Showing 108001 words to 111000 words out of 196754 words

Chapter 37 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15376

fa na siyarwa halima rannan baki ga yanda take
saye ba yanzu, da ta ga babu harka za ta bugo min waya.”

Ta juya garin wanda yake a yar farar leda tace

“Toh, zan gwada.”

“Yauwa ‘yar gari, wannan ma sai kin ji aikinsa kya taho min da kudin makaranta.”

Sai bayan sallar la’asar sannan sukayi sallama Maman Surayya ta kama hanya. Ta dawo dakin tana
kwashe kayan da suka yi amfani da su, ta dauki kullin garin ta kare masa kallo.

“Zan gwada.”

Ta fada a fili. Tun kafin ma Mommy ta tafi ba wani abun kirki yake tabukawa ba sai minsahrin tsiya, balle
yanzu da ta tafi da sai ya wuce sati bai ko bi ta kanta ba. Toh ita kwanakin ma da tayi da aure tana more
wannan harkar ai kadan ne, hakuri kawai takeyi shi yasa yanzu duk wani gyara ma bai dameta ba. Ko ba
komai hausawa sun ce sa rai da koshi yana janyo kwanan yunwa, in bata sha komai itama kawai sai ta bi
dare tayi ta bacci abinta. Amma yanzu da yake akwai ragowar maganin da Kaka ta bata toh za ta gwada.
Dama ta kasa amfani da maganin saboda rashin tabbas din Abban don bata son ta kuskure, don dole ma
wannan maganin yayi aiki in ba haka ba ina zata sami dubu dari ta biya. Sai dai idan sata zata yi a
wajenshi don kuwa bata da su bata da dalilinsu.

Kafin magriba ta shiga kicin don dora abincin dare, tuwon alkama ta dafa da miyar kuka sannan da yake
shiri take nema tayi masa kunun Aya wanda yaji madara. Tana saukewa ta sa a flask don ta san sai bayan
isha’I zai nema, ta barbade miyar da garin ta juya sosai ta rufe. Kusan kullum kafin ya zo cin abinci ta riga
ta ci nata saboda baya zama da wuri, don haka bayan ya dawo ta ajiye masa abincin tace

“Bari naje na kwantar da yara nayi wanka.”

“Toh sai kin fito.”

Ta shige daki. Nawwara da Ummi a wajen Zulaiha suke kwana don haka Hanan da Baffa ne kawai a
wajenta, ta gyara musu kwanciya sannan ta shiga wanka. Tana fitowa ta zauna a gaban mudubi tana
gyara jikinta. Ta kula da shi ma yau cikin walwala yake don haka bata sa rai za a sami wata matsala ba ko
da yake tunda dan gudan hantarashi ya sami lafiya ai dole yayi walwala.

Shi kuwa Abba yana gama cin tuwon nan ya cika kofi da kunun Aya ya shanye, yayi gyatsa sannan ya
tashi ya koma kan kujera ya dau remote ya kunna TV. Bai fi ashirin da zama ba ya ji amai yana taso masa
don haka sai ya tashi daga kashingide ya zauna daidai, ya ga dai zaman ba zai yi masa ba don haka sai ya
mike ya je dining table ya tsiyayi ruwa ya kora. Yana shan ruwan nan kamar ya tsokano aman, da kyar ya
tare bakinsa da tafin hannunsa ya fada bandaki da gudu. Yana shiga ya tsuguna a gaban toilet, tsaf ya
amayar da abinda yake cikinsa. Yayi yunkurin tashi yaji ba zai iya ba don ya fara daina gani sosai don
haka ya koma ya zauna.

Ta fito daga dakin nata tana ta faman kamshi ta doro irin hijabin nan har kasa a kan kayan da ta saka.
Tayi mamaki da taga kofar dakinshi a bude haka don baya taba barin kofar nan a bude. Da sassarfa ta
karasa sai kawai ta jiyo nishinsa daga bandaki, a guje ta karasa. Ta tsuguna ta taro bayanshi don kokari
yake ya kwanta a wajen
“Subhanallahi, Abba me ya same ka?”

Kasa cewa komai yayi ya kwanto jikinta yana numfarfashi da kyar, ta duba fuskarshi taga duk ya bata jiki
da amai, a rude tace

“Amai kayi Abba? Me yake faruwa ne?”

