Showing 102001 words to 105000 words out of 196754 words

Chapter 35 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15354

yana can dai mun baro shi a asibitin.”

“Uhm, Allah ya bashi lafiya.”

“Amin. Bari nayi wanka nazo ma ci abinci don yunwa nake ji.”

Ta amsa ta fita tana murna.

Ta saba ajiye masa abinci a dining table kafin ya fito amma saboda bata son komai ya sami wannan
abincin sai taki kawowa kan table ta barshi a kicin a kan sai ya zauna sai ta kawo. Jimawa kadan ta cewa
Zulaiha su fita da yaran tsakar gida suyi wasa saboda ya saba bawa yaran abinci in yana ci suna kusa da
shi kuma wannan shi kadai take so yaci. Suna fita tsakar gidan Muntari ya bugowa Zulaiha waya don
haka tana amsawa ta nemi loko ta zauna, su kuwa yara Nawwara ta ja su suka nufi fanfon dake tsakar
gidan suka kama wasan ruwa.
Baya son abinci a flask don haka irin kwanukan nan ne na tangaran ta zuba masa tuwon da miya aciki, ta
doro a tray ta fito. Ta dauka zuwa kan table din kenan Ummi ta shigo a guje tana kira

“Umma.”

Bata kula da Umman a gabanta ba ta nufi kichin nemata, ai kuwa kafin ace wani abu ta fada jikinta da
karfi. Kwanukan suka watse suka fado a bayan Ummin ita kuma Saudan tayi taga taga saura kadan ta kai
kasa ta samu ta tsaya, ai kuwa ta kama Ummi ta fara duka tana kumfar baki

“Baki da hankali kike wannan uban gudu a cikin gida, kin saka nayi bari. Idan kika jin ciwo fbak

Nan da nan Abban ya mike ya dauke Ummin yace

“Shike nan kuma Sai ki fara dukanta, baza ma ki duba ko ta ji ciwo ko bata ji ba kuma kika san menene ya
biyo ta za ki kama ta da duka?”

Zulaiha ta karaso ciki da sauran yaran, Abba ya dubeta yace

“Waye ya koro Ummi?”

“Kara ta taho kawowa, Nawwara ta kunna famfo suna wasan ruwa, ashe ‘bari tayi.”

Ta fada tana duban tangarayen da sun riga sun fashe a kan abincin. Saida ta share kwalla saboda takaici,
Abba yace

“Kar ki sake dukar min yara na gaya miki bana so.”

Ya dubi Zulaiha yace

“Goya Baffa ki zo ki share wajen.”

Ya shige daki yana lallashin Ummi, ya dauko alawa ya basu ita da kannenta. Yana fitowa Saudan tana
tsugune tana kwashe tangarayen ya huce ya shiga kicin. Ta bishi kicin din ta same shi yana kokarin hada
shayi tace

“Akwai wani tuwon bari na zubo maka.”

Ya dauki shayin yace

“Ki kawo min daki.”

Yana fita ta leka kwandon sharar dake kicin din ko zata hango ledar maganin ta duba ko zata samu
burbushinsa, sai a lokacin ta kula ashe ma ta juya ledar kuma babu ko burbushin a ciki. Ta share kwallar
takaici ta shiga zuba masa ragowar tuwon. Dubu dari fa aka ce zata bayar idan ta ga aikin wannan
maganin ga shi ko amfani bata yi dashi ba abincin ya zube. Ta ja tsaki ta kwashi abincin a wani tray din ta
kai daki ta ajiye masa, da yake yunwa yake ji tas ya cinye tuwon kuma ya shanye shayinsa. Bayan ta fito
da kwanukan ta dubi kwanon da yaci tuwon ga alamar yatsun shi a kai tayi tsaki a fili tace

“Aikin banza kawai.”

Da yake dai akwai sauran daya maganin da kaka tace mata na kwanciya ne shine abinda yake dan bata
nutsuwa. Ranar haka ta wuni ranta a bace tana jin haushin Ummi, wadda ita bata ma san tayi laifi ba.
Bayan sallar magriba Abba yace da su Baba su shirya gaba dayansu za su je su dubo Madu. Sai da ya
gama shiryawa ya fito ya sameta a daki yace

“Daga masallaci za mu huce mu dubo Madu.”

