Showing 183001 words to 186000 words out of 196754 words

Chapter 62 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15386

take
zaune, ta koma ta kawo masa ruwa sannan ta shige daki wanda yake cikin falon. Bayan ya gaida Baba
Yalwa sun dan taba hira yace

‘Baba wallahi daman wata ‘yar matsala ce ta taso a gidan na rasa yanda zan yi da ita.’

Ta tashi zaune daga kashingidar da tayi ta gyara zama

‘Subhanallahi, to Allah ya warware.’

Nan ya gaya mata abinda yake faruwa, tunda ya fara magana take sallallami da tafa hannuwa, tace

‘A gidan naka Usmanu?’

Ya sunkuyar da kai kawai.

‘Yanzu ita kuwa yarinyar nan me yasa take haka don Allah, kazafi da zargi irin wannan ai komai
kiyayyarka da mutum bazaka yi masa ba.’

‘Wallahi Baba, to ni yanzu kinga sun sakani a tsaka mai wuya. Nayi-nayi suyi sulhu a gida sun ki, ita
Mommy saboda zancen yana ta yawo a gari ta fi so aje ayi sulhun a kotu don mutane su san an wanketa
amma ni wallahi Baba bana son aje kotun. Kinga kamar ‘yayankane biyu suna fada su tafi kotu, duka
nakane babu wanda za ka goyi bayansa don kiyayya shi yasa sulhun a gida ya fi sauki. Ita Rabi idan na
bata hakuri gani take kamar ina son goyon bayan Saudah ne ita kuma Saudah gani take kamar na ki na sa
baki ayi sulhu a gida.’

‘To ai ita Saude bata da bakin magana wannan ai babbar ta’asa tayi, ita kuwa Mommy da gaskiyarta don
haka dole sai dai a bita a hankali.’

Ya sunkuyar da kai, sukayi shiru na dan lokaci

‘Yanzu yaushe ne shari’ar?’

‘Gobe ne da karfe sha biyun rana.’

Ta jijjiga kai

‘To ai baka sanar dani da wuri ba, ko daya ma ban san abinda yake faruwa ba kuma naga ko Juma’ar da
ta wuce kana nan.’

‘Wallahi Baba nayi zaton zamu samu ayi sulhun a gida shi yasa nayi shiru da zancen.’

Ta jijjiga kai cikin damuwa

‘To yanzu ka ga dare ya fara yi da safen in sha Allah zan zo gidan na san Mommy ba zata ki hakura ba,
amma wannan yarinya gaskiya Usmanu idan baka mayar da hankali ba zata rusa maka gida. Yaranka da
matarka masu tarbiyya da jin magana amma daga lokacin da ka auro yarinyar nan fitna wannan na bin
waccan, gaskiya ya kamata ta canza hali ta bari a zauna lafiya. Yanzu idan sukaje kotu ai da kai da
yaransu suka tozarta.’
Suka sake yin shiru, jimawa kadan tace

‘Kafin sha daya zan zo gidan in sha Allahu muga abinda hali zai yi.’

‘Na gode Baba.’

Magariba ta kusa don haka yayi mata sallama ya fita.

Ana idar da sallar magariba Zulaiha ta dauki waya ta fita waje bakin gate ta kirawo Ummanta ta sanar da
ita abinda yake faruwa. Duk da tayi mamakin hakan sai da tayi dariya tace

‘Kai lallai yarinyar nan bata da saiti, ta zata duk abinda tayi zata sha shi ya sa to gashi nan ta debo ruwan
dafa kanta.’

‘Wallahi Umma, lallaba Baba Yalwa zanyi ta tafi dani na kalli dramar da za a tafka.’

‘Ai ko ni din ma in sha Allahu kafin goma ina gidan da ni za a je kotun nan naga idon mara kunya.’

Sukayi sallama kowa na Shirin zuwa kallon yanda zata kaya.
EPISODE 39

RANAR SHIGA KOTU



Daga masallaci suka fito bayan idar da sallar asuba, Baban Farida ya karasa da sauri wajen Abba. Bayan
ya amsa gaisuwar su Ahmad ya mikawa Abban hannu sukayi musabiha, ya rike hannun Abban ya dan ja
shi gefe. Bayan sun dan matsa daga wajen yaran yace

‘Alhaji ashe abinda yake faruwa kenan, mata sun dage sai sun je kotu.’