Ta mike tsaye tayi kokarin daga shi suje daki taji bazata iya daga shi ba, ta fara janshi taji wari tana
dubawa taga ashe gudawa yayi a nan inda yake zauna. Tuni hawaye suka wanke mata fuska, cikin karaji
take kwalawa Zulaiha kira babu kakkautawa. Nan da nan kuwa sai ga Zulaiha a guje, kafin ta karaso tace

“Kirawo su Ahmad Abba bashi da lafia.”

A guje ta juya tana zuwa ta fada falon, Ahmad din ta fara gani yana zaune a kan kujerar dining yana shan
shayi. Ya kalleta da alamar tambaya a fuskarshi tayi kasa da idonta ta manta abinda tazo yi na dan lokaci,
Salim yace

“Zulai kanki kalau kuwa za ki shigo a guje ki kotse a nan ko kin sha wiwi ne?”

Nan da nan ta tuna abinda tazo yi tace

“Umma ce tace ku zo Abba bashi da lafiya.”

Kafin ta koma dakin Baba da Ahmad sun riga ta. Suna karasawa Baba yace

“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, me ya same shi?”

Cikin rawar baki tace

“Nima ban sani ba, kawai ina daki na zo na tarar dashi yana ta amai da kashi a wandonsa.”

“Gafara mana.” Ahmad ya ture ta ta huce cikin bandakin.

A nan su Madu suka karaso da sauran yaran duk suka leka cikin bandakin. Madu ya karasa yana fadin

“Faduwa yayi.”

“Amai yake yi da gudawa.”

Nan suka tura sauran yaran waje duka kamashi suka wanke masa jiki, ta basu kaya suka canza masa. Har
suka gama suka kwantar dashi a tsakar dakin a kan dadduma idanuwansa suna rufe amma dai yana
numfashi. Baba yace da Madu

“Juya mota mu kaishi asibiti.”

Kafin ya juyo motar ya kirawo likitansu ya gaya masa abinda yake faruwa. Tana jin yayi zancen asibiti ta
shiga ta canzo kaya don basu isa wannan karon su kaishi asibiti su hanata zuwa ba da ita za a tafi. Su
ukun suka kamashi suka fita dashi da kyar da dabara suka saka shi a bayan motar, Saudah ta zagaya ta
shiga ta daya gefen ta dora kanshi a kan cinyarta. Madu ya hau kujerar direba shi kuma Baba ya zaga ya
shiga gaban motar ya leko yacewa Ahmad

“Ku taho masa da kaya don kafin muje ya bata na jikinsa.”

Ahmad ya koma ya janyo CR-V ya sa Auta a gaban mota yacewa Salim
“Kai da Khalifa ku zauna za muyi waya kada a bar gidan ba kowa ga dare.”

Kafin suce wani abu sun fice Bala yana musu Allah ya sauwake.
EPISODE 25



Suna isa asibitin aka basu daki, nan da nan likita ya sa aka dauki jinin Abba da kuma kashin da yake yi da
yake aman ya tsaya. Aka saka mishi drip aka yi masa allurai sannan likita ya fito yace su biyo shi office. Su
uku suka bishi Baba karami da Madu da kuma Saudah, suna shiga office sun bayan likitan ya zauna ya
dubi Baba yace

“Ai da kun bar kanwar taku a gida sai…”

Kafin ya karasa Madu yace

“Ba kanwarmu bace matarsa ce.”

Likitan yayi sauri ya dago daga duban takardar da yake yi ya dubi Saudah yace

“Uhm, Allah sarki.”

Ya saita fuskarshi sannan ya dubeta ya nuna mata kujera yace

“Zauna Hajiya.”

Ta karasa ya zauna yayinda Baba karami ya zauna a daya kujerar shi kuma Madu ya tsaya a bayan Baban.
Kafin likita yayi magana aka shigo aka kawo sakamakon gwajin da aka yiwa Abban. Ya dan duba
sakamakon sannan yayi gyaran murya ya dubi Baba yace

“Food poisoning ya samu, ka gane ko? Wani abun ya ci wanda yake ya sami contamination ko kuma
wanda yake da allergies na wannan abun shi yasa jikin yaki karba. Gashi nan duk ya fitar su, ruwan
jikinshi ne ya fita sosai wajen amai da gudawar shi yasa saboda dehydration sai ya kasa tashi.”

