Showing 165001 words to 168000 words out of 196754 words
Chapter 56 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
dole ta
lallabashi ya zo ayi auren nan tun kafin kowa yayi aure ya barta. A hankali kuma tunaninta ya karkata kan
Ummanta, ta fara tunanin Ummanta ce ta janyo mata wannan sawarwarar. Haka kawai tana zamanta a
Bichi ta daukota a kan dole sai ta auri Baba karami. Ko da yake kuma ga shi tayi karatunta ba tare da
matsala ba, ana gama wannan semester din ta gama ta sami degree.
…………
Yana jin kunyar Alhaji Usman kuma ya san kasuwancin da yake takama da shi idan Alhajin ya so zai iya
karya shi baras ya tashi ba uwar kudi babu riba. Alhaji Usaman yana daya daga cikin mutanen da suka
nuna masa kasuwa har yake cin ribarta, shi ya sa ma ba tare da wata fargaba ba ya shiga neman auren
nan. Da ace a wani wajen yake neman auren da tabbas sai dai kawai su nemeshi su rasa, amma ba zai iya
yiwa Alhaji Usman haka ba. Ko babu komai yana so ya cigaba da daga masa kafa a kasuwa. Haka kawai
ya ji ya fasa auren, gaba daya ma Zulaihan ta fice masa a rai don ko son ganinta ma baya yi. Yanzu
mutum daya yake so a duniya kuma a kan umarninta ne ya fasa auren nan; wato uwargidansa uwar
yaransa. Babu yanda ya iya dole ya samu abokinsa Hadi ya sanar dashi. Shima Hadin fada yayi tayi yana
tambayarsa toh da me yasa zai je yace yana sonta. Babu yanda bai yi da Hadi a kan yaje yace wa Alhaji
Usman ya fasa auren Zulaiha ba amma sam yace shi ba zai je ba.
“Babu yanda za ayi na ciji hannun da yake bani abinci, haka kawai ka sa ya rage kayan da yake bani. Sai
dai kai kaje ka fada tunda yanzu ta gidan ta shanyeka ta hanaka auren.”
Haka suka rabu baran baran. Ba zai iya gayawa Madu ba don ya san ko Alhaji ya so ya raga masa in ya
biyo ta hannun Madu toh an yanke harkar arziki da shi. Don haka ya sami Lalo ya tsara shi yace ya sanar
da Alhaji, yace masa amma don Allah kar ya fada a gaban Madu. Don haka ya sami Alhaji shi kadai ya
sanar da shi Muntari ya ce ya fasa auren Zulaiha amma don Allah ayi masa afuwa babu yanda zai yi ne.
Sosai Abban ya ji haushi, ransa yayi matukar baci. Lalo yana fadan sakon ya bar wajen don haka Abban
ya dubi Sani wanda yake zaune a kusa dashi yace
“Lallai Muntari wuyansa ya isa yanka. Shi da kanshi ya ga yarinyar nan ya ce yana so amma don iskanci
bayan ya bata mana lokaci ya zo yanzu yace ya fasa.”
“Alhaji ai sai hakuri.”
“Toh idan wata matsalar ya shiga ya fada Mana duk ai yiwa kaine sai a duba a ga yanda za a taimaka
masa.”
Bashari da bai sa musu baki ba wanda shima abokin kasuwancin Muntarin ne yace
“Alhaji babu wata matsala fa, ta gidan ce ta murza kambunta. Yanzu maganarta kawai yake ji don duk
abinda tace yayi jiki na rawa yake yi. Auren ma ita ta hanashi, dama kuma tun farko ta gaya masa bai isa
yayi mata kishiya ba ya zata wasa takeyi sai yanzu ta tabbatar masa malaminta yafi nasa aikyac
Mamaki ya kama Abba
“Ikon Allah, toh Allah ya sauwake. Idan haka ne ma sai muce gara ma da ba ayi auren ba na bashi ‘yata
su je su mayar da ita baiwa shi da matarsa.”
Har aka tashi daga kasuwa Abban yana cikin damuwa, don shi gani ma yake shi Muntari yayiwa
wulakanci.