Ya jijjiga kai cike da damuwa

‘Wallahi Dakta, na so kwarai suyi sulhu a gida amma abun ya ki.’

‘Ikon Allah, to Allah ya kyauta. Ai abun ne gaba daya babu dadi wallahi an rasa yanda akayi aka kirkiri
wannan zancen kuma yake ta yawo a unguwa don ka san ko ni sai da liman ta tambaye ni jiya fa.’

Ya kalleshi da mamaki

‘Allah Dakta? Amma ni bai yi min maganar ba kuma ko jiya da na dawo daga kasuwa mun gaisa.’

‘Eh ai ba zai iya yi maka ba shi yasa ni ya tambaye ni, na dai tabbatar masa babu wannan zance kage ne
kawai.’

Ya sunkuyar da kai kawai yana jijjiga kai ba tare da yace komai ba.

Baban Farida ya cigaba

‘Itama mai dakina tace min zata bi su kotun don zata bayar da shaida idan ta kama.’

‘Allah ya kyauta.’

‘Amin ya Allah, ka san idan aka ce zance ya shiga hannun shaidanun mutane sai inda ya tsaya. Amma dai
da sun tsaya sun yi sulhun a gida kambda zai fi.’

‘Wallahi babu yanda banyi ba ka gan ni, to har yanzu dai ban fitar da rai ba ko kafin sha biyun ita
Mommy ta canza ra’ayi.’

‘To Allah ya warware.’

‘Amin ya Allah, Amin Dakta. Na gode.’

Sukayi sallama a daidai lokacin da suka kawo gidan Dakta, ya shige gida Abba ya wuce yana hango su
Ahmad da suka wuce suka barsu da Dakta.

……….

Tun jiya aka koma makaranta, da yake dama Sallah break aka basu suna komawa sati biyu zasu yi su fara
jarrabawar fita. Bata cikin hayyacinta don haka kawai ta yanke bazata makarantar ba, yara dai ta shirya
su Ahmad ya kai su. A firgice ta kwana saboda ta sami tabbacin cewa Mommy bata janye kara ba kuma
bazata janye ba, haka ta tashi a birkice. Shi kuwa Abba da yake har yau baya kulata ba ma a dakinshi ta
kwana ba duk da shi dinma ba a nutse ya kwana ba. Ji yake kamar ‘yayanshine guda biyu za su shiga
kotu; dukansu yana sonsu baya so ayi abinda zai taba kowa, don haka wannan shiga kotun ji yake kamar
shi za ayiwa tonon asiri. Da wuri ta tashi ta shirya ‘yan makaranta wadanda Ahmad ya hadasu da Auta da
Khalifa ya kai su makaranta. Nan da nan ta hada abincin safe ta dora a table tanayi tana gode Allah da
yasa yau zata fita daga gairki don ta gaji da wannan gabar da Abban yakeyi da ita, don har wani
hantararta taga yana yi. Haka take yin aikin tana yi tana share kwalla. Wajen karfe takwas da Rabi Yaya
Ummu ta iso, da yake Abban bai riga ya ci abincin safe ba sai ta bude dakin baki ta sauke ta a nan. Bayan
sun gama gaisawa tace

‘Wai yanzu an rasa wanda zai yiwa matarnan magana dole sai kunje kotun?’

Ta kalleta saroro tace

‘Uhm.’

Kafin ta sake cewa wani abu ta mike ta barta da su Hanan tace

‘Bari naje na dan kintsa.’

Ta fito ta fara shiga dakin Abban ta sanar da shi Yaya Ummu tana dakin baki sannan ta wuce nata dakin.
Ba wai wani abu zata yi a dakin ba amma dai bata son magana, yanzu ma so kawai takeyi sha biyu tayi
ayi duk abinda za ayi a wuce don tana cikin matsananciyar damuwa. Kafin ta karasa gaban gadon ta jiyo
sallama daga falon wadda in dai ba kuskuren gane murya tayi ba to Sa’a ce ko Zulaiha, a sanyeye ta
dawo falon inda ta hango Sa’a daga bakin kofa ta amsa sallamar tace

‘Anti Sa’a ce? Karaso mana.’

Ta karaso ciki tana ta wani washe baki ta zauna a kan kujera, itama Saudan ta karasa ta zauna. Bayan sun
gaisa tace

‘Lafiya dai na ganki da sassafen nan.’

