Showing 54001 words to 57000 words out of 196754 words
Chapter 19 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
ake ‘kin kaza amma ana son abin cikinta ba sai a wajen
Sa’a.
Ranar da Abba sukayi maganar Zulaiha da Baba bai jira ya ja lokaci ba ya kirawo Atikun ya sanar masa.
Cikin mamaki yace
“Shi Baban ne yace baya son Zulaihan.”
“Eh, ai dama na gaya maka in da yana sonta tunda suna gida daya ai da tuni zancen ya fito don haka
maganar Zulaiha a barta kawai. Allah ya fito mata da miji na gari.”
Ya gyara zama ya kara bata rai yace
“Amman kuwa ban ji dadi ba wallahi, Allah ya sa hakane ya fi alkhairi. Lallai ‘dan yau sai a barshi.”
Yace
“Amin.”
Suka yi sallama. Ya juyo ya dubi Anti Hauwa da take zaune kusa da shi tana danne danne a waya yace
“Dan yau sai a barshi, ko da yake Yayan shima da shi, ba Umarni ya bayar ba shi yasa, shawara ya bayar.
In da umarni ya bashi ai bai isa ya tsallake ba.”
Kafin tayi magana yace
“Bari na kirawo Sa’an kafin na manta.”
Da kuzarinta ta ‘daga wayar don ta san maganar su kuma ta zata komai yayi daidai. Bayan da suka gaisa
ya labarta mata abinda Yayan yace, sai da taji kamar an yanke mata hukuncin kisa. Da kyar ta tattaro
natsuwarta ta cigaba da mita kamar za ta fasa wayar, domin Hauwa da ba da ita ake wayar ba tana tsintar
abinda take cewa daga nan inda take. Haka yayi ta bata hakuri tana turjewa sai da yayi da gaske sannan
ta bari sukayi sallama. Yana ajiye wayar ya juyo wajen Hauwa ya bata labarin abinda ke faruwa. Ta bude
baki cike da mamaki tace
“Yanzu Baban Khalil in banda abinka ya za ayi ku sa rai ‘yayan Rabi za su auri yaran Sa’a? Ka san kuwa
abubuwan da Sa’a ke yiwa Rabi? Kuma duk a gaban yaran take yi, su kuwa wacce irin kwakwalwa ce da su
da za su yarda da wannan hadin?”
“Ya za ki ce haka?”
“Ya bazan ce haka ba abinda yake faruwa a bainannasi, ai kowa ya sani.”
Nan ta bashi labarin wasu daga cikin abubuwan da suka faru a kan idonta. Bayan ta gama yace
“Allah ya kyauta. Ai shikenan sai ya je ya auri waccan yarinyar?”
Tace
“Ba ka ce akwai matsala ba da ita yarinyar, sai dai ya sake nemo wata kawai.”
Yace
“No, babu ma wani abu tunda dai wannan din bai tabbata ba shikenan.”
“Toh ai sai ka gayawa Abban don kuwa idan kuka rabashi da yarinyar da yake so a kan son zuciya ba zai ga
girmanku ba daga kai har Abban kuma baku yi masa adalci ba.”
Nan da nan ya kira Abban ya sanar da shi ya ma sake bincikawa babu matsala don haka Baba ya cigaba da
neman Khairiyya. Shi kanshi Abban yayi farin ciki domin yanayin da yaga Baban ya shiga da yace masa
abun ba zai yiwu ba ya san lallai akwai matsala. Don haka ya shirya yi masa albishir da zarar ya zo weekend.
Satin da su Mommy za su dawo a satin ‘yan jami’a suka koma makaranta, a satin kuma aka yi bikin Jamila
mai aikin Saudah. Ta so matuka ace ta samo mata wata mai aikin amma hakan bai yiwu ba, ta kawo wata
mata babba amma ita kuma bata kwantawa Saudah din ba. Kannen Jamilan kuma duk maza ne, haka dai
aka shiga hidimar bikin nan ba tare da ta sami wata mai aikin ba. Sai da suka gama registration aka kafe
timetable, da yake tana da carryover ta courses guda hudu sai ta ga timetable din ta cika. Kusan kullum
tana da lecture 12pm to 2pm in banda ranakun alhamis da take da 8am to 12pm sai 4pm to 6pm, ranar
jumaah ma lecture daya ce da ita 11pm to 2pm. Idan ta kalli timetable din sai gabanta ya fadi saboda
dauko ‘yan makaranta. Ta tabbatar Abba ba zai raga mata ba saboda dama ba son karatun yake yi ba,
musamman yanda take barin yara a gidansu Jamila. Toh Baffa da Hanan ma ina za ta barsu tunda gashi an
yi wa Jamila aure kuma gidansu yanzu babu ‘yan mata, babarsu kuwa baza ta karba ba saboda kullum cikin
sana’arta take ta abincin sayarwa. Don haka gabaki daya a birkice take. Ta yi tunanin ko gidansu za ta
dinga kaisu amma ta ga gidansu sai ta koma baya, sannan kuma dauko yara kashi biyu ma ba abu ne da
zai yi sauki ba.
