Showing 156001 words to 159000 words out of 196754 words

Chapter 53 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15400

ya tsuguna a gabanta ya leka fuskarta, ta dauke idonta daga kallon
falon ta dubeshi, yayi murmushi yace

“Mommy kin dawo ko?”

Tayi murmushi ta shafa kansa tace

“Na dawo Khalifa.”

Yayi dariya sannan ya zauna nan kusa da kafarta. Ahmad ya shigo da kayan ya wuce ya kai dakin sannan
ya fito suka sake fita shi da Khalifa suka kwaso sauran kayan. Bayan sun gama zuba mata kayan a daki
suka dawo suka zauna a falon. Ta dubi Ahmad tace

“Falon yayi kyau, kai da Baba ne kuka gyara ko?”

“A’a Mommy Abba ne ya kawo kujerun da carpet sauran ne muka yi shi kuma Salim ya sa wall paper.”

“Ma sha Allah, yayi kyau sosai Allah yayi muku albarka.”

“Amin.” Suka amsa gaba dayansu

Ta mike tana fadin

“Kada ku gayawa kowa na dawo idan sun dawo sa ganni.”

“Mommy har Yaya Baba? Yanzu fa ya tafi airport zai wuce Abuja.”

Auta ya tamabaya.

“Toh ka barshi ya sauka tukunna sai ka gaya masa.”

Ta shige dakinta ta turo kofa. Nan ma fes ta ganshi an saka sababbin labulayen da zanin gadon, ga dan
karamin kafet din ma an canza shi an saka wanda ya shiga da sabbin labulayen. Ta karasa gaban mudubi
ta ajiye jakarta a kan mudubin, ta kalli fuskarta a mudubin tayi murmushi.

Har cikin zuciyarta ta ji dadin dawowarta, nan ta saba nan gidan da take rayuwa da mutanen da take so.
Idan ba dole ba waye yake son rabuwa da masoyi, sai dai ita ta san wannan ‘yar rabuwar da suka yi ta
bude mata alkairai masu yawa. Yanzu ne take jin ta fahimci wacece ita da kuma me take so, tabbas
yanzu ta san ta wuce a nadeta a bai bai a cuce ta kamar yanda itama bata fatan ta cuci wani. Har ta
zauna a gefen gadon tana shirin kashingida sai kuma ta tuna ta dade bata yi girki ba don haka ta fito don
ta ga me zata dafawa yaran suci abincin dare. Tana fitowa ta samesu a falo tace

“Khalifa ku zo muje kicin na gani menene daku a gidan na dafa mana abincin dare.”

Ahmad yace

“Ai Mommy Khalifa ne yake mana abincin dare, da kin barshi da anyi sallar magriba zai dora.”

Khalifa yace

“Eh Mommy, ki bari gobe kya yi.”

Tayi dariya tana fadin
“Ni zanyi, kunsan rabo na da girki kuwa?”

Ta wuce kicin din suka bita a baya. Ta dan karewa kicin din kallo a takaice, ta juyo ta dubi Khalifa tace

“Ya naga kayan abinci da yawa a kicin din, ba kwa barinsu a store ne.”

Auta yace

“Ai Abba ya sa an bawa Umman su Nawwara mukullinki na store, shine idan muka siyo namu kayan
baincin sai mu ajiye a nan.”

“Uhm.”

Ta karasa cikin kitchen din ta dudduba a hankali. Ta samo couscous sannan kuma ta sami kayan miya a
fridge da kaji, ta dubi Ahmad dake tsaye a bakin kofa tace

“Ka siyo mana cabbage, carrot da green beans a bakin titi ka hado da lemon bawo.”

Ya amsa ya juya ya fita. Nan da nan ita da su Khalifa suka hau dora abinci, suka dora couscous da miyar
cabbage da kuma zobo. Zuwa magriba abinci ya sauka, ta zuba a flask suka jera a kan dining table ga
zobo wanda aka hada da lemon bawo ta juye a jug ta jefe kankara aka jera dinga table. Ahmad da su
Auta sai walwala suke yi suna kallon abincin nan don tunda Mommy ta tafi rabon da su sake jera abinci
haka a table. Suka fice suka tafi masallaci itama ta shige daki don yin Sallah.

