Showing 9001 words to 12000 words out of 196754 words

Chapter 4 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15416

ba balle ya sa ran za ta
kai masa yarinyar nan asibiti. Suna isa asibiti aka yi scanning, likita ya duba ta.

“Alhaji sai dai kuyi hakuri abinda ya ke cikinta mutu, shi ya sa ta fara bleeding. Yanzu zamu kwantar da ita
mu yi mata allura ta haife shi in sha Allah sai a sallameta.”

Likitan yayi wa Alhaji bayani.

“Toh likita dama ana haka. Haka kawai Sai yaro ya mutu kafin ma a gama halittarsa? Ko kuwa dai wata
matsala aka samu?.”

Ta fada kafin Alhajin ya ce wani abu.

Likita ya bata amsa:
“Ko da akwai matsalar bazan iya gaya miki ita yanzu ba sai bayan an gudanar da bincike a kan abinda ke
cikin naki. Amma wannan ba wani abu bane yana yawan faruwa, Allah shi ya san ainahin matsalar amma
binciken mu ya nuna yawancin yaran da ake samu suna irin wannan ko an haife su ba za su zo da lafiya ba.
Ka da ki damu kwanan za ki sake samun wasu yaran.”

Ciwo yana ta kara takura mata don haka nan da nan suka tashi aka basu daki a ka yi mata allura ta kwanta.
Ya kirawo wayar mahaifiyarta ya sanar da ita don su turo wata babba ta zauna da ita a asibitin. Kakarta ce
ta taho da wata yar’ kanwar mahaifiyarta. Suna.isowa shi kuma ya tafi. Ya dawo gida ya sanar da Rabi. Ta
nuna masa ko ana bukatar wani ya zauna da ita yace mata ai an zo daga gidan su son haka ta zauna a gida.
Shi kuma ya je ya debar mata kaya, kuma ya karbar musu abinci da ruwan zafin a wajen Rabi ya koma.

Suna nan a kanta da kyar aka samu ta haifo shi, yaro ne namiji cikin wata bakwai. Likita ya nade ya mika
musu, aka saka mata ruwa ta wanke jikinta bayan an mata allurai. Bayan likita ya fita Suka zauna suna
tattaunawa kaka tana ta jujjuya gawar yaron.

“Wannan da man ba lafiyayye bane, yanzu haka sa hannu ne.”

Kaka ta fada.

Yaya Ummu (Yar uwarsu da Suka zo da Kaka) ta bata amsa:

“Babu mamaki tunda maigidan yana ta rawar kai kamar wanda ba’a taba yiwa haihuwa ba ai kin ga in an
ji haushi sai a jangwale musu yaron.”

“Gaskiya dai biri yayi kama da mutum. In ba haka ba yaro yana ta wutsil-wutsil din shi a ciki haka kawai a
ce ya mutu. Gaskiya da sa hannu. Bari mu je gidan.”

Inji kaka tana ta wani jijjiga kai.

Duk bayanin da likita ya yi musu basu gamsu ba. Sun so tafiya da ita gida domin a yi mata magani, amma
da kanta ta ki, ta ce ita su huce gidanta in ya so sai su yi mata kwanaki har ta samu lafiya. Don haka gidan
nata ya huce da su.

Da yake ya gayawa Rabi suna kan hanya kafin su karaso ta gama abincin dare, don magariba ta yi. Tuwon
shinkafa ta yi da miyar kubewa danya inda ta kwashe musu duka naman. Ta sa aka siyo mata kaji guda 2
tayi wa mai jego farfesu. Duka ta juye a flask.

Da suka dawo bayan sun zauna da kanta ta dauki flask din Khalifa ya raka ta da sauran. Suna shiga yana
fitowa daga wajen, ta dan jajanta masa sannan ta huce ciki. Koda suka shiga a daddakile aka amsa
gaisuwarsu, duk da ita bata kawo komai ba ta zata damuwa ce kawai da suke ciki. Bayan sun gaisa da kaka
da Yaya Ummu, ta basu abincin suka kwashe zuwa kichin.

Har suka gama zamansu a falo bata fito ba, Sai dai Ummu ta shiga ta fito ta ce musu wanka take. Ta gaji
da zare idanuwa ta ce:

“Bari mu je na dawo idan ta fito.”