Tana ta murna da taga Zulaiha ta dawo sai kuma itama Zulaihan ya kama kusan kullum tana da lecture da
rana. Satinsu daya da fara lecture aka samo mata gidan da za ta dinga kai su Hanan, da yake ta je ta ga
gidan babu laifi harma ya fi na su Jamila nan da nan ta fara kai yaran bayan ta sha mita a wajen Abba. Baya
son a kai masa yara ajiya, ya tsani wannan karatun ba don komai ba sai don yanda yake tunanin ana saka
masa yara a damuwa. Haka dai ya hakura ba don ya so ba. Da yake satin farko ne karatu bai kankama ba
sai ta dinga hakura da wasu lectures din nata tana dawowa ta dauki yaran, lecture din yamma kuwa mafi
yawancinsu hakura ta dinga yi da su saboda in ta dauko yaran duka ta dawo toh sai kuma ta kasa sake fita.
Zuwa yanzu karatun ya gama ficewa daga ranta sai dai kawai za ta karasa ko don ta bawa marada kunya.
--------
Duk gidan Babu wanda ya san yau Mommy za ta dawo don haka da suka ji mota sun zata Baba ne kadai.
Ihun Auta ne ya sanar da mutanen gidan harda Mommy aka dawo ai kuwa nan da nan aka rude da murna.
Shi kanshi Bala me gadi ma ya shiga cikin ‘yan murna don rabon da ya sami abinci sau uku a rana tun da
Mommy ta tafi, mafi yawancin lokuta abincin dare kawai Saudah take iya bashi. Lokacin da yaji hayaniyar
yana zaune a falon Saudah suna hira, ya dube ta yace
“A’ah bakin Dubai ne suka dawo.”
Kafin tace wani abu ya tashi yayi waje. A wajen motar ya same su Auta ya kama hannun Mommy ya rike
gam suna ta raha. Yana karasowa yace
“A’ah mutanen Dubai shine ko a gaya mana mu saka red carpet.”
Ta kyalkyale da dariya tace
“Sai kace wata VIP?”
Yace
“Eh mana. Ina Barakan ko har ta huce Jigawan?”
“A’ah, ta Abuja muka biyo tana can gidanta na Abujan.”
“Toh ma Sha Allah, sannunku da hanya.”
Suka karasa cika aka baje a falo aka hau surutu kamar wadanda sukayi shekara basu hadu ba. Khalifa da
Salim ne suka shige dakin Mommy suka gyara shi tsaf, daga baya duk yaran suka koma dakinsu suka bar
su ita da Abba.
“Dubai fa ta karbeku, ko Saudiya zan ce ne?” Ya fada ya a murmushi.
Tace
“Saudiya dai, mutum yana dakin Allah ai dole yayi fes.”
Ya nuna hannunta yace
“Ni yaushe aka fara lalle irin wannan a Dubai ne?”
Ta kyalkyale da dariya tace
“Haba dai, a Abuja aka yi mana da yake tun shekaran jiya muka dawo na tsaya jiran Baba.”
Haka sukayi ta hira har wajen sha biyu sannan ya ce
“Bari na barki ki bacci koh, da safe ma hadu.”
Suka yi sallama ya tashi ya fice ya koma wajen Saudah. A falo ya sameta ta saka kayan bacci yaran ma duk
sun yi barci tana zaune tana ta cika tana batsewa. Ko sallamarshi bata amsa ba tace
“Ai na zata can za ka kwana saboda zumudi?”
Yace
“Toh a nan zan kwana sai ya ya?”
Ya huce ta bishi dakin. Haka ya kwana yana tunanin Rabi, ya so ya kwana a wajenta amma saboda ya san
halin Saudah, babu abinda ba za tace masa ba in ya kwana a can don haka ya hakura sai gobe.