Sai da aka kusa sallar isha’I sannan Abba suka dawo shi da Madu da Salim. Bayan su Khalifa sun gama yi
masa oyoyo ya wuce wajen Saudah don bai san da dawowar Mommy ba. Su kuma su Madu suka nufi
falon Mommy, shine a gaba yana shigowa ya dan tsaya daga bakin kofa ya kalli dining table ya kalli
Ahmad da yake kwance a kan kujera yace

“Mommy ta dawo?”

Ya sha kunu yana so yace masa a’a dariya ta kwace masa

“Fyiiiitt, wallahi ta dawo.”

Suka fashe da dariya Salim ya karaso ya ajiye ledar burodin da ya shigo da ita a kana table din, da gudu
ya wuce dakin Mommy duk da sun saba sai sun buga tace a shigo suke shiga amma yau ya manta sai
ganinshi yayi a tsakiyar dakin. Tana zaune a kan dadduma tunda ta idar da sallah, nan ya tsuguna a
gabanta yace

“Mommy sannu da zuwa.”

“Yauwa Salim sannunku da zuwa.”

Nan Madu ya shigo ya samesu ya tsuguna shima yana gaisheta, Salim ya dubeshi yace

“Mommy kada ki kulashi, shine yake addua kada ki dawo.”

Ya dungureshi yace

“Mommy da ne da naga kamar an rainaki amma yanzu ai an yi one one, kowa ya san matsayin kowa gara
da kika dawo.”
Ta kai masa duka ya goce.

……………

Yanda ya barta haka ya sameta, kuma dama ya saba in tana fushi dashi bata zama a falo don haka tana
daki ya shiga, bai ko bi ta kan inda take ba ya wuce dakinsa. Sai da yayi sallar isha’I ya canza kaya ya fito
ya zauna cin abinci, macaroni da miya ta dafa don haka kadan ya dan taba ya kara da ayaba guda biyu.
Sai da ya gama cin abincin sannan ya tashi ya dawo gaban TV ya kunna BBC. Yana nan zaune shi kadai
yana kallo har wajen karfe tara, ya tashi ya fita don yaje ya dubk su Auta kafin ya kwanta.

Tun kafin ya shiga falon yake jiyo hayaniyarsu yana mamaki, ya tura kofar ya shiga da sallama. Duka suna
zaune a kan dining table suna cin abinci sunata hira, sai da yayi gyaran murya sannan suka kula da shi
suka yi masa sannu da zuwa.

“Yau party kuke yi ne nake jiyo santinku har waje.”

Suka yi dariya

“Couscous muke ci Abba.”

Da ya san couscous suka dafa ai da nan zai zo yaci abincinsa, amma aka saka shi cin macaroni bisa dole.

Ya dubi Salim yace

“Idan akwai zobon da baku saka suga ba sam min na sha.”

Khalifa ne ya tashi ya debo masa zobo a fridge sai ya kara orange juice a kai ya zubo a kofi ya kawo masa.
Ya zauna a nan falon ya kurbi zobon, ya rufe idonsa yayinda da ya hadiye makwarwar farko. Da ba dan
kada yara suyi masa dariya ba da sai yace Rabi ce ta hada wannan zobon don ita kadai take hada zobo
irin wannan. Ya kurba ya sake kurba, yana cikin wannan santin zobon yaji auta yace

“Abba Mommy fa ta dawo tana daki.”

Sai da ya dan yi kokawa da nutsuwarsa kada yara suyi masa dariya yace

“Allah Yusufa.”

Kafin su amsashi ya tashi ya wuce dakin nata. Tana zaune a gefen gado tana fitar da kayanta daga
akwati, ya tura kofar ya shiga da sallama. Bayan ta amsa sallamarshi tace

“Sannu da zuwa.”

“Yauwa Rabi, ke zan yiwa sannu da zuwa ai.”

Ya karasa ya zauna a gefen gadon gaban kayan da take ajiyewa.

“Shine baki gaya min za ki dawo ba ai da na zo na dauko ki.”

“Toh ai dama na ce zan dawo.”

“Kwarai kuwa Alhamdulillah, kin cika alkawari kuma na ji dadi sosai.”

Ya zauna yana kare mata kallo har kallon ya fara damunta. Can yace
“Bari naje na rufo gidan na dawo.”