Ya mayar da dubansa ga Saudah yace

“Meye abincin da yaci na karshe Hajiya?”

Tayi gyaran murya sannan ta amsa

“Uhm tuwo dai yaci na alkama da miyar kuka sai kunun aya, kum duk ya saba ci.”

Likita ya dan yi rubutu a takardar da ke take gabansa sannan ya dubeta yace

“Kuma bai ci wani abu bayan wannan ba ko da wani snack ko biscuit?”

“Eh bai ci komai ba, bai fi ma minti talatin da cin abincin ba na fito na tarar da shi a wannan halin.”

“Ruwan kuma da ya sha mai kyau ne?”

Kafin ta bada amsa Madu yace

“Sai dai ko ace me aka zuba masa a tuwon yaci ba wani kame-kamen ba?”

Ta dago kai ta dubi Madun wanda ya tsattsare ta da ido, ta dauke idonta ta dubi Baba wanda shima
kallonta yake yake yana jiran amsar tata. Ta mayar da dubanta ga likitan sannan ta bayar da amsa

“Babu abinda na zuba, yanda na saba dafawa haka na dafa sai dai ko idan a kasuwa ya ciyo wani abun.”
“Muna tare aiba kasuwarma abincin da kika zuba masa yaci.”

Likita yayi gyaran murya

“Uhm ina ga a barshi ma tunda dai an samu komai ya tsaya…”

Madu ya katse shi kafin ya karasa

“Ka barta doctor ta fadi abinda ta zuba masa don a san ma maganin da za a bashi ai ruwa baya tsami
banza.”

Ta dago ta harare shi sannan ta mayar da kanta kasa. Baba karami ya dafa hannun Madun da yake ajiye
a saman kujerar. Likita yace

“Babu komai ma zuwa an jima zai farka in sha Allahu sai dai a nan zai kwana don mu dinga kalawa da shi.
Sannan kuma idan kun koma gidan a dauke ragowar abincin da ya ci a kawo min shi gobe don mu duba
shi.”

Suka yiwa likita sallama suka fita. Dakin da Abban yake suka koma gaba dayansu har Saudan, ta riga su
shiga don haka ta tsaya a daidai kanshi su kuma suka tsaya a daidai kafafunshi. Babu wanda yacewa
kowa komai sai ita da take matse hawaye. Madu ne ya gaji da jin zukar majinarta yace

“Toh wai kukan me za ki dami mutane da shi, mu da kika nemi kashewa uba bamu ce komai ba sai ke za
ki zo ki samu a gaba kina kuka don bai mutu ba.”

Ta dago kai ta dubeshi ta kawar da kai ta share hawaye ta cigaba da duban Abban. Ya sake bude baki zai
yi magana Baba karami ya rike hannunshi yana masa alamar ya bari, jim kadan ya fizge hannunshi ya fice
daga dakin. Jimawa kadan shima Baban ya fito suka hadu gaba daya da su Ahmad suka zauna a kofar
dakin. Sai da aka sake jimawa Ahmad ya duba agogo yaga karfe sha daya har ta wuce ya dubi Baba yace

“Ai sai ku tafi ki, in ya so ni na kwana da Abban.”

Baba yace

“A’ah ku tafi dai tunda ka ga ni gobe zan koma Abuja in ta kama sai an kuma kwana sai ka kwana.”

Ahmad din ne ya karbi mukullin motar ya fita ya siyowa Abban ayaba da kuma cereal da kayan shayi
kamar yanda likitan ya basu umarni. Yana dawowa yace Salim ya kirawo Saudah su tafi. Ya bude kofar ya
shiga dakin ba tare da yace mata komai ba ya leka fuskar Abban ya ga har yanzu bacci yake yi sannan ya
dubeta yace

“Ki zo mu tafi gida.”

Kafin ta amsa ya fice. Ta yi tunanin da tace baza ta tafi ba sai kuma ta tuna ta baro yara a gida don haka
jiki babu kwari ta fito ta same su a wajen motar. Tana karasowa Madu ya mikawa Ahmad mukullin don
ya gaya masa su tafi su barta yace da ita za su tafi don haka yace shi ba zai tuka ba. Ahmad ya zauna a
kujerar direba, Madu ya shiga gaba yayinda ita da Salim suka shiga baya.

