Showing 3001 words to 6000 words out of 196754 words
Chapter 2 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
shekararta 19, shi kanshi ya bata shekaru uku, sa’ar kaninshi ce.
Ta san kishiya ba ta dame ta ba amma gaskiya ba za tayi sharing miji kuma tayi sharing kichin da falo ba.
Nan da nan ta fara tunanin yanda za ta yi idan ya sake ta, domin ta gano kura, rigima za ayi sosai ita kuma
ba gudu babu ja da baya. Ko babu komai ya za ayi a ce kana da wadannan balagaggun samarin a gida kuma
ka saka amarya a kusa da dakinsu ka shiga rawar kai ka ce za a zauna lafiya. Ba zai yiwu ba, dole ta san
abun yi kafin ya dawo.
Har bayan azahar tana ta tufka da warwara.
Daga karshe dai ta yanke shawara za ta je gidan kanin mahaifinshi wanda suke kira Baffa Hassan ta gaya
masa.
Shi Baffa Hassan baffanshi ne wanda yake kallo a matsayin mahaifinshi tun bayan rasuwar mahaifin nashi.
Kuma Shima Baffan yayi musu riko na amana, don haka akwai kauna da girmamawa a tsakani.
Har ta shirya sai ta tuna yan makaranta za su dawo kafin ta dawo. Nan da nan ta yago takarda ta rubuta
musu note ta jiye a kan taga. Ta ajiye musu mukulli a wajen da ta saba, ta fito tacewa maigadi ta fita.
Tana isa gidan ta yi sa’a Baffan yana masallaci, tunda dama shine mai limanci da yake yana da ilimin addini
sosai.
Nan da nan aka tura yara suka kirawo shi. Ya sameta suna hira da matarsa Baba Yalwa.
Bayan sun gaisa tayi masa bayanin duk abinda ya kawo ta.
“Toh diyata (haka yake kiranta da ita duk matan yayansu) tunda gidan zai ishe ku mai zai hana ki basu
gurinsu.”
Ya fada mata yana murmushi.
Yanda ta kwaso zance ta tsara shi bata zata Baffa zai ki goya mata baya ba. Duk da haka ta muskuta kadan
ta amsa:
“Baffa da yake yaranmu dukansu maza ne, manyan cikinsu kuma duk sun balaga. Yarinyar da ake magana
ma fa Baba Karami shekara 3 ya bata. Sai naga kamar yawan cudanya da kuma saka mata daki kusa da
nasu zai iya haifar mana da fitna. Ga shaidan ba zai barmu ba. Sai na ga kamar idan ya ware mata wajenta
ko tsakanina da ita ma fitna zata yi mana sauki, shima kuma ya fi jin dadin sakewa da kowacce, tunda dai
Allah ya hore masa. Boys quarters din kuma da nake magana dakuna uku ne manya zai iya mayar da su
duk yanda yake so. Tunda su Alhajiji suka gama jami’a suka tafi babu kowa a ciki.”
Ya yunkura zai katseta kuma sai tayi sauri ta ci gaba.
“Da yaran na ce su koma boys quarters din toh amma shi da kanshi ya ce ya fi sonsu a cikin gida saboda
tarbiyya. Yana so kowa ya shigo cikin gidan karfe 10:00na dare na rufe kofa, kuma yana so a dinga ganin
inda suke kwana saboda yanda yanzu yara ke yawan shaye shaye da kawo abokan banza ba tare da iyayen
sun sani ba. Shi yasa aka barsu a cikin gida.”
Ta yi shiru yayinda shi ma ya dan yi jim na lokaci kadan.
“Lallai diyata zantukan ki na kan hanya. Ka hada yaro da yaro kuma mace da namiji a wannan zamanin
lallai akwai matsala. Kuma hakan ma da kuka yi kuka killace yaranku yayi daidai. Shi yasa gasu nan kullum
abun sha’awa. Lalacewar zamanin nan kuwa ta kai inda ta kai gashi nan muna fama. Tunda za a ce yaro ya
gama lalacewa da shaye-shaye amma ki ji uban da ya haifeshi ya ce bai sani ba, kuma uwar ma haka. Lallai
kun yi dabara. Kuma zai zo ya same ni. Tunda a addinin ma babu inda Allah ya ce sai ka hada mata guri
daya, musamman ma kuma da yake Allah ya hore maka daidai gwargwado. Zai zo ya sameni.”
