Showing 60001 words to 63000 words out of 196754 words
Chapter 21 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
iya kokarinta tana yi ga shi yanzu ko mai aiki bata da shi tunda wadda Jamila ta kawo mata ta
gudu. Zulaihan ma da take ganin za ta dinga taimaka mata yanzu ta daina yawan zaman gidan;da zarar aka
ce Juma’ah sai tayi tafiyarta gidansu sai litinin za ta dawo. Don haka ma ita kanta ba ta samun lokacin kula
da kanta. Ta karfin tsiya ya sa Mommy dole kullum ranar da bata da girki sai ta yi masa abincin tafiya
kasuwa, tun tana fada tana kin yi har dai ta gaji ta hakura. In ya dawo sai ya ci abincin dare a wajen Saudah
din.
Baffa Atiku ne da kuma Baffan Bichi suka shirya zuwa gaisuwa da neman aure gidan su Khairiyya, ko da
Baffa Aliko ma yaji labari yace shima zai je da yake lokacin yana Abuja. An yi musu karba ta mutunci da
karramawa, iyayen Khairiyya sun ce nan da wata shida ma za a iya zuwa da komai a yi biki kafin nan ta
gama bautar kasa. Suka rabu kowa yana farin ciki. Baffan Bichi shi ya bawa matarsa labarin zuwansu da
yanda ya gano dukiya a gidan uban Khairiyya ga mutunci. Da yake suna shiri da Sa’a a guje ta kai mata
labari. Hankalin Sa’a ya yi matukar tashi, duk da ta biya wani malami yayi mata aiki amma shiru.
Tana cikin wannan tashin hankalin Kuma mahaifin Zulaihan yazo da wani zance. Yace mata Malam Ashiru
makocinshi yana nemawa yaronsa Habu auren Zulaiha, shi kuma ya riga ya amsa tunda a iya saninsa babu
wani tsayayye. Duk wani bayani da ta yi masa bai dauka ba sai ma cewa yayi
“Nan da shekara daya fa za ta gama karatun nan, in bata auri habu ba ni zata aura koko jikata za kiyi ki
sha? In dai ba wanda ya fi habu ta kawo min ba toh dole kuwa ta aureshi domin shima yana da sana’arsa
yana sayar da dabbobi daga nan har kudu.”
Yanda ta san shi da taurin kai ta san zai aikata ga shi kuma danginsa duk suna goyon bayan shi. Nan da
nan ta kirawo Zulaiha tace mata kar ta kuskura ta zo gida har sai in itace ta tace tazo in ba haka ba ta zama
matar Habu. Awakanta ta hada guda uku ta sayar a ka hadata da wani sabon malami ta je wajenshi neman
taimako. Bayan ya ji duk bayanta yace taje gobe ta dawo zai yi mata duba, amma ta bayar da abinda tazo
dashi. Nan da nan ta dauki duk kudin awakin nan gaba daya ta mika, malam ya dafe ya sallameta. Bayan
ta dawo ta shiga wajen shi ta zauna tana sauraronsa. Yace
“Wannan al’amarin akwai duhu a ciki sosai.”
“Malam babu yanda za ayi a sa mana hasken kuma?”
“Ba mu da wannan ikon. Idan dai kina so za a yi miki aiki yarinya za tayi farin jini, amma wancan al’amari
babu haske a cikinshi ko kadan.”
Yanda yake ta muzurai ya bata tsoro, amma da ta tuno duk abunda ta mallaka ne ta bashi sai ta daure
cikin rawar baki tace
“Malam yanzu wancan din babu wata dabara da za a yi?”
Ya kyalkyale da dariya sannan ya sha kunu ya bata amsa
“Duk inda duhu yake ba ma shiga, kema idan kika shiga ba za ki kai labari ba.”
Dolenta ta baro wajen malamin nan ba kudinta kuma babu biyan bukata, sai da ta kwana biyu tana zazzabi
saboda takaici. Bayan ta warke ta kirawo Zulaihan ta sanar da ita kuma ta gaya mata duk yanda za ayi tayi
kokari ta samo miji a nan Kanon.