Ta kalleta da dan mamaki tace

‘Uhm! Kin san mu mutanen kauye mun saba da sammako ai.’

‘Uhm Allah sarki, Allah ya sa dai lafiya?’

‘A’a lafiya kalau wajen Yayan nazo dama.’

Ta mike tsaye tana fadin

‘Yanzu zai fito ai, bari naje na karasa aikin da nake yi.’

Ta wuce dakin kafin Sa’an tace wani abu, ta bi kofar dakin da kallo tana dariya a ranta tana fadin

‘Damu za aje in sha Allahu ayi maganin mara kunya.’

Da yake akwai wuta sai kawai ta mike ta kunnawa kanta TV din dake falon.

…………..

Tun dare lawyer din Mommy ya sanar da ita shari’arsu sai sha biyun rana amma ya kamata ace goma
zuwa goma da rabi suna kotu don haka da wuri ta gama duk wani shiri da zata yi. Karfe tara da rabi
lawyer yana bakin gate inda yake jiransu a motarsa; ya sanar da ita nan din hanyarsace don haka idan ya
fito zai tsaya sai su wuce tare. Suma Baraka da Mubarak da yake sun kwana da shirin zuwa Kano karfe
tara a cikin Kano tayi musu. A gidan Yaya Shafa suka hadu, suna zaune a falon Yaya Shafa bayan sun
gaisa ta dube su tace

‘Allah ya sauwake, ku dai don Allah kada ku dinga zuga ku bari suyi sulhun ba sai an yi shari’ar ba tunda
kunga abune na cikin gida.’

Baraka ta juyar da kai tace

‘Ai yanzu kam ya zama abu na kwararo Yaya Shafa.’

‘Hakane Kam. Nima din zan je asibiti ne tunda sai sha biyu za a shiga zan sameku a can.’

Mubarak ya mike ya dubi Baraka yace

‘Ai sai mu wuce ko?’

Sukayi sallama da Yaya Shafa ta wuce asibiti wajen aikinta su kuma suka wuce gidan Rabi. Karfe tara da
rabi ta gota kadan suka isa, gaba daya yaran suna nan don har Ahmad yau excuse ya dauko daga banki
don yana son ganin shari’ar. Baba karami ne kawai bai sami zuwa ba sai karshen sati. Suna jiyo Muryar
Baraka suka fito gaba daya bayan sun gaggaisa suka zauna a falon suna hirarrakinsu. A nan Mommy ta
dauki wayarta ta kirawo Maman Farida wadda itama zata bayar da shaida a kotun idan ta kama. Ba
jimawa ta shigo a shirye suka zauna a nana ana ta ‘yan hirarraki.

………….

Shima Abban yana dakin ne ba don yana wani abun ba sai don bai san me zai yi ba. Ya dan yi bacci
saboda Baba Yalwa ta yi masa alkawin zata zo tayiwa Rabi magana, amma gashi yanzu har wajen tara da
rabi bata karaso ba. Baya son yayi mata waya kada ya dameta amma a zahiri ya fara shiga damuwa. Haka
dai ya tashi ya shiga wanka bayan ya fito ya shirya sannan ya fito falon. Bai san da zuwan Sa’a ba don
haka yayi mamakin ganinta a falon, wajenta ya wuce ya zauna. Bayan sun gaisa yace

‘Lafiya kuke dai ko?’

Ta karkata kai

‘Lafiya kalau Yaya. Dama zuwa nayi na dubaku da yake na kwana biyu ban zo ba, um kuma da yake ina so
na rokeka ka dan kara min jari Yaya. Ka san ina sayarda ruwa da kayan lemo amma kwana biyu na daina
saboda babu jarin, to yanzu da yake zafi yazo shine nake so ko za ka taimaka min na samu na cigaba.’

Ya san da sana’ar don shine ma ya saya mata firij din tun kafin ya auro Saudah. Yace

‘Eh, ba zai gagara ba amma dai ba yau ba ki bari zuwa wani satin in sha Allahu za muyi magana.’

‘To Yaya na gode, Allah ya kara arziki Allah ya raya zuri’a.’

‘Amin ya Allah.’

Suka dan yi shiru, jimawa kadan ya mike yana fadin

‘Bari na ci abinci, ko za ki dawo nan mu ci.’
‘A’a wallahi Yaya na ma karya Alhamdulillah.’