Tunda aka fara maganar neman auren Zulaiha bai yi magana da Sa’a ba da mahaifinta yake magana,
kuma yanzun ma dole ya sanar dashi halin da ake ciki. Fatanshi dai Allah ya sa haka ne mafi alkhairi
kuma Allah ya bawa Zulaiha miji na gari. Saida yayi ta maza sannan ya iya kiran mahaifin nata ya sanar da
shi halin da ake ciki, yayi masa nasiha sosai ya nuna masa ba wani abu bane a dai cigaba da addu’a Allah
ya fito mata da miji na gari. Ya kara bashi hakuri sosai kuma yace itama Zulaihan ya bata hakuri. Sai da
suka gama waya sannan ya kirawo Atiku ya sanar da shi suka kara jajantawa yace masa shi ma ya bawa
Sa’a hakuri da Baffan Zulaihan.
Mahaifin Zulaihan kuwa yana gama waya da Abba ya shiga ya sanar da Sa’a halin da ake ciki, Abban ya
riga ya bashi hakuri kuma yana ganin girmasa don haka ko zai ce wani abu sai daga baya. Tunda dai
yanzu Zulaiha bata gidansa toh komai ma ya zo da sauki.
Lokacin da aka yi wannan maganar lokaci ne da Sa’a bata bukatar Karin tashin hankali saboda tana ta
fafutukar yanda zata yi ta rusa maganar auren su Baba, don a fadarta in dai ba a aura a danginsu ba sai
dai a auro bare. Yanzu kuma gashi an gaya mata maganar da ta rusa duk wani farin ciki nata. Wai me
yasa ma Yaya yake yi mata haka, ba zai kirawo ta ya gaya mata wannan maganar ba sai ya gayawa Baffan
Zulaihan. Yanzu ta san fitar nan da yayi tafiya zai yi ya gayawa ‘yan uwansa su kuma sun sami abun yiwa
dariya. Saboda tsabar bakin ciki ranar da matsanancin ciwon kai ta kwana, don hatta sabon gidan da
Muntari ya kai Zulaiha sai da ta dauko hotunan ta turowa Umman ita kuma ta turawa kawayenta suka
gani. Tabbas za ta sha kunya idan maganar fasa auren nan ta fito.
A zaune take a falo ita kadai ta kunna tashar NTA hausa tana kallo ta jiyo muryar Maman Farida suna
gaisawa da da Malam Bala. Kafin ta gama mamakin taji sallamarta a bakin kofa, ta mike ta bude kofar
tana amsa sallamar. Ta shigo suka karasa tare suka zauna
“Rakiyar kura za muyi kenan ko me zance, dazu fa na shigo.”
“Wallahi daga wajen biki nake ko gidan ma ban shiga ba.”
“Ga alama nan, bikin wa kuke yi.”
“Bana jin zaki san su, can baya ne layin masallaci. Nima ba a nan unguwar na sansu ba uwar amaryar ce
tare muka taso da ita.”
“Allah sarki, Allah ya sanya alkhairi.”
Ta mike tana fadin
“Bari na kawo miki ruwa yanzu haka a kas kika je har layin masallacin.”
Ta dafe hannunta
“Ai bar ruwan nan.”
Ta dawo ta zauna tana mamaki, kafin tayi magana maman Faridan ta cigaba
“Ni dai bana son abun ya zo kamar na miki gulma amma gaskiya ba zan iya zama ba sai na gaya miki ko
babu komai ki dau mataki.”
Gabanta ya fadi ta dan zaro ido
“Toh!”
Cikin sauri ta katseta
“Kishiyarki wai wace irin yarinya ce ne Abban Khalifa ya auro? Kin san kuwa me taje tana fada a unguwa?
Can a gidan bikin nan fa kalli nisan layin da nan amma acan na jiyo wai ai anji daga gareta yawon bariki
kika tafi da Abban Khalifa ya koreki, wai yanzu halin da ake ciki ma cewa yayi sai kin yi gwajin kanjamau
sannan zai yi rabon kwana dake wai gwajin ne baki yi ba shi ya sa ta bar muku gidanku in kin yi gwajin ya
je ya dawo da ita.”
Ta jijjiga kai kamar me tashi daga bacci ta bi Maman Farida da kallo tace
“Ban gane ba Maman Farida, ki yi min bayani a hankali.”