Kaka ta amsa ta:

“Eh, ba kamai an gode.”
Suka fito ita da Khalifa jiki babu kwari. Bayan sun zauna a falonta Khalifa ya ce:

“Mommy tsohuwar nan sai faman harararki take.”

“Kai Khalifa, ka cika sa ido. Sai kace wata mara aikin yi za ta zauna tana hararata daga shiga jaje? Kai dai
da rigimarka.”

Haka ta tashi ta barshi da maganar don ita bata fahimci komai ba.

Da yake kwananta ne nan Abban Khalifa ya ci abinci. Ta jajanta masa sosai da bashi baki.

“In Sha Allah yaran suna tafe, ka san Khalifa yana son kanne da yawa, kamar goma haka.” Ta fada.

“Tunda kun mayar da ni gyada sarkin yaya’ ai sai ku bada himma.”

Ta kyalkyalce da dariya.

“Ai kuwa sunan ya dace da kai. Allah ya kawo masu lafiya. Kasan ko nima sai da na yi bari sau biyu kafin
Baba Karami, daga nan kuma nayi ta haihuwa har sai da na ji kamar na bar garin.”

Ya harareta ya ce:

“Hmmmn! Toh ya akai kuma kika fasa barin garin.”

Ta kara kyalkyalcewa da dariya.

“Da naga ba za ku iya rayuwa babu ni ba kai da yayan’ ka sai na hakura.”

“Allah ko? Ko kuma dai ke ce ba za ki iya rayuwa babu mu ba.”

Nan dai suka gama hirarrakinsu kowa ya kwanta.

_

Washe gari ranar Juma’ah ce Kuma ta yi daidai da good Friday don haka yara ba za su makaranta ba.

Wajen karfe 8:30 na safe yaran duk sun fito. Khalifa ya same ta a kichin tana ta fama girki inda Madu da
ya rigasu tashi yake tayata.

“Mommy Ina kwana.” Inji Khalifa.

“Lafiya Lau auta.”

Ta cigaba da ayyukan ta.

“Mommy wai wadancan kikewa abinci?” Khalifa ya tambaya.

Ta galla masa harara. Nan da nan ya sunkuyar da kai.

“Su nake dafawa, kana da magana ne? mara kunya.”

Ba zai taba cewa Anti ba sai dai ya ce waccan, ta hansa shi amma ya ki, sai ya ce wai mantawa ya ke yi.

Bayan yayi shiru kadan ita da Madu suna ta aikinsu ya matsa ya dauki kofi ya fara hada shayi. Can Kuma
ya ce:
“Mommy abincin jiya fa bayarwa suka yi. Har farfesun kazar ina kallo aka juyewa mai gadi. Aka kirawo Ladi
ta zo ta karbi tuwon a flask dinki ta kai gidansu ta dawo musu da flask din.”

Ta bishi da kallo, Sai Kuma tace:

“Kai wa ya gaya maka?”

“Mommy a gaba na fa aka yi ina tsakar gida.”

“Toh shike nan babu komai. Je ka sha shayinka.”

Ya fice daga kicin din suka ci gaba da aiki Madu shima ya fara yi mata mita.

Haka dai har ta gama ta hada abincin a kwanuka.

Ko da maigidan ya fito ta gama komai. Ya zauna ya ci ya koshi sannan ya tashi zai tafi wajen amarya.

“In ka je idan Antin ta tashi kayi min flashing sai mu kawo musu abincin ni da yara.”

Ta ce.

Ya amsa tare da daukar flask daya yana fadin:

“Bari na rage muku wannan.”

Yau Madu ne ya rakata don Khalifa tunda ta fara shirin zuwa ya fada bandaki. Don haka ta sa Madu ya
dauki flask din suka huce.

Ko da suka shiga yana zaune a falon. Ta so ta ji motsin shigewar amaryar amma bata kawo komai ba.

Kakace ta fito suka gaisa. Ta ce musu yanzu ko ta shiga bandaki.

“Yanzu fa ta bar wajen nan, har ta shiga bandaki?”

Baban Khalifa ya bata amsa.

Kafin su amsa kuma ya mike yace:

“Bari na je na gani.”

Ya shige dakin na ta.

Ita kuma Kaka ta juya ta shige kitchen ta barsu nan ba tare da ta ce komai ba.

A kwance ya same ta a kan gado.

“Mommy ce fa ta shigo ki fito ku gaisa mana.”

“Uhm! Mara ta ta dan rike ne, ka barta kawai in an jima na shiga wajenta mu gaisa.”