Ya zauna a kan table ya zuba abinci ya fara ci, yanayi yana tunanin hanyar da zai bi ya sallami Sa’a ta
koma inda ta fito don ya san idan dai ta shaida duk ma abinda zai faru yau toh tabbas har Bichi sai
labarin ya kai. Shi kuwa ya fi so a bar yawo da zancen haka. Kafin ya cinye abincin dabara ta fado masa
don haka yana gama cin abincin ya tashi ya shige dakinsa, jimawa kadan ya fito da kudi a hannusa naira
dubu biyu. Ya zo ta bayan kujera ya mika mata yana fadin

‘Ga wannan kya hau mota ko.’

‘To Yaya na gode Allah ya bar zumunci.’

‘Amin. Yaushe za ki tafin ne?’

Ta karkata kai tana murmushi tace

‘Zan dan jira rana ta daga wajen sha daya haka zuwa sha biyu don zan shiga kasuwa kafin na wuce
wanda nake sayayya a wajensa baya fitowa da wuri.’

‘To to ma sha Allah.’

Ya fada yana shafa haba, tabbas ba haka ya so ba don ya san muddin sa’a taji abinda zai faru yau kowa
sai ya ji, amma ba zai iya korarta ba don haka ya wuce ya koma daki ya rabu da ita. Yana shiga ya duba
agogo karfe goma da minti biyar Baba Yalwa bata zo ba, to ko dai ta zo ne tana wajen Mommy amma ai
da ta zo za su zo su gaya masa. Ya karasa ya zauna a kan kujerar da ke cikin dakin yana sake duba agogo
cike da damuwa. Tun safe wajen bakwai da rabi da ya shiga suka gaisa da ita ya fito bai sake komawaba,
a yanzu ma dai tsoron komawar yakeyi don idan ta kama za aje kotun to Yaya ma za ayi tafiyar? Ya san
dai yara za su dauki Mommy su kaita, to ita Saudah shine zai kaita ko ya za ayi? Ko kuma dai shine zai
saka su a gaba ita da Rabin ya kaisu. Ya daga hannunsa yana kallon sama ya fada a fili

‘Allah ka sa ba za ayi shari’ar nan ba, Allah ka kashe zancen nan ya fita daga bakunan mutane.’

Ya ajiye hannun ya dafe kai, tabbas yana cikin damuwa.

……………..

Suna nan zaune a falon Mommy ma ta fito ta zauna yayinda su Ahmad suka koma daki. Ta dubi Mubarak
tace

‘Ka ga yau Baraka ta hanaka zuwa aiki, ko da yake kai din ma baka ganin nisan hanyar Kaduna zuwa
Kano.’

‘Babu ruwanki gara muje ayi da mu, wannan ai ba karamin abu bane kuma duk wanda ya hada jini dake
abun ya shafe shi.’

Maman Farida tace

‘Wallahi hakane.’

Tayi murmushi tace
‘Na gayawa lawyer din fa idan munje kotun in dai ta amsa laifinta ta nemi sulhu to a bar shari’ar muyi
sulhu alkali ya shaida amma idan bata nema ba to ayi duk abinda ake yi a shari’a.’

Baraka tace

‘Wallahi da ma kin bar mara kunya ta girbe shukar da ta dade tana yi, a zanewa banza jiki wallahi.’

Maman Farida tayi murmushi tace

‘Kai Hajiya Baraka ai hakan ma yayi, wannan kawai ya isa ki ga an bar wancan zancen an kama yada
labarin kotu. Ai in dai ta amsa laifinta a kotu sai ayi sulhun kawai.’

‘Ya zanyi kun fi karfina, bana son raini ne wallahi. Yarinya tun kafin a haifeta kike zaman aure bakiyi
barikin ba sai yanzu da aka haifeta ta san dadin miji.’

Sukayi dariya gaba daya.

Wajen karfe goma da rabi lawyer ya kirawo Mommy yace mata yana bakin gate ya kamata su fito don su
isa da wuri. Ta mike tana fadin

‘Barrister yace mu fito yana gate sai mu tafi gaba daya, bari na dauko mayafina sai mu wuce.’

Ta leka daki inda su Ahmad suke ta sanar da su su fito sannan ta wuce nata dakin don ta shiryo. Jaka
kawai ta dauko ta yafa mayafinta ta fito falon ta tarar Ahmad, Madu da Salim suma suna falon suna
zaune a dining table suna jira. Tana fitowa tace

‘Ai sai mu tafi ko?’