Da gari ya waye kafin Mommy ta fito yara sun gama hada abincin safe sun jera a dining table, bayan sun
gama breakfast ta janyo akwatinta ta fara rabon tsaraba. Kowa sai da ya sami wani abun har Bala me gadi
ma sai da aka bashi jallabiya da dadduma, kuma aka bashi dabino da alawa aka ce ya kaiwa yaranshi.
Aikuwa ya dinga godiya yana cewa
“Allah ya maimaita mana.”
Suna zaune a falon Baba karami ya fito daga daki, bayan ya gaida su Mommy ya zauna a kusa da Ahmad
wanda ya rigashi fitowa. Suka dan yi jim kadan Abban ya dubi Baba yace
“Kai yarinyar nan da kayi maganarta kwanaki nace Baffanka ya ce a bar maganar toh ka cigaba da neman
aurenta, ina ga ma idan ka shirya ai sai muje mu kai kudin auren ko?”
Nan da nan ya gyara zama yana shafa kai ya ce
“Toh shikenan Abba, in sha Allahu da naje Abujan zan gaya mata za a kawo kudin yanda muka yi zan muku
waya.”
Suka shiga hirarrakinsu na duniya. Mommy tana mamakin yanda aka yi aka fasa, da kamar ta ce wani abu
amma sai tayi shiru da yake ta ji ba a ma ambaci sunan Zulai ba. Amma tana nan tana jiran lokacin da zata
nuna masa ba zata hada jini da Sa’a ba. Duk kiyayyar da Sa’an take yi mata ba ya gani, sai ta kure ne zai
bata hakuri idan an yi wani abum
Bayan da suka kwana biyu da dawowa Mommy ta koma islamiyya da sauran harkokinta.
Tuwo miyar kuka ta dafa sannan ta dafa wa Abba shayi mai kayan kamshi ta zuba a flask. Bayan ya dawo
ya ci abinci suka dan taba hira da yara daga baya kowa ya tashi ya tafi makwancinshi. Kafin ya je ya yiwa
Saudah sallama har ta gama shirin baccinta don haka a dakin ya sameta har ta riga ta kwanta sai dai bata
yi bacci ba waya ce a hannunta tana chatting. Bayan ta amsa sallamarshi yace
“Har yanzu chatting din bai kare ba?”
Tayi murmushi tace
“Ya kare tunda ka zo.”
Suka yi dariya gaba daya. Bayan ya gama shiryawa yayi shafa’I da witri yana zaune a kan daddumar ya juya
ya kalleta
“Har yanzu ba kiyi bacci ba.”
Tace
“Ban yi ba, karatun tauhidi ne wanda aka yi bana nan shine aka yi min voice note nake ji.”
Ya dan yi jim sannan ya dauki wayarshi ya duba, ya mayar da wayar ya jiye ya dube ta ya dan yi gyaran
murya sannan yace
“Dama akwai wata magana da nake son muyi.”
Ta gyara kwanciyarta ta cigaba da kallonsa
“Yaran nan Ummi da Nawwara, ya za ayi ne da dauko su makaranta? Kinga ita uwarsu yawancin ranakun
tana da lecture gashi su Salim duk suna makaranta.”
Tace
“Allah sarki na gani ai sun shiga makaranta, Allah ya sa albarka. Ai sai kayi magana da Umman nasu ko?”
“Eh ai na gaya miki ita yawancin ranakun tana da lecture.”
Tace
“Allah sarki “
Ta cigaba da abinda take yi don ta fahimci inda ya dosa kuma bata so a zo wajen don baza ta yarda ba,
don haka ta yi masa shiru. Shima shiru din yayi, aka dan yi jim ta juya ta gyara kwanciyarta tayi barci ta
barshi. Ko da gari ya waye da walwalarta ta tashi, da yake ya siyo burodi sai ta dafa farfesun kaza da shayi
mai kayan kamshi. Tare suka zauna cin abincin safen da yake Madu ya fita da yaran don kai su makaranta.
Suna cin abincinsu suna hira, ya kurbi shayinsa ya ajiye kofin yace
“Yanzu wai ba za ki sami lokacin da za ki taimaka ki dinga dauko yaran nan daga makaranta ba, tunda saura
shekara daya ta gama karatun da zarar ta sami hutu sai ta cigaba.”