“Ah, to ai da za ku dawo sai muje duka har yaran muma mu dubo shi.”

“A’ah kuyi zamanku ma, mutumin da baya hayacinsa.”

“Toh ai ko Zulaiha da kun tafi da su ita da Nawwara.”

“A’ah, duk suyi zamansu yanzu zamu dawo.”

Ya fice kafin ta kara cewa wani abu. Ta so kwarai da gaske taje ta gano halin da yake ciki ko kuma a kalla
ya tafi da Zulaiha amma duk ya ki. Ita a yanda ma suka yi magana da kaka ta gaya mata Malam yace ba
zai kai azhar a garin nan ba sai sun tafi dashi kuma ba zai sake dawowa ba. Don haka yanzu ma gani take
kamar idan su Abban suka je asibiti baza su same shi ba.

Ana idar da Sallah suka shiga CR-V din Abba Ahmad yana ja suka kama hanya sai gidan Baffa, sai da
sukayiwa su Baffa sayayya sannan suka huce. A tsakar gida suka sameshi Baba Yalwa tana tuka tuwo
yana mata hira saboda Baffa ya hanashi fita, bayan sun gaisa da Abba yace

“Baba Yalwa yau kina tuwo maigida yana miki hira.”

Tayi dari tace

“Toh me yafi raina tunda shi wancan ‘yan matan Habuja sun kwace min shi.”

Suka yi dariya gaba daya, Baffa ya leko daga falo yayi musu iso suka karasa. Bayan sun gaggaisa an dan
taba hira Baffa yace Ahmad suje gidan Malam su karbo sako, suka fice shi da Auta suka tafi. Tofi ne da
akayi a ruwan zamzam sannan kuma da ayoyi a rubuce a takarda Malam ya zaunar da Ahmad yayi masa
bayani

“Wannan na robin kowa ya sha daya har Abban naku, gashi nan kuma tunda kun iya karatu kullum kowa
ya dinga karancewa bayan la’asar da bayan asuba. Ku cigaba da azkar kullum kar ku fasa safe da yamma.
Hasbiyallahu lanilaha illa Huwa alaihi tawakkaltu wa Huwa rabbul arshil Azim kada bakunanku su dinga
bushewa da fadin ta. Ku dinga yawan sadaka kuma, kada ku yiwa kowa sharri. Mahaifiyar taku ma muna
ta rokon Allah za a ganta in Sha Allahu.”

Ya kawo wani sassaken itace ya basu yace

“Yau kafin ku kwanta ku turara wannan a gidan, kuma kullum kowa ya dinga karanta suratul mulk kafin
kwanciya kuma ayi tasbihi.”

Suka karba suka yi godiya suka dawo gidan Baffa. A gaba ya saka su saida kowa ya shanye nasa, shi
Madu kam har ya gaji saboda jarka guda aka kawo da ya tashi neman ruwa sai Baffa yace wannan zai
sha. Ya sa su a gaba ya kara musu nasiha da kuma wasu addu’oin na tsari. Nan suka zauna suka ci tuwon
dare suka yi sallar isha’I, sai da za su tafi Baffa yacewa Abba
“Suma wadancan kananan yaran idan an kwana biyu ka kawo min su Malam ya basu tofin saboda tsari.”

Ya amsa sukayi sallama suka tafi. Bayan sun fito suka biya ta asibitin Premier suka dubo Alhaji Mustapha;
abokin Abba me na amana don tare sukayi yarinta a unguwa daya sai dai shi Alhaji Mustapha ma’aikacin
gwamnati ne, paralyze ya samu shine aka kwantar dashi. Abba ya ji dadin yanda yaga jikin nashi ba
kamar ranar da aka kwantar dashi ba, mafi yawan sassan jikinshi yanzu sun fara motsi gashi maganarshi
ta dawo kamar da sai abinda ba a rasa ba. Sosai Abban ya ji dadi da suka dan yi hira don haka da
walwalarsa ya taho gida.

Yana shiga babu kowa a falon sai ita da yake yaran sun yi barci, Zulaiha ma tana daki. Yanda taga
fuskarshi da walwala yasa taji tana son yin amfani da daya maganin da kaka ta karbo mata, sai dai kuma
ba haka ta zata zai dawo ba. Ta zata zai dawo a birkice saboda Madu ya gudu, yanzu da ta gan shi da
walwala sai ta shiga rudani. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya zauna a nan kusa da ita, tace

“Ya jikin Madun, na ga kana ta walwala ko ya sami lafiya?”

