Showing 132001 words to 135000 words out of 196754 words
Chapter 45 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
ya kalli Baraka ta tuntsire da
dariya
“A’ah kanina ka karaso?”
Ya dubi Yaya Shafa yace
“Yaya kin san Allah da ba don auren Baban Ummin da yake kan matar nan ba da sai an yi min faskaren
bishiya na zaneta da shi ko kuma na zane su zance ne.”
Suka saka dariya, ya karaso ya zauna kusa da Yaya Shafa. Ta dube shi tace
“Wai sun gaya maka zuwansu.”
“Ai jiya da yamma sukayi min waya suka gaya min.”
Mamakin Yaya Shafa ya kara yawa ta kallesu sannan ta kalleshi tace
“Kai din ma dama da saninka ai bakin ku daya, ka damu mutane da zarya daga Kaduna zuwa Kano.”
Ya bita da kallon mamaki da bakinsa a bude, kafin yayi magana Rabi da Baraka suka tuntsire da dariya ya
hararesu ya dubi Yaya Shafa yace
“Wallahi Yaya ban sani ba sai jiya da suka kira ni, in banda haka ai da ba zan dinga zuwa haka ba.”
Ta kalle shi ta tabe baki tace
“Allah dai ya shirye ku gaba daya.”
Kafin suce wani abu wayarta tayi kara ta dauka Mubarak ya cigaba da hararar su Rabu suna masa dariya.
Bayan ta amsa wayar Yaya Munzali yace mata gashi ya zo ita da Baraka su fito da Mubarak din don ya ga
motarsa. Tace ai ya shigo kawai, don haka ya ajiye wayar ya rufe motar ya shigo ciki. Kafin ya karasa
sallamar da ya fara ya hango fuskar Rabi, a hankali ya karasa ya zauna yana binsu da kallo daya bayan
daya. Ya dubi Yaya Shafa yace
“Shafa, a ina kuka samo ta?”
“Hmm! Ka san duk wannan tashin hankalin tana gidan Baraka hankalinsu kwance sun hanamu bacci.”
Da mamaki ya dubi Baraka yace
“Baraka! Wannan wane irin rashin hankali ne kuka aikata haka? Ku biyu a rasa wanda zai sa wani a
hanya?”
Mubarak yace
“Nima haka nace.”
Yaya Shafa ta harareshi sannan ta dubi Munzali tana nuna Mubarak din tace
“Shima har da shi duk bakin su daya.”
Ya gyara zama ya dubi Mubarak din sannan yace
“Ah, yanzu kai sai ka biyewa mata? Gaba daya kun sa mu a tashin hankali.”
Ya juya ya dubi Rabi
“Kin bar yaranki a tashin hankali, babu inda bamu cigita ba nemanki.”
Mubarak yace
“Wallahi Yaya ban sani ba fa nima jiya suka sanar dani toh da naga za mu hadu a nan shine ya sa ban
gaya maka ba.”
Ya harareshi yace
“Za ka aikata, ai da kai da su kayuwanku duk iri daya ne.”
Ya sake duban Rabi yace
“Yanzu ke da aurenki fa kika tafi har Jigawa ba tare da izinin mijinki ba, gaba daya kika daga mana
hankali kwana kusan arba’in. Ko sakinki yayi ai wajena ya kamata ki zo balle da igiyar aurensa a kanki fa.
Sai kawai kika wuce wajen kannenki suka boye ki kuka bar mu a tashin hankali.”
Mubarak yace
“Yaya wallahi babu ni fa.”
Ya juyo yana nuna shi da yatsa yace
“Ka san Allah Mubarak zan iya make ka idan baka yi min shiru ba.”
Ya gyara zama ya bata rai shi kuma ya mayar da dubanshi ga Rabi da Baraka wadanda suke zaune a kan
kafet sun sunkuyar da kai yace
“Toh yanzu me kika dawo yi?”
Ta bata rai tace
“Na ji rasuwar Baffa ne na zo na yi musu gaisuwa.”
Ya dubi Shafa yace
“Kin ji wai amsa take bani.”
Ya mayar da dubansa ga Rabin yace
“Toh wace gaisuwar Baffa za ki je mutumin da kika sa ya dinga kuka da hawaye saboda an ce kin bata, ya
sa Usman din a gaba da fada da koken dole sai an nemo ki.”
Baraka tace
“Yaya don Allah kayi hakuri.”