Tunda Baba karami ya koma Abuja ya sayi wani abun gwajin blood sugar ya ajiye, don haka yana isowa ya
bawa Abban kuma ya nuna masa yanda ake amfani dashi. Da kanshi ya dauki Abban suka je wajen likitan
ya sake dubanshi ya tabbatar masa komai lafiya sai dai tun tuni yake bawa Abban shawara ya dinga zuwa
wajen motsa jiki ya ki. Baba yace
“Ai ban sani ba Doctor, in sha Allah zai je.”
“Yauwa, ai gara haka. Shi kanshi sai ya fi jin dadin jikinshi.”
Nan likita ya yi rubuce rubucensa a takarda yabawa Baba yace
“Wajen kwararru za ku je ga wannan ka bawa coach din don su san irin abubuwan da suka dace da jikinsa.”
Shi dai Abba yana jinsu yana mamaki yanda kiriri Baba ya maida shi kamar wani yaro. Sai da likitan ya basu
kwatancen gym din da za su je sannan suka fito. Suna tafiya a hanya suna hira Baba yace
“Abba ai za kaje gym din ko?”
“Zan je Baba, sai dai muje mu gani idan ba lokacin kasuwa bane in sha zan je.”
Da yake wajen hanyar gida ne sai suka tsaya don su gani. Coach yayi musu bayani sosai kuma ya
shawarcesu da Abba ya dinga zuwa kullum karfe 5:30pm.
“Alhaji ka san motsa jiki ya fi tasiri idan kullum za kayi kadan a kan ace za ka dinga yi kana fashi. Nan da
nan za ka ji dadin jikinka.”
Kafin Abban yayi magana Baba yace
“Sai kawai ka dinga tasowa daga kasuwa kana hutowa nan, kana gamawa sai kahuce gida.”
“Toh Allah ya bani iko?”
Aka yi musu lissafi Abba ya zaro ATM card ya mika, Baba karami ya karbe ya bayarda nasa katin yana fadin
“Abba next time ka biya.”
Kafin su tafi sai da Baba ya karbi lambar coach din. Da yake annual leave ya dauko sai da yayi sati biyu da
kanshi yake zuwa kasuwa ya taho da Abban ya kaishi gym din har ya saba kafin ya koma.
Wannan zuwa gym din da Abba yake yi ya sa yana dawowa gida da wuri don haka duk lokacin da Saudah
take da lecture din yamma a kan idonshi take dawowa. Da yake su Nawwara yanzu a makarantar bokonsu
suke islamiyya sai biyar suma suke tashi don hak duk tare take daukosu su huce gida. Yanda take shigowa
da su Hanan kaca-kaca yana bata masa rai don wadanda suka wuni a makarantar ma sun fi su kyan gani.
Kullum haka za ta tarar da su in taje daukarsu kamar da kayan jikinsu aka goge gidan ga fuska duk a bushe
da majina, haka kuma yana kallo za ta zauna basu abinci suna ci kamar wadanda suka wuni basu ci ba. Yau
ma haka ta shigo da su kaca-kaca ta same shi a falonta tana karatun jarida; da yake itace da girki. Bayan
ya amsa sallamarta yace
“Wai matar da kike kaiwa yaran nan wace irin kazama ce ne? Yanzu dubi fuskar yaran nan fa wata majina
da gani tun safe take.”
Da yake itama a gajiye take ba so take ta ja rigima sai ta kwantar da murya tace
“Hmmn, abun ne sai hakuri.”
Daki ta huce da su nan da nan ta yi musu wanka don bata son ya sake maganar kazantar nan. Kafin ta
gama yi musu wankan nan har Baffa ya fara kukan yunwa gashi kuma an yaye su sati biyu da suka huce.
Goya shi tayi ta dauko Hanan ta zo ta ajiye ta a wajen Abban ta shiga kichin ta hado musu cerelac. Yanda
yaga suna karbar abincin ya tabbatar da yunwa a jikinsu. Ya dube ta ranshi a bace yace
“Wai ba kya kai musu abinci ne, kullum fa haka kike dawo da su kana kallonsu ka san yunwa suke ji.”
“Ina kaiwa wallahi, kuma tana basu. Watakil dai da yake yau ban dawo da wuri bane.”
“Mtseww! Allah ya sauwake, ya dai kamata kiyi mata magana.”