Da yake Baffa ya riga ya gaya musu ko da wasa kada su bari kowa ya san Madu ya sami lafiya sai ya bata
fuska yayi kalar tausayi yace

“Uhm, da sauki dai za mu ce, ana nan ana fama. Wajen Mustapha muka biya shine za a ce ya sami lafiya
don yana motsi yanzu sosai gashi har hira muka dan yi da shi.”

Sai yanzu ta gane walwalar tasa amma dai za ta so yayi mata bayanin halin da Madun yake ciki sai dai shi
ta kula baya so ta yi maganar Madun ma. Tace

“Kai ma Sha Allahu, Allah ya kara musu lafiya baki daya.”

Suka dan yi shiru na gajeren lokaci ya dube ta yace

“Abincinki fa zai yi kwantai don mun ci abincin dare ni da yaran.”

“Ai kuwa za ka ci dumamenshi da safe don tuwo nayi.”

Yace

“Ah indai tuwo ne daman a ajiye min abuna.”

Ya tashi ya shige daki.

Sai da ta gama komai ta shirya tsaf ta yi amfani da maganin kamar yanda kaka ta nuna mata sannan ta
same shi a daki. Yana kashingide yana duba waya. Ta kwanta a gefen gadon yana duba wayar suna hira,
tana ta gyangyadi yana kara janta da hira. Wajen sha biyu saura ya gama ya ajiye wayar ya tashi ya
gama shirin baccinsa, yana shirin kwanciya wayarsa ta fara waka. Yana dubawa yaga Mustapha, yace

“Ikon Allah.”

Ya kara wayar a kunnensa yayi sallama, ba tare da an amsa sallamarsa ba aka sanar da shi rasuwar Alhaji
Mustapha da kuma jana’iza karfe takwas na safe. A rude ya ajiye wayar yana ta maimaita

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.”
Take taji zuciyarta tayi fari tas domin ta dauka ce masa aka yi Madu ya gudu ko kuma ya mutu. Ta tashi
zaune tace

“Lafiya Abban Nawwara?”

“Ina fa lafiya, ce min aka yi Mustapha da nace miki naje dubawa dazu ya rasu.”

Ranta ya baci saboda ba haka ta so ji ba, amma dai ta daure tace

“Allah sarki, Allah ya sa ya huta.”

Ta zame ta gyara kwanciyarta. Nan ya zauna a bakin gadon ya shiga kiran abokansu yana sanar dasu
rasuwar Mustapha, sunata alhini. Ita dai Saudah tana jin ya kira kusan mutum goma, da ya gama kuma
ya kirawo Baba ya sanar dashi sunshirya gobe za su je jana’iza. Nan ya tuna masa gobe da asuba zai
koma Abuja amma zai sanar da su Ahmad. Ya gama ya ajiye wayar, ya dan zauna shiru yana alhini sai
kuma ya tashi ya shiga bandaki ya fito da alwalarsa. Yana rufe kofar bandakin ya jiyo kukan Baffa Karami
daga dakinta yana

“Ummaa”

Tayi lamo kamar bacci take yi, ya karaso ya dan taba kafarta yace

“Ga Baffa can ya tashi kije ki gani.”

Ta tashi tana muttsike idon karya ta fice daga dakin, yanda yayiwo alwalar nan ta san ba zai ma saurare
ta ba. Inda Allah ya so ta akwai sauran maganin don dama Kaka ta gaya mata na amfani biyu ne, don
haka tabbas za ta sake tarar wani lokacin. Ta dai fi so ace kafin satin nan ya huce domin ta matsu gidan
ya koma hannunta, ta fi so duk abinda ta fada Abban ya aikata ba tare da musu ba. Ta gaji da wannan
mulkin mallakar da ake mata ita da ‘yayanta.

Tana fita Abban ya tayar da Sallah. Ya san ba zai iya bacci ba shi yasa ya tada sallar, ita kadai ce take
bashi nutsuwa tunda Rabi ta bata. Abubuwan da suke faruwa yanzu kuma suna kara saka shi cikin
matsananciyar damuwa don haka in ya ga zuciyarshi ta fara takura sai kawai ya tada Sallah. Idan ya gaji
sai ya zauna yayi ta hasbunallahu wa ni’imal wakil a hankali sai ya fara samun nutsuwa.