Mai dakinsa Baba Yalwa da take zaune tana sauraranso sai yanzu ta saka musu baki:
“Gaskiya ne Malam. Ke kuma mommy abinda za kiyi shine don Allah ki yi hakuri kinji. Ba a taba yi min
kishiya ba amman na san da ciwo. To kiyi hakuri, ki zauna lafiya ki ja girmanki. Shi kuma ki kau da kanki
daga duk wasu abubuwa da zai yi miki, dama aure na mai hakuri ne. Ki zauna da yarinyar mutane tsakani
da Allah kin ji ko. Ni ina kyautata miki zato saboda kina daya daga cikin matan ya’yan da muka aurar ko
aka auro mana da bamu taba jin kanki da mijinki ba.”
Baffa ya ce:
“Wannan haka yake. Ki ci gaba da hakurin da dama kin saba. Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya
da zuri’a ta gari baki daya.”
“Amin, na gode.”
“Sai kiyi Maza ki koma rana ta yi. In sha Allah baza ku samu wata matsala ba kuma aurenku daga nan har
Aljannah.”
Ta samu natsuwa har cikin zuciyarta.
Ta yi Masa godiya tare da Baba Yalwa ta tashi ta koma gida.
Tana fita ya dau wayarshi sai da ya saka gilashi ya dauki dogon lokaci yana lalube a wayar sannan ya samo
lambar Usmanun.
Yana kira kuwa ta shiga.
Ko da yaga kiran Baffan nashi Bai kawo ba domin idan ya kwana biyu bai je ya gaida shi ba ya kan kira shi
su gaisa, don haka nan da nan ya daga waya.
“Wa alaikum salam.”
Ya amsa sallamar Baffan nashi cikin murmushi da jin dadi.
Bayan sun gama gaisawa Baffan ya ce:
“Kwana biyu na ji ka shiru. Ina fatan jikin da garin da kasuwar duka lafiya.”
“lafiya kalau Baffa, hidima ce kawai tayi yawa.”
Ya fada yana sosa Kai alamar jin kunya kamar Baffan yana ganinsa.
“Toh ma Sha Allah. Yau idan ka tashi daga kasuwar Ina son ganinka.”
Baffan ya fada.
“Toh in Sha Allah kuwa Baffa da wurin zan tashi ma don na iso da wuri mu samu mu danyi hira.”
“Yauwa Alhajin Allah (haka Baffan yake kiranshi idan ya so raha). Allah ya kawo ka lafiya. Allah ya bada
tarin kasuwa mai albarka.”
Suka yi sallama kowa ya ajiye waya.
____
Kamar yanda yayi alkawarin da wurin kuwa ya tashi daga kasuwar kafin ayi kiran magariba. Domin yana ji
da Baffan nan nashi wanda yan’ biyu suke da Hussain mahaifinshi (wanda aka sawa baba karami sunansa).
Tunda mahaifinshi yayi mutuwar funji’an shi da yan’uwanshi suka dauki duk wata kauna da suke masa
suka dorawa Baffa Hassan, duk da kuwa ba shi kadai ne dan’uwan mahaifinsu ba kuma shi ma yana da
nashi tarin yayan. Shima kuma ya rike su kamar shi ya haifesu da shi da mai dakinsa.
Sai da ya sayi kayan shayi masu tsada da kuma kayan marmari; ayaba, lemon da kankana masu kyau. Ya
hada da yalon da ya siya a kasuwa musamman (saboda Baffa yana son yalo sosai) sannan ya kama hanya.
Yana isa ana kiran sallar magariba don haka bayan sun gaisa da Baba Yalwa ya yi alwala ya bi Mallam
masallaci.
Da aka idar da sallah bayan Mallam ya gaisa da mutane, shi kuma Usmanu ya gaishe da mutane sanan
Baffa ya kamo hannunshi suka fito suna tafiya suna hira suna yan darerakunsu na da da uba a hanya, da
yake haka Baffan yake da duka yayanshi da na dangi.
Suna shigowa Baba Yalwa ta riga ta shinfida musu tabarma ta dora carpet a kai. Bayan sun zauna ta kawo
ruwa ta ajiya, sannan ta koma gefe kusa da kofar falo ta zauna. Da yake da wutar NEPA Kuma ga hasken
farin wata wajen babu wani duhu.
“Diyata ta zo dazu.”