Ta fada tana yatsina fuska.

“Oh toh bari kawai na ce ta shigo.”

Ya fada yana shirin juyawa.
“Aah. Don Allah Ka barta ni bana son damu wallahi.”

Ta kauda Kai tana shirin sa kuka.

Kwana suka yi Kaka da Ummu suna gaya mata yanda kishiyarta ta shirya mata asiri saboda tana bakin cikin
itama ta haihu a gidan. Tun tana tantama har ta yarda. A karshe kaka ta gaya mata ta yi waya da malaminta
tun suna asibiti ya ce zai fara wani aiki don haka kada su bari Rabi ta ganta har sai ya gama aiki an kawo
magani ta yi wanka da shi. Shi ya sa kwata kwata suka ki yarda su hadu.

Yana cikin bata baki Kaka ta shiga dakin da bokiti a hannunta, bayan sallama ta ce:

“Toh Alhaji bari ta yi wanka.”

Ta dube ta ta ce:

“Tashi mu je ke kuma.”

Nan da nan suka fada bandaki suka rufo kofar.

Ya saki baki yana kallon ikon Allah. Ya juyo ya fito daga dakin yana matukar mamaki. Ya same su inda ya
barsu ya ce:

“Uhmm! Ta dan shiga wanka ne. In ta fito ma za ta shigo miki in sha Allah tunda ta sami lafiya.”

Suka yi masa sallama suka fito suka barshi a nan.

Tunda suka fita Kaka ta fito ta sa shi a gaba tana ta bayanin yanda suke da yakinin an yiwa yarsu asiri kuma
bata boye masa Rabi take zargi ba. Gaba.daya ta cika masa Kai don haka ya tashi ya fito kada ya makara a
kasuwa. Kafin ya fita sai da ya shiga wajen Rabi ya ce mata ta daina dafa musu abinci za su dinga dafawa.
Itama ya barta tana ta sake-sake.

Ta riga ta bayar an yi mata chefane don ta dafa abincin rana da su duk da ta san ba itace da girki ba a
ranar, za ta yi musu ne dai kawai saboda Maijego. Gaba daya ita sun rikita ta ma. Me.gadinsu ta bawa ya
yo mata chefanen. Ko da ya kawo mata chefanen sai ta dauki abinda take so ta ce ya dauki sauran ya kai
gidanshi, ta bashi naira dubu ta ce ya sai shinkafa. Har kasa ya zube yana mata addua.

Ta kasa nutsuwa har ta yi sallar walaha. Ta dai zauna tayi ta addu’a , kuma ta yi niyyar yin sadaka.

__

Bayan la’asar suka fita shi da abokinshi a mota za su je wata gaisuwa daga kasuwa. Suna hanya yake labarta
masa abinda yake faruwa.

Nan abokin ya kara gamsar da shi cewa hakan na faruwa don shi ma an yi a gidansa. Ya tuna masa da
yanda dama ya ce Rabin ta ki sakewa da amaryar.

Kafin dai su rabu ya fara tunanin lallai zargin su zai iya zama gaskiya.

Zuciyarshi ta dinga tuno masa yanda lallai Rabin bata kaunar amaryarsa.

“Amma kuwa Rabi ta cuci kanta Kuma ta bashi mamaki.”

Yayi alkawarin lallai zai bincika.
Tun daga wannan lokacin ya fara wani dan ‘dari-dari da Rabin.

Ta gane ya canza mata, amma bata san dalili ba. Don haka sai ta barshi kawai tunda duk wani hakki nata
na aure yana bata.

Yan uwa shi duk sun zo jaje, haka itama Rabin, nata yanuwan duk sun zo duba amarya. Duk da dai basu ji
dadin yanda ake musu ba.

Ita kuwa amarya Allah ne ya san yawan rubutun da ta sha bayan jike jike. Ga hayaki kala kala duk na karya
asiri da neman tsari. Hatta maigidan ma sai da aka bata abinda za ta yi masa amfani da shi wai kada a yi
mata asiri a jikinshi.

Bayan an kwana biyu amarya ta sami lafiya su Kaka sukayi tafiyarsu gida tunda a fadarsu yanzu sun gama
katange ta, duk abinda aka aiko mata komawa zai yi.