Tace
“Gaskiya ba zan sami lokaci ba.”
“A’ah. Sha biyun rana fa? Na zata ko wani aikin gidan ne zuwa sha biyu ai duk an gama. Dauko su fa kawai
za kiyi.”
“Idan kuma na dauko su sai na kawo su gida na shiga hidimar kula da su har lokacin da zata dawo? Ka san
fa sha biyun ranar nan lokaci ne da nake yin bacci in yara suka taso sai na tashi mu ci abinci mu huce
islamiyya, ka ga bani da lokaci.”
Ya bata rai ya ajiye kofin shayin da ya riga ya shanye yayi gyaran murya yace
“Abu ne fa na dan lokaci….”
Ta ajiye kofin ta katse shi
“Ka san wani abu, mu bar zancen nan. Na riga na gama da dauko yara daga makaranta tun tuni, kuma
wallahi na manta yanda ake raino. Ta dauko su kawai, ko ma kai ne za ka dauko su ai ba matsala idan ma
kuma a yaran ne za ka cire ‘daya daga tashi makarantar ya dinga dauko maka su don ta samu tayi karatun
duk daya. Ni dai ku cire ni daga wannan lissafin don gaskiya ba zan iya ba.”
Ta dauki kofin shayi ta ta mike tana fadin
“Bari na hada maka lunch dinka a kwando yau ko zubawa ban yi ba.”
Ta juya ta huce kichin ta barshi nan zaune yana takaici. Shi ya zata wannan ba wani abu bane kuma bai
taba zata za ta ki ba don duk yaranta ita ta dinga dauko su daga makaranta har suka girma, duk da
makarantar ma kusa da gida ce. Ya riga ya cewa Saudah zai sa Rabi ta dinga dauko su ga shi ta ‘ki. Ta hada
masa abincin ta kawo kan table din ta ajiye, ya tashi ya karasa shiryawa ya dau abincinsa ya fice. Yana
ficewa tace
“Tunda ni ce jakar gida na gama dauko nawa yaran yanzu na fara na kishiya don lalacewa, uban ‘yan son
kai.”
Tunda Baffa Atiku ya sanar da ita abinda ake ciki a kan maganar Baba karami ta shiga tashin hankali, don
bata taba tunanin zai ce haka ba. Gashi sai kashe kudi take a kan ayi auren nan amman ya ki yiwuwa, duk
da akwai aikin da ta bayar a yi bayan ta dawo daga Kaduna kuma ba a gama ba saboda bata cika kudin ba.
Shi kanshi baban su Zulaiha sai da ya gane rashin nutsuwarta, sai tamabaya yake ko bata da lafiya tana
cewa a’ah. Ta kirawo Zulaiha sau babu iyaka tana ta faman tambayarta ko akwai wani cigaba amma babu,
har tsoron ‘daga wayarta Zulaihan take yi saboda yanda take takura mata da tambayoyi. Gashi itama ta
fara shiga damuwa tunda sun shiga level 3, bata son abinda zai sa ta gama karatun nan ta koma gida ba
tare da miji ba. Duk wata dabara da ta san za tayi ta ja hankalin Baba kuma ta yi, amma abinda ta kula
dashi dawowar Mommy ma kamar gaba ya fara da ita don ko gaisuwarta bai amsa ba.
Da Sa’a taga dai wayar baza ta biya mata bukata ba sai kawai ta sa rana, ta samo Inno ‘yar wajen Inna
Hajara wadda kusan sa’anni suke; a fadarta wai Rabin tana ganin mutuncin Inno don haka su zo suyi mata
magana. Ta riga ta tsarawa Inno da su Inna Hajara cewa Baba yana son Zulaiha amma Rabi ta hana saboda
bata son ta. Sai da suka zabi lokaci daidai lokacin da ta tabbatar kafin su iso Abban ya fita sannan suka
taho.
A falo suka sameta ita kadai da yake yaran duka sun tafi makaranta, nan da nan ta tashi ta kawo musu
ruwa. Ta yi zaton ko sun zo yi mata sannu da zuwa ne don haka cikin fara a suka gaggaisa tace
“Inno amma dai Sa’a ce ta janyo ki ko don na san ke daga biki sai suna.”
Duka suka sa dariya. Bayan sun ‘dan sha ruwa suka yi jim sai Inno ta fara magana kamar yanda Sa’an ta
tsara mata.