Ya fara kokarin mikewa ta dafa hannunsa ya koma ya zauna, tace

“Ahmad dai ya rufe mana kofa, kayi zamanka a can kawai ka ga fa ina jin bata ma san na dawo ba. Nan
din kuma ka ga duk kayan wardrobe din nan ma sai na saukesu na gyara ga yara sun kasa sun tsare, ka
kwana a can sai gobe a sake raba kwanan.”

Ya kura mata ido, tabbas maganarta tana kan hanya. Sai yanzu ma ya tuna da Saudah tabbas da ta san
da dawowar Rabi dole sai tace wani abu. Yace

“Hakane kam.”

Ya sake gyara zama, ya cigaba da binta da kallo tana aikinta sun hira. Sai da goman dare ta wuce sannan
ya tashi yayi mata sallama ba don ya so ba ya fice. Har yanzu tana daki, yanda yaji shiru ma yayi tunanin
bacci sukeyi. Yana son ya sanar da ita dawowar Rabi don gobe za su fara rabon kwana don haka sai ya
wuce ya bude kofar dakin a hankali ya leka. Ta juyo ta dubeshi tana zaune a kan dadduma, yace

“Idan kin idar da sallar kizo ina kiranki.”

Kafin ta amsa ya koma ya ja mata kofar. Har ya gama shirinsa ya kwanta bata shigo ba don haka ya yi
zaton ko bacci ya kwashe ta, yana kwance a kan gadon yana ta faman juyi. Ya so kwarai ace a dakin
Rabin zai kwana domin yayi kewarta fiye da yanda yake tsammani. Ko yanzu ma da ba don yana tsoron
abinda Saudah zata yi ba da tunda bata zo ba wajen Rabin zai tafi, amma baya so ya tafi don saboda
kada ta bata masa yanayin da yake jin kansa na walwala. Don haka ya hakura, ya gyara kwanciyarsa ya
kashe fitilar. Sai da bacci ya fara daukansa sannan ta turo kofa ta shigo dakin, a tunaninta yana bukatar
tane shi yasa ta zauna ta gama bata masa lokaci kuma ta shirya kalar jan ran da zata yi masa don a yanda
ta kudirce kafin ta amince masa sai yayi mata alkawarin kujerun nan ko wasu kudi masu tsoka. Ta
kwanta a kusa da shi ta ja abun rufar da ya rufa ta dan rufe kafafunta da shi. Ya kai hannunsa ya kunna
fitilar saman gadon wadda makunninta yake kasa kusa da durowar gadon sannan ya tashi zaune. Ya yi
gyaran murya yace

“Ai na zata bacci ya kwashe ki.”

Ta yatsina fuska a yangace tace

“Um um, kintsawa nayi na gama abinda nakeyi kafin na fito.”

“Uhm.”

Suka dan yi shiru tana daga kwance tana jira taga ta inda zai fara, ya fuskanci jiran abinda zai ce take don
haka yace

“Kin san Rabi ta dawo ko.”

Ta kau da kai don bata san me yasa yake mata zancen wannan matar a wannan lokacin ba

“Um, ai ka gaya min.”

“A’a ina nufin ta dawo gidan nan fa, tana dakinta don yau ma ita tayiwa yara abincin dare.”
Ji tayi kamar ya buga mata guduma saboda takaici, da kyar ta rike guntuwar nutsuwarta daga inda take
kwance ta tabe baki tace

“Uhm, ai ban sani ba tunda babu wanda ya gaya min.”

“Toh yanzu na gaya miki, in ya so gobe in sha Allahu sai a fara raba kwana da rana sai ta karbi girki.”

Sai da ta hadiye malolon bakin cikin da ya tokare mata makogoro sannan tace

“Um, Allah ya jai mu.”

“Amin amin.”