Suka yi shiru na dan lokaci ya mayar da hankalinshi kan TV. Jim kadan kamar wanda ya tuno da wani abu
ya kalleta yace
“Ni fa shi yasa bana son wannan karatun wallahi, yara duk a wahale. Wadannan su wuni a makaranta
wadannan a kwararo.”
Ta saba jin wannan kalamin nashi kuma bata da amsar bashi domin ba za ta fasa karatun ba tunda yake
ma ta kusan gamawa. Don haka sai ta tashi ta shige kichin ta barshi da yaranshi.
Bayan dare ya yi ne ya shiga wajen Mommy don yayi mata sallama kamar yanda ya saba. A falo ya sameta
ita da Khalifa da Auta suna hira, ita da Khalifa suna ta yiwa Auta dariya shi kuma yana ta zumbura baki.
Bayan ya zauna yace Khalifa wai me kayiwa danjar Mommy ne naga yana neman fashewa.
“Abba babu abinda na yi masa fa, sai wani lissafi yake yiwa Mommy na abubuwan da zata yi da bikinsa
shine nace ya bari ma a sami matar don sai na dage kafin na sami wadda za ta iya zama da shi saboda
rigimarshi da sangarta shine yake ta wani zumbura baki.”
Shima Abban sai da yayi dariya sannan yace
“Toh kai a su wa da za ka nemo masa mata? Ai uwanininshi ce za ta samo mishi wadda ta dace da shi,
wannan aikin ai sai ita.”
Khalifa ya kara tuntsirewa da dariya shi da Abban. Mommy tace
“Toh ya ishe ku haka, rabu da su ka ji auta. Matar ma sai sun biya kudi sannan su ganta in ba suyi wasa
ba.”
Haka suka yi ta hirarrakinsu har yaran suka tashi suka tafi suka kwanta. Ya mayar da hankalinshi kan
Mommy yace
“Matar da ake kaiwa su Hanan gaskiya bata kula da su.”
Tace
“Allah sarki toh ai sai Umman nasu tayi mata magana, tunda ai biyanta take yi.”
“Ita din ma da kyar fa aka sameta balle ayi tunanin canza gida.”
“Hakane, magana dai za ta yi mata tunda biyanta take yi sai kaga ta gyara.”
Ya dan yi shiru yana duba wayarsa. Ya dago ya dube ta yace
“Da ina son nace ta dinga barinsu a nan…”
Kafin ya karasa ta datsi numfashinsa tace
“Nan wajen wa? Rainon nawa yaran ma da ‘dai ‘dai fa nayi shi ina zan iya da biyu.”
“Ai ba dadewa take a makarantar ba na ‘dan lokaci ne, gashi ma ta kusa gama karatun gaba daya.”
“Toh su karasa a haka ko ta canza gidan raino.”
Yanda ta yi kicin-kicin ta bata rai ya tabbatar masa ba za ta saurareshi a yi wannan zancen ba don haka ya
tashi ya fice ya bata waje. Bayan ya fice ta ce
“Dan yana cikinta ma ya mutu an ce ni na kashe balle wadannan, ko sauro ne ya cije su cewa za a yi nice.
Allah ya tsari gatari da saran shuri.”
Can ma wajen Saudan da ya koma mitar dai ya ci gaba. Ta dube shi tace
“Toh ko Umma zan yi wa magana in ya so ko a can kauyensu sai ta samo min wata a danginsu ta dinga
zama da su a nan naje na dawo.”
“A’ah. Ba sai an yi haka ba zan dai sake dubawa.”
Tun lokacin da ya kama su Kaka suna bata kayan tsafe tsafe yake tsoron ganin ‘yan uwanta a gidan, balle
a ce wata a danginsu ta zo tayi masa zama na dindindin. Ta Dade tana ce mishi a kawo mata daga garin su
Umman yana ki kuma har yanzu ba ya jin zai iya nutsuwa da su.