Nan da nan fara’ar dake fuskarsa ta kauce.
Baffan ya kalli idonsa shi ma ya bata rai sannan ya ce:
“Au ni ba ubanta bane da baza ta zo wajena ba? Ka fi son ta tafi gidan su ko?”
Nan da nan kuma ya fara yake yana shafa kai.
“A’ah, wallahi Baffa ba haka bane.”
Baffan ya ci gaba:
“Toh na ji duk bayananta. Yanzu idan banda kai wa yake cewa mace zai koreta, ai ai ta rainaka, tunda dai
iya fadan naka kenan.”
“Toh Baffa ni da gidana Amma kirikiri matar nan ta rufe mini daki wai bazan saka amarya a ciki ba fa.”
Ya fada bayan ya dan muskuta.
“Toh ai hakuri za kayi. Tunda ka dauko aure ai dama ka taro rigima, a hankali za ka bi. Kuma ina baka
umarni lallai ka gyara wannan boys quarters din inda su Alhajiji suka zauna ka saka amaryar ka, in ka so
ma ka dora bene kuyi yanda kuka so kai da ita.”
Yayi gyaran murya zai yi mita Baffan ya daga masa hannu ya cigaba:
“Ba wai saboda matarka nace ka raba waje ba, saboda yaranka. Ka ga dan yau duk wani motsinka yana
kallo. Sannan kuma kazo ka sa wa matarka daki kusa da yaranka maza baligai wadanda ba ita ta haifesu
ba lallai za a sami fitna, tunda dai duk wani motsi naka da nata suna kallo. Sannan kuma al’amarin kishi,
yaran nan suna kallo za a batawa mahaifiyarsu rai, Koda kuwa itace da tsokana su babu ruwansu; babu
dan da za ka juri batawa uwarsa rai ka zauna lafiya da shi. Za su Raina ka idan aka samu haka, kuma su
Raina matar da ka auro. Amma idan ka ware wa matarka waje ina ga abubuwa da dama na fitna da tsokana
ta mata za a kauce musu.”
“shikenan Baffa. In Sha Allah za a raba.”
“Yauwa Alhajin Allah. Tunda za ka kara iyali sai ka dinga tunani sosai ka hada da siyasa. In ba haka ba ka
ga ka gina iyalanka tsahon shekaru 24 kuna rayuwarku cikin nutsuwa da kwanciyar hankali toh idan ba
kayi da gaske ba matan nan biyu za su sa kayi watsi da wannan ni’imar da Allah yayi maka. Su saka ka ka
rushe ginin kuma ya rikito muku a ka gaba dayanku.”
“Hakane Baffa.”
Ya fada yana jijjiga kai.
“In kun gama kuma ya matso in rankwashe shi tunda ‘yata zai yiwa kishiya kuma yake fada a gabana.”
Baba Yalwa ta Sako musu baki a daidai nan.
Suka tuntsire da dariya gaba daya:
“Ka ji ta ko. Ai mata duka bakinsu daya, sai dai mu ce mu maza Allah ya bamu hakuri.” Inji Baffa.
“Allah dai ya bamu hakuri Mallam, tunda dai mu za a daka kuma a hana mu kuka.”
Ta basu amsa.
Sukayi ta yi mata dariya.
Nan dai suka yi hirarrakinsu, har aka Kira sallar isha’i. Shi da Baffa suka tafi masallaci. Suna dawowa suka
tarar Baba Yalwa ta ajiye musu tuwa miyar Kuka da ruwan sanyi ga kuma filas din shayi na Mallam a gefe
da kofuna.
Nan ya zauna ya ci tuwo ya koshi domin yau bazai ci abincin Rabi ba saboda rigima bata kare ba, domin ya
kudiri niyyar tunda aka saka shi ya rushe shirinsa toh sai ranta ya baci. Yana tunanin ma sai an kara ko da
wata daya ne kafin bikin don kuwa gyaran boys quarters din nan zai dau lokaci.
Haka dai ya gama cin abincinsa yayi musu sallama ya nufo gidan.
_____
Duka yaran a bakin gate suka taro shi suka rako shi. Yana shigowa gidan tana zaune a falon da remote na
TV a hannunta.
“Sannu da zuwa.”