Ya kwanta ya bata baya ya gyara rufarsa. Ta bi bayansa da harara, wato tana zaune a gidan amma bata
isa a gaya mata za a dawo ba sai dare yayi sannan yana wani gaya mata gobe za ta karbi kwana, shi
abinda ma ya dame shi kenan. Tabbas yau ta tabbatar mutumin nan ya raina ta kuma a banza yake
kallonta, wato saboda matarsa ta dawo ne yake ta wannan rawar kan sekace wanda yayi wata sabuwar
amarya. Minsharinsa ne ya katse mata tunanin ta bi shi da harara, wato ita abinda ma yasa ya kirawota
kenan don ya gaya mata gobe da tsohuwar matarsa zai kwana. Shekaran jiya ya gaya mata bakaken
maganganu har da gorin kujeru yanzu ta zata kiranta yayi ayi sulhu amma ya juya mata baya yana
minshari, lallai gobe za ayi rigima don ba zata dauki wannan rainin hankalin ba. Tashi tayi ta fice daga
dakin saboda yanda minsharinsa ya fara cika mata kwakwalwa yana hanata tunani, tana sane ta buga
kofar don ta tasheshi aikuwa sai da ya farka yaga fitarta. Haka ta koma dakin ta kwanta har asuba tana
juyi tana tunanin ta inda za ta bullowa wannan rainin hankalin da yazo mata da shi, don ba za ta dauka
ba.
EPISODE 34



Karfe takwas take da lecture ranar litinin din ga yara za su je makaranta, da kyar ta tashi saboda yanda ta
hana kanta bacci ta kwana da bacin rai. Haka ta tashi ta hada abincin safe ta shirya yara zuwa
makaranta, itama ta shirya. A daki ta same shi ya fito daga wanka ta gaisheshi a tsaitsaye ta sanar masa
ita da yara sun shirya; da yake idan tana da lecture 8am tare yake fita da su ya ajiyeta a gidansu ita da su
Hanan daga nan sai ta wuce tata makarantar. Har ya fara sauri ya shirya sai kuma zuciyarsa ta raya masa
abinda ya dade bai yi ba, ya dauki wayarsa ya kirawo Salim yace ya karbo mukullin mota a wajen Madu
yazo ya aikeshi. Tana falon ya kwankwasa ta bude ta kalleshi ba tare da tace komai ba

“Kice masa gani.”

Ta mayar da kofar ta rufe ba tare da tace komai, da dai ace wani abu yazo nema da baza ta kirawo masa
Abban ba amma da yake itama Abban take jira sai ta wuce dakin. Bayan ya amsa sallamarta tace

“Kada fa yara su makara ga Salim ma yana jiranka.”

Ya biyo bayanta suka fito sai da suka zo falo yace

“Ku fito Salim ne zai kaiku.”

Bai saurareta ba balle tayi wani korafi ya fice, don haka ta hado kan yaran ta dauko jakarta suka fice. Ya
fito ya sanar da Salim din ya kai yara sannan ya ajiyeta a gidansu. Duk da ba ya son kaita amma babu
yanda zai yi don basu iya rashin ‘da’a ba, don haka ta zuba yaran a gaban mota ta hau ya ja suka fice.

Karfe goma suka gama lecture din kuma babu abinda za su sake yi don haka kamar yanda ta saba sai ta
wuce gidan Ummansu don ta jira lokacin dauko su Nawwara. Tana shiga gidan bayan sun gaisa da su
Umman da kaka, kakan ta dubeta tace

“Ya maganar mu?”

Ta kauda kai tace

“Yanzu zan tura yaro ya kirawo min Kamilu ya zo ya karbi wayar nan, ya ce in ya karba yanzu kafin la’asar
zai kawo min kudin sai na bayar.”

“Toh gara dai don gaskiya mutumin nan ba zai raga mana ba idan kudin nan basu fito kafin wa’adin da ya
diba ba.”

Tana nan aka kirawo matashin yaron Kamilu; wanda daman sana’arsa ce sayar da wayoyin da kayan
waya. Ta cire simcard ta yi resetting wayar sannan ta mika masa hade da chaja da earpiece, ya karba ya
duba yace

“Wannan zata iya yin saba’in haka.”

“Kamilu ba haka mukayi da kai ba, tamanin dai ko da biyar ne don Allah ka ga dai wayar nan babu abinda
tayi ga chaja da earpiece dinta ma duk gasu nan.”

“Wallahi Anti hakane kin san yanda kasuwa take, amma wallahi zan miki kokari in sha Allahu duk abinda
ya samu za ki jini zan kirawo ta wayar Ummu sai ki ji.”
“Toh shikenan, ina jiranka don Allah.”