Karfe 5:00pm ya fito daga kasuwa don tafiya gym. Sai da ya zauna ya tayar da motar sanan ya ga lokaci
yayi tunanin yana da dan lokaci don haka ya yanke shawarar zai tsaya a IBB way wajen abokinsa Alhaji
Fatihu. Abokin sa ne na kusa don duk wata harkar kasuwanci tare suke yinta, wani lokacin ma tare suke
tafiya China ko Dubai su yo order. Bayan sun gaggaisa suka shiga hirarrakinsu na duniya har dai suka
gangaro kan iyali. Alhaji Fatihu yace
“Ya amarya kuwa?”
“Tana nan lafiya wallahi.”
“Toh ma Sha Allah, ina Uwargida sarautar mata? Ya kamata na zo na kwashi gaisuwa fa.”
Sukayi dariya suka tafa, suka cigaba da hira. Nan yake gaya masa matsalarshi daya da Rabi bata tausayin
Saudah da ‘yayanta. Yace
“Ban gane bata tausayinta ba.”
Sai da yayi tsaki sannan ya bashi amsa
“Kwata kwata ba ta raga mata. Ka ga ita Saudah tana degree a nan BUK amma Rabi baza ta rike mata yaran
ta je ta dawo ba, ga wadanda aka saka a makaranta babu Mai daukosu Amma ita baza ta dauko su ba. Har
cewa nayi Bala ya dauko su in ya so ya kai su wajen Rabin kafin uwarsu ta dawo amma matar nan kiri-kiri
Taki amincewa.”
Mamaki ya cika Alhaji Fatihu yace
“Tana gidanka a matsayin matarka Amma baza ta rike maka ‘yaya ba? Ai ko kare ka kawo gidanka ya
kamata ta rike maka shi balle yaran da aka haifa maka.”
“Wallahi ba dai Rabi ba, don a kan rike yaran nan ba yanda banyi da ita ba. Tun Ina lallabata har fada muka
yi amma tace ita ta gama raino, wai indai sun iya kula da kansu toh su zo tunda gidan ubansu me amma
wanda sai ta yi musu komai ita bazata iya ba.”
Alhaji Fatihu ya gyara zama yace
“Amma gaskiya Rabi ta ban mamaki, ta bata wayonta. Ko da yake kai ka bata dama, ni ga shi nan su uku a
gidana duk inda za su wadda take gidan kawai za a barwa yaran ko kwana nawa za ayi kuwa. Kuma Hafsan
da take Babba itace kusan kullum tana gida don haka nan wajenta suke zama.”
“Toh ka godewa Allah kawai.”
“Toh ai ni ba zabi na basu ba, doka tace dole a bita don wallahi mace sai dai ta bar gidan nan a kan yaran
nan tunda su gidan ubansu ne. Ai in dai kana auren mace dolenta ne ta kula maka da yara ko ba ita ta haifa
ba.”
Haka dai yayi ta nusar da Abba yanda yayi sanyi da yawa har matanshi basa jin maganarshi. Daga karshe
suka yi sallama Abban ya huce gym yana ta tunani domin har yanzu baya son yanda ake jai masa yara wani
kazamin gida.
EPISODE 15
Tun da aka kafe timetable din jarrabawa hankalin Saudah ya tashi. Sha daya ga watan azumi za su fara
jarrabawa, ko babu azumi jarabawa tana bata tsoro balle ga azumi ga hidimar gida. Duk da tana saka rai
Abba zai dinga cin abinci shi kadai a gida saboda diabetes dinshi amma jarrabawar tana bata tsoro. Ita a
hakan ma tana ga kamar gara abincin kasuwar da na wanna diabetes din da kake rasa me za ka dafa ga
Abban shi ma da taurin kanshi. Duk inda take jin za ta sami mai aiki a unguwar nan ta sa an duba mata
Amma bata samu ba, gashi kuma yace mata bai yarda da me kwana ba. Karin tashin hankalinta kuma
yanda taga karatun nata yana baya baya saboda duk an yi CA test bata ci abun kirki ba saboda bata samun
lokaci tayi karatu. Gashi tana son a zo a tayata daga gidansu amma duk ya hana, da yaga ‘yan gidansu zai
fara tambayar yaushe za su tafi dama tuni ya hana Yaya Ummu zuwa.