Ana idar da sallar asuba Baba karami ya kama hanyar Abuja, dama tun jiya ya kamata ya koma ya tsaya
don ya ga jikin Madu. Su Abba kuwa karfe bakwai da rabi suka fice suka tafi jana’izar Mustapha.
EPISODE 24



Sai da Baba ya kwana daya da dawowa Abuja sannan yaje wajen Khairiyya. Kamar yanda ta saba haka ta
tarbeshi ta kawo masa ruwa da lemo, suka yi hirarsu kamar yanda suka saba ta kara jajanta masa
Mommy. Sai da suka gama hirar ya fara shirin tafiya sannan tace

“Daddy fa yana so ku turo a sa rana.”

Ya dubeta suna hada ido suka yi wa juna murmushi yace

“Wallahi nima ina so, amma ke kin san halin da ake ciki. Daddy ba zai daga mana kafa zuwa bayan
Babbar sallah ba?”

Ta jijjiga kai

“Gaskiya ban sani ba, ka san an sa bikin Yaya Bash da Jamila shine yake so a hada duka mu ukun ayi biki
daya.”

“Toh ko nasa Baba Aliko yayi masa waya?”

“Gara dai su zo din kawai.”

Yayi jim yana tunani sannan yace

“Toh, bari mu gani. Zan yi magana da su Baban in sha Allah.”

Sukayi sallama ya hawo motarshi ya kama hanayar komawa dakinshi. Ya kasa gane me yake faruwa, an
rasa Mommy kwata-kwata. Har tracking layinta ya saka ayi masa an ce dai last time da aka yi amfani da
layin nata a nan unguwarsu ne kuma kwanan watan da lokacin da aka bayar yayi daidai da ranar da ta
tafi. Yanzu kuma an ce ba za a gane inda layin yake ba har sai an sake kunnashi, gashi tun daga wannan
ranar ba a sake kunnashi ba. Abba ya cuce su, da ya sani ya ce su dauketa da baza ta kara kwanar masa a
gida ba amma ya koreta. Yanzu ina ta shiga? Ya za ayi yayi wani aure ba tare da an san inda Mommy take
ba? Ga shi Abban ba lafiya ce da shi, ga Madu ma in banda Allah ya takaita musu wahala wa ya san inda
zai tafi. Gaskiya yanzu baya cikin yanayin da zai iya aure kwata-kwata. Toh wa ye yayiwa Madu wannan
abun don ya tabbatar asiri ne? Shi dai aljanin yace mace ce don da aka tambayeshi cewa yayi ‘bamu
santa ba amma sarki ya santa’ kenan mace ce. Kafin ayi haka ya zata a kasuwa ne don ya san kasuwa
tana cike da hassada kuma wani haka kawai a kan matsala kadan sai ya kassaraka, amma yanzu ya fi
zargin Saudah. Ya fahimci tana jin haushin su gaba dayansu amma bai taba tsammanin haukanta ya kai
haka ba. Gashi Malam da Baffa sunce ba za a bincika a ji waye ba, shi Baffa ma cewa yayi gaba daya kada
su bari kowa ya san labarin rashin lafiya Madu, ko an tambayesu suce zazzabi yayi. Amma bari abun ya
lafa ko ma wacece za su kamata ne, an dai rage musu aiki tunda sun gane mace ce.

Kafin ya koma dakin dai ya yanke shawarar ba zai yi maganar aurenshi ba don ba zai ma iya ba, idan aka
ga Mommy, kai ko gawarta aka tsinta in komai ya wuce sai yayi auren. Sai da yayi kwalla da ya tuna
akwai yiwuwar Mommy ta riga ma ta mutu. Haka ya kwana cikin matsananciyar damuwa saboda rashin
sanin inda mahaifiyarsu take.
Tunda Madu ya kwanta tare Abba yake tafiya kasuwa da Salim, yau ma haka suka tafi. Tun da suka shiga
kasuwar yake jin babu dadi da yake yana shan maganin malaria kuma maganin haka yake masa ya saka
shi ya dinga ji babu dadi. Don haka ko awa biyu basuyi a kasuwar ba ya bar Salim ya taho da Lalo don ya
sauke shi a gida ya koma.