Ranar wata Lahadi sai ga Hajiya Sa’a. Yayar Baban Khalifa ce amma ko daya basa shiri da Rabi. Ita Rabin
bata san me tayi mata ba amma dai ba ta sonta, kuma bata boyewa har kowa ya sani a dangi.

A wajen amarya ta sauka kamar yanda ta saba tunda ya kara aure. Sai da ta kwana sannan ta shigo wajen
Rabin. Ta yi sa’a yaran duka basa nan da haka ta sami Rabin a falo ita kadai.

A dakile Suka gaisa duk da ita Rabin tana ta kakalo fara’a.

“Bari na kawo miki ruwa.”

“Aah! Barshi ma na sha ruwan roba a wajen amarya.” Ta dakatar da ita tana wani yatsine fuska.

Ta gintse dariyarta ta koma ta zauna dama itama bata so kawo ruwan ba. Bayan ta gama tambayarta
mutanen gidan suka dan yi jim.

Can Hajiya Sa’a ta ce:

“Zuwa nayi in gaya miki gaskiyar da kowa ya kasa gaya miki, don ke kin san bana jin tsoronki.”

Rabin ta kawar da Kai don ta saba jin irin wadannan zantukan daga bakinta.

Da bata ce mata komai ba ta ci gaba, tana yi tana nuna ta da yatsa tana yatsina fuska:

“Wallahi ki ji tsoron Allah. Shi ke nan ke ba za a haihu da mijinki ba?.”

Ta kalle ta da mamaki ta ce:

“Ban gane ba?”

“Daga yarinya ta samu ciki sai bakin ciki. Sai da kika san abinda kika yi kika lalatar da cikin sanna kika sami
nutsuwa.”

Gabanta ya fadi ta dan dake ta ce:

“Yaya Sa’a kamar Yaya?”

Ta kare mata harara kafin ta bata amsa:
“Za ki tambaye ni mana. An shiga malamai an zubarwa da yarinya ciki ana mana wasu kame kame. Toh
wallahi baki isa ba. Mallakar ma da kika yiwa mijin naki mun karya alkadarinta balle wani abu daga baya.
Ba za ki kai labari ba Rabi. Wallahi Allah ya fi ki.”

Gaba daya kanta ya kulle tana kokarin ta gano me Sa’a take son ta ce. Wato ita ma ake zargi a kan haihuwar
da amarya ta yi babu rai, lallai kam ta so ta fahimci wasu abubuwa.

Hajiya Sa’a ta mike:

“Na gaya miki dai wallahi baki isa ba don an fi ki kayan aiki. Kuma yanda kika haihu in Sha Allah yarinyar
nan ma sai ta cika gida da yara sai dai dan bakin ciki ya mutu.”

Ta tashi ta fice ta barta nan a zaune ta kasa magana.

Haka ta wuni tana tunani kala kala tana jiran Abban Khalifa ya dawo don wannan zargin da ake mata lallai
sai ta gaya masa, don bata san me za su gaya masa ba shi din.

Yara suka yi ta tambayarta ko bata da lafia tana cewa A’ah.

Haka har ya dawo daga kasuwa.



Ba wajenta yake da kwana ba don haka sai da zai kwanta sannan ya shigo. Ya huce dakinsa ta bi bayanshi
tana rike da flask din shayi, duk da dai kwana biyu daman ya rage shan shayin. Ta ajiye kayan bayan ta
masa sannu da shigowa. Ta koma gefen gadon ta zauna. Ya dan fara danne danne a waya Sai Kuma ya ce:

“Bari na je sai da safe ko.”

Ta ce:

“Yau Hajiya Sa’a ta shigo min da wasu maganganu.”

Ya ce:

“Na me fa?”

Nan ta labarta masa abinda ta gaya mata. Ta rufe da cewa:

“Ya za’a yi ta ce ni ce na lalatawa amarya ciki, haba mana?.”

Ya kura mata Ido na dan lokaci kamar yana karanto wani abu a fuskarta. Abinda bata sani ba shine sun
tattauna da Sa’a kuma ya nuna mata ya rasa yanda zai yi confronting Rabi, amma yanzu ya samu hanya.

Ya ce:

“Toh ke me kika ce mata?”

“Yaya me na ce mata? Wannan fa kazafi ta zo tayi min da cin fuska sannan ka ce me na ce mata? Toh
Wallahi zan dauki komai Amma ba zan dau sharri irin wannan ba gaskiya.”