Tun bayan da Ahmad ya gama bautar kasa ya raba takardunshi na neman aiki gashi yanzu har kusan wata
shida amma shiru. Akwai wanda ma Abban ya hadasu a banki kuma yayi alkawarin samar masa aiki amma
har yanzu shiru. Sai da ya rage saura sati daya azumi katsam sai mutumin na ya kira Ahmad. Yana zuwa
bankinsu ya sa aka yi masa interview ya ce ya dawo gobe. Tun dare yayiwa Abba waya yace Ahmad yaci
interview din don haka gobe zai fara aiki. Nan da nan aka kama murna da farin ciki. Saura kwana uku azumi
Baba karami ya zo hutun karshen mako, a inda ya sanarwa Abba Baban Khairiyya ya ce bayan Sallah su Kai
kudin aure. Abban ya dubi Baba yana murmushi yace
“Iyye, ai sai na fara kiranka ango kawai.”
Ya shafa kanshi yana dariya.
“Toh a ina za ka ajiye amaryar ne Babana?”
“Abba gidajen Abujan nan sun yi tsada bazan iya dasu ba, amma kafin Sallah zan sa a duba min a Kano in
na samu gida wanda zan iya sai na siya, musamman a nan kusa.”
“Ka yi dabara, Amma ai gara ace matarka na kusa da kai ko musamman da yake ita gidansu yana Abujan.”
Ya shafa kai yace
“Hakane Abba, amma sai dai ko daga baya don itama na gaya mata a Kano za mu zauna kuma ta yardyac
“Toh shikenan, nima din zan duba kafin sallar naga abinda zan iya yi in sha Allah.”
Ranar da Baba zai koma Abujan a falon Saudah ya sami Abba don sallama, bayan sun gama sallamar Abba
yace
“In ka je Abujan ka nemi Barrister, yanda kukayi na ji.”
“Toh Abba in sha Allah.”
Sukayi sallama Baba ya kama hanya. Bai kawo komai ba saboda ya saba karbowa Abban sako a wajen
Barrister ko kuma ya bashi takardu yace ya sa hannu a madadin Abban shi yasa ma bai tambayi bayani ba
da aka ce yaje wajen Barrister. Wajen sha daya na safe jirginsu ya sauka a Abuja, da yake gidan barrister
ya fi kusa da airport sai yayi masa waya suka hadu. Bayan barisster ya fito suka gaisa ya dubi Baba yace
“Toh za mu iya fita yanzu kuwa na ganka da kaya kamar yanzu ka shigo garin.”
“Eh, ai na zata sako za a karbar masa shi ya sa na tsaya da yake wajen da nake da nisa daga na.”
Barrister yace
“Bai gaya maka ba kenan. Cewa yayi mu je Suleja da Maitama ka duba a gidajenshi wanda yayi maka a
bawa ‘yan haya notice su tashi karshen shekara a gyara a canza takardu su koma naka don ka kusa aure.”
Zare ido kawai baba yayi yana kallon barrister, da kyar sami harshensa yace
“Wallahi bai gaya min ba.”
“Bari in dauko mota kawai muje yanzu don tun kafin ma kazo na ce ba za mu je Suleja ba sai dai Maitama,
Suleja ai karamar unguwa ce ba za a baka gida a can ba ga na Maitama.”
Nan da nan Barrister ya dauko mota suka kama hanya. Baba ya san da gidajen domin tunda ya fara aiki a
Abuja shine a kan harkar kadarorin Abba na Abuja. Gidajen Suleja block ne kowanne block hawa biyu da
gidaje shida, na Maitama kuwa flats ne guda hudu a jere da juna, kowanne da gate dinsa kuma da daki
uku, falo, kichin, dining area da kuma bandakuna sannan kuma ga filin tsakar gida wanda aka kewaye aka
sa gate. Suna tsayawa Baba yace
“Ai ba ma sai mun shiga ba tunda da mutane, wannan na farkon ya yi min in ya so idan suka tashi na shiga
na gani.”
“Toh shike nan, ka same ni a office duk lokacin da ka sami dama sai ka sa hannu a takardu shi kuma Alhaji
in ka je Kano sai ya sa hannu ka dawo min da su don alkali yayi stamp.”
“Toh in sha Allah ranar Talata zan zo.”
Suka juya Barrister ya kai shi masaukinsa sannan ya huce. Yana shiga gidan karfe uku
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good