Ya juya ya dubi Baraka zai yi magana Rabi cikin muryar kuka tace
“Yaya da azumi fa a bakinmu yace na fice masa daga gida, a gaban su Khalifa. Kuma ya tsaya yana jira sai
na fita yanzu yanzu, sai da ya tabbatar na fita sannan ya fita. Ai da yana so na zo gidanka sai ya kawo ni
ko kuma ya yi maka waya yace ka zo ka daukeni. Amma ko girmanka bai gani ba ya kore ni.”
Ya gyara zama yace
“Hm, Allah ya sauwake. Toh yanzu yaran da Usaman din sun san kin zo.”
Baraka tace
“A’a, babu wanda ya sani ai zuwan mu kenan.”
Ya dubi Shafa yace
“Ai kuwa ba zata je gaisuwar nan ba tunda gaba daya yaranta suna wajen, don Baba karami ma jiya da
daddare ya iso kinga kuwa duka suna can. Suna ganinta za su hargitsa wajen ana zaman makoki. Ta
zauna a nan muje muyi gaisuwar mu dawo sai mu saurari abinda Usman din zai zo da shi.”
Baraka tace
“Toh amma kuwa Yaya in dai yana so ta koma sai yayi Biko kuma sai ka ja masa kunne.”
Ya kalli Shafa sannan ya kalli Barakan da mamaki yace
“Baraka wai ke sai yaushe ne bakin ki zai mutu.”
Ta sunkuyar da kai ta barshi da mamaki. Suka dan yi shiru, Yaya Shafa ta janyo faranti ta zubawa Yaya
Munzali ruwa ta mika masa tace
“Bismillah Yaya sha ruwa sai muje muyi gaisuwar nan don ka ga ni sha biyu zan je aiki.”
“Hakane.”
Nan suka sha ruwan da lemon sanna suka taso suka fito suka bar Rabi ita da Zahra a nan, suka shiga
motar Munzali suka kama hanya.
Tunda suka tsayar da motar Ahmad ya hangosu da yake shi da Baba da su Tijjani a rumfar waje suka
zauna. Don haka ya taso don ya tarosu ya raka su wajen su Abban da suke zaune a wata rumfar da take
farfajiyar gidan. Bayan sun fito daga mota auta ya hango Baraka da anti Shafa don haka ya taso shi ma.
Bayan ya gaida su Baba Mubarak ya matsa ya gaida su Anti Shafa ya matsa kusa da Baraka ta sa
hannunta a kafadarsa kamar wasu kawaye sannan tayi masa gaisuwa, bayan ya amsa ta rada mishi a
kunnenshi
“Idan ka ga mun fito za mu tafi ka zo in gaya maka wata magana.”
Yace
“Toh.”
Ahmad ya raka su Yaya Munzali har wajen su Abba shi kuma Auta ya shige da su Yaya Shafa wajen Baba
Yalwa. Nan suka yi mata gaisuwa suka yiwa su Amina ‘yayanta gaisuwa suka nemi waje suka zauna. Suna
kallon Sauda tana kallonsu ta ki kulasu, sai wani kawar da kai take yi tana muzurai. Yaya Shafa da ta kula
da haka ta matsa kusa da ita tayi mata gaisuwa, ta amsa a dakile. Sai da suka dauki kusan awa daya a
gidan makokin sannan suka taso za su tafi, suka tsuguna gaban Baba Yalwa suna sake yi mata gaisuwa da
sallama, Baraka ta dauko kudi a jakarta ta ajiye mata; Rabi ce ta bata naira dubu biyu a cikin ragowar
kudinta tace ta bawa Baban sadaka, ita kuma ta kara dubu takwas a kai ya zama goma suna mota da ta
fito da kudin tana kirgawa kuma Yaya Shafa ma da ta ji ta kara dubu biyar don haka dubu goma sha biyar
ta ajiye mata. Suka fito suka sake yiwa su Abba sallama yayinda su Mubarak ma suka taso Ahmad da
Baba suna yi musu rakiya suka nufi mota. Har sun kusa shiga mota Auta ya sheko da gudu ya tsaya a
kusa da Baraka yace
“Anti baki gaya min ba.”
“Kawo kunneka.”
Ya matso ta kama kunnensa tace
“Mommyka tana gidan Yaya Shafa.”
Ya fizge kunnenshi ya dubeta zai yi magana ta sa hannu ta toshe masa baki alamar yayi shiru. Ya kasa yin
shirun yace
“Allah Anti?”
“Allah.”
Suka karasa shiga motar Yaya Munzali ya ja suka tafi. Da sauri ya karaso ya fada jikin Baba suka bishi da
kallon mamaki yace
“Yaya Baba Anti Baraka ta ce min an ga Mommy tana gidan Yaya Shafa.”
Duka sukayi dif sai kuma Ahmad yace
“Kai wannan wane irin wasa ne?”