Ya karbi wayar ya fice ya barsu nan zaune. Babu abinda ta iya cewa saboda tsabar takaici, bata so haka
ba tana matukar son iphone dinta. Yanzu da wanne za ta ji, da takaicin aikin bai yiwu ba ita bata mallaki
mijin ba wayarta da ta riga ta mallaka kuma ta rasa. Ranar ko hirar kirki ba ayi da ita a gidan ba saboda
yanda ranta yake suya ga shi kuma Rabin ta dawo gashi har an fara nuna mata iyakarta. Sai can wajen
karfe uku na yamma bayan sun ci abincin rana sannan ta karbi wayar Yaya Ummu ta kirawo shi. Tana yin
sallama ya dauki muryar, bayan ya amsa sallamarta tace

“Da wayar Ummu nake kiranka an sace min tawa wayar a makaranta.”

“Subhanallahi, garin yaya aka sace miki wayar.”

Ta kwararrabe murya kamar me shirin kuka

“Wallahi nima ban sani ba, ni dai kawai tana jakata sai da muka idar da sallah zan fito daga makarantar
na laluba ban ganta ba.”

“Toh shine kike kuka.”

“A’ah.”

“Toh Allah ya tsare, idan na dawo gidan ma ji. Allah ya kiyaye.”

Suka ajiye waya ta mikawa Ummu wayar. Jimawa kadan Ummun ta dube ta tace

“Rabin kuma tana nan a gidan yanzu an cigaba da raba muku kwana da ita.”

Tayi tsaki ta kawar da kai

“Tana nan mana, ni har yanzu ma ban ga kalarta ba. Jiya dai ya sani a gaba yana gaya min wai yau zata
karbi kwanan saboda tsabar rainin hankali.”

“Ai kuwa rainin hankali, mace taje ta gama yawon barikinta ta dawo miki cikin gida ace wani ku cigaba
da rabon kwana kamar komai bai faru ba.”

“Uhm to ya zan yi, ni gaba daya ma haushinsa nake ji don tunda aka ce an ga matar nan yake bude min
shafuka na wulakanci. Kinga ni na tambayeshi kujeru duk da ban nuna masa wadanda nake so ba amma
da ya tashi sai ya kawo mata kujerun tun bata dawo ba ma ni kuma ya zauna yana gaya min wasu
maganganun banza. Ba za ki gane ba gaba daya sai wata rawar kai yake kamar me sabuwar amarya.”

“Ai shikenan kin shiga uku tsohuwar guzuma ta dawo. Allah ya sa kalau take in ba haka ba bayan an
gama dora miki ciwon zuciya kuma a saka miki ciwon sanyi ko uwarsu kanjamau.”

Ta kalleta da mamaki

“Sanyi kuma?”

“Eh mana, yo bariki wasa ne ta gama biye-biyenta ai Allah ne kadai ya san cututtukan ma da ta kwaso
muku, Allah ya sa ma babu kanjamau gashi ana ta rawar kafa za a koma mata ya dangwalo ya dangwala
miki.”

Suka dan yi shiru tana zare ido, jimawa kadan tace
“Babu mamaki tunda kinga sai da akayi wajen wata ba a san inda take ba, bayan an san inda take kuma
aka ce tana Abuja, tana Kaduna, tana Dutse kafin nan aka ce ta dawo Kano. Kinga kuwa komai ma zai iya
faruwa tunda babu inda bata je ba a kasar, haka kawai a cuce ka a banza.”

Ta jijjiga kai

“Ah toh, gara dai ki san abin yi. Don kin ga dai wahalar da na sha farkon lokacin da ya auro min ‘yar
bariki, nayi ta zarya asibiti kullum shan magani daga baya na ya sake ni don bakin wulakanci. Kin san ko
bayan auren ya mutu sai da na wahala kafin wannan sanyin ya fita daga jikina.”

“Uhm.”

Jimawa kadan ana kiran sallar la’asar Kamilu ya dawo da kudin wayar tata an siyar a kan naira dubu
saba’in da biyu. Ranta bai so ba don ta san wayar ta fi haka, haka ta karba don dai kawai babu yanda
zata yi. Ta zuba dubu biyu a jaka ta mikawa Yaya Ummu dubu saba’in tana fadin

“Don Allah Yaya ki mika mata ta sakar mini mara nayi fitsari.”

Ta karba tana dariya tana fadin

“Bari na kai mata na dawo nima don Allah ki bani dari biyar na sa kati.”

Ta fice ta barta tana takaici. Jimawa kadan suka yi sallar la’asar ta taso ta

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login