Ta fada tana share kwallar dake idonta.
“Toh ki kare kanki mana. Kai da bakai laifi ba ai kai kake da hujja. Ki kare kanki. Kin yi mata wani abun ne
ko bakiyi mata ba?”

Ta dago idanuwanta da suke cuke da kwalla ta kalli cikin idansa; domin yanzu ta fahimci inda ya dosa; ta
share hawayenta da bayan hannunta ta ce:

“Idan dai har a shekaru 25 da mukayi a tare ban kai ka bayar da sheda ta ba toh lallai babu wanda zai iya
shedata a duniya. Kai ka san bana shirka, kuma bana sharri. Amaryarka ba ta kai nayi asarar lahira ta
saboda ita ba, ko kai ma ba ka kai nayi asarar lahira ta saboda kai ba, balle ita. Ko cikin shege kayiwa
karuwa a yanzu babu abinda zan yi mata na cutarwa balle matarka ta aure, cikin halal wai na lalata.”

Ta dan tsaya da magana ta sake kallonshi tana murmushi yayin da fuskarta ta riga ta jike da hawaye.

Ta dora hannunta a kan hannunshi da yake ajiye a kan gadon, sannan ta ci gaba:

“Idan da ina yin wadannan abubuwan auren ne ba zan bari kayi ba, amma bana yi kuma da yardar Allah
har na mutu ba zan yiwa wani asiri ba. Allah ya bayyana gaskiya kuma Allah ya saka min.”

Ya zare hannunsa ya mike tsaye:

“Toh me aka yi miki da za ki ce Allah ya saka miki?”

“Babu abinda aka yi min. Duk wanda aka yiwa ma Allah ya saka masa.”

“Ai shikenan. Ni bari na je sai da safe ma karasa zancen.”

Ya fada yana nufin hanayar kofa.

“Mun ma gama in Sha Allah. Allah ya bamu alkhairi.”

Ta fada cikin kosawa.

Ya fice ya barta a nan tana tunani kala kala tana share kwalla.

Yau ita mijinta ke zargi da yin asiri ta kashe mishi da.

Tabbas yanzu ta fahimci dalilin da yasa kwana biyu ya canza mata, ko don shi ma kada tayi masa asirin ne.

“Lallai idan ba’ayi maka kishiya ba baka gama ganin jarrabawar aure ba.”

Ta fada a fili tana share hawaye.
EPISODE 4



Shi bai daina shiga dakinta ba amma abubuwa duk sun chanza. Sai ya dinga wani cika yana batsewa, ko
magana ta yi da kyar yake amsawa. Da ta gane haka sai ta daina tsayawa su hadu, idan ta ajiye Masa
abincin sai ta bar wajen. Yana cin abincin daidai gwargwado amma duk yanda yake son zobo da shayi ko
ta ajiye ya daina Sha, sai dai ita da yara su shanye kayansu. Da aka kwana biyu ma sai ya daina cin abincin
kwata-kwata, duk da haka bata fasa girkawa ba tunda shi ma bai fasa chefane ba. Ta kasa gayawa kowa
wannan abun takaici, sai dai kullum dare ta ware awa daya da take tashi tayi Sallah kuma ta yi addua.

Khalifa ne ya fara jiyo zancen a wajen abokinsa a islamiyya

“Kai Khalifa wai na ji fa ana bawa mamanmu labari wai mommynku ce ta kashewa amaryar gidanku baby
tun yana ciki.?”

Ya tambayi Khalifa.

Ya rasa amsar da zai bayar don bai ma fahimci zancen ba. A guje ya karasa gida yana haki, yana shiga ya
huce kicin inda ya jiyo motsinta.

“Ina ka baromin auta na kake wannan uban gudu…?”

Kafin ta rufe bakinta ya fada jikinta gaba daya yana haki hawaye na bin idonsa. Gabanta ya fadi.

“Kai da waye Khalifa? Ina kaninka?”

Ta jero masa tambayar a cikin yanayi na razana.

Kafin ya bata amsa Auta ya shigo da sallama, ya ja ya tsaya ganin yanayin da suke ciki. Sai da ya dago ya
kalli fuskarta sannan cikin shesshekar kuka ya tambayeta

“Mommy wai da gaske ke kika kashewa amaryar Abba babyn da ta haifa ba rai tun kafin ta hatambayet

Gabanta ya sake faduwa, ta shiga tsananin damuwa,

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login