“Hmn, Saudah ko? Toh ta gama yayatawa a unguwa wai yawon bariki kika tafi yanzu ma ta sa Abban
Khalifa yace sai kin je kin yi gwajin kanjamau zai cigaba da zama dake, in ba haka ba sai dai ya zaba ko ke
ko ita.”
Ta rufe idanuwanta tana jijjiga kai
“Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Wai wannan yarinyar me take so da ni
ne? Zina! Ni za ta yiwa kazafin zina? Ta gama yi min kazafin kisan yaron cikinta yanzu kuma ta nan ta
bullo. A gidan biki?”
“Kwarai kuwa don ni din ma bana jin an san alakar mu da ke aka yi zancen a kusa dani. Tunanin da nake
dai matar da take mata wanke wanke ce; Balaraba ko? To itace ta je musu da zancen don har da ita a
masu yin aikatau din bikin.”
Suka yi shiru na dan lokaci. Takaici ya kama Rabi ta sa hannu ta share kwalla, ta dafa hannun Maman
Farida
“Yau kika ji zancen nan Maman Farida?”
“Eh, yanzu ma kuwa. Sai dai kamar ba yau suka fara maganar ba mai da zancen kawai sukeyi. Kuma
dama tun wajen sati biyu da suka wuce Sala me min kitso ta so ta gaya min wata magana me kama da
wannan ba taga fuska ba ta hadiye zancenta. Ni kuma ban zata abun ya kai haka ba kawai sai na dauka
gulmammaki ne nasu da sai sun yi tunda dai kin fita kin dawo.”
“Uhm, lallai ne.”
Suka sake yin shiru na dan lokaci, Mommy ta nisa tace
“Lallai yarinyar nan tana bukatar na koya mata hankali, tabbas yanzu za ta gane bata da wayo. Da ni take
zancen.”
“Gaskiya dai ya kamata ki dauki mataki a kanta saboda ta wuce gona da iri.”
“Har shi ma Abban Khalifan tunda ai ko babu komai shi ya bata dama, kuma na tabbatar ta gaya masa
wannan maganar shiru yayi min. Ko kuma shine dalili da yasa ta tafi, don kin san da yace min ta tafi nima
ban nemi karin bayani ba kuma ya san bana son hirarta don haka shima bai ce ba.”
Maman Farida ta dan sassauto tace
“Toh amma dai ki bi a hankali, ki saurari abinda Abban zai ce. Tunda ke da gani a zamanku daga
dawowarki zuwa yanzu idan yana zarginki da wani abu kin sani.”
“Wallahi babu wani alamar zargi komai normal, don da na dawo ma kwanana daya ya raba kwanan
muma tare muka kwana. Tun daga ranar kuma babu fashi sai ranakun da ba a nan take ba. Har yanzu ma
wani lallabani yake don ni har abun ya fara bani haushi bana son naga kamar ana tsoro na nafi so normal
kawai yanda nima zan zama normal.”
“Toh kin ga kenan ita ta san kinibibin da ta kulla.”
Suka dan yi jim, mommy ta gyara zama tace
“Toh ko ma shi ya sa ta tafi gidan nasu shi kuma yaki binta?”
“Babu mamaki ta zo masa da zancen ya ki saurararta shi ya sa ta tafi gidan ta zata zai bita da magiya.”
“Hmn, ai kuwa zan yi maganinta da ita da duk wanda ya tsaya mata.”
“Toh gaskiya dai ya kamata don wannan iskancin nata ya fara yawa, ko a addini wannan kazafi biyun da
ta yi miki hukuncinsu mai zafi ne.”
Suka yi sallama Maman Farida ta fita ta bar Mommy ranta gaba daya a bace. Ta rasa me ya sa yarinyar
nan ta damu da rayuwarta, duk yanda zata yi ta bata mata suna shi take so. Tabbas wannan karon ba
zata saurara mata ba da ita da duk wanda ya tsaya mata sai sai sun gane kurensu, idan kuma ma Abban
ne ya tsaya mata zata ji. Haka yara suka sameta ba yanda suka barta ba, suka yi ta faman tambayarta me
ya sameta. A karshe dai da ta gaji sai tacewa Auta kanta ne yake ciwo amma ta sha magani. A haka suka
tayata ta yi abincin dare ta gama tsaf ta jera a table. Daf da Magriba ta shiga daki bayan ta sanar da su
idan ta idar da sallah ba zata fito ba hutawa zata yi. Tayi sallah ta zauna a kan dadduma ta dauki lokaci
tana addu’ointa bayan ta gama ta tashi ta koma kan gadon ta dan mike.