“Wallahi Ya Ahmad da gaske ne.”
Ji suka yi kamar su kurma ihu yayinda Auta yake ta kyalkyala dariya.
Baba ne ya kama hannunshi yace
“Kai mutuwa fa aka yi kake dariya.”
Sai ya dan sha kunu amma ya kasa nutsuwa, ya juya zai ruga da gudu Ahmad ya rike shi
“Wai ina za ka?”
“Ya Madu zan gayawa ya zo mu je mu gani.”
Baba yayi sauri yace
“Kai, rabu da shi yana kusa da su Abba, ka tsaya a nan zan turo maka Salim ku tafi da mota ta idan kun
sameta ku yo min waya.”
Ahmad yace
“Turo Salim din ni ma ai da ni za a je.”
“Kai kada fa a ga muna ficewa ana zaman makoki.”
“Ai sai dai ayi mana uzuri.”
“Toh ni bari na koma ma yi waya, in ya so sai mu taho da Madu.”
Yana shiga ya turo Salim, bai gaya masa komai ba kawai ce masa yayi ya zo waje Ahmad yana nemansa.
Yana tashi Khalifa ma ya biyo bayanshi don haka gaba dayansu da Ahmad, Salim, khalifa da Auta suka
tafi. Duk gudun da Ahmad yake yi gani suke kamar baya sauri, sun yi tsit babu mai magana don gani suke
kamar in suna surutu za su hana motar sauri.
Su Baraka suna isa kofar gidan Yaya Munzali ya saukesu ya wuce don tun suna hanya ake masa waya
yana da baki a gidan gona, ya tafi da tunanin ai Rabi ta dawo nan gidan Shafa za ta zauna su ji me Usman
zai zo dashi. Shima Mubarak ko shiga bai yi ba yayi musu sallama ya kama hanyar Kaduna. Suna shiga
cikin gidan Yaya Shafa ta saka kayanta na nurse ta ce musu za ta je asibiti sai biyun rana za ta dawo don
dama 8 to 2 take da aiki samu tayi aka rike mata gashi yanzu har daya tayi za ta je ta gani yanzu za ta
dawo. Nan ta fice ta bar Mommy da Baraka a falonta suna ta hirarrakinsu da yaranta kananan; Fathiyya
mai shekara goma sha takwas da kanwarta Amira da suka dawo daga tahfiz bayan fitarsu.
Suna nan zaune auta ya shigo da gudu yana sallama, Mommy tana zaune a kan kafet sai da ya zo
gabanta kamar zai fada kanta sannan ya tsuguna suna hada ido hawaye ya fara bin fuskarsa, ya sa
tafukan hannunsa zai goge ta bude masa hannayenta ya fada jikinta yasa kuka harda shessheka. Khalifa
da Salim ne suka shigo kowa yana kokarin ya fara shiga suma nan suka zube a gabanta. Ta share kwallar
dake idonta ta saki auta. Khalifa ya kura mata ido ta sa hannu ta lakace masa hanci yayi dariya yace
“Mommy muna ta nemanki.”
Itama murmushi take tace
“Ba gani ba.”
Baraka ce ta yiwa Zahra da su Fathiyya alama suka tashi suka shige dakin su Fathiyyan suka barsu su
kadai. Ahmad ya zagaya gefenta ta mika hannu ta kama hannunsa tace
“Ahmadu.”
Ya dubeta yana murmushi yace
“Mommy duk mun zata fa sace ki aka yi.”
Tace
“Ina gidan Baraka.”
Salim yace
“Amma wayarki kullum a kashe.”
Kafin ta bashi amsa yace
“Kuma Anti Barakan tace mana itama bata san inda kike ba.”
Tace
“Ku tsaya Mana na amsa muku tambayoyin da daidai da daidai “
Suka yi dariya gaba daya Salima yace
“Toh mun tsaya Mommy.”
“Gidan Baraka na tafi, nice na ce mata kada ta fadawa kowa ina can don ko su Yaya Shafa ma sai yau
suka san ina can da muka zo.”
Auta yace
“Amma tazo harda kawo min chocolate tana taya mu kuka.”
Tace
“Yanda kuke yi min kai da Khalifa kuyi laifi ku hada baki kuce ba haka bane nima haka muka yi muku da
kanwata.”
Suka sa dariya gaba daya. Ahmad yace
“Amma kuwa mun sha wahala Mommy.”
Tayi dariya tace
“Allah ya sa kaffara ne.”
Suka sake tuntsirewa da dariya tace
“Ina Babana da Muhammadu.”
Ahmad yace
“Au, ai kuwa bari na kirawo su.”