“Wajenki muka zo fa Mommy.”
“Toh ai gani.” Mommy ta fada tana gyara zama.
“A kan maganar yaran nan.”
“Wadanne yara kenan?”
Inno ta gyara zama sannan ta kwaso bayani
“Ni ina ganin idan gida bata koshi ba ai ba za a kaiwa dawa ba. Yaron nan Baba fa in ya auri Zulai ai
zumuncin mu za a karfafa. Ko ma meye a tsakaninku ku iyayensu ai ya kamata ku ajiye kuyi mana wannan
alfarmar. Ni ina ga wannan abu in ya tabbata ma ai Abban nasu sai ya fi kowa jin dadi.”
Sai da ta gyara zama sannan ta bata amsa
“Uhm, hakane Inno sai dai da yake babu wannan zancen. Dama Baba bai taba sonta ba kuma da aka nemi
ya aureta ya gayawa Abban baya sonta. Ina ga kuwa ai an gama magana ko?”
Kafin wani yai magana Sa’a ta café
“Ni ko sai naga kamar an yi garajen yanke hukunci. Yaran nan fa da za a barsu a basu dama ai dcaf
Kafin ta karasa zancen Mommy ta mike tsaye saboda ta jiyo wayarta wadda take kara daga kicin. Kafin ta
‘daga kafarta Sa’an ta mike ta sha gabanta tana fadin
“Bamu gama magana ba za ki tashi.”
Ta kalleta cike da mamakin irin wannan tarewa da tayi mata. Sai da ta kalli kwayar idonta sannan tace
“Sa’a ki rubuta ki ajjiye ko bayan raina ‘dan da na haifa ba zai auri ‘yarki ba, ko babu komai linzami ya fi
karfin bakin kaza. Ko Baba yana son Zulai ba zai aure ta ba ballantana baya sonta, ko baki gane sakon
bane?”
Ta bude baki za ta bata amsa suka ji sallamar Madu, yanda yaga tsayuwar Mommy da Sa’a ya san ba lafiya
ba
“Fyiiiiit”
Yayi fito. Mommy ta tsani wannan fiton kuma duk lokacin da yayi a gabanta sai ta yi masa fada Amma yau
sai ta ji fiton yayi matukar yi mata dadi kamar wata busa. Yace
“Mommy akwai matsala ne?”
Kafin ta bashi amsa Sa’an ta ja baya kadan, ya karaso ya shigo. Sai a lokacin sannan yaga Inno don haka ya
rage tsaho
“Inna barka da safiya.”
Tace
“Yauwa Madun Kano, kana lafiya?”
Ya juyo wajen sa’a yace
“Ina wuni”
“Lafiya kalau” ta amsa babu yabo ba fallasa. Ta koma ta zauna jiki a sanyaye.
“Me ka dawo yi?”
Mommy ta tambayi Madu.
“Ina makaranta Abba ya kirani wai ya manta cheque book a gida na dauka na kai masa shi na zo dauka.
“Toh ai sai ka dauko yana ciki.”
Ya huce dakin Abba don dauko abin da yazo dauka. Gaba daya jikinsu yayi sanyi musamman Inno wadda
gaba ‘daya ma bata fahimci abinda yake faruwa ba duk da ta ji maganganun Rabi tsaf. Mommy ta huce
taje ta dauko wayarta sannan ta dawo ta zauna. Shima Madu da ya dauko cheque book din sai ya zauna a
dining table yana jira sai sun tafi sannan ya tafi. Sai da Sa’a taga babu hali sannan ta tashi tace
“Toh mu za mu tafi.”
Tana daga zaune a inda take tace
“Ku gaida gida, Allah ya kiyaye hanya.”
Ta dubi Inno tace
“Don Allah ki gaida Inna.”
Sukayi sallama suka fice.
Tun kafin su Mommy su dawo daga Umrah yake jin wata kasala, ga shi kuma yawan shan ruwansa ya karu.
Haka dai yake ta lallabawa sai dai idan abun yayi yawa sai ya sha panadol ya kwanta, ko a kasuwar ma
walwalarshi ta ragu don har ya ‘dan rame. Yau ma haka ya tashi bayan ya gama shiryawa yana zaune yana
cin abincin safe a wajen Saudah ya dube ta
“Yau bana jin dadin jikina haka nake ji na duk babu kwari.”
Tace
“Sannu. Tun tuni fa
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good