Ta fada kamar yanda ta saba.Ita dai ba ta fahimci ya amsa ko bai amsa ba, amma dai ta san bai kalli inda
take ba. Ya huce dakinshi, Khalifa ya bi bayanshi da jakarshi da babbar rigar shi. Sauran yaran Kuma suka
yi zamansu a nan.
Tun wajen 8:45 ya shiga dakin, amma har 9:30 Bai fito cin abinci ba. Har yaran suka tashi suka koma
dakinsu suka barta ita kadai. A al’ada da ya canza kaya yake fitowa ya ci abinci ya zauna nan wajensu ita
da yara su dan yi hira kafin kowa ya tafi ya kwanta. Duk da dai ta san kwanan zancen amma sai da gabanta
ya fadi, saboda komai fadan da suka yi bai taba kin cin abincin ta ba. Ta tashi ta bi shi dakin. Yana kwance
yana ta faman danne danne a wayarshi. Ta shiga da sallamarta wadda a yanzu kam ta tabbatar bai amsa
ba.
“Baka fito ka ci abincin ka ba, lafiya dai ko.”
Ta fada a sanyaye.
Ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa:
“Ba zan ci ba.”
“Uhm! Allah ya sa dai lafiya.” Ta sake tambaya.
“Lafiya kalau. Sai da safe.” Ya bata amsa tare da juya mata baya alamar shi bacci zai yi.
Ta dan tsaya kamar baza ta fita ba tana bin bayanshi da kallo, sai kuma ta bi bango ta fice tare da rufo
masa kofa.
Tana fitowa daga dakin kwallar da take tarewa ta fito daga idonta. Ta san tabbas za ayi rigima tunda bata
taba kai kararsa ba, amma bata taba tunanin zai ki cin abinci ba domin ko fada suka yi sai ya ci abincin da
ta girka yake kwanciya, sai dai ya ki kulata na dan lokaci.
Haka ta kwana zuciyarta babu dadi baccinma dai bata san tayi shi ko bata yi shi ba. Duk da haka tana tashi
ta fada kichin ta shirya abincin safe.Amma ko da ya fito bai kalli inda take ba ita da abincin. Yara suka fito
yan makaranta suka shiga mota, ya bawa manyan kudin makaranta ya fice.
Ita kuwa daman tunda tace masa ina kwana bai amsa ba abincin ma bata iya yi masa tayi ba, amma dai ta
jera a dining table kuma ta san ya gani, domin har wanda yake fita da shi na rana ta zuba kuma ya gani.
Da Baba Karami ya zo zai dauka ma ce masa yayi:
“Kai barshi ba zan tafi da abincin nan ba yau.”
Nan aka barta da kayanta.
Yana fita babu jimawa ma’aikata suka zo. Ko bi ta kanta basuyi ba suka kama aiki, sai da taji hayaniya ta
kira maigadi ta tambaye shi me ke faruwa. A haka suka kwashe sati biyu, bata fasa komai nata ba amma
shi kam ko kallo bata ishe shi ba. Har dai yara suka gane.
Baba Karami dayake shine babansu Kuma yana matukar damuwa da fushinta shi ya sa ta a gaba da
tambayoyi:
“Mommy Daddy fushi yake yi miki ko?”
Ta kalle shi da mamaki, toh amma ta san ya kai ya san me ake ciki don shekarunsa 23 Kuma bashi da yawo
sosai balle ace bai gani ba.
“Eh Baba, amma laifi nayi masa kuma in Sha Allahu zai hakura.”
Bai gamsu da amsar tata ba don haka ya sake jefo mata wata tambayar.
“Mommy don zai auri wannan kwailar ne ko.?”
Mamaki ya cika ta kwarai da gaske don da yana kusa da ita sai ta rankwasheshi don takaicin maganarsa.
“Kai Baba ka iya bakinka fa! Matar uban naka ce kwailar? Haka za ta zo kana Babba ka dinga janyo min
magana ko. Toh ka fita wannan zancen, ka ji na gaya maka.”
Ta fada tana nuna shi da yatsa.
Ya sunkiyar da kai ba tare da cewa komai ba.
Da yaga dai bata bashi fuska ayi zancen ba ya mike zai fita ya ce:
“Mommy bari na je nayi karatu ina da test gobe.”
Ta ce: “Allah ya bada sa’a.”
Ya fice.
