin nan.”

“Ok, za ki zo Kanon kenan?”

“Ban sani ba sai yanda ta kama.”

“Rabi.”

Ya sake kiran sunanta a karo na babu iyaka.

“Na’am.”

“Toh kin ga don Allah idan kin zo kawai kiyi zamanki gidan Yaya Shafa, kinji. Tunda dama ai cewa kika yi
da kin sayi gida za ki koma ko?”

Cikin kosawa tace

“Yanda ta yiwu, in sha Allah duk yanda ta kaya za ka ji.”

Ya fuskanci kosawarta kuma da yake yanzu lallabata yake yi daga ya ji ta fara kosawa da hira yake
rabuwa da ita, yace

“Toh Allah ya sa na ji alkhairi.”

Sukayi sallama suka ajiye wayar. Ya dubi fuskar wayar yana jijjiga kai, wai kai da matarka da da kake bata
umarni ta dauka ka dawo kana ‘yar murya. Ya sake jijjiga kai ya mike ya fice daga dakin, yayiwa su
Ahmad sai da safe sannan ya wuce ya koma makwancinsa.

………….

Ta gyara zama ta dauko kafafuwanta ta dora a kan dan tebur din da yake gaban kujerar a dakin Baraka.
Wannan nacin na Abba ya fara isarta, kuma da yake itama ta fara tunanin komawa Kanon. Tun lokacin
da suka dawo daga Kaduna Abban su Ummi yana nan don annual leave ya dauko, gidan yana da girma
kuma part dinshi baya kusa da na Baraka sosai don haka tunda suka dawo ma sau daya suka hadu. Duk
da haka a takure take, gani take yi kamar ta hanashi sakewa a gidansa, ko babu komai ai shima zai ga
wautarta tunda ya san Abban yana binta ta koma. Tana nan zaune Baraka ta turo kofa ta shigo, bayan ta
amsa sallamarta ta dubi wayarta taga lokaci karfe 9:10 na dare. Ta dubeta tace

“Na zata kin kwanta.”

“Hmm! Yayi baki kuma ba masu tafiya yanzu bane tunda ya sa an kawo musu abinci ma.”
Ta karaso ta zauna a kan kujera kusa da Rabin, tana zama Rabin tace

“Ina son tafiya Kano fa.”

Ta dubeta da mamaki tace

“Toh ai ba a gama cinikin gaidan ba.”

“Babu komai, sai na zauna gidan Yaya Shafa idan aka gama sai na koma gidan ko kuma gidan su Baba.”

Ta dafa cinyarta tana fara’a

“Gidan su Baban dai Hajiyata, Abban Khalifa fa ya riga ya gane kurensa, kuma ke kin san da baya sonki ba
zai yi ta faman binki haka ba. Ba ke ba ni kaina fa har wani kirana yake kullum yana gaishe ni.”

Tayi murmushi ta kawar da kanta sannan tace

“Wallahi nima na san da haka Baraka, na san zan koma din kuma na san idan na koma zan fi natsuwa.
Ina dai tsoron abinda zai je ya zo ne. Bana son wulakanci Baraka, musamman daga wajen wanda nake
ganin na kai ya raga min. Allah yasa dai idan na koma ya barni nayi rayuta a nutse.”

“Zai barki mana Bibi, shifa har cewa yayi idan kina so ya raba muku gida ma zai raba.”

Tayi dariya ta dafa kafadar Baraka tace

“Bana son ya raba mana gidan nan zan zauna tunda a nan din ma babu inda muke haduwa da matarsa,
kawai dai yayi abinda ya kamata shikenan.”

“Ai zai yi in sha Allahu.”

“Kinga yanzu da tunani nakeyi gobe zan tafi.”

Ta dafa ta tare da tsuke fuska tace

“Gobe fa litinin, gaskiya bari za kiyi sai ranar Juma’ah. Kinga gobe mu fito da turaren wuta da humarar
nan da kika hada mu zuzzuba a kwalaben, jibi in zan fita office tare za muje nan da nan za ki ga an fara
ciniki. Suma bedsheets da burners din da mukayi order daga Lagos gobe da safe za a karbo su daga tasha
don tun dazu driver din yace sun zo kin ga duk sai mu hada mu zauna ayiwa komai kudi sannan mu dau
talla.”