Yana jan motar ta gyara zama ta cigaba da goge hawaye. Ta kasa daina kuka, wannan abun da maman
Surayya ta bata menene shi ne. Shi kadai ta sa a abincin wanda bata saba ba amma a kasa da minti
talatin har ya ci abincin ya fice daga hayyacinsa. Tabbas da ya mutu yau baza ta yafewa kanta ba, da
wane ido za ta dubi su Nawwara tace ta kashe musu uba. Bata taba ganin shi a yanayi mai kama da
wannan ba, tabbas da babu kowa a gidan bata ma san yanda za tayi ba. Allah ya sa dai babu wanda yaci
ragowar tuwon Abban da ya bari a dinga table. Motar tana tsayawa a tsakar gidan tayi sauri ta fita daga
motar kamar wadda take zaune a kan ‘kaya. Ahmad ya bude kofar motar yace mata

“Ki bawa Zulai ragowar abincin da ya ci ta miko.”

Kafin tayi magana Madu yace

“Da ma ka rabu da ita baza ta baka ba wani daban za ta baka.”

Ta juyo ta harareshi ta wuce cikin sauri, ta tsani wannan Madu amma shi saboda tsabar sa mata ido ya
san abinda za ta yi kafin ta aikata. Tana shiga babu kowa a falon, ta riga ta san sun yi bacci don haka ta
wuce kichin. Kwanukan abincin suna nan yanda ya bari Zulaiha ta rufe kunun ayar dai suka shanye ita da
yara. Da yake flask din da yaci abinci mai uku ne sai kawai ta dauki wankakken wanda bata yi amfani da
shi ba ta debo miya daga tukunya ta zuba kamar an rage , ta rufe ta hado da na tuwon ta fito dasu. Tana
zuwa kofar falonta ta kwalawa Bala kira ta bashi tace

“Ka kaiwa Ahmad kace masa yara sun shanye ragowar kunun ayar da ya bari.”

Ahmad din ne ya bude kofar don haka shi ya karbi kwanukan daga hannun Bala. Ya karasa da su ya tarar
da Madu a kicin din yana shan ruwa, ya kalle shi yace

“Kada fa ku wahalar da shariah baza ta baka wanda ya ci ba ka san ta iya wasan kwaikwayo.”

“Ka bari dai a basu suyi aikinsu.”

Haka suka kwana suna zullumi, sai rashin Mommy ya dawo musu sabo gaba dayansu kowa sai da yayi
kuka kafin su kwanta.

Gari yana wayewa Salim ya dafawa Abba dashishi da miyar alaiyahu suka zuba masa ruwan zafi a flask
suka kama hanya suka tafi. Tana ji suka tafi bata ce komai ba, ta so kwarai taje amma da ta tuna da
Madu za a je sai ta ji bata son zuwa. Suna shiga dakin suka sami Abba a zaune suna hira da Baba Karami
yana cin ayaba, sun ji dadin ganinshi ya wattsake duk da ya dan rame kadan. Nan suka zauna aka shiga
hira, suka zuba masa abinci ya ci ya koshi ya dubi Baba yace

“Ko likitan nan bai sallameni ba yau tafiya zan yi don na kula shi babu abinda yake so kamar ya kwantar
da mutum.”

Yayi dariya yace

“Haba Abba ai in ya ga ka ji sauki zai sallameka shima.”

Basu jima ba likitan ya shigo bayan an gaggaisa yaran suka fice sai Abba da Baba da Ahmad, likitan ya
dubi Abba yace

“Ah jiki yayi kayau, ai yanzu ma zan sallameka Alhaji.”

“Yauwa.”

Yayi gayran muray ya cigaba
“Alhaji wani abun kaci wanda jikinka Bai karba ba shi ya janyo wannan wahalar, sai dai nan gaba duk
abinda za ka ci ka tabbatar an kula dashi.”

“Toh likita tuwo dai naci miyar kuka sai kunun aya, ban san inda matsalar take ba. Rabon dai a sha
wahala Allah ya sauwake.”