Yana matukar jin haushin babansa tunda ya fahimci halin da suke ciki, amma kuma ita bata basu damar
su raina ubansu ba sannan kuma shi ma uban nasu bai bada wata kofa ta a raina shin ba. Don haka sai dai
kawai yayi ta fushinsa idan sun shiga daki su hadu da kannenshi suyi ta mita.
Bayan wajen sati biyu ana gaba kuma wata ran da ya dawo daga kasuwa da daddare ya sameta a falo ita
da Khalifa yana homework. Ta yi Masa sannu da zuwa ta ji amsa, nan mamaki ya cika ta. Ya huce dakinshi
ya turo kofa. Tana na zaune kuma sai ta jiyo shi yana kiranta. Ta yi tunanin kunnenta ke gaya mata karya
don haka bata amsa ba, sai da Khalifa ya ce:
“Mommy Abba fa kiranki ya ke yi.”
A sanyaye ta shiga dakin ta tsaya daga bakin kofa ta ce gani:
Ya ce: “Yunwa nake ji, me kika dafa ne.”
Ta ce: “Ban ma yi abincin Daren ba don na zata ba za ka ci ba, ragowar na rana muka ci ni da yaran.”
Ya ce: “Toh yanzu ya za kiyi da ni don cikina har kugi yake yi.”
“Bari dai na shiga kichin din na gani ko indomie sai a dafa maka.”
Nan da nan ta shiga kichin kuwa. Tana ta tunanin murna za ta yi ko mamaki, don har ta fara sabawa da
shariyar da yake mata.
Nan da nan ta dafa indomie, ta dora masa daffen kwai a kai. Ta hada masa shayi mai kayan kamshi.
Yana ci yana Dan Jan ta da hira tana bashi amsa a takaice saboda tana tsoron kada ta je ta fadi wata
magana ta bata masa rai a koma gidan jiya.
Da ya gama ta kwashe kayan ta gama abun da zata yi a kitchen ta fito yana kallon labarai shi kadai a falon.
Ta yi masa Sai da safe da niyyar tashige daki ta kwanta.
“Idan kin shirya ina jiranki.”
Ta kalle shi da mamaki ta ga ya wani dauke kai.
Daga wannan lokacin suka shirya.
Kafin sati uku an gama aiki, an chanzawa boys quarters kama. An yi gini harda bene.
A sati na hudu Kuma aka daura aure.
Kayan fadar kishiya sai da yayi mata sutura masu tsada kala 12, leshi 4, atamfa 4, material 2 da shadda 2.
Ya tambayeta ko zata yi taro ta ce baza tayi ba, don haka ya cika mata store da kayan abinci, ruwan roba
da uma lemo yace saboda ko yanuwa za su zo.
Sannan Kuma ya kawo kudi naira dubu hamsin ya bata ya ce mata nata ne kyauta ya bata.
Duk da ta ji dadin kyautar musamman ta kudin amma zuciyarta a jagule take saboda kishi, don ma dai
kullum cikin addua take da kuma sallar dare. Babu yanda bai yi da ita ba akan ta shirya su je dinner wadda
ya shirya wa amarya ta ce baza ta ba.
“Ka fahimci wani abu Abban Baba, baza ni dinner din nan ba. Yau ranar ta ce ita kadai, don Allah ka je ka
tattara nutsuwarka a kanta, ka barta ta more ranar aurenta.” Ta fada masa.
“Toh ai shikenan tunda kin ki. Ni din ma ba dadewa zan yi ba, don dai ta matsa ne zan je, abu ne na yara.”
Ya fada tare da yi mata sallama ya dauki babbar rigar shi wadda ba ya son ya ware mata guga sai ya je ya
fice.
“Allah dai ya sittiri bukwui inji kishiyar mai doro.”
Ta fada a fili tana yatsina fuska bayan ya fice.
Nan dai suka zauna ita da kanwarta da kuma goggonsu wadanda suka zo don taya ta karbar amarya, tunda
ta hana yanuwa su zo mata da yawa.
Haka dai har aka gama biki lafiya aka zo aka yi kafi aka kawo amarya.
Zaman su babu yabo babu fallasa. Ita dai sau daya ma ta taba shiga wajen amarya, shi ma sai da yayi da
gaske da ita.
Suka je suka zauna yayi musu nashiha ya raba musu kwana.
Da fari duk safiya sai amarya ta leko ta gaishe ta amma da aka kwana biyu ta ga ita babu wanda ake aikawa
ya gaishe ta daina zuwa. Ita
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good