Ta dubi su Ahmad tace

‘A motar Mubarak za mu tafi ni da su Maman Farida ku sai ku taho a motar babanku.’

Ta dubi Salim tace

‘Kaje kacewa Babanka za mu tafi, yana wajen su Nawwara.’

Ya amsa ya fice, suka dan yi jinkira suna jiran ya gayawa Abban sai su wuce. Kafin ya dawo suka jiyo
sallama daga bakin kofa ta daga labule ta shigo da murmushinta. Da sauri Mommy ta karasa tana fadin

‘Sannu da zuwa Baba, maraba.’

Ta amsa ta shigo inda Mommy din ta karasa da ita kan kujera ta zauna tana fadin

‘Na ganku a tsaye ko fita zakuyi ne?’

Ta sunkuyar da kai yayinda su Baraka suka dawo suma suka zauna. Gaba daya suka gaggaisa da Baba
Yalwa, yaran suma suka karaso suka gaisheta. Mommy ta dubi Salim wanda ya riga ya dawo tace

‘Ka koma kace da Abba ga Baba ta zo.’

Ya amsa ya fice.

Bayan sun gama gaisawa Mommy ta tashi ta shiga kicin don kawowa Baba Yalwa ruwa yayinda Madu da
Ahmad suka fice daga falon. Ta dan tsaya a tsakiyar kicin din tana mamakin zuwan Baba Yalwa a daidai
wannan lokacin. Gaba daya ma sau nawa Baban ta taba zuwa gidan? Kuma duk zuwan nata haihuwa aka
yi don ko da auren Saudah ma bata zo ba sai da ta haifi Nawwara sannan tazo barka. Ta bi kicin din da
kallo tana tunanin to ruwa ma zata kai mata ko lemo? Tana nan tsaye Salim ya shigo Abba na biye da shi,
yayi turis don bai san da zuwan su Baraka ba yana mamaki to suma kotun suka zo rakiya kenan. Ya fara
bawa Mubarak hannu suka gaisa da yake shine a gefe, kafin ya tsuguna a gaban Baba Yalwa tace

‘Ai sai ka kira Sauden ko? Sai mu gaisa gaba daya don kamar dai na makara ko?’

Ya mike yana fadin

‘Hakane.’

Ya juya ya fita kafin su karasa gaisawa, ya bar su Baraka suna kallon ikon Allah. Tun bayan data gaisa da
Sa’a ta shige daki bata sake fitowa ba sai yara da suke kaiwa da kawowarsu tsakanin dakin baki wajen
Yaya Ummu da falo wajen Sa’a. Ya wuce Sa’a a falon ya bude kofar dakin ya shige, tana nan a kwance a
kan gado tana faman tunani har kanta ya fara ciwo. Yace

‘Ki taso muje falon Mommy Baba Yalwa tana kiranki.’

Da sauri ta mike da ta ji an ambaci Baba Yalwa, ta goge fuskarta tace

‘Ina zuwa.’

Ya tsaya yana kallonta yace

‘Wucewa zakiyi muje ai ba wai kina zuwa ba.’

Don haka sai ta dauki hijabi a kan dadduma ta saka ta wuce gaba yana binta a baya. Suna fitowa falon
Hanan ta rugo da gudu ta kama kafarta tana fadin

‘Umma jan je.’

Kafin tayi wani yunkuri shima Baffa ya karaso don haka ta rike hannuwansu tace

‘Bari na kaisu wajen Yaya Umfadi

Ta mayar da su wajen Ummun ta sanar da ita Baba Yalwace ta zo. Take ta mike ta kama yaran tana fadin

‘Ai sai muje tunda in hakuri za a bayar ai nima na sa baki mu hadu mu bata hakurin ko.’

Ta so tace a’a to amma sai taga hakane, gara su hadu musamman da yake Abba yana ganin harda laifin
Ummun a ciki watakila idan ta bada hakuri duk a yafe. Suna fitowa falon Sa’a ta mike tace

‘Bari naje na gaida Baba Yalwa Yaya ya ce ta zo, daga can sai na wuce gida.’

Kallonta kawai Saudah tayi da takaici ita kuwa kafin suyi wani yunkuri ta ma riga ta fice daga falon ta

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login