Likita ya yi masa tambayoyi sannan ya rubuta masa magani ya sallamesu suka kamo hanyar gida.

Duk da bata sa rai za a sallameshi yau ba amma kafin su dawo ta wanke bandakin ta gyara dakin tsaf. Ta
ji dadi sosai da taji muryarshi Bala yana masa sannu yana amsawa. Yana shiga falon ta fito don yi masa
sannu da zuwa. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ta matso tana kokarin kama shi yace

“Zan iya ai, na sami lafiya.”

Don haka sai ta bi bayansa ta raka shi dakin, yana shiga ya ya fada wanka.

Da yake a gaban Zulaiha aka yi tun daren ta kirawo Ummanta ta sanar da ita, don haka kafin sha daya sai
ga mutanen Bichi, kungiya guda suka yo shatar mota suka taho, ga kayan dubiya lemo, ayaba da goba
harda kajin hausa guda biyu da Inna Hajara ta bayar aka yanka aka tahowa da Abban. Ba Abba ba kowa
sai da yayi mamakin ganinsu,a nan suka wuni sai da yamma sanan suka kama hanya.

Yamma tana yi Baba karami ya bi jirgin karfe biyar ya koma Abuja .

……….

Basu hadu da Abdallah ba sai wajen goman dare da Abdallan ya dawo dakin, yana shiga dakin ya mika
masa hannu

“Mutan Kano sannu da hanya, ya ka baro mutan gidan.”

“Alhamdulillah.”

“Ya labarin Mommy kuwa?”

Ya kauda kai ya amsa da murya kasa-kasa yace

“Hmmn! Babu wani labari.”

“Subhanallahi toh Allah ya sa a sameta.”

“Amin ya Allah.”

Ya janyo faranti ya zauna ya zazzage abinda ya zo da shi a leda, kaza ce gasasshiya da gurasa ya zunguri
Baba yace

“Tashi za ka yi fa muci don ba za ka sani zubar da kudi na ba.”

“Ai kwarai kuwa, don yunwa nake ji.”

Suka fara cin abincin suna kora lemon five alive, jimawa kadan Abdallah yace

“Wai mutumina ya Khairy kuwa? Kun yi waya over the weekend?”
“Tab, wallahi bamu yi ba. Tunda na isa Kano na kirawo ta bata dauka ba nace sai dare yayi zan kirawo ta
toh daren kuma a asibiti muka kwana da Abba, na so kiranta amma bana son na dameshi gaba daya
kuma sai na manta. Ai ni me laifi ne ma jiya ne birthday dinta amma saboda ban zauna ba kuma a rude
nayi weekend din gaba daya ma na manta.”

Abdallah yayi dariya ya kara kai loma yace

“Ko da na ji, toh bari mu gama na siyar maka da wata jarida.”

“Allah mutumina ka shako gulma.”

Suka yi dariya suka cigaba da cin abincinsu. Sai da suka gama cin abincin sannan Abdallah ya dauko
wayarsa ya budo instagram, ya mikawa Baba wayar yana fadin

“To ka ga inda aka yi birthday party mutumina.”

Khairiyya ce da ita da wani wanda daga gani ka san saurayinta ne yana rike da hannunta suka shigo
wajen, sauran mutanen da ke zaune a kan kayataccen tebur din suka mike suna tafi. Suka karasa ya ja
mata kujera ta zauna sannan Shima ya zauna. A nan video din ya kare, Abdallah ya sa hannu ya tura
shafin sama ya nuno wani video din. Cake ta yanka tare da hannunshi a kan nata ana ta yi musu tafi, ya
dauki guntun cake din ya sa mata a baki. A nan video din ya kare Abdallah zai budo wani video din Baba
karami ya ture wayar gefe don haka ya dauke wayarsa. Yace

“Toh ka san waye saurayin nata? Dan gidan sanata Mamman Yelwa ne fa.”

Ya kawar da kanshi yace

“Ta yiwa kanta.”

“Ni ma haka nace mutumina bata dace da kai ba, Allah ya baka mace ta gari.”

Sai da ya nisa sannan yace

“Amma ta bani mamaki, ban zaton haka daga wajenta ba kuma ko kusa ban ga alama ba. Sai dai ko
bayan su Baba Aliko su zo maganar auren mu sannan

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login