……
Kamar kullum sai bayan isha’I Abba suka dawo daga kasuwa shi da Madu, saboda yau Salim bai je
kasuwa ba yana project defence a makaranta. Har ya gama duk wata hidimarsa bata fito ta je masa
sannu da zuwa kamar yanda ta saba ba, da yake yara sun gaya masa abinda tace sai ya rabu da ita zuwa
jimawa. Yana zama cin abinci ta fito, bayan tayi masa sannu da zuwa ta ja kujerar ta zauna a dining a
table din
“Sannu. Kan yayi sauki kenan?”
“Eh, Alhamdulillah.”
“Toh ma sha Allah, amma dai ya kamata kiyi hakuri gobe ki je ki ga likita. Kinga zazzabin nan sai kwantar
da mutane take yi gara ki je a duba ki sosai.”
Tayi murmushi tace
“Ko yanzu ma kan yayi sauki, amma in dai ya kuma ciwo daga nan zuwa goben sai na je asibitin.”
“Toh Allah ya kara lafiya.”
Suka dan taba hira har ya gama cin abinci.
Sai da suka gama duk abinda za su yi sukayi shirin bacci bayan ya idar da shafa’I da witri ya tashi daga
kan daddumar ya koma kan kujera. Ta matso gefen gado yanda za su fuskanci juna tace
“Abban Khalifa.”
Ya dago daga kallon wayar da yake yi yace
“Na’am.”
“Ashe kunyi magana da Umman Nawwara wai yawon bariki na tafi don haka sai nayi gwajin kanjamau za
kayi rabon kwana da ni?”
A zahiri taga razanar da yayi don saura kadan wayar ta subuce daga hannunsa, ya ajiye wayar a kan
daddumar da ya tashi ya matso da kujerar ya dawo gabanta sosai yace
“Subhanallahi, yanzu yarinyar nan bata ji maganar da na gaya mata ba kenan?”
Ta dago kwayar idonta wadda tayi ja ta dube shi
“Au kaine ka gaya mata kenan?”
“Ya za ayi na gaya mata, kwanan da take magana tun yaushe aka raba kuma wannan ai ke za ki bada
labari.”
Suka dan yi shiru, nan da nan hawaye suka wanke mata fuska. Ya kara matsawa gabanta da kujerar ya
matso gaban kujerar sosai ya kamo hannuwanta da suke ajiye a kan cinyarta
“Rabi.”
Ta dago ta dube shi da idanuwanta da suke cike da hawaye
“Ni ne mijinki ko, toh wannan tafiyar da kika yi ji nake kamar ina tare da ke ne duk ma inda kika je. Ni na
san ke tawa ce ni kadai bana zarginki da komai kuma ba zan taba zarginki ba. Ita ta kirkiri zancenta, ta
gaya min kuma na gaya mata bana zarginki ni na san inda kika je da abinda kika yi a can kuma sannan na
tuna mata girman kazafin zina a musulunci amma bata ji ba. Wanna kam ba da ke take ba da ni take don
sunana take son ta bata.”
Tayi ajiyar zuciya, ya saki hannuwanta ya tallafo fuskarta
“Ki daina kuka, bana son kukan ki ko daya.”
Ta janye fuskarta daga hannuwansa ta sa nata hannun ta share hawayen
“Dole nayi kuka, ta gama bazawa a unguwa cewa yawon bariki na je harma ta baka sharadin sai nayi
gwajin kanjamau sannan zata kwana da kai wai shi yasa ma ta tafi gida in ka sa ni gwajin sanna ta dawo.
Yanzu haka bayan an gama gulmar ta saka ka koreni yanzu kuma an koma ana cewa yawon bariki naje.
Dama ga wancan karon da ta ce na kashe mata yaron ciki.”
Ya jijjiga kansa wanda kawo yanzu sarawa yake yi, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun toh ya zai yi da Saudah
ne. Don yanzu in ya saketa ma gani yake ba zai huce ba, wannan cin zarafi da ta yi masa har ina? Ko shi
ma dole ya dauki mataki a kanta. Ya tura kujerar baya ya zauna a gabanta kamar mai rokon gafara
“Ki bari zan dauki mataki a kanta.”