……..

Da yake hutun Sallah bashi da yawa kwana hudu bayan Sallah yara duka suka koma makaranta. Suma
‘yan jami’a an koma amma da yake semester bata kankama ba sai nan da sati kowa zai koma, don haka
gidan gaba daya babu kowa daga ita sai yaranta da Zulaiha.

A zaune take a falo ita kadai tana ta tunani, yau kwana uku kenan da aka fita da Madu daga gidan amma
ita bata san inda yake ba, ta sa Zulaiha ta tambayar mata Ummanta ko ta sani amma su a Bichi basu ma
san Madun bashi da lafiya ba kuma sun yiwa Abban waya yace lafiyarshi kalau. Shi kuma Abba duk
lokacin da ta yi maganar Madun sai yace mata yana asibiti, wane asibitin? Ya ki gaya mata kuma ya ki ya
kaita dubiya. Tana ji a jikinta Madu yana nan lafiya don idan da bashi da lafiya ko ba a ganshi ba da
tashin hankalin Abban ya fi haka. Toh ina yake? Me Abban yake boye mata? Allah ya sa dai basu gane
itace tayi masa aike ba, duk da dai bata ga wani canji ba a wajen Abba. Yana nan dai a yanda yake tunda
matarshi ta bata, ba shi da cikakkiyar walwala da kayi magana yace in aka ga Rabi. Wani lokacin ma sai ta
dade tana magana dashi ba tare da ya fuskanci komai ba don haka ita yanzu ba ta ma son hira dashi. So
take kawai ta sami dama tayi amfani da ragowar maganinta ko Allah zai sa Abban ya dawo hannunta.

Zulaiha ce ta katse mata tunani yayinda ta fito daga daki Baffa da Hanan suna biye da ita, ta yi musu
wanka ta shirya su. Tace

“Anti mun shirya, za mu dan je gidan su gidansu Fauza.”

“Yauwa sai kun dawo, kafin ku dawo ma na samu na dan rage aiki.”

Sukayi mata sallama suka fice suka tafi gidan su Fauza; kawar Zulaiha ce wadda a nan unguwar suka
hadu sai kuma ya zama dukansu BUK suke zuwa don haka suka kulla kawance. Gidan su Fauza yana
bayan gidan ne don haka sai ta ja hannun yaran suka fice. Suna fita ta tashi ta shiga kichin ta fara gyare-
gyare, tana cikin aiki wayarta tayi waka. Ta bar aikin ta dauko wayar, tana dubawa taga Maman Surayya
wadda kawartace tare suke karatu kuma itace take kawo musu da kayan mata da yake a Sokoto take
aure. Yanzu ma da taga wayarta ta san zancen kenan tunda ta dawo daga hutu. Ta kara wayar a
kunnenta ta cigaba da aiki

“Hajiyata kin dira kenan?”

“Umman Nawwara, na iso. Ya kike ya yarana?”

“Lafiya kalau muke, ya maigidanki?”

“Lafiya kalau muke? Kaya sun sauka fa aminiyata ya za ayi ne na daukar miki ko sai kin zo?”

“Hmn! Kawata ba zan sayi kayan nan ba wallahi, ba wani labari.”

“Ya za ki ce haka kawata, maigidan baya gari ne? Ko so kike tsohuwa ta fi ki performing?”
Tayi dariya kafin ta bata amsa.

Daidai nan Abba ya shigo falon, da yake bai saba dawowa a irin wannan lokacin ba kuma da ya dawo
Bala baya bakin gate don haka bata ji shigowarsa ba. Da sallama ya shigo falon amma saboda tana waya
ga aiki tana yi da kuma kasancewar bata sa rai da zuwan wani ba a daidai wannan lokacin bata ji shi ba.
Shi kuwa da ya jiyo motsinta a kicin sai ya nufi kicin din, yana kawo kai ya jiyo karshen hirar tasu

“Baza ki gane ba kawata, ki dai godewa Allah mijinki yaro ne daidai ke mu da muke auren tsoffin nan mu
muka san halin da muke ciki. Babu abinda suka iya sai bacci da minsahrin tsiya. Don ni yanzu babu
yarinyar da zan bawa shawara ta auri tsoho, tsofar da

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login