Nan da nan ya kirawo Madu, yana dagawa yace
“Fita daga cikin mutane muyi magana.”
Sai da ya fito ya dan yi nisa da rumfar sanna yace
“Na fito.”
“Mommy ta dawo ga mu da ita a gidan Anti Shafa.”
Saura kadan ya sa ihu ya daure tace
“Mugaye shine kuka sulale baku gaya min ba.”
Ya katse wayar ba tare da ya ji me za su ce ba. Yana juyowa zai dawo ya ga Baba karami ya biyo shi. Suna
hada ido suka tuntsire da dariyar jin dadi yace
“Au sun gaya maka kenan.”
Ya fara laluben mukullin mota a aljihunsa yana fadin
“Mu tafi mu gani.”
Baba yace
“Gara dai mu gayawa Abba.”
“Kayi masa waya kawai kace masa ni na tafi don in ya san ina nan zai iya tsayar da ni yanzu mutanenshi
za su zo daga kasuwa.”
Don haka Baba karami ne ya kirawo Abban bayan ya dauka yace
“Ya aka yi Baba, ina kuke ne kai da kannenka?”
“Abba anga Mommy fa tana gidan Anti Shafa su Ahmad suna can nima yanzu zan wuce.”
Sai da zuciyarshi ta tsallake bugu daya, ya dubi mutanen da ke gefenshi sannan ya tuna a inda yake ya
dan yi gyaran murya yace
“Ma sha Allah, toh kuje ni ma in sha Allahu in muka sallami baki zan taho. Alhamdulillah.
Suka ajiye waya, ya dubi Aliko wanda yake kusa da shi yana sauraron ya ji hamdalar da yake yi yace
“Mommyn su Baba ce, tana gidan yayarta Shafa da suka zo dazu.”
Ya dubeshi da murna yace
“Yace Alhamdulillah, dama Baffa yace za a ganta babu rabon su gana.”
Suka matse kwalla suna murmushi, Alikon ya dubi Abba yace
“Ba za ka je yanzu ba.”
“Mutanen mu za su zo Mana gaisuwa daga kasuwa gashi ana ta zuwa ma, zuwa la’asar idan aka ragu sai
na je tunda dai yanzu tana gidan Shafan.”
Nan ya zauna suka ci gaba da karban baki, ko ma ina ta buya ya san tunda yanzu ta zo toh nan gidan
Shafan za ta zauna. Yanda yaran suke murna Ku
Kuma ya nuna masa cewa lafiya take, duk da bai san inda aka ganta ba amma ‘yan uwan nata yake zargi
da boyeta. Koma dai menene yau in sha Allahu gidansa Rabi za ta kwana.
………….
Tana nan zaune Baba karami da Madu suka shigo, suma nan gabanta suka zube. Baba karami ne ya fara
magana
“Mommy ina wuni.”
“Lafiya kalau, ya hakurin mu.”
Bayan ya amsa gaisuwar ta dubi Madu tace
“Kai kuma fa da kake ta muzurai haka.”
Dariya yayi yace
“Mommy Anti Baraka ce ta boyeki ko?”
Baba karami yace
“Ko gaisuwa sai tamabaya”
Mommy tayi dariya tace
“Ita ce akwai magana ne?”
“A’a wallahi Mommy tayi min daidai godiya ma nake so na sake yi mata.”
Ta jijjiga kai tace
“Allah ya shiryeka kai dai.”
Nan suka zauna sukayi ta hirarrakinsu, jimawa kadan su Baraka suka fito aka yi ta hayaniya ana raha. Aka
zubo abincin rana duk suka ci suka yi sallar azuhar. Haka har Yaya Shafa tazo ta same su aka ci gaba da
hira. Sai da aka yi kiran sallar la’asar mommy tace ya kamata su koma gidan makokin ko don su yiwa
Baba Aliko kara, nan da nan suka fara shirin tafiya. Auta ya dubeta yace
“Mommy ba za mu tafi gida ba?”
Tayi dariya tace
“Toh ai mai gidan cewa yayi na fita bai zo ya ce na koma ba.”
Ya sunkuyar da kai murya kasa-kasa yace
“Hakane.”
Tace
“Kada ku damu ai yanzu kun san inda nake, bari na baku lambata ma yi waya in an jima.”
Zahra tana daki wajen su Fathiyya don haka Mommy ta kwala mata kira, ta fito tace
“Inna gani.”
“Ki kawo min wayata na basu lamabar ko ki gaya musu.”
Madu yace
“Mommy wai ke ce Innan.”
Tayi dariya tace
“Toh an gaya maka kowa bature ne irinka.”