Ta dago kanta ta kalleshi da idanuwanta masu cike da hawaye tace
“Ka dauki naka matakin nima zan dauki nawa, don wallahi sai na yi kararta. Gobe Ahmad zai samo min
lawyer mu hadu a kotu, wallahi ba zan yarda ba.”
Ya sake kama hannuwanta ya dubi idanuwanta yace
“Hakan yayi, idan kina so ma da kaina zan samo miki lawyer da safe kafin na fita sai kuyi magana da shi.”
Haka suka kwana yana lallashinta yana faman bata hakuri tare da jaddada mata goyon bayansa. In dai
har ta bashi dama zai hada ta da lawyer ne babba kuma shi zai biya komai don ko shi ma ya fi so Saudah
ta girbi abinda ta shuka. Yanda suka yi maganar nan bai taba zaton za ta fitar da ita ba amma ashe wai
har ta baza a unguwa, sai yanzu ya sake yin nadamar korar da yayiwa Rabi kuma ya sake nadamar auren
Saudah. Ita kam Rabi da yake yana ta tarairayarta daga baya bacci ya dauketa, amma shi yanda yaga
dare haka ya ga rana. Sai bayan ya dawo daga masallaci sallar asuba sannan ya samu ya dan yi baccin. Da
yake ‘yan makaranta suna hutu Ahmad bai fita da wuri sosai ba, a zaune Abban ya samesu shi da
mommy a kan dining table. Ta riga ta gama yi masa bayanin abin da ya faru kuma lawyer take so don yau
take so a shigar da kara su hadu a kotu. Shima Ahmad din ranshi yayi matukar baci, nan ya gaya mata
idan ya fita zai tsaya wajen abokinsa wanda lawyer ne don ya sama masa lawyer. Ya karaso ya ja kujera
ya zauna bayan ya amsa gaisuwar Ahmad yace
“Ai na gaya miki ni zan hada ki da lawyer in ya so idan aikinsa bai yi miki ba sai ki nemi wanyac
“Na fi so dai ka bari na nemi wani, ka ga har yanzu ita din matarka ce kuma uwar ‘yayanka ce idan kayi
shari’a da ita baka yiwa yaranka adalci ba kuma ka bar musu abun fada musamman su da suke mata.”
Ya sunkuyar da kansa, tabbas maganarta haka take amma yana so ya koyawa Saudah hankali. Ya dago ya
dubeta domin gaba daya ta goge masa lissafi da maganganunta wadanda a zahiri abinda ta fada gaskiya
ne. Ta dora tafin hannunta a kan hannuwansa da suke dunkule a kan table din tace
“Babu komai ka barni da ita, kada kayi abinda za ku barwa yara abun fada ka bari su ji da wanda ita kadai
ta janyo musu.”
Ya jijjiga kai alamar ya amince, ya dubi Ahmad yace
“Duk wani payment da za ayi ka sami Madu kada ka sake ka biya ko sisi.”
“Toh Abba.”
“Bari na kawo maka abincin.”
Ta mike ta shiga kichin domin ta dauko abincin da bata riga ta jera ba saboda yanda ta tashi ba a yanayi
na walwala ba. Ahmad ya tashi ya bita kicin din ya tayata kawo abincin, bayan sun gama ajiyewa yayi
musu sallama ya fita.
Kafin ya shiga banki sai da yayiwa Baba magana ya sanar da shi halin da ake ciki, inda yace ya bar masa
maganar yanzu zai samo lawyer. Wajen karfe goma Ahmad din ya kirawota ya sanar da ita Baba ya samo
lawyer zai zo ya ganta sannan ya hada lawyer din da Madu yace su je gida ya kaishi wajen Mommy din.
Duk wasu tambayoyi da lawyer din yake da su Mommy ta bashi amsa da duk wasu bayanai da yake
bukata, ya sanar da ita zai so su kara samun hujjoji musamman ta hannun wadanda suka fitar da zance
tayi masa alkawarin za a samu. Yayi mata alkawarin yanzu yana fita zai je ya shigar da kara yanda suka yi
zata ji.
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good