“Wallahi har tsoro nake Baraka, kada na kasa sayar da kayan nan, kusan dubu dari hudu fa kuka hada ke
da Mubarak da Baba karami.”

Tayi murmushi tace

“Kada ki ji komai, kaya in sha Allahu ba za suyi kwantai ba. Kinga ranar Laraba da Alhamis kuwa saloon za
ki wuni sai Jumana ta gyare fatar ki ita kuma Cynthia ta gyare gashin ki tsaf kuma a dandasa miki kunshi
a gama da wankan amarya.”

Ta harare ta tace

“Sai kace wata amarya.”

Ta kalleta tana zare ido
“Amaryar ce mana, ai yanzu ko a amaren ba kowacce akewa ‘yar murya yanda ake miki ba.”

Suka kyalkyale da dariya sannan tace

“Gaskiya dai ba zan yi kunshi ba, amma gyaran jiki kam in sha Allahu zan yi.”

“Babu laifi, yanda kike so haka za ayi domin nima lallabaki nakeyi kafin Usmanu ya sa ‘yan sanda su kama
ni.”

Ta harareta, sannan tace

“Ki tashi ki tafi wajen mijinki ya fi lada akan wannan sa idon da kike yi min.”

“Ai dole in sa miki ido kafin Usmanu yace bana kula dake.”

Nan ta mike ta fice tana ta yiwa Mommy tsiya.

Ita kanta ta san dole ta koma gidan mijinta, kawai dai tana jan kafa ne saboda abubuwa da yawa da tayi
hakuri a kansu a da yanzu ba za ta sake dauka ba. Ta kai hannu saman kujerar ta dauko littafin da take
karantawa wanda daya ne daga cikin littafan da suka siyo da Baba karami. Ta kalli littafin ta shafa
bangonsa, tana son karatu kuma tabbas ta yi kewar karatu. Haka ya ganta da son karatun ta, lokacin da
tana amarya ma yakan siyo mata littafi. A hankali kuma sai ya daina siyowa sai dai idan tana so ta turawa
Mubarak sunan littafi ya siyo mata, ko kuma kafin ayiwa Baraka aure ta sa ta kawo mata. Daga baya
kuma da ta fara tara yara sai ya zama idan ya sata wani aiki ya dawo bata yi ba tace masa ta manta sai
yace

‘kina nan kina wannan karatun dama yaushe za ki tuna.’

‘wannan karatun ne ai ba zai bari ki yi komai daidai ba.’

‘haka kawai wasu su rubuta karya kuyi ta karantawa kuna murmushi saboda rashin akin yi.’

Idan kuwa ya kirawo ta bata dauka toh dama fadan kenan tana can tana karatun da ba amfanarta zai yi
ba yana ta yi mata waya bata dauka ba. Zuwa lokacin da ta haifi Madu kuwa ga aiyukan gida ga hidimar
yara sai ma ya zama bata da lokacin karatun. Sai dai lokaci zuwa lokaci akwai gidajen da take aro littafan
a wajensu ta karanta, sai dai mafi yawancin lokaci idan ta aro tsakanin Ahmad ko Baba sai an sami
wanda ya yaga, tayi ta faman bada hakuri tana biyan kudin littafi. Don haka gaba daya ma sai ta sallama
ta daina karatun. Yanzu da take zaune ita kadai tana karatu ba karamim dadi take ji ba, duk da wasu
abubuwan sai Baraka da Zahra suna temaka mata saboda littafin na turanci ne ita kuwa ta manta rabon
da tayi karatun turanci. Haka dai ta dan kara karanta shafi biyu sanna ta kwanta bacci.




Kafin ma ranar litinin din wanda gidan su Rabin yake hannunsa ya kirawo Yaya Munzali yana gaya masa
wani mutum ya zo yana so ya sayi gidan gaba daya da shagunan, ya gaya masa ba na sayarwa bane
amma mutumin yace a hadashi da masu wajen shine ya kirawo shi ya ji. Nan da nan ya sanar dashi za su
sayar amma ya sallami mutumin tukuna sai sun yiwa gidan kudi sai su nemeshi. Ba tare da wani bata
lokaci

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login