Zahra ta karaso kusa da ita ta zauna ta kwantar da kanta a kafadar Mommy tace
“Gaya masa dai Inna mu fulani ne.”
Kafin Mommy tace wani abu ya bushe da dariya yace
“Shi yasa hausar ma kuke yi da fulantanci.”
Suka bushe da dariya gaba daya, ita kuma ta kara shan kunu. A nan Fathiyya ta zo wucewa ta dube su
tace
“In dai Yaya Madu ne kika biye masa yanzu zai manna miki hauka ki barshi kawai malejinsa muke yi.”
Suka sake bushewa da dariya Baba karami ya mika mata wayarshi yana fadin
“Rabu dashi kin ji sa min lambar a nan.”
Ta karbi wayar ta saka masa lamabar ta mika masa tace
“Inna za ka sa mata ba Mommy ba.”
Ya karba yana murmushi yace
“An gama ai daga yau ma ta koma Inna.”
Khalifa yace
“Ikon Allah muna zaune an kwace mana uwa har an canza mata suna.”
Mommy ta lakace masa hanci tace
“Kuma an fi ku matsayi ba.” Kafin su amsa ta dubi Baba tace
“Ka ga wannan surutun ba karewa zai yi ba ku tashi ku koma kada su tashi baku isa ba.”
Suka yi musu sallama suka shiga mota suka koma gidan makokin. Suna fita Baraka ta mike tace
“Muma ai sai mu kama hanya kada muyi dare.”
Rabi ta mike ta fara neman mayafinta, Yaya Sahfa ta dubeta tace
“Ban gane ba wai Jigawan za ki koma?”
Ta matsa kusa da ita sannan ta bata amsa
“Can zan koma Yaya.”
Ta kalleta suka hada ido ta sunkuyar da kanta, Shafan tace
“Na zata tunda kin zo shike nan kuma ba sai muyi zaman mu a nan ba.”
“Zan dawo nan din ma Yaya Amma Sai an kara kwana biyu tukunna mu ga abinda hali zai yi.”
Suka sake hada ido tace
“Kar ki damu Yaya, ai kuma yanzu kun san inda nake ga kuma lambar waya ta nan ko da wanne lokaci za
ku iya kira na.”
Bata ce komai ba ta dubi Baraka kamar wadda take neman tabbacin abinda Rabin ta fada, ta kada mata
kai alamar haka ne. Ta matso tace
“Kada ki damu Yaya Shafa, Allah ba za mu sake yin komai ba sai mun yi magana dake.”
Rabi tace
“Kin ga sai ranar bakwai ma zan dawo na yiwa Baba Yalwa gaisuwa.”
“Toh Allah ya kyauta.”
“Toh don Allah ki gaya wa Yaya Munzali.”
Suka yi mata sallama ba don ta so ba suka kama hanya.
Sai wajen karfe shida na yamma lokacin an fara watsewa sannan Abba ya dubi Aliko yace
“Bari na je, in sha Allah kafin magriba zan dawo.”
Ya rike hannun da ya mika mishi suyi musabiha yace
“Babu damuwa ka isar da gaisuwa ta.”
Sai da ya shiga ya sanar da Baba Yalwa ganin Mommy da akayi sannan ya fito ya kama hanya. Su Sa’a da
Saudah ma sai a nan suka ji labarin da yake duk suna gidan. Da yake yaran sun riga sun dawo Salim ya
dauka don ya kaishi. Sai da Salim ya shiga yayi masa iso sannan Yaya Shafan ta bude falon baki tace ya
shigo. Bayan ya zauna aka kawo masa ruwa sannan Yaya Shafa ta zauna suka gaisa, ta sake yi masa
gaisuwa bayan ya amsa ya dubeta yace
“Bata kusa ne Rabin na ji shiru.”
Tambayar da yayi haushi ma ya bata don haka nan ta godewa Allah da suka tafin ma, ta kula kamar har
yanzu bai san yayi laifi ba don magana yake kamar babu abinda ya faru. Tace
“Au, ai sun koma Jigawa ita da Baraka.”
Ya kalleta da mamaki, ya cire hular da take kansa ya ajiye a gefe yace
“Ikon Allah, wai dama can ta tafi wajen Barakar ko labari.”
Tace
“Wallahi kuwa, muma sai yau da suka zo muka san tana can.”
Ya dan yi jim sannan ya dube ta yace
“Toh yanzu sun tafi kenan?”
“I, ai yanzu ma sun kusa isa Jigawa kam.”
Yayi sake yin jim sannan ya mike yana yi mata sallama, har ya kusa fita ya dawo ya zauna yace
“Yaya Shafa.”
Ta
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good